shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday, 8 May 2016

WAYE SANADI? 8-9 & 10

waye-sanadi.jpg

[9:15PM, 5/7/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI?

8


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

ko kalon kayan banyi ba na mike na tafi washe gari ina zaune a soron gidanmu ina cin wake da shinkafa wani yaro bai fi shekara sha uku ba ya leko yana gani na ya hau dariya yana tsokanata.nana a daki maza nana a daki aiko na taso muka zuba gudu Allah ya ban sa'a ina fitowa na rike shi na hau dukansa,yana ihu yana zagina ni kuma ban fasa dukansa ba wani mahaukacin zagi ya lallayo mun kan ya rufe bakinsa na gwara kansa da kofar gidanmu wata gigitacciyar kara ya saki karar da yayi ne yasa kaka da umma lekowa da gudu,salati suka hau yi kaka ta karaso."baki da hankali kina gani kin fasa masa kai amma ba zaki sake shi ba,watau dan haka kika zo soron ci abinci to wallahi bbu ruwana ba zaki sake shi ba tana magana ta kowan duka,mota tayi parking ya fito da sauri haba nana me yasa kike san jawo magana (haka kawai yau yayi min kwarjini) sake musu yaro ban ce kala ba na sake shi nayi cikin gida ban san ya suka yi da yaron ba.umma ta shigo "kizo yana son ganinki.har zan ce ba zani ba sai kuma ba mike na zauna a soro na zo bbu sallama ya ganni kawai a tsaye meye kake kirana? bai damu da yadda na tsaya masa ba yana murmushi yace "rukayya a tace kina son magana dani oh ce maka zanyi tunda kace sai ka aureta to in dai zaka aureta sai dai ka aureta da yarta bbu me rabamu sannan in kana so na amince ka aureta sai ka samomin admission a B.U.K nayi candy kuma takarduna sunyi kyau karka auri babata ka ganmu a karkashinka kayi tunanin zaka juyani ko zaka ban umarni ko kuma kace zakai min fada bbu ruwanka da rayuwata,magana nida kai bata zama dole ba duk abinda na shiryawa kaina baka isa ka hanani ba in har ka amince,to na amince ka aureta.nana zan samo miki admission a B.U.K zan kuma dau nauyin har ki gama karatunki nana kina gani inna rabu dake kina duk abinda kika ga dama Allah ba zai kamani da laifin haka ba a matsayina na mijin mahaifiyarki wanda inda kara zaki iya bani matsayin mahaifinki to in kuma bbu sai ki ban matsayin duk da kika ga dama."baka da matsayin da zan baka ko takalmina ya fika...' karar wayarsa ce ta katse maganar yana gama wayar ya juyo yana kallona yafi ki shiru kinyi shuru ina jinki ci gaba "bazan cigaba ba kuma wallahi bazan yarda a ka aureta ba,sai ka kawon sabuwar waya black berry da kuma nokia original one sim oh daughter kawai rigima nima nayi niyyar zan sai miki wayar nana irin son da nake wa rukayya zan iya yi miki komai in kika kwantar da hankalinki har mota zan sai miki kinga daman mace bata hawa machine fatana nana ki nutsu ki daina sa mahaifiyarki bakin ciki,


Abbagana hausa novels @facebook.
[8:13AM, 5/8/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI?

9


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

Kinga kuma macece zaki aure ki haihu ki so yarki ta dinga yi miki abinda ki kewa ummanki a yanxu ba please my daughter ki tausayawa ummanki kar kisa wata cutar ta kamata ummanki tana masifar sonki karki samata ciwon zuciya inta m........." kaga malam ya isheka meye ruwanka da rayuwata wai kaga mallam zakai min wa'azi ka wani bude baki kamar kofar gar......." marin daya sauka a fuskanta na daga kaina ina mai kuma ya kawo mallam mado "ke dai wallahi kinyi asarar hankalinki shegiya mara kunya kaini wallahi tunda nake a duniya ban taba ganin shedaniyar yarinya irin ki ba,wadda bata dau iyayenta da mutunci ba, kai kuma Alhaji ka zauna yarinya tana zaginka kana lallabata in anzo daurin aurenta ki hana ko ki tsine mata "baba kayi hakuri kasan har yanzu nana yarinya ce komai zai daidaita a hankali dole sai an dinga binta a hankali" wannan shedaniyar yarinyae ce ta san abi ta a hankali,to wallahi in baka ci ubanta ba ba zata saurara maka ba dan...."sai dai aci naka uban,banza munafiki kuma wannan marin kayi na farko kayi na karshe dan wallahi duk ran da hannunka ya kara karanbanin mari na sai na rama banza anga mai kudi ana rawar kafa Allah yasa dan yankan kaine." na juya cikin gida da gudu sun jima suna tattaunawa da malam,sannan ya shigo zayi kiran vaba ina zaune ta shigo nana na dago ido ina kallonta.me ya same ki a fuska? ba ke ki kasa mallam ya mare ni ba ido ta zazzaro haba nana ya za'ayi nasa malam ya dake ki wallahi ban san ya dake ki ba,me kika yi mini da zansa ya dakeki dan Allah nana kiyi hakuri yanzu yace ki kai masa takardun nawa zai tafi dasu kuma dan Allah nanan k dinga sanin maganar da zaki dinga gaya masa kin ga koni ya girman bare ke kar ma dai ta dan in Allah ya yarda sai ta hadu da aljanu.tayi masu rashin kunyar taga in zatayi nasara' na mike ina harararta.ina Allah ya yarda kene zaki hadu da aljannu su shanye miki kafa da hannu'yana tsaye yana dan yin waya na tura masa takardun suka rufe wayar murmushu yayi yana duba ya dago yana kallona nayi mamakin dana ga takardunki haka banyi tunanin ganinsu haka ba,kwarai kin ban mamaki kuma naji dadi Allah yasa ki dore haka am....'" kan ya karasa nayi shigewata.

BAYAN WATA UKU

yau alhaji nasiru yazo ya shaidan gobe zan fara zuwa makaranta dan fara karatuna, to nana gobe zaki fara zuwa makaranta kuma kin san makarantar nan ba irin makarantar da kika saba bace,wannan ta hada maza da mata kuma yare kala-kala dan haka ki tsaya ki nutsu kiyi abinda ya kaiki.


Abbagana hausa novels @ facebook.
[8:15AM, 5/8/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI?

10

MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

ba ruwanki da kowa karatu yana bukatar nutsuwa,nana zanyi farin ciki ace yau kin zama barrister fatana ki maida hankalinki Allah ya taimake ki ki kammala karatunki lafiya" sannan ga alkawarinmu na waya kuma duk wasu kudi da makaranta take bukata na riga na biya na gama komai Allah ya taimaka ya baki sa'a ya mikon wayar "ki turon ummanki" na gode na juya nayi ciki washe gari aka daura auren umma da alhaji nasiru ranar kuwa na fara zuwa makaranta.tun tara na safe na tafi sai biyar na dawo na tarar da gidan cike da mutane,bbu wanda nayi magana na shige dakinmu umma na tarar tana kwalliya" sannu nana yan jami'a ya karatu? karatu gashi mun fara,umma kwalliyar me ki keyi? kaka ce ta shigo tambayar me kike mata?? harara na zabga mata sannan tace. kwalliyar me take? kwalliya za'a kaita gidan mijinta ko zaki hana? ba zan hana ba,amma kin san kafata kafarta ke ma baki isa ki hana ba vaba dan Allah kiyi hakuri karki haka saboda maganar mutane to wannan bankaddaddiyar yarinyar ce take gudun maganar mutane shegiya.
"ni ba shegiya bace kije can ki nemi shegiyarki mutum ko baka saka magana da shi ba sai ya saka dan gulma an girma ba asan an gir........." bugun da ya sauka a bakina ne yasa nayi shiru da ban shirya ba umma tayi saurin shiga tsakaninmu tana bawa vaba hakuri sannan ta vita umma ta juyo wajena,"haba nana ke kullum kin fison ki sani cikin bakin ciki,baba kakarkice amma kin maida ita kamar yar aikin gidanku bakya rangonta mata,kuma maganar ta fiya kin san da bakin ki kukayi magana da shi kice sai nayi sati daya zaki tawo ba sannan kuma yanzu ki zo da wata maganar, kawai umma kice ba kya son nazo gidanki,saboda kin auri mai kudi' haba nana har akwai wani arziki da zan samu wanda ya fiki naba saboda irin son da nake miki yasa vaba take jin haushina,nana ki tausaya mu rabu da vaba cikin farin ciki,kin ga yanzu in nace na amince zan tafi dake yau vaba ranta zai baci kar kiyi fushi dani ni nayi miki alkawarin rana ita yau da kaina zan zo in dauke ki kiyi hakuri"tana magana tana shafa kaina haka yasa zuciyata ta sauko. shi kenan umma Allah ya kaimu kuma kin san babba ba abincin ta take ba ni ba in kuma so kike inyi iskanci na samo to"


Abbagana hausa novels@ facebook.
Share:

8 comments:

  1. Ummu Amaturrahaman8 May 2016 at 02:42

    Babban Magana Dan Sanda Ya Ga Gawar Sojaaa

    ReplyDelete
  2. tnxs yaya abba

    ReplyDelete
  3. fathima ibrahim8 May 2016 at 09:15

    gaskiya nana yar rigimace amma muje zuwa abba

    ReplyDelete
  4. tnx abba, mungode aci gaba mana

    ReplyDelete
  5. inuwa Muhammad11 May 2016 at 07:10

    acigaba dan Allah

    ReplyDelete
  6. Abubakar Ibrahim20 May 2016 at 14:23

    Albasa batayi halin ruwaba

    ReplyDelete
  7. Kaine sirina

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).