shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 27 May 2016

AMINAN***JUNA 201---220

aminan-juna.jpg

[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNAWISDOM HAUSA WRITERS.
Na Xarah~B~B211-215"Dan Allah kiyi hkr ki rage wannan damuwar zarah dube yadda kika koma fa, duk kin saka ummah a cikin damuwa", "hmmmmm! futha kenan dole ne na damu dufa ba kiga tun muna yara muke tare da amrah babu wanda ya taba jin tsakanin mu har muka girma, lokaci daya ta tsane ni akan abinda bansan nayi ba" sai kuma ta fashe da kuka, ahaka dai futha tayi ta rarrashinta har sai da taga tasamu natsuwa, sa'annan ta rinqa yimata fira bai ban dariya har dai ta saki ranta

Alhamdulillah yau abun na zarah da sauki dan kuwa har abinci taci sosai, ummah taji dadi sosai ganin yadda futha take kula da zarah, a cikin hirar ne futha tace " zarah dan Allah ki tashi ki shirya anjima idan ya Affan yazo daukana sai mu dan fita ki nuna mana garin naku", murmushi kawai tayi tace "Allah ya kaimu", aranta kuwa taji dadi sosai saboda itakan ta tasan tayi kewar ya Affan ba kadan ba.

Amrah ce kwance kan gado sai juyi take ta rasa meke mata dadi a duniya gashi tana kiran wayar Farouk amma layin a kashe yake idan takira musty kuma sai yace basa tare duk abun duniya ya isheta kullun sai qara jin tsanar zarah takeyi dan ita aganin ta duk itace silar wannan abun, kullun Mum da Dad suna qoqari gurin ganin sun fahimtar da amrah amma abun yaci tira, suna tausayawa 'yar tasu duk tawani koma wani iri da ita.

Ringing biyu ta daga "hello ya Affan ina wuni?" a dayan bangaren aka ansa da "lfy qlw kun shirya?" " eh, kai kawai muke jira" "ok ganin na kusa qarasowa sai ku fito", " ok sai ka iso" A ranshi kuwa baya ma iya misilta irin farin cikin da yake ciki shidai harga Allah yana jin zarah a ranshi........Urs Zarah~B~B.


216-220A daki suka samu ummah bayan sun gaida ta futha tace "ummah ya Affan yazo zan wuce", "Allah sarki ashe har tafiya kenan, Allah ya saka miki da alkhairi yabar zumnci" ummah ta fada "ameen ummah ai yiwa kaine" sa'annan tace "ummah dan Allah inason zarah ta rakani naga gari", "tou bakomai sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya" duka suka ansa da"amin" sukayi sallama da ummah suka fita

Jingine da motar shi suka same shi yana latsar wayar shi, dago kanshi yayi sukayi ido hudu da zarah wani murmushin jin dadi yasaki wanda ke qara fitar mashi da kyanshi itama mayar mashi tayi, sa'annan ya bude mata gaba tashiga futha ta shiga baya sa'annan suka wuce, a mota sai kallun2 sukeyi, futha kuwa dariya kawai take masu tana farin cikin taga yayan ta cikin farin ciki, a haka har suka isa a "A G G MALL" sayayya mai yawa ya Affan yayiwa zarah tundaga kayan sawa, kayan make up dadai sauran su hakama yayiwa futha saidai na zarah sunfi yawa, daganan suka wuce shan ice cream, ranar sunyi yawo domin kuwa zarah har ta manta da wata damuwa hakan ba qaramin dadi yayiwa ya Affan ba.

A bakin kofar gdn su zarah yayi parking, kallon ta yayi yace plz zarah ki bude wayar ki rashin jin muryar ki ba qaramin illah bace a gareni, ok yaya insha zan bude yauwa qanwata tnx alot, daga nan sukayi sallama ta wuce cikin gd......Urs Zarah~B~B.

WISDOM HAUSA WRITERS.Fatima~Bello~Bala.
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA

WISDOM HAUSA WRITERS


Na Xarah~B~B


201-205

A parlour suka samu ummah zaune ta lula duniyar tunani dan halin da 'yar ta ke ciki abin tausayi ne,, zarah kuwa cikin yan kwanan kin nan duk ta canxa ta rame tayi baqi ba ci ba sha sai aikin kuka da zaman daki.


Sallamar su ce ta dawo da umma daga duniyar data lula, cikin karfin halin ta tashi da yaqe ia fuskar ta wanda yafi kuka ciwo, iya fuska kawai ya tsaya, "sannun ku da zuwa hajia" suka ansa da "yauwa ya muka same ku?" " lfy qlw wlh hajia", anan ta kawo masu ruwa suka sha, shiru ne ya biyo baya, ummah kuwa a zuciyar ta tana tunanin to me yakawo su mumyn Amrah a gdn dan da datagansu tayi tunanin cin mutunci suka zo suyi mata sai taga akasin haka, ammi ce takatse shirun da cewa"ummah nasan bazaki rasa sanin dalilin mu na zuwa nan gdn ba, da farko dai muna son mu tamby ko zarah nan tazo da ta baro katsina? dan bada sanin muba ta zo" jin bayanin ammi yasa ummah ta tabbata cewa itace Ammin da su zarah sukaje gurinta a katsina, ajiyar zuciya tayi kana tace "eh ammi nan tazo kuma ta fadaman duk abinda ya faru har dalilin ta na dawo wa batare da sanin ku ba" Alhamdulillah ammi ta fada kana tace ina zarar take ne? tana ciki inji ummah, anan dai sukayi mgn akan matsalar tare da ba ummah hakuri, futha shiga ciki ki kira zarah inji mumyn Amrah, "tou ta fada hade da mikewa tayi hanyar dakin...........Urs Zarah~B~B


206-210Kwance ta same ta kan gado tafi 5mnt tana kalln yadda zarah ta sauya haka sai kace wanda tayi jinyar 1yr, a sanyaye ta iso daidai gurin da zarah take kwance wanda ita zarah har tym din batasan da wanxuwar Futha a dakin ba, jin antabata yasata firgigit ta tashi daga kwancen da take, ganin futha a gabanta yayi matuqar bata mamaki sake da baki take kallon ta, daqar bakin ta ya iya fadin futha sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi, kwallar da ke maqale a idon Futha suka fara zuvuwa zama tayi kusa da zarah tare da riqo duka hannun ta biyu ta fara bata baki harsaida taga ta dan samu natsuwa kana tace tashi muje parlour su ammi na kiranki hijab kawai tasa suka wuce parlour akasa suka zauna, mumyn amrah da taga yadda zarah ta canxa ta tausaya mata sosai duk da wanigafen zuciyar ta naso ya yarda da abinda 'yarta ta fada amma ganin halin da zarah ke ciki yasata qaryata abinda zuciyar ta ke raya mata, zarah bakida lfy ne? Ammi ta fada, shiru tayi sai sasshekar kukan da takeyi akeji ganin bata niyyar yin mgn yasa ammi cewa "zarah kiyi hkr ki rage wannan damuwar kada kijawa kanki wata matsalar daban",
Mum tace "ba ke ba, ba Amrah ba, kowacenku babu natsuwa a tare da ita",
Ammi kam cewa tayi "duk kansu sunbi sun rame har futha, Allah dai ya kyauta ya kawo maku qarshen komai",
Duka suka ansa da "amin".

Sallamah Yaa Affan yayi cikin natsuwa, ummah ta ansa sallamar fuskarta dauke da dan guntun murmushin rashin sani, ammi tace "shigo daga ciki mana", takowa yayi ya zauna yana qarewa Zarah kallo ko gaishe da ummah bayyi ba, ammi tace "wai kai baka ji ana maka magana ne?, yayi saurin zabura yana sosa qeya yace "ina yini ummah"
"Lafiya lau" ta bashi ansa, duk kansu sun fahimci irin kallon da yakewa Zarah, Ammi ce ta fara miqewa tace "alhamdulillah! Tunda tana gida ai komai yayi kyau, ku tashi mu tafi an bar Amrah gida ita kadai",
Mom ma ta miqe amma sam futha tace ita ba yanxu zata tafi ba, da Ammi ta hana amma ganin Zarah na kuka yasa tace "ki zauna anjima sai Affan yaxo ya dauke ki",
Dadi taji sosai shima Affan din haka, dan yasan ya samu damar da zai sha love da Zarah wanda yayi kwanaki basuyi ba.Yanxu meye amfanin abinda kayi?ka tashi totar babu ba zarah ba amrah suma kuma ka tarwatsa masu farin ciki, wlh idan baka gaggauta sanin abunyi ba to ina gujemaka haduwar ka da ubangijinka musty ya fada, shikuma Farouk dake kwance sai famar hawaye yake a zuciyar shi kuwa wani irin zafi yakeji kamar ya hadiye rai ya mutu dan bakin ciki......Urs Zarah~B~B.
WISDOM HAUSA WRITERSFatima~Bello~bala.
Share:

0 comments:

Post a comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).