shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 27 May 2016

AMINAN***JUNA 1---60

aminan-juna.jpg

[7:38PM, 5/20/2016] my mtn: Zarah B B
Na Xarah~B~B


Gargadi: ban yarda wani ko wata su juya mn wannan labarin ta wata siga ba, haka zalika ban yarda ayi editin a cire ko a qara wani abu ba.

Godiya: godiya ta musammam ga Allah mad'aukakin sarki daya bani iko da baiwar rubuta wannan littafin duk da yake shine littafi na na farko, ina godiya gareku masoyana aduk inda kuke.

1-10
Tafiya takeyi cikin natsuwa da kaganta kaga natsatsatsiyar yarinya, kyakkyawa ce ta karshe, komai nata yayi daidai da ita,fara ce tas, sanye take da hijab dogo har kasa purple in colour,shekarun ta bazasu wuce 18yrs ba, can na hango ta ta shiga wani matsakaicin gida da ba wani babba ba, sallama tayi, bata tarar da kuwa a haraba ba sai me gadi dake dakinshi yana sallah, shi ya bata damar shiga dakin da ke kallon ta, nan ma bata tarar da kuwa ba, jin motsin ruwa a toilet ya tabbatar mata da cewa "Aminiyar ta na ciki" tana fitowa ta tarar da"abar kaunar ta"da fara arta tazo wajen ta tana fadin "oyoyo my AMRAH", sorry plz kin tarar dani ina wanka", "bakomai my ZARAH", nan ta hau yin shiri light make up tayi tasa kayanta riga da skirt ne dai dai jikin ta sun mata kyau sosai,zaune sukayi suna ta firar su, " my ZARAH ina umma ne ban ganta ba?", "tana bedroom dinta", "ok muje na gaida ta bcos zan wuce yamma tayi" ,"ok muje",zaune suka tarar da ita kan sallaya da alama ta gama sallar la'asr, bayan ta qare addu'a zuka gaisa da Amrah sa'annan sukayi sallama, har bakin gate ta kaita kasan cewar ba nisa a tsakanin gidajen nasu...............Urs Zarah~ B ~ B.
[23/02 2:06 PM] Zarah B B : AMINNAN~JUNA


Na Xarah~B~B

11-20

Babban gida ne naga ta shiga daganin shi kasan naira ta kuka agurin, tsaya wa fada maku tsaru warshi bacin lokaci ne, ya zarce duk tunanin mai karatu, palour naga tashiga Wow! aljannar duniya komai na palourn white nd purple ne, manyan mutane ne wanda daka gansu kaga mutane masu kamala ke xaune a parlourn suna tattaunawa akan irin amintakar dake tsakanin 'yarsu da qawarta, shigowar tane ya katse masu mgnr tasu, da fara arta ta zauna gun Dadynta "ina wuni dady ya aiki?, ya ansa da "lfy qalau ya kika baro zarar taki?", "lfy qlw take dadyna tace na gaida ka, Mum ina wuni?", cikin xolaya mum dinta tace "banaso sai yanxu kika ganni?" "No mum am sorry", tayi murmushi tace "bakomai my daughter, kije kici abinci", "ok Mum",



"yau ta kama Sunday zaune suke suna breakfast cikin jin dadi da walwala, "Amrah! Na'am Dad, gobe zaku fara zuwa skul keda qawar ki insha Allah, duk abunda ake buqata an riga an kammala, Plz my daughter ku maida hankalin ku ga studies dinku", "insha Allah Dad mun gode sosai Allah ya qara girma", duka suka ansa da "Ameen Ameen", bayan sun dawo palour Dad ke cema Amrah "my daughter close ur eyes", cikin zumudi ta rufe, Dad ya azamata key din car a hannun ta, sa'annan ya umurce ta da ta bode idanun ta" Wow! Dad nawa ne?" ya gyada mata kai alamar eh, tsalle naga tayi sai can cinyar Mum dake ta famar murmushin ganin yar tata na cikin farin ciki, sa'annan ta kuma gun Dadynta "Dad tnx alot, i dnt knw how 2 even tnx a Luvly and caring Dad lyk u tnx alot once again my Luvly Dad" da gudu ta wuce dakin ta cike da farin ciki a ranta, toilet ta wuce don yin wanka, bata 6ata tym ba ta fito ta shirya cikin riga gown ta material lemon green in colour,tayi matuqar kyau kamar kasace ta ka gudu, komai nata lemon green ta sa, tafito domin kaima Aminiyar ta albishir, nan suka fita harabar gdn don ganin car din Amrah, wow! Ta hadu iya haduwa kirar camry ce, bayan su qare Amrah tayi masu sallama ta wuce gdn su Zarah........Urs Zarah B B
[7:38PM, 5/20/2016] my mtn: AMINAN JUNA

Na Xarah B B

31-35

Asalinsu.
Zarah d'iya ce ga malan Usman da malama Zainab, iyayenta sunyi auren soyayya da qaunar juna, tun Zarah na cikin ciki mahaifinta ciwon ajaliyya ya kama shi ya mutu, malama Zainab tayi kuka sosai na rashin mijinta, daga baya kuma ta fawwalawa Allah komai.

Har ta haifi Zarah ba wani abu gareta ba sai rufin asiri da kuma temako da suke samu daga maqoptansu,wato gidansu Amrah.




Asalin Amrah.
D'iya ce ga alhj. Abubakar da hjy Salmah, sun taso cikin dukiya sosai da temakon talakawa, unguwarsu d'aya dasu Zarah, shekarar Amrah da Zarah d'aya kuma suna qaunar junansu, haka suka tashi cikin kulawar iyayen Amrah, bayan sun isa shiga skul ma Alhj Abubakar ya sama masu wata private skul me tsada.

Haka sukaci gaba da skul d'insu cikin qaunar juna, so da yawa wasu na ce masu twince ne su, saboda yanayi rayuwar su komai tare suke yasa har ake ganin kamarsu.

Bayan sun kammala secondary skul ne dadyn Amrah ya kammala wani katafaren gininshi da yakeyi nesa da gidansu na da, sunsha kuka sossai lokacin da zasu rabu, mum Amrah tace "ku kwantar da hankalinku, ai sai ku ringa xumunci ko?", malama Zainab tace "aikam, indae kuka riqe xumunci komai nisa zaku ringa xiyarar junanku", haka suka rabu cikin kewar juna da qaunar junansu.

Canja unguwar da sukayi kuma bai hana su xumunci ba har yanxu da dadyn Amrah ya nema masu UDUS..........Urs Zarah B B


[25/02 5:24 PM] Zarah: AMINAN JUNA

Na Xarah B B

36-40

Ci gaban labari.
Koda suka koma gida a gajiye suke, Amrah na kwance tana baccin gajiya sai taji wayar ta na ringing, rejecting tayi ta sake juyawa, sake kira akayi ta qara latsewa tare da yin tsaki, jin an dame ta da kira yasa ta tashi dan daman bata gabatar da sallar la'asar ba, sai da tayi off na wayan sannan ta nufi toilet tayi alwala, koda ta gama sallah ta kunna wayan don ganin nataccen dake kiranta, new number ta gani yasa tayi d'an guntun tsaki taci gaba da addu'anta.

Bayan ta gama ta nad'e sallayarta tana qoqarun nad'e hijab wayanta ya sake ringing, a daqile ta d'auka tace "hu is online?", kyakkyawar ajiyar xuciya yayi yace "ki bari mu gaisa sannan na miki introducing kaina", "nop bana son gaisuwar, just tell me, who am I talking with?", da d'an murmushi yace "its me Farouk", "wane Farouk?" Ta fad'a dan ita tama manta da sun had'u da wani a skul d'axu, yace "hmm! Farouk Adam, we met at UDUS 4hours ago", ta d'an nisa tace "kayi mn yanda zan gane malan, ni bansan na had'u da kowa ba", dariya yayi da har sai data fito, yace "wanda har kika saima abinci a Hikimah restaurant", yana fad'in haka ta tunashi tace "sarkin surutu zakace mn sai in gane ai", Farouk yace "ehh nine fa da kaina, I just called to say hi", Amrah tace "ka kyauta, thanks", "naji dad'i dana kyauta miki" ya fad'a had'e da kanne mata ido kamar yana gabanta.

Haka kawai ta tsinci kanta da jin dad'in wayar da sukayi, pillow'n ta ta runguma tare da maimaita maganganun da ya fad'a mata, tana cikin haka taji qarar shigowar text a wayanta, dubawa tayi taga numbern da Farouk ya kirata dashi ne,

"Nyc name with nyc voice, stay cool my dear".

Murmushi tayi a ranta tace "mashiririci kenan, ji wannan d'an text daya mn, anyway, ka kyauta tunda ka kula dani".

Da dare ma kafinta kwanta sai daya kira ta yace "ina fatan kinga text ina?", tace 'ehh na gani', yace "shine kuma babu respond", tace "tou me zan ce maka?", sai daya d'an yi mirmushi sannan yace "nothing bae, yanxu dae kije ki kwanta nasan ke raguwa ce da wuri kike kwanciya", tace "ehh naji dae koma me zakace ka fad'a, gud nyt", shima "gud nyt" din yace mata tare da kashe wayar.

Haka Amrah ta kwana cikin tunanin Farouk, ita kanta mamakin kanta take ta yanda lokaci d'aya taji Farouk ya kwanta mata a rai.............Urs Zarah B B
[7:38PM, 5/20/2016] my mtn: AMINAN JUNA

Na Xarah B B

21-25

Yau ta kama monday, ranar da Amrah da Zarah suka fara registration, bayan sun gama registration suka tafi cafe d'in dake cikin makarantar, course registration form suka fiddo a ranar suka gama signing baki d'aya, Capteria me kyau suka nema a skul d'in, Amrah ta siya masu abinci suka ci sannan suka kama hanyar gida, a mota Zarah tace "my Amrah skul akwai wahala fa", Amrah dake driving ta juyo ta kalli Zarah tace "dama wa yace miki skul akwai sauqi?,ai in kina shirya shan wahala qwara ki shirya ma wlh, kin dae ga girman UDU ai ba sai an baki labari ba", Zarah tace "hakane kam, tou ya xa'ayi ai dama duk me nema sai yasha wahala, Allah dai yayi mana jagora", Amrah tace "amin".

A daedae qofar gidansu Zarah Amrah tayi parking da mota, Zarah tace "kina nufin baxaki shiga ba kenan?", Amrah tace "ni na isa in ce baxan shiga ba?, ki fita zan gyara parking ne ki jira ni".

Ba qaramin dad'I mahaifiyar Zarah taji da ganin yaranta va, tace "yau kunji yanda skuk take ko?" Amrah tace "wlh ko Ummah akwai wahala", ummah tace "tou Allah ya temaka, ku ringa fita da 5point", dariya sukayu su duka sannan Amrah tace "tou ummah ni zan wuce", ummah tace "tou sai anjima Amrah, ki qara yi mana godiya wurin dadynki, nima insha Allahu zanzo", Amrah tace "babu komai ummah sai anjima", har qofar gida Zarah ta rakata sannan ta tambayeta sau yaushe zasu koma skul tace " mu bari sai next week tunda dae Allah yasa mun gama komai kinga kafin nan lectures sun kankama", Zarah tace "tou shikenan insha Allahu zanxo cikin weekend", Amrah tace "tou my Zarah Allah ya kaimuh", ta amsa da "amin" ta isa bakin motarta...............Urs Zarah B B
[24/02 12:53 PM] :Zarah : AMINAN JUNA


Na Xarah B B

26-30

Ranar monday tun da safe Zarah ta shirya cikin riga da skirt da atamfa red, ta saka red hijab, tayi kyau sosai ta kira Amrah tace "na shirya ke nake jira", Amrah tace "fito kawai na kusa zuwa qofar gidan nasan kafin in qaraso kin fito", Zarah tayiwa umma bankwana sannan ta fita waje, ta samu har Amrah taxo, bud'e motar tayi ta shiga, ta bata hannu suka gaisa sannan suka kama hanyar UDU.

sun samu har malamin ya shiga ya fara dictation, seat d'in daya tari gabansu babu kowa suka zauna suka fuskanci malamin, hour 2 yayi cip sannan ya fita, time table Amrah ta fiddo daga jakarta ta duba tace "my zarah akwai 1o-12 fa", Zarah tace "wane course ne?" Amrah tace "Bio 1211 ne, Botany kenan", Zarah tace "ina ne venue d'in ?" Amrah tace "wai a mini theater ne ta sciences", Zarah ta miqe tace "ta mu tafi kar mu makara dear, kinji ance malaman Bio d'in nan ba wani mytunci ne dasu ba".



Qafe 12 daedae suka fito lecture, capteria suka nufa dan suci abinci, irin wurin xaman nan ne me seat 4, kwatsam wani saurayi kmhad'ad'd'e yaxo wurinsu ya zauna, "hello babes", ya fad'a tare da kanne ido d'aya, Amra ta 'bata rai tace "wa alaikumussalam", saurayin ya riqe baki yace "sorie ashe ba sallama nayi ba, wlh bakin ne nasha janshi akan ya ringa yawan sallamah, amma kuyi haquri baxai kuma ba" abn ma dariya ya vama Amrah, Zarah kam ta duqar da kanta qasa tana latsar waya, a lokacin waiter ta kawo masu abinci, Farouk ya ce "au abn rowa ne ko? Ni baxa'a sai mn ba kenan?", Amrah tace "sorie", ta kira waiter tace "qaro 1 plate", ta zaro 5k tace "ga kud'in".

Bayan sun gama Farouk ya nemi numbern Amrah, sai data ja mashi aji sannan ta bashi, yace "sunana Farouk, and youh?", Amrah tace "am Amrah and shes Zarah", "wow! Nyc names" ya fad'a sannan yayi masu bankwana ya tafi.............Urs Zarah B B
[7:38PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA

Na Xarah~B~B


51-55


Yace kamar dai yadda kika sani, suna na "Farouk Adam" ni dan asalin Zamfara state ne, a gusau L/G, acan aka haife ni a shekara ta 25/5/1989 acan nayi karatuna na addini dana boko tun daga primary skul har Scondary skul dina.

Mahaifina Alhaji Adam Muhammad tare da mahayfiya ta Hajiya Baseerah, Auren soyayya sukayi tare da mahaifina, Har Allah ya azurtasu da ya'ya.

Mu biyu ne ga iyayen mu, ni da qanwa ta mai suna Amina, yanxu haka tayi aure harda ya' daya.

Alhamdulillah muna cikin jin dadi da farin ciki duk da mahaifina rufin asiri ne da shi, bayan result dina ya fito ne, na neme admission anan Sokoto state.

Cikin yarda Allah nakuwa samu a nan UDUS, yayin da nake karatun pure chemistry, adan dafe har Allah yanu na man nakai 300 level.

A dai dai wannan lokacin suka iso gurin shan ice cream, anan aka kawo masu ice cream kala kala tun daga vanilla ice cream, strawberry ice cream da dai sauran su.

Anan ne Amrah ta kalle Farouk cike da tausayi, tace hubby na insha Allah daga yau ka fita quncin rayuwa, inason duk tym din da kake da wata buqata ka sanar dani kaji hubby na.

Zarah dake zaune tana sauraron su tun tym din da Farouk ya fara mgn, tayi ajiyar zuciya tare da fadin "Allah yasa muda ce da rabun sa" duka suka ansa da "amin".

Ido suka hada suna wa juna murmushi wanda ke qara fitar da kyan su," Farouk da Amrah kenan " Farouk kyakkyawa ne bt saidai ba fari ne ba wankan tarwada ne wanda turawa ke kira da{Chocalate colour}, aranshi kuwa yana ta ayyana abubuwa daban daban, sai murmushi yake yi wanda da ka ganshi kasan na mugunta ne..........Urs Zarah~B~B


55-60


Lokaci daya suka tashi, suka nufi motar su bayan duk sun shiga, Amrah ta jasu basu tsaya ku ina ba sai a wani babban mall ciki suka shiga gafen boutique suka fara zuwa ta kalle Farouk tace "hubbyna ka zabi kayan da kake so" kallo kawai ya bita da shi, murmushi tamai tace oya dauka mana, anan ya fara za6ar kaya, ganin ya tsaya da ibar kayan yasa ta cigaba da za6ar masa, kaya masu yawa da daukar masa harda shoes ta hadamai da su, daganan suka wuce suma suka za6a ita da zarah komai iri daya suka dauka, haka kayan cosmetic, sunyi sayayya mai yawa, sa'annan suka je Amrah ta biya kudin aka saka kayan a booth suka wuce,

Yinin ranar haka sukayi ta cikin jin dadi da farin ciki sunyi yawo har son gode Allah, sai da yamma suka wuce UDUS suka maida Farouk kasan cewar a hostel yake bayan sun ajiye shi, ya dauki kayan shi dake booth niqi niqi sukayi sallama da shi ya wuce,

Zarah ta dawo seat din mai xaman banxa suka wuce, a hanya Zarah ke cewa Amrah "gaskia kina son Farouk da yawa" Amrah ta kalleta kawai tayi murmushi kamar ba xatayi mgna ba kuma sai tace "Nima haka kawai nake jinshi araina kamar idan ba shi rayuwa ta bazata zama complete ba" Zarah tace to Allah yayi mana za6i mafi alkhairi a rayuwar mu duka suka ansa da "amin" ahaka har suka isa gdn su zarah, "Amrah ta kalle Zarah tace plz ki gaida ummah" Au baxaki shigaba ne cewar Zarah "plz my zarah kiyi hakuri kinga an kusa sallar magreeb kinji" tace ok bakomai ki gaida Mum, ok zataji insha Allah, ahaka suka rabu sunawa juna bye bye.

Da isarta bayan tayi parking ta wuce parlour bata tarar da kuwa ba ta wuce room dinta da shigar ta' ta ajiye hand bag dinta ta wuce toilet wanka ta farayi sa'annan ta dauro alwala ta fito, bayan ta shirya tsaf cikin kaya marar nauyi ta zira dogon hijab dinta don gabatar da sallar magreeb.


Ban garan Zarah kuwa haka ta shiga da kaya niqi niqi a hannun ta, dakin ta ta wuce ta ajiye su, itama toilet ta wuce bayan tafito ta gabatar da sallar magreeb daganan ta wuce da kayan da Amrah ta siya mata room din umman ta, zaune ta same ta kan gado bayan ta gaishe ta, Ta hau nuna mata kayan da Amrah ta siya mata ummah sai murmushin farin ciki take tana qara sawa ya 'yan nata albarka

Zaune yake shi da abokin shi yana nuna mai kayan da Amrar shi ta saya mai bt aranshi yana fadin "Amrah am sorry" maganar da Mustapha keyi wanda suka fi kira da Musty ne ta dawo da shi, yace ya akayi ne aboki na? Farouk ya fitar da iska hade da yin ajiyar zuciya..... .
[7:38PM, 5/20/2016] my mtn: AMINAN JUNA


Na Xarah B B
41-45

Soyayya mai karfi da shaquwa suka shiga tsakanin Amrah da Farouk, wanda ya kasan ce akuda yaushe idan har suna skul to suna tare, idan kuwa suna gd to fa suna nan maqale da waya.

Yau ta kama Saturday, zaune take tana tunani kala kala aranta,, bude kofar da akayi ne ya maida ta daga duniyar data lula, ganin Aminiyar ta kuma abar kaunar ta yasa ta sakin wani sakaran murmushi wanda ya qara fito mata da kyan ta, itama murmushin ta maida mata,, "My zarah yaushe kika zo cewar Amrah" banjima da zuwa ba Mum tace na duba ki kina daga ciki.

Fira sukayi sosai cike dajin dadin ganin junan su, kusan ranar acan Zarah tayi ni don kuwa ba ita da wucewa ba sai da yamma tayi, sa'annan suka fito ta ma Mum sallama ta wuce.

Haka rayuwa ta kasan ce masu ita da Aminiyar ta kuwanne daga cikinsu baya sun bacin rai daya, soyayya kuwa tsakanin Amrah da Farouk har ba'a mgn domin kuwa Amrah har mmkn irin son da takewa Farouk takeyi.

Kwance yake yana ayyana abubuwa aranshi yana murmushin muganta sai kuma naji yana cewa "Yes" burina ya kusa cika, "ni ku Xarah nace wani burine na Farouk ya kusa cika?" can naga ya dauke wayar shi ya latsa wa, sai naji yana fadin sannunki da hutawa farin idaniya na, wanda ba ku sai anfada ba "AMRAH ce, dayan bangaren akayi mgn bt banji me aka ce ba, sai naji yana fadin da gaske kikeyi" My luv" ok gani nan zuwa,, sai ya katse wayar ya nufi toilet bayan 30m sai gashi ya fito sanye da jalabiya yana goge kanshi da towel din hannun shi,

bayan ya shirya tsaf cikin shadda light blue da hula duk da shaddar ta dan tsufa bt tayi mashi kyau sosai.

A bangaran Amrah kuwa bayan sun qare waya da hubbyn ta, Ta kira Zarah ta fada mata cewa ta shirya zasu unguwa, daga nan toilet ta nufa don yin wanka 30m ta dauka kafin ta fito, Ta wuce gaban madubi don shiryawa........... Urs Zarah~B~B


46-50

Ta kammala shirinta tsaf cikin atamfa brown da digon fari dinkin yayi mata kyau sosai gyalen ta ma fari da dauko hand bag din ta duk ta ajiye akan gado.

Bangaran Farouk kuwa har ya fito ya ciro wayar shi ya kirata domin ta mashi kwatancen area tasu, ringing biyu ta dauka "Hello my luv daga dayan bangaren tace hubby ka iso ne? Yace a'a taya zan iso baki man kwataccen gurin ba, tace au na manta, kasan Sama road? Yace a'a bt zan tambaya ok da ka iso ka kirani kawai yace" ok"

Haka kuwa akayi bai sha wahala sosai ba kasan cewar mashin din da ya daukeshi yasan unguwar, da zuwan shi ya kirata ya shaida mata cewar ya iso.

A palour ta same Mum dinta a zaune kusa da ita ta zauna ta gaida ta, Mum ta ansa fuskar ta dauke da murmushin, Mum ta ce my daughter ina zuwa haka kin kuwa ga yadda kikayi kyau sai kace balaraviya, Amrah ta sunkuyar da kanta tana murmushi Mum gdn su Zarah xanje, Mum tace ok Allah ya tsare hanya my dear, Amrah ta ansa da "Ameen Ameen" ki gaida umman Zarah plz " ok Mum zataji insha Allah" sukayi sallama ta fita.

Motar ta ta nufa bayan sun gaisa da baba mai gadi ya wangale mata gate ta fita, can nesa kadan da gdn su ta hango Farouk yayi matuqar yimata kyau"Aranta tana fadin really Luv my Farouk "a haka har ta isa inda yake bayan sun gaisa ya shiga Motar basu tsaya ku'ina ba sai bakin gdn su zarah.

Ita kuwa zarah tun bayan kare wayar su da Amrah ta same umman ta ta fada mata cewa zasu unguwa da Amrah, Ummah ta amince tare dayi masu fatan alkhairi.

Daga nan zarah ta wuce dakin ta bawani 6ata tym tayi ba ta shirya cikin atamfa green nd white tayi kyau sosai kasan cewar mafi yawancin kayanta duk dadyn Amrah ne ke masu, some tyms ma komai iri daya yake masu.

Bayan Amrah ta gama parking tace da Farouk ina zuwa 2m plz, da fara arta ta shiga gdn bayan sun gaisa da Ummah take tmby ina Zarah? Ummah tace da ita tana ciki, zaune ta same ta tana latsar wayar hannun ta.

Oya my zarah tashi muje yana mota yana jiran mu, Zarah ta xare ido wake jiran mu my Amrah? Amrah tayi murmushin dake qara fito mata da kyan ta, tace hubby na mana, zarah tace au shin da shi za'ayi fitar? Kai kawai Amrah ta gyada mata alamar"eh"tace ok muje,

Anan harabar gdn suka same Ummah tace har kun fito suka ansa da eh tace to Allah ya tsare hanya duka suka ansa da"amin"suka bar gdn rike da hannun junan su,suka nufi motar suka shiga, Zarah a baya, Amrah a driver seat yayin da Farouk yana seat din mai zaman banza.

Driving take ahankali, can sai da kalle Farouk tace "hubby na" ya ansa da na'am my luv tace ina son kabani labarin ka, Farouk ya kalle ta yana murmushi yace ok my luv angama, Ta madubi take kallon Aminiyar ta suka ma junan su murmushi sa'annan ta maida hankalin ta ga Farouk tace "hubby na ina sauraron ka" Farouk wanda shima ita yake kallo ya nisa yace.............UrsZarah~B~B
Share:

2 comments:

  1. Abubakar Ibrahim3 June 2016 at 14:59

    Allah ya kareku daga sharrin samarin zamani

    ReplyDelete
  2. ALLAH YA KARA BASIRA

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).