shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 27 May 2016

AMINAN***JUNA 251---270

aminan-juna.jpg

AMINNAN JUNAEXTREME HAUSA WRITERS


Na Xarah~B~B
251-255Kwance yake sai juyi yake yi ya rasa abunda ke mashi dad'i sai tunani yake, yasak'a wannan ya kwance wancan, rurin wayar shi ne yasa shi dawowa daga tunanin daya keyi, ganin mai kiranshi ne yasa shi d'aga wa "Hello abokina ya kake?", a d'ayan b'angaren bansan me aka fad'a ba naji dai yace "da gaske musty? kai amma naji dad'i Allah ya sanya alkhairi", musty ya ansa da"amin" "wacece amaryar tamu?" Farouk ya fad'a", "zaka santa amma ba yanxu ba", a haka dai har sukayi sallama tare da katse wayar".


Kwance tashi ba wuya agurin Allah, dan kuwa ya Affan da Zarah har ammasu baiko, ita kuwa Amrah taba musty daman ya turo iyayen shi, Alhamdulillah abubuwa na tafiya yadda ya kamata, matsalar su d'aya ce shine rashin Shirin su da junan su saboda yanxu Amrah ta fara saukowa.


Zaune yake yayi tagumi, a ranshi kuwa ya gama yanke shawarar zuwa har gidan su Amrah domin fad'a mata gaskia abunda ya faru kuma ya neme gafarar su baki d'ayan su koya samu kwanciyar hankali a rayuwar shi, saboda tin ranar da abun ya faru bai qara samun natsuwa a tare da shi ba, sai yanxu magagganun da musty ke fad'a mashi suke dawo mashi, tabbas yayi Babban kuskure a rayuwar shi daya biyewa son zuciyar shi, gashi yanxu ya tashi tutar babu, domin kuwa ba Amrah ba Zarah uwa uba gashi ya rasa karatun shi.

Lallai hausawa sunyi gaskia da suka ce duk abunda mutum ya shuka shi zai girba......... Urs Zarah~B~B.

-256-260
Zaune suke a parlour ita da Mum suna firar su abun gwanin ban sha'awa, shigowar baba maigadi ce ta katse masu firar bayan yayi sallama anbashi izinin shigowa suka gaisa sa'annan yace "Hajia anayi wa Amratu sallama" ido ta zare "wake man sallama baba mai gadi?" "idan kika je ai zaki ga koma waye" Mum ta fad'a tare da cewa baba maigadi yace tana zuwa, "uhm uhm gaskia ni Mum bazan jeba dan bansan ko waye ba" "to idan kika je ai zaki sani, garama ki tashi kije ki ga", da kyar Mum da lallaba ta sa'annan ta saka hijib dinta ta fita


Tsaye yake a bakin gate, tin kafin ta k'araso taji gaban ta na fad'uwa, shikuwa Farouk aranshi sai tunanin ta inda zai fara yake, a haka har ta k'araso dai2 inda yake tsaye, sallama tayi ya ansa d'ago idnuwan ta dazatayi suka had'a ido da Farouk "wana ke gani a kofar gdn nan?" murya na rawa da kyar ya iya furta "Am... rah......." kuma sai yayi shiru.

Shiru ne ya biyo baya kowannan su da abunda yake tunani a ranshi, Amrah ce tayi k'arfin halin katse shirun da cewa " me kuma kazo yi? ko kuma kazo ka k'arasa abunda baka k'arasa ba a shekarun da suka wuce?tou ka koma wurin Zarah badai wurina ba, Farouk na tsane ka na tsani rayuwarka, bana son ganinka, domin kuwa ganin ka yana 'kara tayar min da wani tabo da nasha wahala kafin ya goge, Farouk idan ba kana so in wulakanta ka bane tou kayi gaggawar barin gidan nan", da kyar ya iya furta "a'a Amrah dan Allah ki saurare ni", "au sai yanxu kasan Allah koh Farouk? Lokacin da ka ruguzaman rayuwa ka rabani da farin cikina duk kana me? shin wai meyasa ka dawo cikin rayuwa ta Farouk?" duk wannan maganar da take cikin kuka take yinta


"Dan Allah Amrah ki saurare ni nasan nayi kuskure Dan Allah ki yafeman, kin san dama d'an adam ajizi ne, ki taimaka min ki saurare ni, wlh da kinsan irin halin dana shiga da kin tausaya man, yanxu zan warware miki duk abun daya faru, amma ina so ki taimaka ki biyo ni muje gidan su Zarah dan nafi so ayi komai a gabanta".
Amrah tace "what? Allah ya kyauta min inje gidan su Zarah. Ai ni da Zarah har abada. Babu ni babu ita, saboda haka tun wuri ma ka tafiyarka dan baka da wani abu da zaka fad'a min".
Da 'kyar ya shawo kan Amrah ta yarda zasuje gidan su Zarah amma da sharad'in bazata shiga gidan ba sai dai ta tsaya a 'kofar gida........ Urs Zarah~B~B
kuci gaba da biyo ni danjin k'arshen wannan labarin, ya kusa 'karewa insha Allah.


Taku har kullun
EXTREME HAUSA WRITERS.Fatima~Bello~Bala.

AMINNAN JUNA
EXTREME HAUSA WRITERS.
Na Xarah~B~B

261-265
Ba yadda ya iya haka ya yadda da sharad'in ta, bata kuma cikin gd ba, kawai tace ma baba maigadi zataje ta dawo sa'annan suka wuce gdn su Zarah.


Bakin ' kofar gdn suka tsaya, nan Farouk ya samu yaro ya aike shi ya kiramai Zarah, ummah ce ita kad'ai zaune a parlour tana kallon wa'azin Dr. Mansur Ibrahim Sokoto a tashar WISAL HAUSA TV, sallamar yaron ne ya katse mata kallon nata, bayan ya gaida ta sa'annan ya fad'a mata cewa anama Zarah sallama a waje, "wake mata sallama?" Ummah ta fad'a, "nima ban san shi ba" "ok kace tana zuwa" tare da mi'kewa tayi hanyar room din zarah.


Kwance take tana waya daganin yadda take wayar basai ma anfad'ama kodawa take waya ba, shigowar ummah yasata tsinke wayar tare da fad'in "ina zuwa yayana, ummah ina wuni?", lfy qlw Zahra'u, kije waje ana maki sallama", ummah ta fad'a fauskar ta d'auke da murmushi, "wake mani sallama a wannan lokacin ummah?" "bansani ba yaro aka aiko amma inkin je ai sai kiga koma waye fatana dai Allah yasa lfy" zarah ta ansa da "amin" tare da zira hijab d'inta, tare suka fito parlour ita da ummah, anan suka rabu Zarah ta fita waje ummah ta cigaba da kallon wa'azin ta.A 'kofar gida ta tarar dasu tsaye suna jiran ta, da sallama ta isa gurin ganin Farouk yasa ta kasa idar ta sallamar ta ta, murya na rawa ta fara fad'in "Farouk me kazo yi anan? bayan ka rabani da Aminiya ta? katarwatsa duk wata ala'kata da ita, kayi man tabon da har in mutu bazai ta6a gogewa ba?Farouk kayi gaggawar bar mana 'kofar gida tun kafin na nemo wanda zasu tafi da kai cikin sau'ki" Haka taciga da fad'in abinda ke ranta hawaye na tsilala a fuskar ta...... Urs Zarah~B~B.

266-270"Zarah ki tsaya ki saurare ni kiji abinda ya kawo ni plz", Farouk ya fad'a cikin mirya ban tausayi, "kai malam kai nake jira kafad'i abinda zaka fad'i dan nagaji da tsayuwa" Amrah ta fad'a cikin tsiwa, baki sake Zarah ke kallon ta dan ita sam bata lura da ita ba sai yanxu da tayi magana.


Kusan 5mnt ba wanda yace da kowa komai, Farouk ne yayi k'arfin halin fara mgn yana cewa "da farko dai ni mai laifi ne a idanuwanku amma dan Allah ina mai rok'on gafarar ko saboda sai yanxu na tabba ta nayi babban kuskure a rayuwata dana biyewa son zuciya ta gashi bata haifa man komai ba sai danasani, Amrah tun lokacin dana fara ganin ku nake bibiyar ku duk wani details naku sai da na samu, ganin ke d'iyar mai kud'i ce yasa ni cewa ina sonki amma mgnr gaskia ni Zarah nake ma SON GASKIA, nayi zaton irin mutanan nan ce wad'anda basu damu da damuwar kowa ba sai tasu, na zata idan na biyo ta baya nace ina sonta zata amince amma sam yadda nayi tuna ni ba hakan bane, domin kuwa sam ban samu amincewar Zarah ba hasali ma idan nakira ta bata d'agawa shine dalilin dayasa kikaga idan na kiraki nake cewa kiba Zarah, Amrah wallahi Zarah bata yaudareki ba laifina ne saboda a wannan Zamani da wahala kisamu aminiya kamar Zarah, na za6i zuwa in fad'a maku gaskia ne badan komai ba sai dan abubuwan da suka faru dani nasan tabbas hakk'in ku bazai barni ba, dan Allah dan darajar Annabi Muhammad (S.A.W)Ku yafe man wallahi nayi nadamar abinda nayi maku, nayi danasanin shiga tsakanin ko dan Allah ku yafeman kuna samu natsuwa a tare dani, ku sani wallahi matu'kar baku yafe man ba tou ina cikin matsala, domin kuwa nasan haka zanci gaba da rayuwa cikin 'kas'kanci da tagayyarar rayuwa", har 'kasa Farouk ya du'ka kuka sosai yakeyi yana ro'konsu gafara.....Urs Zarah~B~B.

Happy birthday 2 u "ASEA~B~ALEEYU" Wish u long life nd prosperity,,,,,, sorie for d late wishing.

LUV U ALL MY CWT CWT FANS
EXTREME HAUSA WRITERS.Fatima~Bello~Bala
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).