WAYE SANADI 11 & 12
[9:24PM, 5/10/2016] Ábbā-Gãñå WAYE SANADI?
11
)MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
haba nana Allah ya tsareki da iskanci,fatana Allah ya tsareki ya rabaki da dukkan mai sharri bara na baki dubu goma ki rike a hannunki ranar sai karfe takwas suka tafi suka kaita lokacin bana gidan karfe goma da rabi na dawo gidan kaka na tarar a zaune a soro "ina kika je tun dazu nake jiranki zan rufe kofata inda kika aiken wajen naje uwata,ai da kin sani kin rufe wallahi da sai na karya kofar kuma na tara miki mutane wani azababban mari ta sakar wanda ya sani yin shiru "shegiya mara kunya wadda bata neman albarka bankadaddiya ki kara gayan magana ta mai da kofar ta rufe ta biyo ni tana bambami ina zuwa na nufi kicin wata sungumemiyar tabarya na dauko n shigo dakin ina dai kin isa dan girman Allah ki kara marina sai in balla miki kai dan kinga ina rabuwa dake bafa tsoronki nake ba,ki kara marina ki gani ina magana ina tura mata fuskata ki mare ni mana ido kawai ta zuban jikinta yana rawa,na saki murmushi "mutum sai tsoron tsiya wallahi yau mu biyu ne ki mun ki ga karyar rashin kunya dama ina ragonta miki dan darajar ummata,to dan Allah yanzu kimin abin da kike min ki gani koh zan rabu dake,wallahi zan yanka ki matsa malama ki ban waje na karasa na kwanta jakata na bude 2 miss call mamaki ne ya kamani ganin har miss call two ni dai nasan bbu wanda yasan number ta duka duka yau kwana uku dasa layin abin ya kara bani mamaki da naga number wata iri dagani lambar wata kasarce sai kuwa naga text message abin da nagani "my momy lafiya nayi ta kewar momina na kira kuma anki dauka please momy a dau wayata. tsaki naja ji wani wahalallen wayar na kashe na jawo littafina ina dubawa.washe gari bbu wanda ya kula wani tsakani da babs nayi wanka na shirya ina jiran lokacin makaranta yayi na fice na jawo jakata na dauko waya na kunna ban fi minti uku da kunnawa ba naji kira number jiya ce a zuciyata nace bara dan na okey wata ajiyar zuciya naji an saki.uhum my momi laifi nayi akai min wannan hukuncin naji wata daddadar murya ta furta momy ki min magana please ko naji dadi " cikin tsawa nace mallam wrong number ka kira kan yayi magana na katse wayar na mayar jaka ina mita na mike na fita ina fita titi na samu adaidaita sahu,bayan na sauka ina tsallaka na shiga ina cikin tafiya naji magana daga bayana sannu ko nayi saurin juyowa ina kallonta ganin yar uwata ce mace yasa na saki fuska tana zuwa sannu tana murmushinta mikon hannu tace jiya kece aka kawo ki class dinmu koh? ke yar ajince? eh ai tun da aka sauke ki a adaidaita sahu na keta miki magana baki ji ba."
12
MUH'D*ABBA*GANA
09039016969
www.abbagana.pun.bz
kawai naji ta kwanta mina tare muke har muka karasa class din daga baya muka zauna.baki gayan sunan ki ba ta tambayeni tana murmushi oh am sorry,nana safiyya mukhtar nake,kuma gaskiya sunan nice name ni kuma sadiya adam nake da fatan zamu zama kawaye kuma mu zauna da juna tsakani da Allah ina murmushi nace na gode da zabata da ki kayi a matsayin kawa kuma insha Allahu zaki same ni kawa ta gari mai kuma......' malami ne ya shigo dan haka mukai shuru bayan ya gama ya fita na juya ina kallon sadiya kawata.kai karatun jami'a akwai wuya musamman ma course dinmu,kai nana ai irinku karatu bazai muku wiya ba saboda me kikace baya mana wuya? nana kin ban mamaki sosai banyi zaton ki haka ba sai naga kin fi haka" kin fa sani a duhu kai kawata kamar ba kya jin hausa.Allah ban zata kina da kokari ba okey zagina zaki bbu batun zagi sai......"waya tace tayi kara na zaro ta a jaka number jiya naga naja tsaki na katse.a'a kawata sweety ne yayi laifi aka ki daga wayarsa na gwalo ido nace waye kuma seweety Allah ya kiyaye dariya tayi sosai."amma kawata ba zaki gayan gaskiya ba duka duka yau muka hadu,dan haka ake boyan mai tsadar to ni dai shawarar da zan baki karki tsaya jan aji har ajin yazo ya tsinke dan yanzu mu muke da tsada muka ji ance daga bayanmu muka yi saurin juyawa.sadiya ta washe baki tana murmushi yayin da ni kuma na hada fuska ina harararsa.kai mun zuwan bazata saukar yaushe tun dare na sauka kina barci kuma yanzu zan wuce kai yaya dan Allah daga zuwanka,to ka zo ka zauna""ta juya tana kallona lokacin na mai da hankalina kan littafina "nana ga yaya na na daga fuskata ba yabo ba fallasa sannu ya gida? lafiya kawarmu ya karatu? na mike sadiya bara na shiga class okey kawata sai na shigo kan na karasa wayata ta soma kara karo na biyu a fusace na dago wai kai mallam ba nace maka wrong number kakira bane kake ta damuna please sister ki daure ki sauraran "kaga mallam kaje can ka nemi yar uwarka karka kara kiran wayata kayi magana"
abbagana hausa novels@ facebook.
tnx u
ReplyDeletetanxs abba muna jiran cigaba
ReplyDeleteMore greese to ur elbow
ReplyDeleteMuna Godiya Dan Allah Akaramana
ReplyDeleteThanks very much
ReplyDeleteTankk you
ReplyDeletetnxs yaya na
ReplyDeleteAngaida hazikin marubuci.
ReplyDeleteAllah saka da alheri
ReplyDeleteGASKIYA RASHIN KUNYAR NANA YAYI YAWA SOSAI
ReplyDelete