shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 27 May 2016

AMINAN***JUNA 161---180

aminan-juna.jpg

[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA


WISDOM HAUSA WRITERS.




Na Xarah~B~B.


161-165




Faduwar wayar da sukaji ne ya maida hankalin su gare ta, da sauri zarah ta nufI gurin da amrah take jikin ta sai rawa yake yi, ganin zarah zata taba ta yasa da k'ar ta iya cewa "kada ki tabani macuciya, azzaluma maci amana" sai kuma ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, tsaye zarah tayi ganin halin da aminiyar ta ke ciki fuskar ta cike da damuwa, a ranta kuwa tana tunanin wace irin mgn ce FAROUK ya fada tunda shi a tunanin shi itace ta daga wayar, muryar amrah ce ta katse mata tunanin da takeyi tana fadin "kin cuceni kin ci amanata zarah, sakayyar da zaki min kenan? daman hausawa sunce tsintatciyar mage bata mage duk abunda namaki a rayuwa da wannan zaki sakaman?," zarah da tunda amrah ta fara mgn hawaye ke ambaliya a fuskar ta tare da girgiza mata kai amma sam amrah taqi ta saurare zarah" futha ce tayi karfin halin cewa "wai meke faruwa ne Amrah? kun barmu a duhu fa" cikin dasasshiyar muryar ta tace "futha yanxu zarah ta rasa wanda zata cuta sai ni, meyasa tun farko bata fadaman SON SHI take ba? meyasa zarah zata man haka? meyasa take son ta tarwasaman rayuwa? meyasa.............. "futha ce ta katse ta da fadin "wa'annan tmbayoyin naki banida ansar su, me tamaki ne? sa'annan wanene take so?" janjayen idanuwan ta tadago tana kallon ta tace "yanxu ta rasa da wanda zatayi soyayya sai hubby na, Farouk wanda nake burin in aura, ashe daman dalilin da yasa ya chanza man kenan a lokaci daya", "wat?" Inji futha..... Urs Zarah~B~B.




166-170




"A'a amrah impossible, hakan bazata taba faruwa ba, kada kiyi saurin yanke mata hukunci batare da kinyi bincike ba nd duk da kinki fadaman me FAROUK yace a waya nasan ba laifin zarah aciki, kada soyayya ta rufe maki ido ki aikata abunda zakiyi nadama a gaba, kada ki manta zarah nada wanda take su kuma take muradin aure nd......" hannun da ta daga matane yahana ta karasawa "dalla malama ki man shiru bana buqatar jin komai, ke kuma" tare da nuna zarah "daga yau bani ba ke, kar ki kuma nuna kin sanni tunda ke matsiyaciya ce, hmmm.....banga laifinki ba Zarah, laifina ne ai da tun farko na nuna miki soyayya fiye da kaina" Ta inda amrah ke shiga batanan take fita ba duk yadda zarah taso ta saurare ta kin yadda tayi kuka sosai zarah keyi[ni kaina saida na tausaya mata ]


Ranar yadda zarah taga rana haka taga dare sam bacci kin zuwa yayi hakan yasa taje toilet ta dauro alwala ta fara nafila wanda ita kanta batasan adadin ku raka nawa tayi ba, bayan tayi sallar asuba ne ta fara hada kayan ta, cikin sa'a kuwa koda ta fito parlour kofar abude take kasancewar ya affan ya je masallaci, haka ta samu ta fita daga gdn ba wanda ya ganta, tafiya takeyi ba dan tasan inda ta nufa ba haka har gari ya waye keke napep ta samu tace ya kaita tasha.....Urs Zarah~B~B.





WISDOM HAUSA WRITERS.



Fatima~Bello~Bala.
[7:39PM, 5/20/2016] my mtn: AMINNAN JUNA



WISDOM HAUSA WRITERS



Na Xarah~B~B.





171-175




Koda suka isa tasha ba mutane dayawa kasancewar da safe ne, sai zuwa 8 aka fara lodi, tana tunanin kudin motar da zai kaita sokoto, can ta tuna da kudin da ummanta ta bata lokacin da zasu tafi katsina, bayan anqare lodi ne suka kama hanyar sokoto, kallo daya kama zarah kasan tana cikin damuwa.


A bangaren su amrah kuwa, bayan sun tashi basu ganta ba ita amrah ko ajikin ta kasancewar wata tsanar zarah takeji, futha ce ta shiga duba ta har toilet amma wayam ba kowa, a parlour ta tarar da ammi a rikice ta fada jikin ammi, ganin yanayin futha ne yasa ammi cewa " futha lfy naganki haka? , "ammi wlh bamuga zarah ba koda muka tashi ammi kuma duk na duba batanan harda kayanta bangani ba", "innalillah wa'inna'ilaihir raji'un" ammi ta fada "to me aka mata ne wanda zaisa tabar gdn ba tare da bankwana ba?", futha tace " ammi daman jiyane suka samu missunderstanding da amrah", nan dai futha ta fadama ammi duk abinda ya faru, fada sosai ammi tawa Amrah, hakama ya Affan kamar tabbabbe ya zama da yaji zarah bata gdn, ya Affan yayita kiran wayar zarah amma switch off, hankalin shi yayi matuqar tashi har gdn aunty beelert yaje amma Zarah bata can, haka ya dawo jiki ba sukuni, a ranshi yana tunanin ko sokoto taje, da wannan tunanin har baccin wahala yayi gaba shi........Urs Zarah~B~B.





176-180




"Assalamu Alaikum" "wa'alaikun salam..., aaaaaaa mutanan katsina sannun ku da zuwa maraba daku, ya hanya?" " lfy qlw umma" zarah ta ansa a taikaice ummah sake da baki tace " lafiya kuwa naganki haka ina amrah ne? "umma............ "Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi, "wai me akayi ne kike kuka? wani abunne yasami Amrah?" kai kawai ta gyadamata alamar a'a "to meya faru?" tare da janta zuwa daki, bayan ta rarrasheta ne tace ta tashi taje tayi wanka taci abinci sa'annan suyi mgn, "tou" kawai zarah ta iya fada tare ta mikewa, bataji ma ba ta fito bayan ta shirya, a parlour ta same ummah bayan taci abinci ne cikin natsuwa ummah ke mata mgn "zarah kinatsu ki fadaman meya faru? meyasa baku dawo tare da amrah ba"? cikin dasasshiyar muryarta ta fadama ummah komai da yadda ta baro gdn har ma soyayyar su da ya Affan bata 6oyemata ba kasancewar zarah yarinyace ba mai boyema mahaifiyar ta abu bace, ummah ta tausayawa yartata, haka ummah tayi ta ba zarah mgn tare dayi mata nasiha har taji ta natsu


Ya Affan ne zaune a tsakar dakinsa yayi uban tagumi duk ya rame yayi baqi ya lula duniyar tunani, Futha ce takatse masa tunanin shi ta hanyar dafashi da tayi "ya Affan plz kadaina wannan damuwar ka dubi fa yadda ka koma cikin qanqanan lokaci" cikin rashin son maganar yace " sister kenan dole indamu mana zarah ta kashe wayar ta, kuma banida tabbacin sokoto ta tafi fa, gaskia ni sister gobe zanje sokoto can inda Mum din amrah infadamata abinda ke faruwa dan nasan amrah bata fadamata ba, daganan anuna man gdn su zarah, ko ya kika gani?" " ehh bruhh, kuma wannan ma dabarah ce, Allah yasa adace, amma ka shawarci ammi kaji tata shawarar", "ok haka za'ayi insha Allah, amma ni ina mamakin amrah wlh saboda koni da bamu wani jima da zarah ba akwai abunda bazan taba yarda zatayi shi ba, ina gujema amrah ranarda zata gane gaskia saboda yanxu soyayya tariga ta rufemata ido", cikin qosawa Affan yace "uhm Allah yasa ta gane gaskiya, amma kam Amrah tayi butulci, ta ha'inci zaman tare, sai kice dai ba AMINNAN JUNA ba? A yanda naji labarinsu fa tun suna yara suke tare, aikuwa yaci ace sun fahimci junansu, su gane abnda ko wacensu zata iya yi.........Urs Zarah~B~B.






WISDOM HAUSA WRITERS.




Fatima~Bello~Bala
Share:

1 comment:

  1. Abubakar Ibrahim4 June 2016 at 15:35

    Kinyi gaugawan yanke hukunci AMRAH

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).