shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday 27 March 2016

BANA KAUNARKA 41 & 42

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

41-42

MUHD*ABBA*GANA 09039016969 -------------------------------------------- baba rabi'u shi ya biyu musu sadaki kowannan su dubu hamsin hamsin (50,000) haidae kuma small boy shi ya hada musu lefe akwati shida shida manya masu tsanin kyau sai sabuwar mota kasaitacciya kirar zamani kai gaskiya koni na yaba haidar domin yayi bajinta sannan na jinjinawa ya al'amin domin shi ya zubawa kannansa kayatattun kayan kicin na azo a gani,ya faruq kuma yayo musu kayan daki ita kuma mai taji da gyaran jiki yaranta takanas ta tura sokoto aka samo me gyaran jiki sannan akwai wata makociyansu yar maiduguri ita tayi rawar gani wajen fito da yaran mom din ina zaune mom ta shigo na kalle ta fuskanta dauke da damuwa,nace nifa mom ban gane ba ni ba amarya ba amma komai sai a dinga yii min irin na amare,anya mom ba wani abu kuka boye min ba? mom ta gyara zamanta tace auta kenan,ai abin da yasa kika ga ana muku haka don anga ku yan biyu ne ya zama dole kome akai miki ayiwa yar uwarki domin tare aka haife ku na kalle ta au shi yasa naga komai ana mana iri daya nifa abin ya daure min kai shi yasa lokacin da yan katsina suka zo naji sunce min amarya,amaryar shahid ni fa ina jin haushin in aka hada ni da shahid to ai ko shima haka abokan wasanku zasu ce masa domin sunga ku yan biyu ne ni dai gwanda a hada ni da wani sam bana so ana hada ni da shahid.......na fafa miki abokan wasa sai hakuri in fa kika nuna musu ba kya so sun dinga ce miki kenan gwanda ma ki saki ranki ki dauki komai ba komaiba nai murmishi farin ciki nace ni kuwa har gabana ya soma faduwa,amma yanzu naji dadi sosai domin na fiso ku barni inyi karatuna mom ta rungume ni tace zakiyi alfahari damu auta.yau saura kwana biyu daurin aure yaune kuma muka shirya zuwa gambu gurin su mom kasancewae mu rubuta komai mun amfani da direban gidanmu domin shima dan gyanmbun ne sai dai wani abu da baku sani ba,ko da wasa bamu sanar dasu mom ba bbu wanda ya san da tafiyar sai nida mahida,ya amin ya faruq sam bamu sha wahala ba wajen gani gidan kasancewar mahaifin mom fitace ne sannan gidansu bac wani boyayyan gida bane in kace gidan tsamiya koda titi ne to za akai ka gidan,munyi sallama dan ma dai dakin gidan mai yar katanga wadda duk rabin gidan ya rushe sai dai an gyara shi ta hanyar jera wasu karare,kallo daya zakai wa gidan kasan mutanen gidan suna cikin kunci talauci munyi sallama turus mukai fakin a zaure domin wata tsohuwa muka gani tanawa wani tsoho fifita zaune suke a soron suna shan iska sai dai da alama wannan tsoho bashi da lafiya domin gaba daya ya koma kalar tausayi,tsohuwa tace sannunku da zuwa yan samari ciki ta koma ta dauko mana taburmar kaba ta shimfida mana muka zauna ta kawo mana ruwa mai sanyi muka sha sannan muka gaishe ta muka gaida wannan tsohon ya amsa da kyar da alamu yana jin jiki mu kai masa sannu matar ta zuba min ido kafin daga bisani tace yan mata yan samari daga ina kuke don Allah ina kuke?

Abbagana hausa novels @ facebook.

www.abbagana.pun.bz

bana-kaunarkajpg.jpgbana-kaunarkajpg.jpg

Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).