shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday 18 March 2016

BANA KAUNARKA!!! 37

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 37 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- kamar yadda nake yi a makaranta sam bana kula samari kai hadda dattawan na kance ammin mji,amma an kusa bikina in naga zaka takura min in ma fata-fata.salamu alaikum,sai dana dan firgita domin ban san zuwan sa ba amin wa'alaikas salam,ya tsungunno sannu bebi ni sunana umran s sulainman tunda kuka shigo gurinnnan na kasa samun sukuni ina son inyi miki wata magana sai dai ki min kwarjini maganar gaskiya naji na kamu da sonki nai murmushi nace ah maganar gaskiya sai dai kayi hakuri domin tuntuni am mana miji ya wani zabura kin san koni waye? nai masa kallon sama da kasa ba shi da wani kyau na tabe baki yace waye shi wanda aka zaba mikin kin san Allah zan iya gogawa dashi nai murmushi na rasa wa zan ce masa sai dabara ta fado min nace ka san shahid yaro dan kwalisa,wai bomboy kike nufi nace ashe ma kasan shi gani nai ya sara min yace na barki lafiya nai murmushi,ina nan zaune sai ga wani guy yace sannu hajiya nace yauwa alhaji to ni sai sunana small ismail na jima ina ganinki sannan na dade ina fama da sonki domin na fuskanci ke yarinya ce nitsattsiya nayi bincike akan gidanku mahaifinku mutumin kirkine,da fatan zaki amsa tayina to mallam small na gode ainun batun so kuwa nima ina sonka da wannan damar kuma nake baka hakuri domin maganar gaskiya am min miji na gode da kika fada min gaskiya don Allah ya sunanki "wahida sulainman muhd,to wahida na gode. wani guy yazo yana zuwa bbu wata sallama ya tsunguna gabana sannu bebi ban kalle shi ba nace bomboy ya kamata mu tafi gida what me kika ce? nace sorry na dauka shahid ne what ina kika san bomboy? nace ban gane ba ai yau saura wata biyu bikinmu kina nufin ke bomboy zai aura,ko ba mu dace da juna bane? no ba haka bane ina mamaki to ko za kai takara dashi ne? no ni da bomboy bama haka na hakura.wani guy ne ya nufo ni hadda masu take masa baya tun kan ya karaso kamshin turaransa ya cika gurin yana zuwa ya tsunguna ya kamo hannuna wata wawuyar sumba ya kai min na kuwa tofa masa yawu tare da fizge hannuna a fusace,nace kai wanne irin dabba ne a fusace shima ya mike yana shirin sharara min mari aka rike shi ta baya,yana kar ka taba musu bebi ka barni in duke ta in yaso inga uban da ya tsaya mata,ita kuwa take da mai tsaya mata kasan ko waccece kar ka yadda ka tafka abin kunya,domin wannan yarinyar kanwa ce ga abokinku bomboy,sannan ta wani bangaran mata domin an kusa bikinsu.....ido ya zuba min da alamu kunya ce ta kama shi na mike da sauri na bar gun,gun motar mu na koma abin haushi har gun motar aka dinga bina raina ya baci na kudirce a zuciyata ni da zuwa fati sai de a aljanna.yaya ni dai gaskiya zan tafi amir yace haba anti wahida ko dan kinga bomboy baya gurin nai murmushi nace ai yanzu muka gama magana ta waya da shi sai sa ma ban damu ba, Abbagana hausa novels @ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

7 comments:

 1. Allah saka da alkairi

  ReplyDelete
 2. Allah kara basira

  ReplyDelete
 3. ayya a karasar mana

  ReplyDelete
 4. tun jiya muna jira yau kuma daya a kasa mana

  ReplyDelete
 5. dan Allah akarasa mana kaunace sila pls

  ReplyDelete
 6. godiya dubu aci gaba

  ReplyDelete
 7. Nice Story

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).