shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday 17 March 2016

BANA KAUNARKA!!! 35

bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 35 MUHD-ABBA~GANA 09039016969 -------------------------------------------- mahida ta mike ni na gaji da jin wannan labarin ya amin yace don Allah zauna mahida mu gama ji ma na muji karshen toni yaya haushin jauro nake ji nai dariya nace ai kuwa babankine tunda mijin babarkine Allah ya sauwake talakan sai,ya faruq ya harzuka tuni muka yi shiru mom taci gaba. koda na kulle mata na kuma kashe kunamar na shafa mata ruwan sai taji dadi har tace in kwantar da hankalina zata kubutar dani nace na gode,amma don Allah ta bari a yankani domin in na fita ban san inda zani ba,ta girgiza kai tace ba zan bari ba yanzu shekarunki nawa? nace sha uku domin shadaya akai min aure gashi ina da shekara biyu ta sani a hanya har titi sai sai sam bana cikin hayyacina,saboda haka wata mota na zuwa tai gaba dani daga nan ban san me ya faru ba illa na farka na ganni a wani kayataccen guri ina bisa gado me dan karan laushi,sanyin AC da kamshin wani irin turare....wata farar mace sanye da farar kaya ta shigo tace min sannu,nace yauwa ta min aune aune sannan tace me yake damunki yanzu na nuna cikina tace wannan sai a hankali saboda barin da ki kayi cikin jikinki ya zube,ku tashi kuyi sallaha ina yaso sai in karasa muku,wayar mahida tai kara ta dauka haba kinga na kalle ta haka aka iya soyayya Allah ya shirya ku,ku ko gajiya bakwa yi,to ina ruwanki ni bana son shiga sharu ba shanu la!! ya amin ka ji tace min shanuwa ko,yi hakuri ke mahida kar ki kara ce mata shanuwa,don Allah ya faruq kaji nace mata shanuwa? ke ni kar ki dame ni ku kenan fada kamar kaji. ina kwance jikin mom suka soma shigowa mom taci gaba,matar na tambaya don Allah a ina nake tace min a kano tace wanda ya kawo ki anjima zai zo nace to.da yamma ina zaune yayi sallama saurayine kyakkyawa in kunga al'amin kun ganshi hannunsa ya zuba cikin aljihu yana kallona na sunkuyar da kai tare da gaishe shi ya amsa yana me tambayata jiki nace da sauki,yace baki sani ba ko na daga kai ya ce nine wanda na bige ki a kaduna sai dai ina sauri ban tsaya a asibitin can ba,na kawo ki nan ni sunana sulainman muhd radda,mahida tace iye iye abban mu ne fa ya faruq ne ya doketa.koda ya bukaci jin labarina ba abin dana boye masa ya tausaya min haka ya dinga ziyarata wataran yakanzo shi da kanwarsa khadija wataran kuma shi da babarsu koda aka sallame ni ma gidansu na koma kanwarsa khadija na soma sani kuma tana hidima dani haka mahaifiyarsu sam bata nuna min kyama na basu labarina ta tausaya min sannan tai min alkawarin rike ni fisabillilahi sai dai me koda yayansa ya dawo ya samu labarina akai masa bayani ai sai ya dinga bala'i muddin yana numfashi sai na bar gidan hakan kuwa akayi sai da yaya yasan yadda yayi ya fitar dani,na rasa inda zani gani dai naje titi amma sam na kasa tsallakawa,sai kalle_kalle kawai nake,oh ni Allah kai min magana wata mota ce irin ta sulainman tai fakin kusa dani mai motar ne ya fito ya jima yana kallona da alama yana mamaki ganin ya juyar da kaina bani da niyyar yi masa magana sai ya karaso, Abbagana hausa novels@ facebook. www.abbagana.pun.bz
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).