shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 4 June 2016

WAYE SANADI?? 25 & 26

waye-sanadi.jpg

WAYE SANADI?

25


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz


mom kar ki kara gayan sunan nan jiya sai da aljani ya kira ni da haka waye kuma aljani? ta tambaya cikin mamaki kan tayi magana wayata tayi kara lokacin tana hannun sadiya tayi saurin miko min kinga ko shine daman yace duk inda nake yana tare dani jiya har kiran sunanki yayi sadiya kirji ta dafe na shiga uku nana dole kawancen mu ya rabu yanzu dai ki daga nana dan shine kika zo makaranta kina kuka, zan je china nan da minti biyu xan kira ki kan tayi magana ya katse na juyo ina kallon sadiya fuskata cike da hawaye kinji abinda yace naji amma ni kuma bazan karba dan bazan iya magana da aljani ba gara ki ce masa bana nab ko ki bawa momin ki Allah ya kiyaye kinga tafiyata,please sadiya ki rufa min asiri kar ki sa ya kashe ni dan girman Allah ki karba ke baki san halin aljani ba kawai ya sanyen baki da jini kema ina jin sonki yake shi yasa ya kyale ki amma ko rashin kunyar da kike masa a baya da tuni ya kashe ki sadiya na roke ki ki min wannan taimakon in.....kan na karasa ya kara kirana a waya yayi daidai da zubar fitsari abin harya bama sadiya dariya ki bani sadiya yana kallonki dan Allah ki karba ta karba ta daga wace ke magana? kai tsaye imran aljani ya bata amsa to ya kake ya kuma yan uwanka aljanu kuma mai kake nufi da kawata "can kuma ta rafka salati Dan Allah kayi hakuri zata daina kar kamata haka wallahi zata daina ka ci gaba da kira kuna gaisawa to na gode na gode kuma insha Allahu tunda kana ganinta zata daina bayan ta gama ta juyo tana kallona wallahi nana Allah yana sonki amma da tuni sunanki gawa sadiya me nayi masa wau tunda ummank tayi aure kike bata mata rai sannan kakarki bakya ragwanta mata ga mijin ummanki bakya ganin girmanshi "bai isa ya canzan rayuwa ba duk abin da zai min yayi na daina tsoronsa shi din me Allah ya fishi yafi waninsa "ke nana kin san me kike fada yana fa ganinmu, yayi abinda zai yi,nana ki nutsu dan Allah ba zan nutsu ba,ki kaini gida zan kaiki amma ki nutsu kiyi shiru kinga fa mutane suna kallonmu,in bazaki kaini gida ba zan tafi ba zaki kara ganina ba har abada.


Abbagana hausa novels @ facebook.


WAYE SANADI?

26


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz


kokarin bude kofar nake tayi saurin rike ni nana dan Allah karki bude bani key din naja mu tafi, sadiya me yake faruwa? naji maganar saifu yauwa saifu taimaka min kakai mu gida nana ce bata da lafiya ya salam ya furta da sauri ya shiga motar sannu saffiya ban iya ce masa komai ba saboda kaina da yake azabban ciwo,sadiya kaina zai cire ki taimakeni ki kaini wajen ummata safiyya kiyi hakuri mun kusa zuwa saifu ya juya yana kallon sadiya komu kaita asibiti 'banso kawai ku kaini gida kona fita saifu dan Allah wai ka kaimu gidan jawo ni tayi jikinta nana gidan zamu kiyi shiru kanmu karasa barci mai karfi ya dauke ni a hankali na bude idona ummata na fara gani a zaune kaina yana cinyarta sannu nana ya jiki? umma naji sauki umma waye ya kawo ni gida? kawarki sadiya da kuma wani,kan nayi magana aka turo kofar aka shigo sannu ya me yake miki ciwo? bbu komai naji sauki Allah ya karo sauki amin, munyi waya dasu suna gaisheki kansu zo "na daga kai umma yunwa nake ji tayi saurin mikewa ta fita kira daya ta yiwa wayar ta shiga hello sadiya kina lafiya lafiya klau imrana ya safiyya maganarta na kira nayi maka okey ina sauraronki "gaskiya imrana ka daina kiran safiyya kana tsoratata yau baka ga tashin hankalin da muka shiga ba a rude yace me ya sameta? take ta kwashe duk yadda abin ya faru cikin damuwa yace to sadiyya ya zanyi ina ganin ka bayyana mata kanka haba sadiya kinfa san halin kawarki kinsan bazata taba karba ta ba to gaskiya ka dai dakata da kiranta ka canja shawara shi kenan sadiya na gode.
washe gari ban je school ba misalin sha biyu sadiya ya ta leko bayan sun gaisa da umma ya juyo ranki ya dade ke fa ake kira da sauri na juyo nace ko dai maryam ke yace dan jiya ma shi ya kawo ki okey kace ina zuwa na juya wajen umma bara naje ki gaishe shi kuma kiyi masa godiya.


Abbagana hausa novels @ facebook.
Share:

9 comments:

 1. Ummu Amaturrahaman4 June 2016 at 07:37

  Ahaaa Aikin Ka Nakyau Muna Jira

  ReplyDelete
 2. Thanks muna jiran sauran pls.... :)

  ReplyDelete
 3. Abubakar Ibrahim4 June 2016 at 15:18

  Muna biye da kai sauda kafa

  ReplyDelete
 4. Karyadaina bata tsoro

  ReplyDelete
 5. Wai kulafia? Abba

  ReplyDelete
 6. Tnx abba muna biye

  ReplyDelete
 7. MUNGODE LBR YAYI DADI SOSAI

  ReplyDelete
 8. a bata tsoro tnxxxx

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).