Thursday, 19 January 2017
Wednesday, 11 January 2017
Ashe kishiyatace
Tuesday, 3 January 2017
Waye Sanadi?? 100 (karshe)
💘WAYE SANADI?💘 1⃣0⃣0⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Mun sauka Kano ranar da za a yi dinner sai da na fara zuwa gidansu Momy da Sadiyya, sannan na tafi gidan Baba. Duk inda na sa kafa nan Imran zai sa tasa har muka tafi gidan Abbana. Na yi matukar farin cikin ganin Ummata. Bayan na gama cin abinci ina tare da Hassan Imran ya shigo dakin da nake Safiyya amaryar Imran kamar yau aka yi tamu dinner ana hararata tare da takan 'yanyatsu Na ce Me ye haka kai kai ka fiya tuna baya, wacce irin kulawa ce bana baka? Ya zauna kusa da ni, ki yi hakuri Safiyya Abba ya hana zuwanki dinner. Na dago da sauri kar ki damu mu yi zamanmu nima babu inda za ni, mu yi zamanmu mu yi tamu dinner mai tarin lada. Na dan yi murmushi Nima bana jin dadin jikina tunda za mu taho marata take ciwo Ya mike da sauri, 'Ban san shirme baki da lafiya tun safe baki gayan ba, ta so maza mu tafi asibiti cikin sirri kamar unguwa za mu, tunda daman da kayanmu a mota Ban yi musu ba na bi bayansa muka fita, don nima marar tawa dada takuran take. Ya yi kiran Doctor Khadijah ya tambaye ta tana asibiti ko gida? kai tsay asibitin Nassarawa muka nufa. Awa biyu da zuwanmu cikin iko na Ubangiji na haifi yarinyata mace. Imran ya rasa inda zai saka kansa saboda farin ciki. Ya shigo dakin hutun ina zaune na zubawa bayna ido cikinso da kauna. Duka awarmu biyar a asibitin muka fito tare da dankareriyar kyautar da Ubangiji ya yi mana Iokacin da muka shiga gate din gidanmu Abbana ne a zaune su da Abban Imran Lokacinda Abba ya ga na fito dauke da yarinya a hannuna bai san lokacin da ya mike tsaye ba Dadyn Imran ya ce Kai Imran yarinyar wace ce? Ya karasa yana dariya ya ce, “Dady ‘yar Safiyya ce daga asibiti muke ta haihu Duk wanda aka gayawa haihuwata ba karamin mamaki yake ba, haka ‘yan party da suka dawo. Ina gani aka tafi aka kai Momy da Sadiya gidajensu. Ba mu yi wani gagarumin taron suna ba sai walima da muka yi. Baby ta ci sunan mahaifiyar Imran Amina. bayan na yi arbain na koma gidana wanda ba mu da nisa da Rukayya illa Sadiyya da take Kano. Zaman da kauna muka shiga shimfidawa. Aminatu ta taso cikin kulawa da soyayya daga kowane bari Alhamdulillahi. Nan na kawo karshen wannan labari nawa mai suna *💖Waye Sanadi?? 💖* *SADAUKARWAR: Na sadaukar da wannan littafin ga masoyana* GAISUWA TA MUSAMMAN A GAREKU 🍄Raheem Jega 🍄Baby Afreen 🍄Hajiya Zahra B.B 🍄Abdul mr smile 🍄Abdulaziz A.A J 🍄Mrs Bilkisu 🍄Kurratulayn 🍄Herleematus Serdeeya 🍄Billy gero 🍄mrs umar 🍄Hauwa jabo 🍄Autan Hajiya 🍄jeedah aleeyu BAN MANTA DA KU BA ... . ➡ONLINE HAUSA WRITERS ➡HOME OF NOVELS ➡NOVELS ➡Hype Hausa Novels ➡ Novels Only ➡ Duniyar Marubuta ➡Home of Nobel ➡Hausa novels ayau Members na group na 📚HOUSE OF NOVELS 1-5📚 da dukkan wanda ban ambata ba nagode INA MIKA SAKON GAISUWATA GAREKU MASOYA NA ALLAH YA SADAMU DA ALKHAIRINSAH *💖Muhammad Abba Gana💖* *09039016969*
Waye SAnadi?? 91 --- 99
[12/27/2016, 10:03 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
9⃣1⃣ & 9⃣2⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
Gadan-gadan su Momyn Yusuf suke shirin biki haka su Abbana, har mun fara ba? Can ma Nassarawa haka suna shirin bikin jika Imran mai masoya da yawa. Yau Momynsa ta taho daga Lagos tare da tawagar ‘yan uwanta da kuma kayan lefe, wanda ya zama kaso
uku ga tun na farko da Imran ya ban ga Alhajin Nassarawa shi ma ya ha?a nasa ga kuma na Abbana, haka duk aka hadu aka kawo gidanniu kaya na ban mamaki, tun kan su kawo Hajiya (Mahaiiiyar Momy) ta gama yi min tanadin duk wasu kaya da zan saka tun da farkon bikin har zuwa karshe?.Ana gobe za a fara biki sai kusan karfe tara muka shigo gidan a gajiye tun safe muka fita kunshi da gyarna gashi. Duk wannan yawan tare da Yusuf da Salim muke
yinsa ni dai ido ne nawa, don zuciyata cike da mamakin ina lmran ya shiga. Abu daya na fuskanta kullum sai sun yi waya da su Sadiya barin ma ?annansa su Khadijah wanda komai tare muke yi,Muna shigowa muka zarce dakinmu, Salim ya tsaya a falon wajensu Baba Sadiya
yana aikin nasa (tsokanarsu). Muna shiga na fa?a kan gado tare da fadin. “Wash! Allahna Sadiya ta dan harare ni ta ce, “Sai ka ce wadda ta yi aikin wahala."Momy ta ce, “Kya ma tashi da mun yi sallah za mu tafi kar6o aikin dinkunanmu.” Na zaro ido waje na ce, “Da waza ku karbo ?inkin? Aysha ta ce, “Da Anty Safiyya.Da sauri na ce, “Ai wailahi sai dai
in ba za ku sa kayan ba, ni kam babu inda zan ?ara fita.’ Na dan juyo ina kallon Khadijah wadda take ta shafa kunshin kafarta. Na ce, “Khadijah ko ke ma za ki kar6o dinkin? Ta kama girgiza kai “Hum Anty na gama fita ni da fita sai gobe, in za mu tafi dinner, tunda nake ban ta?a gajiya irin ta yau ba, ita daman Aysha ta saba tafi haka tunda ita ma ‘yar kano ce.” Momy ta kalli su Sadiya ta ce, “Bara na yi sallah sai mu je don sun san sun kama komai a hannunsu.” Ta mi?e ta yi cikin bandaki.Bayan fitarsu muna zaune da Khadijah muna cin
abinci babu abin da take sai yabon UMMIN BABA mai kunshi take. Ni dai dariya kawai nake mata na dago kaina ina kallonta. hadijah baki taba kunshi mai kyan haka ba ne?Ta ?an yi
murmushi, ‘Allah Anty ban ta?a yin mai kyansa ba, sai wata ran da na zo Kano muna biki aka yi kiran RUMA kawar wata ‘yar uwarmu ce ita ma ta iya ?unshi, har yaya Imran ya ce in dai a yi aure zai dinga kawo matarsa ana yi mata. ?azu ma da muka yi waya na gaya masa kunshinki ya yi kyau shi ne ma na dauki tafin ?afarki a hoto na tura masa.?an na yi magana ta mi?e ta shiga bandaki. Tana shiga wayarta ta yi ?ara na yi shiru ina sauraran muryar Imran tana karatun Al?ur’ani
mai tsarki cikin taushin murya wanda khadijah ta yi recording din ta kuma dora a ringin tone nata, har ta katse Kadija bata fito ba. Aka kara kira karo na biyu na ji muryar Khadija tana cewa. ‘Anty Safiyya ki daga.” Ba don raina ba na daga wayar na kara a kunnena. Na yi shiru ina sauraren mai zai ce.“My sister ina ta kira baki daga ba ko aikin tsaran lafiyar NANAH ne ya hana ki dagawa?”na ce, ‘khadijah tana toilet. ’ Cikin sauri ya ce, “Safiyya ce? Na daga masa kai kamar yana kallona. Kin yi shiru Safiyya kina lafiya?” Na dai yi shiru na yi shiru ina sauraran muryarsa na kuma kasa katse wayar. ‘Safiyya ki yi magana ko ba kya jina? “Ina jinka mana.” Ban san lokacin da bakina ya
furta haka ba.Na ji sautin dariyarsa. Safiyya kina nan kalau, ya su Abba? ?an na yi magana Khadijah
ta fito na yi saurin mika mata wayar.“Hello Yaya.”Da sauri ya ce, 'A’a Khadijah ina Safiyyar?”
Ta kwanta barci ne ‘Sister ban san karya.‘Allah yaya da gaske nake yau mun gaji da yawa.Okey kara mata wayar a kunne zan mata magana Ta karaso wajena ta karan wayar a kunne na ji muryarshi mai cike
da tarin sanyi.“Safiyya ki karbi wayar mu yi hira ga abokaina na duk suna gaishe ki suna dokin gobe ta yi su ga tauraruwar Imran.” Ya ?an yi shiru ya ji mai zan ce shiru babu maganata.
Don Allah Safiyya ki min magana ko na ji dadi.Na ce, “Don Allah ka rabu da ni barci nake ji fa. Ya sauke numfashi da sauri, ‘Shi kenan Safiyya Allah ya tashe mu lafiya na ji da?n hakan ma da ki ka gayan ki yi barci mai dadi tare da mafarkin mijinki mai kaunarki Imran.” Yana fa?ar haka ya katse wayar. Na lumshe ido ina murmushi, Khadijah ta ce, “Anty ki ri?e wayar na yi sallah tunda na ga hirar taku ta yi dadi Na bude idona da sauri na ?an yi murmushi na ce, “Ai mun gama hirar ta ma katse.Gaba ki daya cikin yini daya za a yi bikin a gama sai kuma in mun tafi can Lagos ?n Momy za ta yi nata.
***Washe gari****
karfe sha biyu su Imran suka sauka tare da abokanansa gidan Baba suka sauka. ?arfe shida za a tafi dinner wanda gidan
Abbana tun safe suke bikinsu, ‘yan uwan sa dukkansu sun zo sai faman girke-girke suke. Ni kam tunda na
yi wanka Hajiya (Mahaifiyarsu Salim) ta shirya ni, ni kaina na san na yi kyau. Momy ta shigo da saurinta
tana waya na dago ina kallonta.Me ye haka ne tun dazu ana kiranki, to Abba ya ce ki fito ki yi wa su Imran barka da zuwa Gaskiya Momy ba zan iya zuwa ba Okey bara na gayawa wanda ya turo ni Ta juya za ta fita na yi saurin ruko ta Yi ha?uri Momy bara na zo sai mu je ki raka ni Tare da Momy muka shigo sitroom din tana gaba. Su wajen goma sha biyar ne a zaune, kallo daya za ka yi musu ka san boko ta ratsa su, duk na diririce na rasa
ina zan zauna (Abin ka da wanda ba ta saba shiga mutane ba)„ “Ahmad bawa amaryar ta mu kusa da angonta ta zauna. Na ji wani daga cikinsu ya fada, wanda ya kira da Ahmad ya mike yana murmushi ya karaso gabana,‘Amaryarmu ga waje. Yana maganar yana nunan kusa da Imran.Na dan juyo ina kallon Momy muna hada ido na karasa kusa da Imran na zauna. Gaba daya rabin jikina yana jikinsa, tunda kujera ce mai cin mutum daya. Wanda ya yi magana da farko ya zaro camera a aljihunsa yana dariya ya ce, “Ya kamata mu fara hoto tun annan , don ina ganin kyan da ku ka yi yanzu ba ku yin shi
a wajen dinnar ba Momy ta ce, “Wa ye ya gaya maka ha'ka? Ni kuma ina tunanin in ka gan su a wajen dinner ba za ka gane su ba.” Wani daga cikinsu ya ce, “Gaskiya Faisal ka fara hoto tun a nan saboda ina ganin ba za su kara kyau
kamar na yau ba.Ni dai kaina yana kasa ina wasa da zobunan da suke hannuna. Shi ko Imran kai faman bude hakora yake, ya kuma kara shige min. Sun jima suna hira da Momy har su Sadiya suka shigo. Ana hita na ji muryar imran a hankali ya ce….
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/28/2016, 10:33 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
9⃣3⃣ & 9⃣4⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
Safiyya kin yi kyau sosai kunshin ya yi miki kyau.Na dan kauda fuskata ya kara
matso da fuskarshi saitin kunnena Don Allah ki yi min magana na ji zazzakar muryarki da take dimauta ni Cikin dabara nasa hannuna a tsakanin jikinmu na
dinga ture Imran, amma ina, ina ture shi zai dawo ya kuma nanike mini. Na dago
ina kallonsu Mommy wanda kwata-kwata hankalinsu baya kanmu hirarsu kawai suke tare da abokanan Imran, na juyo ina harararsa a hankali na furta.Allah zan mare
ka.Ya zaro ido waje kamar za su fado yana murmushin da yake karawa fuskarshi kyau
ya kuran fuskarshi.My lovely wife Bismillah. ” Na daga hannu da nufin na mare shi ya rike hannun ya dora a kan fuskarsa ya dan daga murya yace Bismillah My wife
Momy ta dago tana kallona, haka su Faisal, ban san lokacin da na hau shafa fiiskarshi ba. Ya saki hannuna yana murmushi ya ce Faisal ban da sa ido.” Suka dan yi dariya. Ya
juyo yana kallona, ‘Kin goge mini?” Na daga masa kai ina murmushin dole.karfe shida da rabi su Imran suka kawo motocin da za a dibe mu don zuwa dinner. Tun karfe shida Hajiya Mahaifiyar (Momy) take aikin yi min kwalliya duk ‘yanmatan da za su je an debe su ya rage
daga ni sai Sadiya don har Momy ta tafi.Karfe bakwai na fita mu da Sadiya. Motoci biyu ne a wajen, Salim da Faisal (Abokin Imran) suka taso da saurinsu. Ya take mana baya har muka karasa gaban bakar Hummer Jeep ya bude mana yana ciki a kishingide yana amsa waya jikinsa
ya yi kyau cikin wani lallausan faria yadi, wanda ya dace da kalar fatarsa. Hular kansa irinsu daya da gwaggwaron da yake kaina. Ana budewa ya juyo yana kallona fuskarshi cike da
wani kyakkyawan murmushi na kara hade fuskata ina harararsa. Ina shiga Faisal ya rufe ya
zagayo ya tashi motar. Imran ya matso kusa da ni yana murmushi.‘kanwata kin yi kyau har kin tsorata ni, kishinki ya cikan zuciya har ina ji kamar mu fasa zuwa dinner nan bana san kowa ya gane min kyakkyawar fuskar nan taki.Yana magana yana gogan kafarshi na daga takalmina na danne ta ya saki wata siririyar kara tare da kama hannuna ya rike gam na dago ina kallonsa
nace “Allah in ba ka sakar min hannu ba zan gayawa dady na ce na fasa zama da kai tun jiya ka ke takuran.” yasaki hannun yana dariya.“sorry Sister.Har muka karasa wajen dinner babu wanda
ya kula wani, motarmu na tsayawa su Momy suka taso, Faisal ya budewa Imran, Khadijah ta bude min. kai tsaye ya zagayo barina muka jera dan shiga wajen ya zuro hannu zai kama hannuna na aika masa da wani mugun kallo ba shiri ya wayence da karbar jakata.Sai karfe sha biyu muka tashi tunda muka shiga nake kuka Imran duk hankalinsa ya tashi, sai tambayata yake dalilin kukana. Na yi masa shiru har muka karasa muna yin parking na fita. Ta sitroom na shiga dakin Abba ya dago da sauri yana kallona na karasa gabansa. ‘Lafiya ki ke kuka?’ Kan na yi magana ya mike ya fita suka shigo tare da su Baba Binta. Har wajen karfe daya ina dakin suna min fada tare da nasiha zuciyata ta yi sanyi. Lokacin da na shiga dakin duk sun yi barci. Na shiga na dauro alwala har karfe uku ina kai kukana wajen Ubangiji Allah ya samin kaunar Imran a zuciyata. Wayar Aysha ta hau kara, na mike na dauko, ina kallon sunan Imran har ta zama missed cail. Ina shirin ajiyewa aka kara kira na daga na yi shiru na ji muryarsa.
Aysha wace ce a dakinku take sallah?” Na yi shiru ina jinsa.Hello Aysha ba kya jina? Hello Aysha ba kya jina? Muryata a dashe na ce, Aysha ta yi barci fa. Safiyya ba ki yi barci ba? Na daga kai kamar yana kallona.“Hello Safiyya ki yi magana mana? Na ce, “Ba na daga maka kai ba Ya dan yi dariya har na jiyo sautin dariyarsa ta fito cikin wayar.Ya ce, “Kin ga bana ganinki balle na ga lokacin da ki ka daga kan ba, ko za ki zo mu yi hira? Da sauri na ce, Allah in ba ka fita a rayuwata ba zan fasa zaman da kai, kar ka yi tunanin in na zo gidanka zan kaunace ka, zuwana gidanka kamar dada karan tsanarka a raina ne, na ga kana wani rawar
kafa da ni, to tun wuri ka fita a hanyata zan zo gidanka don zaman wacin-gadi zuwa lokacin da za ka gaji ka sake ni. Tun farko ban 6oye maka ba, na tsane ka, bana sonka, bana kaunarka, ba kum Wata mahaukaciyar tsawa ya dakan ba shiri na cire wayar a kunnena na ji muryarshi. Nima na tsane ki, bana sonki, kina so ki samin ciwon zuciya ne za ki sha azaba muddin ki ka shiga hannuna Yana fadar haka ya katse wayar.Tunda gari ya waye muka je muka gaisa da Abba
nake cikin dakin har karfe bakwai, lokacin da za mu tafi dan Lagos gidan Imran. Baba Sadiya ta
shiga da saurinta.“Wai Muntari hirar mai ku ke haka ta shirya mu tafi.Abba ya mike “Ina kara mata fada ne, Safiya ku je bara na yi wanka sai a kai ta can dorayi wajen Rukayya daga nan sai mu wuce filin jirgi.karfe uku muka sauka a Lagos motoci hudu daga gidan su Imran aka turo da su. Tun da muka taso babu abin da nake sai aikin kuka, su Baba Laure suna rarrashina har sun gaji sun yi shiru. Su Momy daman ba su zauna a kusa da mu ba. Kai tsaye gidansu muka nufa wanda yake cike da yan biki, tunda ita yau take nata bikin.Su Baba na hutawa suka tafi ganin dakin amarya. Hajiya Amina
ta shigo fuskarta cike da murmushi ta karaso gabana.“Haba ‘yata me ye abin kuka ko ba kya san zaman
Lagos? Na girgiza kaina. Ta kara cewa, “To ba kya san zama da Imran ne?” Na kara girgiza mata kai.
To ki yi hakuri ki bar kukan nan kar kanki ya yi ciwo in ba kya so a kai ki can ki gayan sai ki yi zamanki a nan, in kuma kewar gida ki ke? Na daga mata kai. tayi murmushi Ki yi hakuri nan ma kamar
gidanku ne duk abin abinda da imran ya yi miki ki zo ki gaya mini, ki kwantar da hankali ki sawa ranki kamar kina tare da iyayenki Na daga mata kai.‘Yauwa Safiyya ki yi shiru duk sati zan zo na ganki, haka Alhaji ma.” Ta mike. “Bara na kawo miki abinci.karfe goma aka sada ni da gidan Imran da yake
bictoria Island. gida ne mai kyau madaidaici, plate house mai dauke da yalwar farfajiya, wanda aka kawata
da kyawawan shuke-shuke. Daga shigarka kyakkyawan falo ne mai zurfi dan kuwa sai ka taka matattakala
kafin ka sauka ciki. A nan ne kuma duk wata mahada take. dakunan barci guda biyu kowanne dauke da
toilet da kitchen wanda aka yi mutukar kawata shi da kayan ado. Bayan gidan madaidaicin lambu ne mai mutukar kyau da ban sha’awa.Tun bayan tafiyarsu Momy nake aikin kuka, ga shi gidan abin tsoro unguwar shiru. Tsoro ya cikan zuciya na ci kuka na gaji sai faman sauke ajiyar zuciya nake. Sai karfe goma sha biyu ya shigo gidan, ya shigo dakin tare da sallama. Ya karaso gabana ya zauna kusa da ni, shiru kowa da abin da yake sakawa a ransa.Ya daure muryarshi na rawa ya ce, “Safiyya ki bar kukan nan kar kanki ya yi ciwo.Kamar ya zuga ni na bude wani shafin sabon kukan. Ya yi jugum yana kallona, kwata-kwata tsoron yi mata magana yake don haka ma ya zamewa rakiyar abokan nasa ya taho shi daya do kar ya sha kunya.
Ya rasa yaya zai yi da kaunar Saffiya duk abin da take masa baya rage kaunarta a ransa, sai ma karuwa
da take a zuciyarsa. Ya dago ya tsura mata ido ya sauke kakkarfar ajiyar zuciya duk da sanyin A.C din da ya sanyaya dakin bai hura shi hada gumi ba. Ya daure karo na biyu ya ce.Don Allah ki yi shiru in ba kya san ganina yanzu zan bar miki dakin. Na shigo na ga lafiyarki ne.” Ya mike tsaye.Ga abinci nan kar ki kwana da yunwa, Allah ya tashe mu lafiya.” Yana fadar haka ya fita daga dakin. Jikina ya yi sanyi da kalaman Imran, tun ranar da ya yi min tsawa na fara shayinsa, musamman in na tuna maganarshi ta karshe da ya ce za ki sha azaba in ki ka shigo hannuna.Na mike da sauri na rufe kofar dakin da nake. Zama na yi a gefen gadon ina kallon kayan da Imran ya zube a gabana, haka barci ya dauke ni daidai da mayafin jikina ban
cire ba iya gajiya na gaji. Kusan kwanana uku ban samu cikakken barci ba, don haka mai nauyi ya dauke ni. A hankali na ji ana bubbuga filon da nasa kaina na bu?e idona muka ha?a ido, fuskarshi cike da murmushi ya ce.
Ki yi ha?uri na tashe ki gani na yi lokacin sallah yayi Na dan hade fuska ina harararsa. Na mike zaune. Na ce, Shi ne za ka bugar min kai.” Ya zaro ido yana murmushi, “Duka kuma Safiyya akan me zan da ke ki? Ki yi
hakuri ba zan kara tashinki ba, su Momy sun zo yi miki sallama kina barci, Hajiyr Momy ta ce kar a tashe ki har sun tafi.Ban san lokacin da na mike tsaye ba, ina kallonsa bakina na rawa na ce, “Sun tafi da gaske? Kalli agogo karfe nawa?’ Na daga kaina da sauri. karfe takwas har da kwata, kuma so Momy karfe bakwai za su
tafi. Ji na yi ruwan hawaye yana bin fiiskata. Shi kenan Momy sun tafi bamu yi sallamaba , yaushe zan kara ganin su su tafi sun barni a hannun mutumin da na tsana a rayuwata.‘Me ye abin kuka ne wai ba ki da wuyar kuka? Kina so ruwan hawayenki ya kare da an kwana biyu za mu je Kano, ki je ki yi sallah lokaci yana tafiya.Yana fadar haka ya fita daga dakin.na shiga toilet na yi wanka, sannan na dauro alwala bayan na idar na dauko jakata na debo kayan kwalliya, na mi?e na bude kwabata na dauko wata atamfa mai ruwan ganye wanda aka yi mata
dinki mai kyau, bayan na zira na ?arasa gaban mudubi domin daura dankwali, ya bude kofar ya shigo sanye yake da farar T. Shirt mai adon zanen ananun taurari masu ruwan toka tare da sanyi da shudin jeans. Ya fito sosai angon nasa. Muka hada ido ta mudubin na yi saurin dauke kaina ya karaso fuskarshi cike da murmushi.
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/28/2016, 9:52 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
9⃣5⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
Kin tashi kalau?” Na daure na daga masa kai.Ya dan tsayar da murmurshin fuskarsa
ya ce, “Wai Safiyya ciwon baki ki ke?” Na dago muka hada ido.Na yi shiru ya dan
daga murya “Ki yi min magana mana sai na dinga yi miki magana sai dai ki dagan
kai ko kiyayyar da ki ke min ce ta hana ki magana.Nan da nan idona suka ciko da hawaye.‘Shi kenan kar ki min kuka bana bukatar maganarki taso mu je ki yi break.
Na bude baki dakyar na ce, “Ni na koshi.Bai yi magana ba ya juya ya fita ya dawo dauke
da kayan breakfast ya dire a gabana.Ki ci abinci ko na yi wa Abba waya na ce tun
jiya ki ke kuka na baki minti goma kar na dawo na ga ba ki ci komai ba.” Yana fadar
haka ya fita na bi bayansa da kallo. Kamar ina cin madaci haka na dinga tura break fast din, ya shigo yana amsa waya sai dariya yake har ya gama ina kallonsa ta gefen ido ya juyo wajena.Ki taso mu je ki ga yadda gidan naki yake. Yana maganar yana kokarin kama hannuna na mike da sauri (kamar wanda aka tsikarawa allura). Ina kallonsa cikin
fushi na ce.Ka fita a rayuwata babu ruwanka da zamana a gidan nan, ina tunanin tun farko ban maka nauyin bakina, to wallahi bara na gaya maka in har ba ka fita daga rayuwata ba
za ka rasa ni har abada. In kuma kana ganin ba zan iya ba to don Ailah ka ci gaba da shiga lamarina babu ruwanka da ni, gara tun wuri ka yi harkarka na yi tawa. In kuma kana ganin za
ka gayawa Abbana to Bismillah.Wallahi Imran duk ranar da ka hada ni da Abbana sai na gudu na bar ka in ya so ka fadi ka mutu.Ya dago idonsa wanda suka canja launi daga fari zuwa
ja. Muryarshi a sarke ya ce, “Na gode Safiyya za kuma ki san Imran dan halak ne.Yana fadar
haka ya juya ya fita yana dafa bango na bi bayansa da harara, a zuciyta na ce Allah yasa ka mutu ma karewar ma bakin ciki.Ina cikin dakin har wajen karfe sha biyu, sannan Khadijah ta zo
tare da su Khalil. Na fito da sauri ina muma zuwansu na ji duk wata damuwa ta kau daga zuciyata. Khalil ya ce, “Anty ina Yaya? Kan na yi magana ya fito idanuwansa boye cikin siririn bakin glass
fuskarshi cike da murmushi yana kallon kannansa.Sister na yi tunanin sai kin kwana biyu kina barci,
saboda gajiyar biki.Ta danyi dariya‘Kai yaya Imran dazu ma da su Anty Sadiya suka zo yi maku sallama ina wanka shi yasa ban biyo su ba.Ya zauna kusa da Khalil “Brother ya ka kwana?” Ya jima suna hira da su Khadijah ni kam hankalina yana ga wayar Khadijah.Ya mike, ‘Sister tunda kuna nan bara na je gida in na dawo sai ku tafi.” Ya mike ya yi cikin dakinsa. Bai jima ba ya fita hannunsa rike da key ya tsaya
a gabana. Kudi ya doran a cinya na.Ga shi ko za ki bukaci siyan wani abu, zan kai dare akwai komai a kicin.” Yana fadar haka ya fita.Yana fita na sake da su Khadijah tare muka shiga kicin muka yi girki, Salim ya fita ya siyo mana filet-filet din C.D har da na cartoon. Na yi farin ciki da ganin Tom & Jerry. Sai karfe takwas, sannan Imran ya dawo . Na shiga daki na debowa su Khadijah turaruka har da kudin da Imran
ya bani, duk na hada na ba su. Har bakin motar Imran na karaso, Khalil ya ce.Anty ki shigo mu tafi tare sai ku dawo.Na danyi murmushi na ce, Zan zo Khalil ka gaida su Momy.Ina shiga ciki na zarce dakina na shiga toilet. Wanka na yi na canja kayan jikina zuwa doguwar riga, na dan gyara fuskata na fito falon na shiga kicin ragowar
abincin da muka yi na zubo na dawo falon na saka cartoon din da su Salim suka siyo na dawo na zauna a kujerar ina cin abinci ina kallona. Ina kaunar Tom & Jerry don haka tunda na san nake dariya, kwata-kwata ban ji shigowarsa
ba, don hankalina na ga kallo, sai shigewarsa na gani na dan rage dariyar da nake bai fi minti goma da shiga ba ya
fito sanye da jallabiya ruwan toka. Hannunsa rike da jarida ya shiga kitchen jim kadan ya dawo. Na ji muryarsa.
Safiyya ina abincina? Takarda na yago a jikin memo na yi rubutu kamar haka: banyi girki da kaiba kar kuma kayi
tunanin zan dinga girki da kai' Ina gama rubutawa na mika masa ya karba da sauri ya karanta. Yana karantawa ya juya cikin kitchen din ina jin kiciniyarsa da tukunya. Har ya dafa Indomie ya fito duk ya hada gumi. Ajiyewa ya yi kan kafe ya koma ya dauko robar ruwa da silba tare da cup har ya zauna ya mike ya kara karfin A.C, sannan ya dawo ya zauna. Duk abin da yake ina kallonsa ta gefen ido haka shi ma ya fara cin Indomie yana kallon carloon din .
Ya gama ya debe kayan ya mayar kitchen ya dawo ya zauna kan kujera yana duba jaridar da ya ajiye.Har wajen karfe goma ina falon, haka shi ma sai da na ji barci ya kama ni sosai sannan na mike na shiga dakina na mayar da kofa na rufe.
Na bude durowa na dauko rigar barci na sa na haye dandashen gadona na ja kyakkywan bargona mai tare da laushi na lullube kaina barci mai dadi ya dauke ni.Haka zaman mu ya kasance da Imran har tsawon sati daya babu mai shiga harkar kowa.
In zan yi abinci sai dai ' na yi iya cikina, wata rana ma in har na dafa ruwan shayi shi kenan ba zan kara girki ba,
sai dai kayan sha na kwanwani. Haka shi ma Imran in ya dawo ya kan shigo ya girka abin da yake so. kullum ya fita sai
ya zube min kudi ko zan bukaci wani abu.Yau da yake weekend ne imran yana gida, don tunda na dafa tea na yi shigewa ta daki. Ina karyawa na shiga toilet na yo wanka har na gama shiryawa ina daure da tawul. Ina gama shiryawa na dawo kan gado na yi kwanciyata. Na rufe idona kamar mai yin barci, na ji ma a haka na ji kamar ana min tafiyar tsutsa a tafin kafata na bude
idona da sauri na ce.“Me ye haka? Ya dago kansa a firgice yana kallona, na yi saurin jan bargo na rufe jikina. Idona cike da hawaye na ce, “Me ye haka za ka shigo min daki kana taban jiki? Ya mike jikinsa ya yi sanyi, “ki yi hakuri ni kaina ban san
na aikata haka ba, kuma ko da na sani ban aikata haramci ba, na shigo na gaya miki anjima Momy za ta zo Yana fadar haka ya
fita daga dakin.Na mike na zura. kayana na fito, babu kowa a falon. Na nufi kicin don shiryawa Momy abinci. Har na gama bai fito ba. Ina gamawa na koma daki na kara shiryawa. Ina shirin fitowa na ji sallamar Momy na fito da sauri ina mata sannu da zuwa fuskarta cike da farin cikin ganina ta zauna. Na zauna 'kusa da kafarta ina gaishe ta ta amsa tare da tambayar lafiyata.
Na mike na kawo mata ruwa. Mun jima muna zaune ta ce, “Ina Imran din? Na ce, Momy yana daki. Ta ce kira min shi. Na mike kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na nufi dakinsa dan tunda na ke ban taba shiga dakin ba. Na shiga tare da sallama yana zaune ya hada kai da gwiwa ga dukkan alamu ya yi zurfi cikin tunani, na karasa gabansa. Ka zo Momy ta zo.” Na fada har sau biyu, amma bai
dago ba. Na kira sunansa ya d’ago da sauri yana kallona cikin mamaki. Na yi saurin kauda idona na juya zan fita na ji ya ruko hannuna,
na yi kasa da murya ina harararsa na ce.Me ye haka? Allah zan hada ka da Momy. Bai saki hannuna ba sai ma jana da ya yi har zuwa gefen gadonsa. Na zauna tare da sunkuyar da kaina yasa hannunsa ya dago fuskata muryarshi na rawa ya ce. Gayan Safiyya ba kya sona, yanzu
nan zan sake ki ki je ki auri wanda ki ke so. Mu je Kano gaban Abba ki gaya masu ke ce ba kya sona.Na zaro ido kamar zan su fado na ce, Momy na jiranka fa. Ya hade fuska.‘Ba maganar Momy muke ba, ki gayan matsyina in kuma baki gayan ba to wallahi yanzu zan gayawa Momy abin da Ki ke min gara kowa ya ya san irin kiyayyar da ki ke nuna min, zan wa Abba waya yanzu na gaya masa.idona ya ciko da hawaye na
ce, Don Allah ka yi hakuri ka bari ta tafi zan gaya maka.Ya mike Mu je. Har na kai bakin kofa ya yi kirana na juyo da sauri ya ce,
Haka za ki fita da hawaye a fuskarki? Na yi saurin sa hannu na goge har na juya zan tafi ya kara kiran sunana.Ki tsaya mu fita tare. Tare muka fito ya karasa gabanta yana murmushi.Momy sannu da zuwa.Sai karfe uku.Momy ta tafi yana fita raka ta na shige daki na kulle
kaina ina jin shi da ya dawo yana ta buga kofar tawa ya ji ta a rufe.Abu kamar wasa sai da muka yi kwana uku ba mu hadu da Imran ba Kullum
ina jin fitarshi zan fito tafasa ruwan shayi na dau duk abin da nake bukata na yi shigewata daki.Yau ina jin fitar Imran na fito don
tafasa ruwan tea kamar yadda na saba, daga ni sai rigar barci iya gwiwa don na san babu kowa a gidan sai ni kadai. Na zuba wanda zan sha a cup ragowar na zuba cikin flaks ma tsaya ina firfita wanda zan sha na juyo zan fita. Yana tsaye jikin kofar kitchen din fuskarshi
a hade na ji wani irin tsoronsa ya cikan zuciya wanda ya yi SANADIN subucewar kofin shayin daga hannuna, duk ya zube a kan kafafuna.
Wani irin azababben zugi ne ya ratsa sassan jikina ban san lokacin da na saka kara ba tare a runtse ido na..
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/29/2016, 9:11 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
9⃣6⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
durkushe a wajen. Ya karaso da gudu yana salati, hankalinsa ya yi mutukar tashi. Sannu Safiyya garin yaya ki ka saki shayin a kafarki? Nama kasa magana sai ruwan hawaye da yake bin fuskata kamar an bude famfo. Cak ya dauke ni ya fito da ni daga kicin din, har zuwa dakinsa ya dire ni a kan gadonshi ya jawo kafar yana min addu’a
muryarshi kamar zai yikuka ya ce.Ki yi shiru in Allah ya yarda ba za ta tashi ba, ki dinga kula Cikin kuka na ce, Ba kai ne ka tsorata ni ba ka sa na zubar da tea din a kafata, ga shi sai zafi take min.ki yi hakuri ba nufina na tsorata ki ba, na tsaya ne dan na ji daiilin takura kanki da ki ke a daki.Na ce, “To me yasa ba ka min sallama ba, dan na san kana tsaye...,Kukan azabar da kafafuna suke ya ci karfina na kasa karasa maganar.
Ya dafe kansa Kin yi shiru don Allah na ji na yi laifi ki yi hakuri don Allah bara na dauko
miki kayanki mu je asibiti.Na daga kaina ina kallonsa na ce, “Ni ba za ni asibiti ba, kawai ka kai ni wajen Abbana, tunda kai ba ka kaunata ka tsorata ni na ko ne a kafa, Allah sai na gayawa
Dady. Ya zaro ido waje Haba Safiyya me ya kawo rashin kaunarki, kin san ni din mai kaunarki ne tsakani da Ailah ke ce ki ke nunan kiyayya, in kuma ki ka gayawa Dady ya yi min fada to nima zan
gayawa Abba abin da ki ke min. Ki yi shiru yawan kuka in mutum ya kone to ko ba ta yi niyar tashi ba in har ana Kuka zai tashi (Amma fa a cewar Imran).Na ce, To kai ni wajen Abbana, in kana so nayi shiru. zaro wayarsa. Bara na yi kiransa na gaya masa in ya ce mu zo to sai mu tafi yanzu kira daya ta shiga, ya daga suka gaisa Imran ya ce, ‘Abba, Safiyya ce ta ke kuka sai na kwo ta Kano shi ne na ce bara na gaya maka in ka ce mu zo sai mu taho yau. Ban san me ya ce masa ba na ga ya mikon wayar. Na karba ina shashshekar kuka na ji muryarsa.Safiyya akan me ki ke kuka sai kin zo kin gan ni?”
Na ce, ‘Abba shi ne ya tsorata ni na kone a kafa, yanzu wajen sai zafi yake min.” Na karasa maganar cikin kuka. To ki yi hakuri insha Allahu nan da sati biyu za mu zo tare da Ummanki, ga ta ma ku gaisa duk su Hassan sun yi kewarki suna gaishe ki..Na ce, Ina amsawa. Abba ban Umman.Ya mika mata muna gaisawa na ji tana kokarin mika masa na ce, Umma ba ki yi min sannu ba, yanzu Imran ya kona ni a kafa.Ta ce, ‘To Allah ya kiyaye gaba ki gaida Imran din Tana fadar haka ta mikawa abba wayar. Na mika masa wayar ya karba yana murmushi. kan na yi magana wayar sa ta yi kara ya zaro ya daga, sun jima suna hira da Faisal na mike zan fita ya rike hannuna ina za ki Safiyya? Na ce zan je dakina na shirya. Kin ga ki shiga toilet ki yi wankan sai na debo miki kayan.Na ce, “Ni fa yunwa nake ji. Ya mike da sauri. “Bara na hado miki shayin ki yi zamanki, ba zan ma fita ba jinyarki zan yi.Da kansa ya hado min break fast bayan na yi wanka ya kawo magunguna ya bani. Na mike zan fita.“Ina zuwa? Ban kalle shi ba na ce, Falo za ni.Tare da shi muka fito ya kunna mana kallo. Kowa ne minti sai ya kalli kafata ya ga ko za ta tashi cikin ikon Allah ba ta tashi ba. Muna falon misalin karfe shida wayar Imran ta yi kara bayan ya gama amsawa ya juyo yana kallona. Kin ji gasu Faisal nan da abokanan aikinmu za su zo duba ki Kan na yi magana muka ji muryar Faisal yana cewa, Mu shigo ko mu koma? Imran ya mike da sauri yana dariya ya bude musu suka shigo. Maza biyu ne duk na gane fuskarsu sai kuma ‘yanmata guda uku. Kallo daya za ka yi musu ka san an gogu a duniya. Cikin isa suka shigo suna raba idon inda za su hange ni. Na dago kai muka hada ido ina dan murmushi na ce, Sannunku da zuwa.Jikinsu a sanyaye suka karaso falon ba su tunanin za su gan ni haka ba, dukkansu sai da suka raina kyan da suke ta da shi. Zuciyarsu ta cika da mamakin gani na tare da hassadar kyawun da Allah ya zuban. Imran ya dawo kusa da ni ya zauna yana kallona ya ce, Safiyya wadannan matan abokanan aikinmu ne, ga Fadila, ga Maryam, sannan ga Sakatariyata Aliya.Na dan yi raurmushi na ce, Sannunku ya hanya? Suka amsa, Ahmad ya ce, Amarya ya kafa, ya kamata ki doka cup din a court bai san a kafar Barrister Ya dauka ba har ya sa abokinmu fashin zuwa aiki. Na dan kalli Imran ina murmushi na ce, Ahmad ai ba zan zama cikakkiyar Barrister ba ka bari sai na yi bautar lasa da na gama har case zan maka a court. Muka dan yi dariya.Nafisa ta ce, Amma Imran kanwarka ce ko? Yana murmushi ya ce, “Me ki ka gani Nafisa?Aliya ta ce, “ku na mutukar kama sosai. Fadila ta ce, Wallahi kamar har ta yi yawa, ga shi kun dace da juna. Tana maganar tana kallona Imran ya zage sai faman hira yake da ‘yan matan. Ina ta'satar kallonsa amma kwata-kwata hankalinsa baya kaina sai dariyarsa ka ke ji, na ji duk zaman wajen ya gundire ni kamar na mike na shage Faisal ya mike, Amarya za mu tafi Allah ya kara sauki Na amsa da amin. Duk suka mike Imran ya ce na taso na raka su, ina harararsa na ce, “Kafata Suna fita na yi cikin dakina ina kuka, wanda na rasa dalilinsa. Ya dawo daga rakiyarsu ya ga bana falon don haka ya shigo dakin. Ganin ina kuka ya karaso da saurinsa yana tambayar abin da ya sani kuka. Ina kuka na ce, Allah sai na hada ka da Dady, na ce ka kawo ‘yan matanka gidan nan kun hadu kuna ta yi min dariya, suna hararata tun da za ku fita ka faman ciwona. Cikin mamaki ya tsaya yana kallona sai da ya ga na fito da wayarshi zan kira ya yi saurin rike hannuna ya karbe wayar na ci gaba da kukana. kusa da ni ya zauna ya zuban ido yana kallon ikon Allah ganin ban da niyar daina kukan ya ce. Safiyya ko da ‘yan matana na kawo bai ci ki yi kishina ba..
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/31/2016, 9:46 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
9⃣7⃣ & 9⃣8⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
ke da ba kya sona ba kya kaunata. To me ye ruwanki da abin da zan yi, kuma wadannan matan da ki ka gani aiki ne ya hada mu duk cikinsu babu wanda maganar so ta hada mu ko da zan yi soyayya da su ba su yi kalar matan da nake so ba. ke daya ce kala ta burin rayuwata, tunda na mallake ki babu gurbin kowa a zuciyata. ki yi shiru kar kanki yayi ciwo ki sawa zuciyarki ke daya ce matar da imran zai yi har karshen rayuwarsa.Ya kawo hannu zai gogen hawayen fuskata na yi saurin kawar da fuskata.ki je ki yi sallah kin ji kira. Zan fita masaliaci, na ga Safiyya shiri take nema da ni. Ya karasa maganar cikin dariya Na bi bayansa da kallo zuciyata cike da mamakin canjin da na samu a zuciyata. A ciki ta yi matukar, karuwa da kaunar Imran, na yi shiru ina ne marwa kaina mafita. Bayan na yi sallah na fito na tadda Imran a kicin yana kiciniyar dafa Indomie ya juyo yana kallona Har kin idar? Na daga masa kai. Ya dan yi murmushi To kin roki Allah ya sa miki kaunata? Na yi shiru ina kallonsa na karaso falo na zauna.Na tambaye ki kin yi shiru? Na ce ni ban yi ba.Ya girgiza kai Shi kenan ni kuma kullum in na yi sallah ina rokon Ubangiji ya sa'miki kaunata. Za ki
ci Indomie na dafa da ke? Kunya ta kama ni ganin ga ni ni a zaune mijina yana kicin zai dafa abin da zai ci har ma yana tambayar ya dafa da ni. A zuciyata na ce shi wai ba ya fushi da mutum Tunanin me ki ke yi, ko kafarce take zafi? Na ce, ‘Ta daina zafin tun
dazu. Ya ce, Ai gara ta daina zafin ko dan na fita aiki. Na dafa miki Indomi ko na zo na
yi miki take away? Na girgiza masa kai.Wai ke bakin ki yana ciwo ne, ni ba magana nake miki ba ne ke ma ki bude ba ki ki yi min magana Na ce, ‘To na koshi fa.Ya hade fuskarsa me ki ka
ci da za ki ce kin koshi ko kina bukatar na yi miki dure ne? Na dan hade fuska ina harararsa na ce, Me ye haka ne? Tun daga ranar na dan sake da lmran in dai muna zaune a falon muna hira sama-sama, amma kusan rabin hirar ta mu fada ne. Duk wata kulawa yana ba ni har tsawon wata uku babu abin da ya shiga tsakaninmu tunda hirar da za mu yi ta minti goma sai mun yi fadan minti takwas
hirar minti biyu. Amma imran ya dau laifin. Shi kam kuilum burinsa mu zauna lafiya A wannan lokacin su Baba suka lafi Adamawa gaba dayansu har Alh. Bashir ni da Imran kawai ba mu je ba, babu irin magiyar da ban yi wa Abbanmu ba kan na zo kano mu tafi tare, amma ya ki. Haka na hakura na sauke fushina akan imran wanda har kawo yau da suka dawo fushin nake da shi.Duk wani dan uwanmu da yake Adamawa tare aka
taho da shi Kano. Kuma a can aka mayar da auren Momy da Abba har su Dady duk suna Kano. Tun bayan da na yi sallar Asubah ban ji motsin Imran ba, wanda kullum bayan ya dawo daga masallaci sai ya shigo dakina ko in zai tafi amma yau shiru har zuwa lokacin fitarsa ban ji motsinsa ba. Bayan na yi wanka na fito na shiga kicin na hada tea, wayata ta yi kara na fito da sauri na dauka na ji muryar Dadyn lmran na tsugunna kamar
yana gabana muka gaisa yake tambayar ina imran ya kira wayarsa ba a daga ba? Na ce ‘Dady ya fita ne kuma ya bar wayar a gida. Ina gama karyawa na dawo falon na kunna kallo na dau wayata na yi kiran Momyta muka
yi hira. Har sha biyu Imran bai fito daga dakinsa ba.ina kallon kofar dakin, amma shiru. har karfe takwas
na dare hankalina duk ya tashi in na yi kamar in shiga dakin na ga lafiyarsa sai kuma na fasa tunda ni duk
zamana a gidan sau biyu na taba shiga dakinsa lokacin da shayi ya zubar min a kafa sai kuma Momy da tasa na yi kiransa.Na mike jikina sanyi kalau na shiga dakina, bandaki na shiga na yo wanka har na yi shirin barci
na kwanta na ji na kasa barcin burin zuciyata sanin halin da imran yake ciki. Babu abin da idanuna suke sai gani fuskar imran na mike da sauri na saka hijabina. Ina zuwa bakin kofar dakin na tsaya ina tunanin shiga kan kwakwalwata ta yi tunanin komai na ji muryar imran cikin mawuyacin haii yana kiran sunan Allah. Ai ban san lokacin da na danna kaina cikin dakin ba. Duk da rashin wadatar hasken da yake dakin za ka iya hangen murkususun da yake a kan gadon. Na karasa gadon da sauri na dago kansa, gabaki daya fuskarsa ta canja, ya ma kasa bude idonsa ya kalle ni, sai faman cije baki yake. A rude na ce. imran ba ka da lafiya? Me ye yake damun ka? Ina maganar hawaye yana zuba a fuskata. Bai samu bakin yi min magana ba sai hannuna da ya kama ya dora akan marar shi, na dauke hannuna da sauri sakamakon shokin din da ha ji a jikina. Na ji muryarsa
a shake Don Allah Safiyya ki kira min Abbana na mutu a gabansa, ki taimakan zan mutu, ga wayata can don Allah ki yi kiransa. Ina kuka na ce, Ka yi hakuri Imran ba za ka mutu ba, don Allah kar ka mutu ka bar ni, ka yi kiran Faisal mu je asibiti ka san Abba suna Kano.Jin shiru bai yi magana ba na kama girgiza shi ina kiran sunansa amma shiru. Hawayen da yake fuskata ya dauke cak tsabagen razana da tsoro suka ziyarci
zuciyata. kar dai Imran ya mutu. Na shiga uku! Yaya zan yi da rayuwata? Hannuna yana karkarwa na dora a kirjinsa kan na dauke na ji muryarshi kamar a mafarki ya kira sunana Na amsa da sauri tare da dago kansa na dora a cinyata, duk da babu haske cikin dakin na san ni yake kallo Muryata na rawa na ce, "Ta daina ciwon?
Muryarshi kamar mai rada ya ce, Ba ta daina ba Safiyya zuwanki ma ciwon karuwa ya yi, na daure ne don kar
na daga miki hankali ban san kina kuka. Na ce, Imran in har ina ganinka a cikin halin rashin lafiya idanuwana ba za su daina zubar hawaye ba, ka taso mu je asibiti don Ailah kar dare ya yi ciwon ya matsa maka.‘Safiyya na je asibiti sau biyu kuma sun bani iya taimamkon da za su iya bani kiyi min addu’a Allah ya ban lafiya marata ta matsan da yawa Ina kuka na ce, Don Allah mu je asibitin ko Faisal mu kira ya kai mu. Ina maganar ina kokar in daga shi naji ya rike hannuwana ba zan koma asibiti ba safiyya kece maganin ciwona ki tausayan halin dana shiga na rasa wane laifi nayi miki kika tsane ni na rasa me zan miki ki kaunace ni yanzu da nake ciwon nan zan
so Allah ya dau raina ko don na huta da kiyayyar da ki ke min Ki daina kuka farin ciki za ki yi zan mutu na bar ki ki huta. Ina so ki rike a ranki Imran mai kaunarki ne, kaunata tsakani da Allah na kaunace ki tun kan na ganki, kuma tun kan na ganki na yi wa kaina alkawarin zama da ke cikin ko wane yanayi, sai na yi rashin dace Safiyya babu
wanda ta tsana a rayuwarta kamar Imran. Na rasa wane gagarumin laifi na yi miki da ki Yayi shiru yana sauke numfashi.
Na ji ya kara matse min hannu sosai ga dukkan alamu mararce ta motsa masa, na kifa kaina a kirjinsa. Ka yi min afuwa Imran waliahi ina kaunarka, in ka mutu ban san ya zan yi da rayuwata ba, tun ranar da na fara ganinka nake kaunarka don Allah ka yi hakuri kar ka mutu ka bar... Kuka ya ci karfina na kasa karasawa. A hankali ya dago fuskata.Safiyya
da gaske kina kaunata Na yi saurin maida kaina kirjinsa Don Allah ki gayan kina kaunata tamkar yadda nake kaunarki? Na yi shiru ina sauke ajiyar zuciya wadda take fal da tunani ‘Wash! Allah na Ya furta a hankali. Da sauri na ce, Ciwon take ko? Kan na rufe baki na ji ya rungume ni a kunnena ya radan 'Safiyya ke ce maganin ciwon marata, ina
fatan yau za ki kawo agajin gaggawa don ceto rayuwata. Yana maganar yana kokarin cire hijabin da yake jikina. Muryata na rawa na ce, Imran ka bari Ya dan tsaya daga kiciniyar cire hijabin yana lalubar hannuna ya dora a kan kirjinsa.
Shi kenan Safiyya ba kya so na warke na bari ba zan taba neman hakkina ba ba tare da amincewarki ba. Ya dago ni daga kan kirjinsa Na gode da kulawar da ki ka ba ni a yanzu, ki je dakinki ki kwanta Allah ya tashe mu lafiya Na marairace ina rike da hannunsa na ce Ba zan iya tafi na barka ka kwana kai daya ba, kada marar ta tashi
No Safij'ya kije dakinki zamanmu tare kamar kara ciwon ki ke, ki tausayan mana ko kina so na mutu? Na girgiza kai. To kin amince mini? Na yi shiru zuciyata cike da tsananin tsoro. Ya dan shafa bayana tsigar jikina ta tashi na yi
saurin rintse idona.Kin yi shiru Safiyya kin amince za ki kawon agaji? Idanuwana na rufe na daga masa kai ya sauke wata kakkarfar ajiyar zuciya.Na gode Safiyya tashi mu je mu yi sallah, don neman albarkar wannan daren.Tare muka
shiga toilet muka dauro alwala. Bayan mun idar ya mike ya fita, ni dai ina zaune a inda ya bar ni tsoro fal zuciyata ya dawo. Na barki ke daya naje rufe kofa ne.Na daga masa kai Ki zo ki kwanta Safiyya Ban yi masa musu ba na taso.
Ya ja bargo har zuwa kanmu.
Tun karfe uku Imran bai rintsa ba tsabar farin ciki ne ya cika masa zuciya ya hana shi runtsawa tun bayan daya lallaba Safiyya ta yi barci. Kaunarta tare da tausayin wahalar da ta sha su suke maza zarya cikin zuciyarsa.
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[1/1, 5:22 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘
9⃣9⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com
Safiyya ta bar mishi tarihin daren da ba zai taba gogewa cikin zuciyarshi ba. A hankali ya zare ta daga jikinsa ya jera matasai kamar jaririya ya shiga toilet ya tsarkake jikinsa ya haye kan sallaya don nuna godiya ga Ubangijinsa. Har aka yi sallar Asubah bayan ya idar ya mike a hankali ya shiga toilet ruwan zafi ya hada mata sannan ya dawo ya dauke ta cak sai cikin bahon wanka. Na saki wata wahalalliyar kara ina kokarin mikewa ya yi saurin rike ni. Ki zauna Safiyya za ki ji dadin jikinki. Na yi shiru idanuwana yana zubar da hawaye saboda azaba, sai da ruwan ya fara sanyi sannan ya sake ni ya kara hada min wani dan tsarkake jikina ya fito. Zanin gadon ya canja, ya shiga dakina ya daukon farar doguwar riga. Lokacin na fito ya karaso da sauri fuskarshi dauke da murmushi. Na dauke kaina na mika masa hannu cak ya dauke ni ya dire a gefen gadonsa. Safiyya fushi ki ke da ni? Na girgiza kai. To me yasa ki ka dauke kai da na shigo ba kya son ganina ko? Na ce, Ka ban rigar nasa ina san na yi sallah Da kansa ya sa min rigar. A zaune na yi sallar. Bayan na idar na juyo wajensa yana zaune a gefen gadon ya zuba tagumi ya ji muryata ina gaishe shi, da sauri ya amsa yana murmushi na ce ya jikin? Safiyya ciwon naki ne tunda kuma kin kawo min agaji na riga na warke Na kwantar da kaina kan kafet ya taso da sauri ya dauke ni har kan gadon. Na runtse idanuwana tare da takure jikina ya kwanta a bayana cikin taushin murya ya ce. Ki saki jikinki Safiyya babu abin da zan miki Na girgiza masa kai idanuna suna fitar da hawaye, na ce, Ni dai ka raka ni dakina ba zan kara kwana a nan ba. Ya juyo da fuskarsa hannu yasa yake gogen hawayen fuskata. Ya jima
yana lallaba ni kamar yarinya har sai da barci ya dauke ni. Karfe bakwai Imran ya farka kai tsaye kicin ya nufa ina jin fitarsa na mike na yi cikin dakina ba tare da ya ji motsina ba. Yinin ranar Imran ko gate bai je ba yana like da ni duk wani motsi da zan yi idonsa yana kai. Daidai da sallah ranar a gida ya dinga yin ta. Bini-bini ya tambaye ni lafiya
ta. Kyakkyawar rayuwa mai cike da dandasheshiyar soyayya muka shiga shimfidawa tsakaninmu da Imran, bana tunanin zan kaunaci wnai abu kamar yadda nake kaunar dan uwana kuma mijina Imran, wanda duk wata kulawa ya dauke ta ya dora a kaina. In yana office ba ma minti goma ba tare da mun ji muryar juna ba, bare kuma weekend. Har ya yi hutunsa ya gama bai zama lallai ya leka gate ba, in har ba lambun gidan za mu shiga ba. Daidai da girki tare muke yi
har raba girki muka yi. Za mu hada break tare da rana na yi ni kakai da daddare ya girka.
Har shara da gyaran dakunanmu tare muke yi A cewarsa baya san ‘yar aiki Zamanmu mu biyu ya fi dadi. Wanki ne kawai ake fita dashi. Rayuwarmu cikin farin ciki Har tsawon wata shida lokacin muka yi bautar kasarmu ba tare da wata matsala ba, Imran ya shiga nema aiki, kuma a lokacin aka tsaida bikin Rukkayya (Momyna) da Yusuf, Sadiya da Salim. Na yi mutukar farin ciki. An tsaida lokacin bikin wata shida masu zuwa. A lokacin cikina yana wata uku babu wanda
ya san ina da ciki da gani sai Imran har muka yi laulayinmu muka gama. Duk wata kauna yanzu Imran ya dankawa cikin da yake jikina. Duk wanda ya kalle ni ya san na canja, na yi kyau iya kyau na gani a fada ta ko ina na fita haka Imran.
Tun karfe bakwai muka shiga kicin ni da Imran domin tarar bakin Kano wanda tun jiya da yamma suka sauka babu irin lallabawar da ban ma Imran ba kan ya bar ni na je na musu sannu da zuwa ya ki. Karshe ma sai da ya lallaba ni na yi barci ya fice ya yi musu barka da zuwa sai farkawa na yi na gan ni rungume da filo.tunda na yi sallar
Asubah ban koma ba, nake kicin nake shirin tarar su Abbana burina na ga Ummata da kannena. Ganin na zage ina aiki Imran sai tsokana ta yake. Sai karfe sha biyu muka gama komai. Na shiga toilet don shiryawa, haka shi ma Imran ya fito sanye cikin lallausan yadi ruwan toka wanda ya dace da kalar fatarsa. Ya shigo muka hada ido ta mirrow ya sakar min tsadadden murmushinsa. Ban yi kasa a gwiwa ba wajen mayar masa da murmushin da yake dimauta shi Ya karaso ya tsaya a bayana muna kallon juna ta mudubi ya dan yi murmushi yana shafa bayana, cikin shagwaba na ce, Ka yi min wayo ka shirya shi ne ka zo ka takuran kasa na kasa shiryawa ko? A yi min afuwa ranki ya dade Maman
Safiyya ina jiranki a falo. Yana fadan haka ya juya da baya ya fita. Sai da na gama shirina tsaf na fito yana zaune ya zubawa kofar dakin ido na fito sanye cikin shadda ruwan kasa. Ya mike da sauri Barka da fitowa. Zuwa na yi na zaunar da shi, sannan na zauna a kan cinyarsa na
sarkafo wuyansa da hannu daya dayan kuma ina shafa kyakkyawan sajensa da yi wa wadatarciyar
fuskarsa kawanya. Ya lumshe ido yana murmushi na ce, Don Allah mu je tare taho da su. Kan ya yi magana muka hangi motar Abba ta shigo gate din gidanmu, na mike da sauri zan fita ya rike hannuna, mikewa yayi ya dan kama kunnena cikin wasa ya ce, Bana hana ki gudu ba kina so ki
dinga wahalar min da Safiyyata ko? To zan miki hukunci na karshe Na ce, Don Allah ka sake ni kar su shigo su gan mu Yana dariya ya ce, Me ye dan sun gan mu? Ai yana da kyau su ganmu dan su ga shaidar kaunar da mukewa juna. Yana kiciniyar goya ni Baba ta fara shigowa na yi saurin zillewa na karasa gabanta cikin kunya Bava barka da zuwa Ina maganar ina kokarin kama hannunta. Tana dariya ta ce, Lallai amarcin yayi karfi haka kika kara girma ga dukkan alamu an kusa sauka
Daidai nan su Ummata suka shigo tare da Abba da sauri na saki hannun Baba na dau Hassan ina dariya,
imran kuma ya dau Hussaini su Malam mado suka shigo na rasa ina zan saka kaina dan farin ciki Yini suka yi a gidanmu har sai karfe biyar muka fito tare da su har gidan su Imran, sannan muka dawo.
Satinsu Umma daya, sannan suka koma nan ma na yi nacin Abba ya yarda na bi su amma ya ce sai bikinsu Momy haka na yi hakuri, amma kullum cikin zuciyata burin lokacin nake. Zamanmu ya dora cikin kyakkyawar
fahimtar juna da zaman lafiya. Haka iyayensa tunda suka fiiskanci ina da ciki Momy kullum cikin aikon da kayan da mai cike take bukata, duk kuma kwana uku sai ta zo ta ga lafiyata har gida Doctor take zuwa ta yi min awo.Lokacin da cikina ya yi wata takwas kullum muna tare da su Momy ta waya muna shirin-shiryen biki. Cikin lokacin duk wani shiri ya riga ya gama kankama, wata kawai muke jira ya kama mu sha biki. Wanda watan bikin ya yi daidai da watan haihuwata. Tun cikina yana wata takwas Baba take san na taho gida.
🅰bbagana hausa novels @ facebook.
Popular Posts
-
Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wadda yake zuwa muku kai tsaye daga shafin “Abba...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 76 BY MIEMIEBEE Hannunsu ta had’a tana murzawa a hankali, “I’m ready Habeebi.” Har yanzu ya kasa yarda, “Flower are...
-
TANA TARE DA NI... TANA TARE DA NI... PAGE 56 BY MIEMIEBEE Wani irin tausayin daya jima be mata irinsa ba ya soma jimata yau, azabarcaccen k...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 89 BY MIEMIEBEE Daidai tashiwan Anas daga bacci kenan, da k’yar ya iya ya raba jikin Fannah da nasa dan wani s...
-
[9:09PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 1 na BABY ZAHRA Kayatatciyar daki ne mai dauke da ko mai na more rayuwa, alarm ce ke bu...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 74 BY MIEMIEBEE D’ayan hannunsa ya aza a hab’arta tare da d’ago fuskartata. “Flower you don’t have to be sorry baki...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 68 BY MIEMIEBEE Kasa koda amsashi tayi wani kunya taji ya rufeta, she can’t believe abinda ta aikata sede kuma ...
-
TANA TARE DA NI... TANA TARE DA NI... PAGE 61 BY MIEMIEBEE ★‡★‡★‡ PRISON HOUSE MAIDUGURI, BORNO STATE. K’aramin gate ne ya bud’u...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 75 BY MIEMIEBEE Sede still bayason miyan kukan yafison ire-iren abincin daya saba ci a London su burger, pizza, buf...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 01 BY MIEMIEBEE ANAS K’auyen Bama dake jihar Maiduguri, Borno. Da yammacin ranan Asab...
About Me
- Muhammad Abba Gana
- Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
Sassa
- AMINAN JUNA
- BANA KAUNARKA HAUSA NOVEL
- DAN ALHAJI HAUSA NOVEL
- DILKA & HALWA
- DOMIN KE DA MIJINKI
- GUZIRI MAFI KYAWU
- HAUSA NOVELS
- INSIYA
- KAUNA CE SILA HAUSA NOVEL
- KUKAN KURCIYA
- MU DAUKI DARASI
- mu koyi sana'a
- MY kitchen
- NA DAINA SO HAUSA NOVEL
- RAYUWAN NIHILA
- rayuwar fauziya hausa novel
- SASHIN YAN UWA MATA
- siffofin uwa
- TSORATARWA.
- WAYE SANADI