KYAUTATA ZAMANTAKEWAR AURE BA TARE DA ZUWA WAJEN BOKA KO DAN DUBA BA.
Ki
sani ya `yar uwata, akwai hanyoyi da dama da mace za ta bi, domin ta kyautata
zamantakewarta ba tare da zuwa wajen boka ko dan duba ba. Ki sani yake `yar
uwa, idan ki ka gyara zamantakewarki zaki samu rabon duniya da na lahira, shi
ko boka ba shi da abin da zai qare ki da shi a gurin Allah, shin me ya sa ba za
ki tsaya ki lura da kyau ba, ki san cewa boka babu abin da yake yi face ya yi
sanadin da zai rarrabe kawunan mutane, babu abin da yake yi face ya shiga
tsakanin mata da miji, boka babu abin da yake yi face ya raba ki da dukiyarki
idan kin yi ganganci har da Imaninki, ya sa ki sami zunubi mai girma, shin, me
ya sa ba zaki tsaya a tafarkin Allah ba, ki yi rayuwar aure mai kyau, wanda
muka koya daga koyarwar Annabinmu Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) da
sahabbansa, da muminai baki daya. Domin hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam) yana cewa: “Lalle Allah madaukakin sarki yana cewa ranar alqiyama,
ina masu soyayya don neman yardata, a yau zan sanya su cikin inuwata, ranar da
babu wata inuwa sai inuwata”. Shin `yar uwa ba za ki tsaya a tafarkin Allah ku
yi soyayya don Allah ba? Kin je wurin boka idan da gangan ne, kin zama kafira,
kin zama mushrika, kin zama `yar wuta, subhanallahi. Haqiqa `yar`uwa idan ki ka
tsaya ki ka lura da kyau, zaki gane cewa boka da dan duba ba su amfana ma kowa
da wani abu, face su raba mutane da dukiyarsu da imaninsu ga wanda ya yi
ganganci, domin hadisin manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Duk
wanda ya je gurin boka da dan duba ya gasgata abin da yake fada, haqiqa ya
kafirce wa abin da Manzo ya zo da shi”. Boka ba ya iya cecen mutum a lahira, ba
zai iya cecen ki ba, Idan ya ga za a sanya ki a wuta, ba shi da wani amfani a
duniya da lahira, boka ya zama shahararren me hada fitina da husuma a tsakanin
mutane, domin Alqur’ani mai girma yana fada mana cewa; “…shaidanu su ne
kafirai, suna karantar da mutane sihiri… kuma ba su sanar da kowa ba, face su
ce lalle mu fitina ne a gare ku, kada ku kafirta, suna neman ilimin abin da ke
rarrabe tsakanin miji da matarsa…”. Saboda haka wannan ya sa mai sihiri ba shi
da wani rabo a lahira alhali yana sane, kuma tir da abin da suka sayar da
rayukansu da shi, alhali suna sane. Shaidan shi ne dukkan wanda ya san gaskiya
kuma ya qi yin aiki da ita, mutum ne ko aljan. Haqiqa `yar uwa ki lura, ki
fahimci abubuwan da za lissafa, zaki samu ki gyara zamantakewarki ba tare da
zuwa wajen boka ko dan duba ba, domin ba zasu amfane ki da wani abu a wurin
Allah ba.
Abu
na farko, shi ne girmama mai gida, haqiqa girmama mai gida yana da matuqar
muhimmanci, ki yarda cewa mai gida yana da wani matsayin da zai sa ki abu, ki
yi, kuma zaki girmama shi, ki dinga ba shi matsayi da girma a matsayin mijinki,
amma yanzu wasu matan ba su gane ba, sun dauka cewa idan suka je wurin boka ya
mallake masu mai gidan, ya zama na sai dai ta ba shi umarni, ya bi, shi ne
matar, ba mijin ba, ya zama kamar yaronta, wai tana ganin kamar ta birge, ita
ce wadda ta yi sa’a, to wallahi ba haka ba ne, Abu na biyu shi ne mace ta
kasance mai lura da tarbiyyar `ya`ya lura da tarbiyyan yara, ya kan sa namiji
ya qara son mace domin tana kula mashi da `ya`ya, yadda ya kamata, koda ba ita
ta haife su ba, da sun wuce a dinga shi mata albarka, ana cewa kalli yarannan
yadda aka yi tarbiyyarsu, kuma abin mamaki ba `ya`yan ta ba ne, riqo ta yi, amma
ta ba su kulawa mai kyau, ki zama kowa na miki addu’a sabo da wannan, inko
`ya`yanki ne, su zama abin kwatance a cikin al’umma, a dinga cewa kalli
`ya`yannan ba ruwansu da shaye – shayen banza, da duk dabi’un banza, duk dabi’u
na banza basa yi. Amma wannan ya gagara, kun kasa ganewa ku mata, haqiqa na
miji ba ya so a ce `ya`yansa sun zama na banza koda shi din na banza ne, ya fi
so a ce ga `ya`yansa sun samu tarbiyya mai kyau, iyaye mata da dama su suke
koya ma `ya`yansu dabi’u na banza, misali sai ku ga ana fada da mahaifiya a
cikin gida, sai ta je ta dauko `ya`yanta, wai su rama mata, ba za ta nuna wa
`ya`yan cewa su ma mutanen gidan na da girma da daraja ba, koda an taba ta, sai
ta yi haquri ta nuna wa `yarta, ta saba da haquri, amma a’a, ko da `yarta aka
taba, sai ta yi ta masifa wai ita an taba mata yarinya, sai ku ga yara sun taso
ba abin da suke yi sai rashin kunya, su taso cikin rashin kunya, su taso ciki
rashin tarbiyya, su taso a wulaqance, babu mai cewa su bari, abin haushi abin
takaici wai sai ku ga iyaye an taso sun zo gurin malamin Islamiyya, sun zo
tambayan dalilin da ya doki yaro, kuma zaku ga yawancin masu yin haka iyaye
mata ne, idan malami ya yi Magana su ce su sun san zafin haihuwa, shin wane
irin wulaqanci ne wannan? Kuma idan kuka bibiya zaku ga yaran ne keda laifi,
domin wasu yaran yadda suka taso cikin rashin kunya idan sun je makarnata haka
suke yi, kuma iyaye sun fi yin haka a makarantun Islamiyya, basa zuwa
makarantun boko idan an taba `ya`yansu, in banda rashin tunani, ta yaya wanda
ya karantar da danki yadda zai bauta ma Allah, amma shi ne idan ya daki danki
ko `yarki zaki sanyo hijabi ki taho wai kin zo ganin malamin da ya taba maki
yaro, Wal’iyazu billah