shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday 20 May 2016

WAYE SANADI?? 15&16

waye-sanadi.jpg

[7:58AM, 5/20/2016]
Ábbā-Gãñå WAYE SANADI?

15


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

tunda muka shiga mota bance kala ba har muka je kabuga safiya kin yi shiru ko kina kewar baba ne kaina ke ciwo ban cika son magana ba,nafi bukatar kwanciya a wannan lokacin,na juyar da kaina.wani tafkeken gate naga mun nufa bayan mun shiga layin runfar shehu gidan horn din da yayine ya dawo dani daga duniyar tunani ina kallon wani yazo ya bude gate din tunda muka shiga nake kallon aljanar duniya sannu da zuwa alhaji yauwa magaji ya aikin.safiya fito mu shiga sai a samo miki maganin ciwon kan,a sanyaye na fito ina binsa a baya har muka shiga gidan babban walo ne muka shiga.daddy sannu da zuwa wata yarinya ta fada tana murmushi,"sannu maryam ina umma? tana daki,daddy ina bakuwarmu "safiyya shigo ki zauna ai daddy tana bayanka aunty sannu da zuwa haka kawai naji ina jin haushin yarinyar dakyar na taushi zuciyata nace yawa na juyo ina kallonsa yana ta faman murmushi ina ummata? safiyyya ki zauna yanzu zata fito nanunan dakinta sanin halina yasa yace ta so muje a cikin falon naga mun shiga wani dan siririn loko sai gamu mun fito wani lafiyayyen falon ya sha kujeru gefen dakuna guda biyu.safiyya ga dakin ki wannan kuma na ummanki da fatan dan gidan nawa ba laifi" na juya na nufi dakin da yace na umma ta ne bbu ko sallama na tusa kai tana zaune a kan sallaya tana gani na ta taso da sauri tana dariya"oyoyo nanata kwana bakwai kamar shekara dubu na ganta wajena ina tunaninki sannu" sai da muka karasa bakin gadonta ta zaunar dani yaushe ya jeya dauko ki? umma kinyi kyau dan haka kika nace sai kin aureshi ashe dadi kika gani,amma ni vaba take min bakin ciki nima nazo na dandali arziki. shigowarsa ce tasa nayi shiru "rukayya na cika alkawari ga safiyyar mu nan na dauko mana tazo gidanmu da fatan zaki zauna da ummanki,please safiyya duk abinda akai miki ki gayan zan dau mataki safiyya na dauke ki a matsayin yata. rukayya baki kawo mata komai ba kuma tace kanta yana ciwo na bawa khalifa key yaje ya karbo mata magani in tasha sai ta kwanta dan ta huta,khalifa da abba sun yi miki sannu da zuwa sun zo ganin ummanki gobe zaki koma bakin karatun nagaya musu kanki ke ciwo gobe zaku hadu gun break bayan fitarsa umma ta juya tana kallona yanzu abinda kike kin kyauta mutumin nan yana yi mana hidima amma baki taba budar bakinki kin masa godiya ba,


Abbagana hausa novels@ facebook.
[8:00AM, 5/20/2016] Ábbā-Gãñå: WAYE SANADI?

16


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz


in yayi miki magana sai ki nuna kamar ba dake yake ba,gaskiya in kina so mu shirya to ki gyara halinki,kai umma har mutumin ya mallake miki zuciya kin daina sona kuma da ki kace yana ta hidima damu to ni nasa shi ko kiransa nayi dan haka bbu abinda ya dame ni da nayi masa godiya"na mike umma zan tafi tunda bakya bukatar gani na,mijinki ya fini.haba nana ina kuma zaki ya riga ya dauko ki kin riga kin dawo nan kawai dan na fada miki gaskiya sai ki tafi ki barni
"umma wannan ba gaskiya kika gayan ba,kawai kin nuna bakya son ganina a gidan nan kuma wallahi in har na bar gidannan ba gaida zani ba sai dai na shiga duniya inda har abada ba zaki kara ganni na ba ina fadar haka na juya zan fita naji umma ta rike hannuna cikin sanyayar murya tace kiyi hakiri nana insha Allahu bazan kara miki fada ba tati ta lallashina har na sauko naci abinci na sha magani umma tace to kije dakinki kwanta kyafi sakewa umma kin san tare muke kwanciya dan haka auranki bazai hanamu kwana tare ba na juya na kwanta.washe gari bayan na idar da sallah na koma na kwanta a hankali umma naji tana bubbuga kafata na bude ido nana ki tashi lokaci yana kurewa kuma tun dazu su abba suke shigowa zaku gaisa.umma sai kace gaisuwar dole ce "haba nana daure ki tashi kin ga zaki makaranta kada lokaci ya kure sai lokacin na tuna da makaranta na tashi na shiga toilet gaskiya rayuwar hutu itace rayuwa Allah kayi mana arziki,abinda na fadi kenan bayan na shiga toilet naga umma tana zaune tana kallona a zuciyarta addu'a take Allah yasa kada na bata kunya.nana in kin shirya kizo muje mu gaisa umma dawa zamu gaisa? nana ai kinsan gidan bamu kadai bane gaskiya umma ba inda zani dole ne sai mun gaisa nifa ban cika sonyin magana,dasu bashi ba na gaya masa bbu ruwana dasu ba" nana yanzu ban isa na saki abu kiyi ba ai ko dan darajata kya je ku gaisa dan Allah kar ki ban kunya ace daga zuwanki har kin fara haka"Allah umma in dai naje yau bazan kara zuwa ba na yarda nana Allah yayi miki albarka taso muje na mike nabi bayanta duk kansu suna falo muka karasa umma kin fito kanwarmu sannu ya bakunta murmushi nayi musu na juya ina kallon maryam aunty an tashi lafiya? lafiya maryam aunty taso muje muyi break a,a,


Abbagana hausa novels@faceebook.
Share:

8 comments:

  1. Gaskiya Yayi Dadi

    ReplyDelete
  2. inajin sai nadaina karatun littapinga saboda abin yana bani muguntakaici

    ReplyDelete
  3. Abubakar Ibrahim20 May 2016 at 14:54

    Wannar ita ake kira goyon kaka

    ReplyDelete
  4. fatima ibrahim ummu faruq20 May 2016 at 23:36

    haba ita kuma karta kwafsa mana

    ReplyDelete
  5. Tnx mungode

    ReplyDelete
  6. Gsky Idan Haka Zata Yi Bata Haduba

    ReplyDelete
  7. Littafin nan akwai abin takaici whl

    ReplyDelete
  8. Adam M.S Bakori23 May 2016 at 08:26

    Sannu jarumin marubuta.
    Keep it up!

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).