shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 24 September 2016

TANA TARE DA NI... PAGE 84&85

tana-tare-dani.jpg

TANA TARE DA NI... TANA TARE DA NI... PAGE 84 BY MIEMIEBEE 9:30PM Farouq ya dawo gida all tired and exhausted kayan jikinsa ya rage, ya ragar da singlet da shorts zalla sannan yachi abinci. “Ya MB Fannah tachi abincin kuwa?” “Eh Boss tachi dinner amman tak’i chin lunch.” “Good ashe dama nasa mata maganin zubda cikin aciki koda shike nasan yadda zanyi na zubar da cikin.” ya sakar dawata muguwar murmushi. Bayan ya gama chin abincin ya nufa d’akin dayasa aka d’auretan, zaune ya sameta tayi shiru abin tausayi. Tana ganinsa tahau b’ari k’ok’arin magana take amman kasancewar bakinta arufe ta kasa, hannu yasa ya b’antare cellotape d’in yana wani shafa kan lips nata ganin bata maqe lips natan chiki ba bata kuma hanasa yi ba yasa sa shiga duhu. Meke faruwa? “Ya Farouq please ka kunche min hannu nagaji dan Allah” tayi maganan cikin wani erin salo da siririyar muryarta me dad’in gaske. Ba musu bale gardama ya bud’e padlock d’in ya since ta. “Ina kashiga yau Ya Farouq?” tayi maganar ba yabo ba fallasa. “Naje processing mana abin international passport d’innan ne did you missed me?” Kai ta gyad’a, dad’i sosai sokon ya jiyo. “Well am here.” “Ya Farouq akwai wata maganar da nakeson muyi dakai dama.” Ta k’are maganar da ‘yar murmushi kwance kan fuskarta. “Mene ne wifey tell me.” “A farko inason baka hak’ui game da abinda na maka d’azu kayi hak’uri bayan nan sekuma batun barin Nigeria dakace zamuyi na zauna nayi tunani tun ba yau ba nakeson zuwa k’asar nan Ukraine nayi nayi da Anas yakaini amman yak’i bature yace oppurtunity comes to life at once so banason missing wannan oppurtunity na yarda zan bika.” Kamar amafarki yake jin zancen. Idanunsa a waje yayi maganar “Fannah? Anya kece kuwa?” “Sosai nice Ya Farouq zan bika Ukraine.” “Why the sudden change?” “Kamar yadda na fad’a maka na zauna ne nayi tunani.” “Oh sweet wifey” ya shafa fuskarta na d’an lokaci ganin bata hanasa ba yasake jin dad’i shi da kansa ya zaro hannun nasa daga baya. “Wifey ina ba wasa kikeson min da hankali ba koh? Dan wallahi nagano tricking d’ina kike me hanani illata ki se Allah.” Zuciyarta taji ya mugun bugawa ji tayi she can’t proceed with the plans sosai tasan halin Farouq har kasheta ze iya in yagano tricking nasa take, nan tabar maganan zucin. “Ya Farouq na tab’a maka wasa ko k’arya ne? I mean what I said just now.” “Toh Anas fa ya kikeson muyi dashi?” “Ya Farouq muddin baraka rabani da abinda ke cikina ba zan iya sadaukar da son danake wa Anas maka.” Baki ya wage wangalau cike da mamaki. “Fannah kinsan me kike fad’u kuwa? Anas fah? Mr. Fauzi!” “Tabbas nikuwa nasani, Ya Farouq a iya ganinka da banyi ba yau na d’an wani lokaci sena jini incomplete na rasa dalili, dana zauna nayi nazari sena gama soyayya ce Ya Farouq kamar yadda kake sona nima haka nake sonka kawai I failed to notice it ne a da se a yanzu ina fatan am not late zaka karb’i soyayya na.” “Kina sona Fannah? Baki tsaneni ba again?” “Ban tsaneka ba Ya Farouq abu d’aya nakeso agareka kamin shi toh I will be all yours zanyi duk wani abinda ka buk’ace ni.” Baki na b’ari dan jin dad’i yace, “fad’i koma meh Fannah, tell me meh kikeso?” “Karka zubar min da ciki, karka rabani da Baby na kamin wannan ka gama min komai. Shiru yayi na d’an lokaci. “Fannah amman aikema kinsan d’an ba nawa bane cikin Anas ne d’an ze zame mana ciwon idanu a rayuwa.” “Ko kad’an Ya Farouq wannan shine ciki na na farko zanso ace na raine sa nakuma haifar, kaga daga nan kaima se in raini naka cikin ko ba haka ba? Ba kace zamuyi aure ba?” “Tabbas na fad’i haka sede kince baraki aureni ba kinada igiyan auren Anas akanki.” “Ada kenan Ya Farouq, ka kwantar da hankalinka a yanzu haka ban damu da igiyar auren ba ni kawai ka kaini Ukraine dreamland d’ina.” “Amgama wifey zakije Ukraine zakiyi zaman Ukraine achan kuma zakiyi rainon ‘ya‘yanmu.” “Kai amman naji dad’i Ya Farouq toh kud’i fa kanada enough? In babu kayi demanding Anas yamaka sending.” “Eh inada, ina guy daya ara min miliyan biyar d’innan? ba nace miki na miyar masa da kud’in sa ba?” Kai ta gyad’a nufin ta gane. Ya cigaba “toh ai andawo da kud’in d’azu sabida yayi tafiya seko wani sati ya dawo kngga ko kafin wani satin mun tafi Ukraine meaning barin biya sa kud’in nasa ba kenan.” “Are you sure Ya Farouq? Barezo ya kama min kaiba? Kasan banason wani abu ya tab’aminafiyarka.” “Yes wifey kinga yanzu inada miliyan 10 kenan ze ishemu settling a Ukraine.” “Sosai ze isa I really can’t wait so yaushe ne tafiyar? Amman still zanso ace miliyan shabiyar mukeda ina gudun kar goma ya kasa.” “Angama wifey zan kira Anas inche ya dad’o min miliyan biyar.” “You will need my help but.” “Ban fahimce kiba wifey” yayi maganar cikin rashin fahimta. “What I mean is that zaka d’aureni kamar yadda ka saba seka d’aukeni hoto ka masa sending nasan yadda yakesona yana gani na a k’ulle ko miliyan nawa kakeso ze baka.” “Wow wifey wallahi you are a genius!.” “Thank you nace yaushe ne tafiyar namu?” “Bare kai nan da sati ba by God’s grace.” “Okay...” Tace blankly. “So wifey yau zamu kwana tare?” “Don’t rush through Ya Farouq nafison se in munyi aure semu soma had’a kwanciya ka gane?” Kai kawai ya gyad’a “Fannah kalleni.” Idanunta ta d’ago tana kallonsa tare da murmusawa. “Wallahi karki min wasa da hankali I love you amman inhar na gano yo are pranking on me wallahi kinji na rantse ba me iya k’watanki.” “Shikenan Ya Farouq tunda baka yarda dani ba ka sake d’aureni kabani waje, dama ku maza duk haka kuke Anas yak’i kaini Ukraine yanzu kai da kace zaka kainin ma dan kaga inaso kafara corner-corner kaima ba damuwa ka d’aureni ka gudu dani Ukraine amman kasani I will never ever love you.” “Ohh wifey dan Allah karkiyi magana haka I’m sorry kawai I want to be sure ne kuma na tabbata dan Allah karkiyi fushi kinji? Yi hak’uri.” Shiru tayi bata ce komai ba. “Please mana Fannah” ya k’are maganar hannunsa kan nata cike da dabara ta janye hannunta daga nasa “naji amman please karka sake cemin haka zuciyata barata iya d’aukawa ba kasan kalan tashin hankalin dana shiga yau kuwa da bansa wannan kyakkyawar fuskar takan a idanu na ba?” “A’a” ya amsa a takaice yana kad’a kai kamar zombie. Daidai kunnensa ta matso ta rad’a masa wani abu ba tare da tabar wani sassan jikinta ya tab’a nasa ba. Tsabagen dad’in daya ji yayi excusing kansa akan bari yaje ya d’auko mata wani abu yana zuwa. Yana ficewa taja wata doguwar tsuka “Allah ya tsine min ne in fad’a soyayya da azzalimi kamar ka Ya Farouq?” Hannu ta d’aga sama “Ya Allah ka jagoranceni in samu in k’wato ‘yancina k’ark’ashin wannan mugun, Ya Allah kabani sa’an gudanar da wannan plan.” Bada dad’ewa ba yadawo dawani package a hannu “gashi its yours.” “Meshi?” Ta tambaya tana k’ok’arin bud’ewa. Wani had’ad’d’en silver bracelet ne ciki. “Uhm Ya Farouq na waye wannan kuma?” “Naki ne wifey yau nagani a store kawai naji I want you to have it.” “Oh is that so? Thank you” ta miyar ta rufe. “Bara kisa bane?” “Zansa mana, meyesa barinsa ba? Sede Ya Farouq nafison se in munyi aure tukuna in fara sa gifts naka kaji?” “But wifey meh aciki dan kinyi accepting bracelet dana baki.” “Ya Farouq trust me ai yanzun ma nayi accepting zan ajiye a wajena kawai sawane barinyi ba ka gane?” “Nagane wifey muje mu kwanta koh?” “Not yet ka manta zaka tambayai Anas kud’i.” “Ohh haka fa!” Nan ya sake d’ad’d’aureta kamar jiya yayi sending message da pictures d’in wa Anas. Hankalin Anas inyayi dubu be tashi ba ganin pictures na Flowersa d’aure again. *** “Hello Farouq dan Allah me kakeso? Me kakeso please kadena bata wahala what is you problem?” “My problem? My problem is money kabani kud’i se in sake ta takwanta.” “Jiya jiya fa na maka sending 3 mil be isaba ba?” “Be isa ba dan bance kayi signing sunan FAHNAS enterprises koh? Eh Fahnas enterprise under my name ba shine zaka tsaya kana gaya min magana? Karka turo kaga d’anyen aikin Farouq.” “Wait.. Wait zan turo nawa kakeso please let her go” “Miliyan biyar nake buk’ata.” “Miliyan biyar Farouq?” Ya zaro weak blue eyes nasa. Me ka miyar dani? ATM machine? Kanada ma hankali kuwa? Ko an gaya maka bana calculating millions da nake maka sending ne? Ina zaka kai 15million please?” “Ina ruwanka? Oversabi zaka turo kokuwa inbar matarka ta kwana haka?” “Zan turo son of a b*tch zan turo please ka saketa.” “Inga alert” ding! Ya katse wayar. Bayan minti goma alert ya shigo masa wani shu’umin murmushi ya sakar “Allah sarki d’an amanah.” Bayan ya dawo da kallonsa kan Fannah yace, “stupid d’in har ya turo.” Sosai zuciyarta ke mata k’ona jin yadda hankalin Anas nata ke a tashe “Anas Habeebi very soon in shaa Allah all this will be over more patience please.” Tayi wannan magana a zuci. “Wifey baki jini bane?” Firgit ta dawo reality. “Na’am kace?” “Nace yayi transferring kud’in we good to go now.” “Wow great!” ** “Wifey are you sure zaki iya kwana achan?” Farouq yayi maganar yana miqe kan gado ayayinda Fannah ke maqure bisa 3 seater dake d’akin ta nannad’e jikinta da bargon ruhuwan daya bata. “Yayi Ya Farouq good night.” “Sleep good” anan ya kashe wutar d’akin. 2:57AM Bayan ta tabbata Farouq yayi nisa a bacci dan uban minsharin dayake ta rafkawa ta miqe sid’ak sid’ak a hankali tho wutan d’kin a kashene amman kasancewar da akwai hasken moonlight dayashigo ta windown yabata damar ganin duk wan abinda ke cikin d’akin clearly, wajen kansa ta dosa tana taku tsili tsili. Wayarsa ta shiga nema dan texting wa Anas location d’in da take, gefensa ta duba bata ga waya ciki ba. Tunanin koya ajiye wayar k’ark’ashin pillonsa ne ya fad’o mata a rai, farcenta tasoma chi a yayinda take nazarin ya za’ayi ta d’aga pillon nasa ganin ba yadda zatayi ta zaune gefe guda tana me cigaba da tunani chan ta miqa hannunta a hankali takai k’ark’ashin pillon nasa har a yanzu baccinsa yake sha wane wanda ya bugu ko k’ara baiji, lalimar k’ark’ashin pillon tasoma amman takasa jin komai bayan ta tabbata babu achan ta nufo side drawern dake kansa dan dubawa danko jiya ciki taga ya zaro sabon waya. Koya akayi bata lura da glass cup dake gabanta ba oho? K’afanta ya bigesa k’ara ya saki akan tiles d’in adalilin haka Farouq ya miqe zaune. “Way-” be k’are maganar ba yaga Fannah tsaye ganin raba idan da take ba taimakonta zeyi ba ta durk’ushe kawai “awchh!” Tafara faking tana matse babban yatsanta “wayyo Ya Farouq k’afana” wutan d’akin ya kunna sannan ya gwada miqar da ita “a’a karka tab’ani please.” Batasan a lokacinda tayi maganar ba. “Mesa?” Ya tambayeta sounding suspicious. “Uhmm uhmmm I mean karka tab’ani k’afan na min zafi.” “Ohh sorry” a hankali ta miqe takoma kan kujerar ta zauna shima ya zauna a gefenta. “Mugani?” Ya buk’ata. “No karka damu zafin ya ragu.” “Me kika tashi yi da tsakar dare haka? Guduwa kikeson yi komeh?” “Haba Ya Farouq wani erin zance kake haka? Kamar ya guduwa inje ina? Kaima kasan _INA TARE DA KAI_ ba inda zani wutan d’akin nakeson in kunna...” Tana maganar ta neman inda switch na d’akin ke kar Farouq ya gane k’arya take thankfully taga switch d’in a saman inda side drawer’n yake. “So nake in kunna I want to use the bathroom sekuma na bige k’afa na.” “Next time ki tadani kinji?” “Toh” a hankali ta miqe tasoma k’ingishi “bari ina zuwa” bayi ta nufa tasakar dawani hamdala “Ya Allah nagode daka kub’utar dani daga sharrin Ya Farouq yau. Huh! I have to be very vigilant” bayan data fito suka koma suka kwanta har ayanzu tunanin yazata samu waya take “koda shike baringa zuwa safiya there must be a way!” Se a yau ne tasamu ta kwanta peacefully tun barinta gida. © MIEMIEBEE

TANA TARE DA NI... PAGE 85 BY MIEMIEBEE Asuban fari ta tashi tayi Sallah da nafilfilunta bata damu da tada Farouq ba danko tasan bayi zeyi ba, bayan ta kammala addu’o’inta takoma kan kujera ta zauna tata Azhkar har garin Allah ya waye. K’arfe 8:30AM ta shiga bayi tayi wanka wani highwaist skirt da karinat blue tasa sannan ta lullub’e jikinta da mayafi babba se 9:30AM Farouq ya tashi ”good morning Ya Farouq” ta gaidashi. “Morning wifey how was your night?” “Alhamdulillah I hope yours too, na had’a maka ruwan wanka kashiga kayi semu karya” ba musu ya miqe yashiga anan ta ciro masa wani sky blue jampa ta ajiye kan gadon. Wajen bayin ta nufa ta kasa kunnenta jin bulbulan ruwa ta tabbata wanka yake dan haka ta nufa wajen side drawer’n kansa, kwalin baby nokia sabi tagani har guda biyar wanda taga alamun kamar an bud’e ta k’arisa bud’ewa tacire se juya baya take gudun kar Farouq yafito. Abin takaici taga ba sim ciki ta duba sauran drawers d’inma babu. “Mschww! Ya Salam!” Cikin wardrobe nasa ta nufa tasoma neman sim card one by one take bin kayakin nasa achan counter’n k’arshe taga sim packs kusan goma hamdala ta saki daidai tasa hannu zata zari d’aya kenan Farouq ya murd’a handle na k’ofan, a gigice ta miyar da su ciki. Da towel d’aure a k’ugunsa ya doso inda take “me kikeyi wifey?” Ya tambayeta ba wasa a fuskarsa. B’arin baki ta soma ganin bata gama miyar da kayan nasa yadda ya bari ba. “Uhmm... Ermm. Ya Farouq har ka fito?” “Eh meh kikemin cikin kaya?” “Bbb.. Babu kaga kaya nake nema maka na cire wancan” tayi nuni da jampan dake kan gadon “sekuma bemin ba nafison kasa farin jampa.” “Hakane wifey?” “Eh Ya Farouq fari zefi maka kyau.” Dad’i sosai sokon yaji “toh ai ga inda nake ajiye fararen kayaki na” nan ta matsa masa ya zaro wani farin half jampa “good kayi ka shirya muje mu karya am hungry.” “Okay wifey” cikin d’an k’ank’anin lokaci ya shirya suka fice zuwa dining room achan aka had’a musu had’ad’d’en breakfast suna hira suna chi Fannah na iya k’ok’arinta dan sakewa da Farouq tanason yayi trusting nata sosai. ANAS 10:36AM Zaune yake a d’akinsa ya had’a uwa uba tagumi gabad’aya ya fita daga hayyacinsa ba aikinsa banda tunanin Fannah rabuwansa da bacci tun da Farouq ya d’auke Fannah. “Anas!” Cewar Abuu yana buga k’ofar d’akinsa. “Kafito mu karya kaji already police d’in suna jiran mu.” Shiruuu... “Anas in shigo?” Nanma shiruu dan haka ya sa kai kawai. Hannu ya dafe a kafad’ar d’ansa. “Anas take it easy wallahi da abinda kakeyi zaka kamu da ciwon zuciya zamu sameta in shaa Allah. Ba kanada bank details nasa ba? Nayi magana da bank d’in za’ayi freezing account nasa.” Cike da tashin hankali ya juyo yana girgiza wa Abuu kai. “A’a Abuu please kar muyi haka wallahi zamu sake worsening situation d’in karmuyi dan Allah banason yayi ma Fannah wani abu.” “Anas wani erin magana kake?” “Abuu please dan Allah kar ayi freezing account nasa ni nasan Farouq.” “Shikenan zan musu magana abari kamar yadda kace yanzu tashi muje mu karya semu fita.” “Abuu fitan nan baida amfani we can’t ever find her hanyan sauk’i shine mu kama Ya Khaleel. yaji an kama Babansa a hannu ze sake min Fannah.” “Anas hakan bame yuwu wa bane we don’t have any evidence da ze nuna Ya Khaleel na aiki da d’ansa.” “Akwai Baba muje mu duba record na Farouq wa yayi bailing nasa am sure Ya Khaleel ne.” “Toh naji yanzu de katashi muje mu karya” Anas ya bud’e baki zeyi magana Abuu ya dakatar dashi “a’a karka cemin bakajin yunwa tashi muje” shida kansa ya miqar da Anas suka nufa dining. ★★★★ FANNAH 1:15PM... Zaune Fannah da Farouq suke akan dining table daidai zasu fara chin lunch kenan aka k’wank’wasa k’ofa “MB get the door” cewar Farouq kamar yadda ya buk’ata haka MB yayi. “Wayene?” Farouq ya tambayui MB. Kafin MB ya amsa yaron yayi magana; “Bad boy ne ya turoni wai abasa kud’insa.” “Ba yayi tafiya?” Yayi maganar yana barin kan kujerarsa dad’i sosai Fannah taji dataga be d’aga wayar saba, yanzu zata iya texting Anas. Har ya kusan bakin k’ofar sekuma ya dawo ya d’au wayar batasan lokacinda tayi tsaki a fili ba. “Wifey lafiya?” ya tambayeta. “Uhmm lafiya, banji dad’in d’aga kan da akayi bane daidai zamu fara chin abinci.” “Karki damu I will be right back” kai kawai ta gyad’a masa ya fice ya rage daga ita se MB a d’akin, abincinta ta nutsu taci se tunanin ya za’ayi tayi texting Anas location d’inta take. Abu kamar wasa fa Farouq be dawo d’akinba. 32 minutes later... K’ofan akayi banging dalilin firgitan da Fannah tayi seda ta yasar da apple dake hannunta tare da juyowa a kid’ime Farouq tagani idanunsa suna wani juyawa kallo d’aya tayi masa tagano abige yake. MB ne ya taimaka ya k’ariso dashi kan kujera ya zaunar dashi. “Omg! Farouq meya sameka haka?” “He had too much to drink” cewar MB. “Okay excuse us zaka iya fita I will take care of him.” Ba musu MB yayi excusing nasu, anitse ta baro kujerarta ta nufa wajensa. “Ya Farouq meya faru? Me kasha haka?” “Karki damu wifey wannan shegen bad boy d’inne yakeson rusa min plans ya dawo kuma yana buqatan kud’insa”. “Toh ka basa mana.” “Wifey kikace miliyan shabiyar kikeso in na basa kud’insa goma ne ze rage.” “Semu sake tambayan Anas ai karka damu kasan me nakeso dakai? Ka huta yanzu kaji?” Kai ya gyad’a mata. Gabansa tayi clearing ta kwantar da kansa a hankali idanunsa suka soma kafewa har bacci yayi gaba dashi. Side pockets na jampan sa ta dudduba bata ga wayarsa ciki ba data leqa setagansa cikin aljihun chest na rigan tunanin ya zatayi ta ciro take seta kai hannunta se tsoro ya hanata danko tana da tabbacin baccin sa beyi nisa ba at any moment ze iya tashi yakamata red handed. Zama tayi gefensa tana tunani chan ta kira sunansa “Ya Farouq!” Shiru ba amsa “Ya Farouq” tad’an buga table d’in. “Urghmmm” yayi groaning cikin bacci. “Ya Farouq ka tashi muje d’aki ka kwanta kaji? Nan is uncomfortable.” “Bari karki damu.” “Dole in damu mana Ya Farouq d’ina na kwance a tak’ure tashi muje d’aki kaji?” A kasalance ya miqe dan yadda ya bugu ko bud’e idanunsa bai iyawa dan bata da wani hali ne kawai tasa hannu ta taresa ganin yakusa fad’i a k’asa. “Astaghfirullah” ta rigayi har seda ta jibgesa kan gadon d’akinsu. Kamar mamaci ya soma sabon bacci wajen. Bad to worse tace a ranta “yanzu ya zanyi inciro wayar yadda yayi ruf da cikin nan?” dabara ce ta fad’o mata. “Ya Farouq ka cire kayan mana zaka fi jin dad’in baccin...” Shiruuu “Kaji Ya Farouq tashi ka cire kayan se ka kwanta” da k’yar ya tashi ya cire kayan ya wurga mata hamdala ta saki. “Rataya min akan drawer” yayi maganan a bige. Yadda ya buk’aceta tayi a hankali ta juyo ta kallesa ganin idanunsa a rufe tasoma lalimo aljihun nasa dan ciro wayar har takai kai sauran cirewa kawaibFarouq ya miqe, da wuri tabar wajen ta k’ariso wajen gadon “mene ne Ya Farouq?” Bakinsa kawai ya toshe agurguje ya ruga bayi amai ya riga kwararowa hakan yabata daman ciro wayar, b’ari duk wani sassan jikinta ke har tasamu tayi texting Anas kamar haka; Anas Habeebi its me Fannah, Mobil filling station Yobe by pass come ASAP and save me please PS don’t call. Bayan tayi sending tayi deleting a take, kafin tace zata miyar da wayan Ya Farouq ya fito daga bayin idanunsa basu sauk’a ako ina ba se Fannah dake riqe da wayansa seda ya k’ariso gabanta ya tambayeta “meh kike min da waya?” Gabaki d’aya ta tsure kasa koda furta ‘A’ tayi se rawa jikinta ke. “Magana nake miki meh kikemin da waya?” “Bbb... Babbu..” Hannu yasa ya fisge wayar, call logs ya shiga ya duba sannan messages nanma bega wani abu ba sede jikinsa na basa ba lafiya ba. “Baki amsani ba nace me kikemin da waya?” “Bb... Babu Ya Farouq wayar ne ya fad’i garin rataya maka kayan naka shine na d’ago.” Tayi magana cikin murya me rawa. “K’arya kike Fannah meh kika min da waya?” “Allah babu Ya Farouq ka duba kaga.” “Fannah kinsan in na gano wasamin da hankali kike zan mugun sab’a miki.” “Ya Farouq ya kake magana haka ne? Kaima kasan wannan ba trick bane inasonka Ya Farouq.” “Barin ga ko dagaske ne kinaso na.” GPS radio yayi turning off sannan ya kira Anas*** ANAS Yana cikin motarsa acikin gari yanzu barinsa police station an yarda da yamma za’a je a duba record na Farouq. Driving yake a hankali koda yaji wayansa yayi k’aran shigowan new message a while ago be damu yaduba ba acewarsa seya isa gida ya duban. Ganin kiransa kuma ake yanzu ya d’ago wayar ya duba sabon layi yagani kafin ya nemi waje yayi parking ya d’aga wayar ya tsinke. Daidai zeyi calling back kenan yace bari ya duba saqon tukunah. K’wararo idanunsa waje yayi bayan daya karanta. “Flower! Its Flower!” Har ya danna numban ze kira sekuma yatuna tace kar ya kirata take yayi mastering numban kar incase zata kirasa. Yakai kan numban Abuu kenan yaga exact numban da Fannah ta turo masa message dashi na kira, ba tare da b’ata lokaci ba ya d’aga “hello Flower??” Wani shu’umin murmushi Farouq ya saki yana kallon Fannah “so its true you called him with my number koh?” kafin ta hankara ya shaqure mata wuya hannunsa tahau bugi “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri ka sak.” Kasa k’arisa maganan tayi dan yadda ya shaqe mata wuya. “Hello Farouq?! Me kake mata please ka saketa. Flower kina jina?” “Anas Habeebi please help me ze kasheni.” tayi maganar da k’yar. “Farouq me kake mata? Ka saketa please dan Allah don’t hurt her.” “Kasheta zanyi ni zata raina ma wayo kasani kayi ban kwana da matarka dakuma d’anka” yana kaiwa nan ya katse wayar. Koda Anas ya sake gwada kira kuwa bai shiga Abuu ya kira da sauri ya fad’a masa location da Fannah ke, shima Abuu ba tare da b’ata lokaci ba ya sanar da police koda ya cewa Anas ya jira sutafi duka a tare k’i Anas yayi he can’t wait to save his Flower. ** “Kiransa kikayi ko meh? Munafukar Allah kawai ni zaki raina ma wayo kiyi tricking d’ina? Me kika yi da wayan nache?” “Aahh..hahhh” ta soma wani erin nishi. “Yya.. Farouq dan-” sama sama nishinta ya soma ganin zata mutu masa ya saketa tari ta hau yi idanunta sun kad’a sunyi jazir suna tsiyayar hawaye. “Wait what do you mean da kikace Anas yazo ya taimakeki, texting masa location d’innan kikayi? Magana nake miki!” Nanma shiru se tari take tayi. “Kin fad’a masa location da muke koh? Hohoho! Smart girl zakiyi bayani.” Akwati ya ciro yasoma had’a musu kayakinsu har a yanxu Fannah bata yi recovering ba daga shaqentan da Farouq yayi bayan yagama had’a musu kayakin ya tattara abubuwan daze buk’ata “tashi mutafi.” “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri karka kaini wani wajen.” “Maganan banza ina ni zaki raina ma wayo? Semuga ya Anas nakin ze cetoh ki” bejira ta sake cewa wani abu b ya fisgota sannan ya soma janta se rok’onsa take amman ko a kwalan rigarsa. Daidai wajen staircase ta durk’ushe ta kankame k‘arafun “meh haka?! Ki tashi mutafi.” “Wallahi barin bika ba mugu kawai ka sakeni.” “Ina wasa dake ne?! Nace ki tashi!” sam tak’i motsawa ganin ba mahalicci se Allah ya sauk’a ya ajiye jakan nasu sannan ya sake haurowa nan suka shiga dambe sam tak’i sake k’arafun gagam ta rik’e ita barata bisa ba seda yayi dagaske sannan ya samu ya sauk’o da ita se fad’anshi take. Wani syrup ya ciro daga cikin jakar. “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri karka sani shan wannan abun, na tuba dan Allah kayi hak’uri...” Ko sauraranta beyi ba yaja hannunta ya danne ta a k’asa tare da had’a hannayenta biyu gu d’aya, kwalban yakai mata baki sede sam tak’i bud’ewa “ki bud’e nace!” Se hawaye take abin tausayi tana girgiza masa kai, “nace ki bud’e” goshi ya gara musu wanda sanadin haka ta bud’e bakinta tare da sakar dawani irin azabartacciyar k’ara, hakan yabasa daman sa mata kwalban a baki seda ya juye mata tas sannan Ya cire, tarawa tayi a bakin nata tak’i had’iyewa “ki had’iye nace!” ganin tak’i had’iyewan kuma tana cinye masa lokaci ya matse mata hanci tun tana iya jurewa har numfashinta ya soma yankewa idanunta sunkad’a sunyi wani irin jaa bayan riqe numfashinta data tayi daga k’arshe kawai ta had’iye ganin zata iya mutuwa ga mugun yak’i sake mata hanci kuma. Daidai nan aka hankad’o entrance door d’in da wani irin force da seda ya k’ofar ya fad’i a k’asa da hanzari Farouq da Fannah ke kwance bisa cinyansa idanunta suna wani kakkafewa ya miyar da kallonsa bakin k’ofar. Fannah kuwa da k’yar idanunta suka iya comprehending mutumin dake tsaye bakin k’ofar. “Anas! Habeebi” kad’ai bakinta ya iya furtawa. “FANNAAAHHH!!!” Ya kira sunanta cikin tattausar murya me uban sauti. Sandarewa Farouq yayi wajen yarasa taya Anas ya samu ya shigo bayan uban securities daya zuba awaje be k’arisa wannan nazari ba yaji an cukumo mai collar riga. Kafin ya hankara Anas yakai masa wani erin mumunar punch da hannunsa me zobuna uku, take hancin Farouq ya fashe ya soma zuban jini. Wani punch d’in ya sake kai masa aciki tare da miqar dashi ko ta kan Fannah beyi ba, nishi yake tamkar zaki. Dogayen k‘afafunsa ya d’aga d’aya ya tunkud’e Farouq dashi seda yayi tumbling a k’asa Anas be barsa ba ba har yanzu. Sleeves nasa ya sake rolling yabi kan Farouq tareda hayewa kansa yasoma kai masa punches tako ina afuska ko wani spot a fuskan Farouq zuban jini yake har yanzu Anas be barsa ba seda yaji muryar Fannah tana kiransa. “Anassss!!!” Da ihu, alokaci guda ya bar abinda yake tare da kewayo wa. “Anas please help me, wayyo Allah !!” ta k’are maganan hannunta dafe kan cikinta se juyi take a k’asan ga wani erin azaban da ita kad’ai tasan yadda takeji acikinta. Hawaye take me tsuma zuciya. A gurguje Anas yayi kanta tare da aza kanta kan cinyansa. Hannunsu ya had’e “shhh! Flower am here, your Habeebi is here kinji stop crying.” A kasalance ta d’ago idanunta ta azasu kan fuskarsa daba abinda ke kwance akai banda tsantsan damuwa da tashin hankali a raunane. “Habeebi I’m sorry, I‘m sorry plea-” bata k’are maganar ba ta sakar dawai irin wahalallen k’ara; “Arghhh! wayyyooo Alllahh cikina Anas help me please zan mutu wayyyooo Allah!!” ta k’are maganar hannunta dafe kan cikinta. “Flower me Farouq ya miki? Meya miki?” Yayi maganar cike da tashin hankali. Da k’yar ta iya nuna masa kwalban da yatsanta, a hanzarce ya miqa hannu ya d’aga “Nooo!! Nooo!! Nooo!! please” abinda yake ta furtawa kenan bayan ya karance jikin kwalban, wani irin k’ara Fannah ta sake sakarwa tuni ya jefar da kwalban tare da d’aga skirt nata jini yaga yana bin k’afafunta unstoppingly. “Noo!! please NOOO! Fannah please noo Flower.” “Anas I’m sorry ple-” bata samu daman k’arisa maganan ba idanunta suka ruhu ta bar motsi kwata kwata. “Flower I can’t lose you please wake up dan Allah kitashi please Flower I can’t leave without you, don’t leave me please” jinin dake bin k’afafunta se dad’a yawa yake. Rungumota yayi a jikinsa gagam tare da had’a musu goshi se kuka yake yana sunbatu. Daga bisani ya mik’e a fusace ya nufi kan Farouq da har ayanzu ya kasa koda motsa k‘afa dan yadda ya bugu kansa Anas ya haye tare da shaqure masa wuya da k’arfin da Allah ya basa, zuciyansa se tafasa yake yana saqa masa ya kashe Farouq kar yayi sparing nasa. “You must die you filthy son of b*tch you are going straight to hell...” © MIEMIEBEE

Share:

5 comments:

  1. kuddos to u miemiee.gaskia inajin dadin wannnan novel din "TANA TARE DANI...."

    ReplyDelete
  2. Kai mungode Allah ya kara basira bt na kusa inga karshen wannan litaffin adai na dely pls. Tnx

    ReplyDelete
  3. 3gbosa 2 u wallahi d buk s intersted acigaba da gashi......................pls

    ReplyDelete
  4. Fatima Abubakar Isah2 October 2016 at 03:33

    Gaskiya Wannan Littafin Yyi Dadi Sosai.

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).