shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 27 July 2016

HEEDAYAH 101-----105

HEEDAYAH!

101
written by miemie


Kwanaki da dama sunja yau kimanin one month 2 weeks knan. Don moha na zaune a parlour yana xane abinku da architecture wayarsa tayi ringing new number ne, "hello?" On the other side akace "mr muhammad on the phone pls?" "Yes" ya fadi a takaice, meshi yace "you are needed now at..." Yamasa kwatancen office nasu heedayah "as a matter of urgency". Nan hankalin don moha ya tashy gashy ba motarsa a gda gdan ummu jalila ya nufa ya ari motarta bada jimawa ba ya iso office nasu heedayah dan wani gudun daya rigayi. Secretary'n wajen yama mgn akan what is going on? tace "are u mr muhammad, mrs heedayah's husband?" Kai ya gyada "yes yes what is it?" Tace "sorry sir but mrs heedayah has fallen sick, tun zuwanta yau take ta amai ynxu haka tana kwance a bay". Cikin murya me nuni da damuwa yace "where is the bay right now?" "follow me" ta fadi suna shiga dakin time din heedayah take fitowa daga toilet tana share bakinta dagani amai tayi, don moha yanufa gunta dawuri "baby whats wrong? Kinbar gda lfya" ta bude baki zatayi mgn se jiri yafi karfinta ta fada a jikinsa, daukanta yayi secretary din tabisu da jakar heedayah agaban mota ya ajiyeta ya amshi jakan tare da ma secretary'n godia key'n motar ya cire yaja motar suka bar gurin.
Yana driving yana kallonta "sorry koh baby, ynzu zamu isa hospital din", Heedayah dake mgn a hankali tace "asibiti? Ni baranje asibiti ba, kawai daga amai sekace xaka kaini asibiti baranje ba take me home, jiya naci sardines nasha milk akai thats why ya bata bin ciki". "Heedayah what are u saying, look at the state of urself kice bara kije asibiti ba, so kke ki mutu min a gda? We're going to the hospital ko bakia so, I wont listen to u this time". Kuka ta fashe masa dashy acikin motar tana shure kafafunta ita barata je asibiti ba haka ba yadda ya iya da ita sukayi gda, tafito daga motar ma takasa dan wani jirin dake dibanta duk sanda ta tsaya shi ya dagota yakaita daki, "me kkeso xaki sha black tea? Kokuma in kira ummu jalila?" T'ake tace "a'a pls dont call her ynxu xata xo ta ta min da hankali am fine stop worrying"...bata gama mgnan ba tajiyo amai hannu tasa ta rufe bakinta ta ruga toilet dagudu ta kwararo amai, don moha yabi bayanta tace "stop there kar ka kariso" sam bejita ba ya karaso yayi flushing aman sannan ya tayata wanke bakinta ya riko ta suka fito kwanciya tayi idanunta se kafe wa sukeyi. Don moha yace "baby ynxu haka kkeson in zauna anan in zuba miki ido, kina vomiting life naki out? To mummy fa? In kirata?" nan ma tace "a'a dont worry i'll be fine," yace "toh ko magani seki sha ai" tace "no need banason magani lemmi get some sleep first" rufeta yayi da blanket ya fice kwata kwata yakasa samun sukuni se tunanin baby'nsa yake haka ta wuni ranan tana amai, duk abinda taci hararwa take akaita asibiti tace a'a akira ummu jalila kosu mummy nanma ta ki, bata damu ba saboda kwata kwata bata kawo hankalinta shigan ciki ne da ita ba.
Washegary kuma ta tashy tana shirin office, don moha ya tarar da ita "ina zuwa kuma?" Tace "office mana" don moha yace "really? Bakida lfyan ne zakije asibiti? Jiya ki wuni kina amai a gdan nan yau kice zaki office? Ure not going anywhere" heedayah tace "but am fine, can't u see?" Don moha yace "this discussion is over baraki fita ba yau," yana kaiwa nan ya fice heedayah ta zauna kan gado tana guna guni "ni shknan se abinda kace inyi xanyi mstw wlh ni Allah ya isa"...bata kare mganan ba tajiyo amai da gudu ta ruga toilet bayan tagama ta wanke bakinta tafito taga don moha tsaye a bakin kofan bangdan yace "a hakan ne zakije office yau? Kuma ki shirya asibiti zamu je now!" "Wlh ni baranje ba sede kaje kai kadai" cewa yyi "ni de na gaya miki ki shirya" ya fice. "Wlh ni baran jeba mstw wait a minute yau meh? Ai yakamata period dina ace yazo what could be the problem? Oh no kode ciki nake dashy? No it can't be possible, let me wait again.
Yau kimanin sati kenan heedayah najiran period nata amman shieu ga issue of amai har ynxu duk abinda taci seta amar dakuma jiri ita kadanta seta fadi duk ta canza kamanni, taje asibiti kuma taki don moha yayi yayi da ita suje amman sam taki hasali ma anytime yayi coming up da talk din kuka take masa tana hada sa da Allah. Yau bayan don moha ya fita zuhr prayer heedayah ta lallaba zuwa chemist dake dan kusa da gdansu ta siyo home pregnancy test har ta dawo don moha be dawo ba toilet ta nufa tayi carrying out test din se addu'a take Allah sa kar ya kasance positive. Yana gama reading yayi showing positive. "Gosh! Noi!"Ta fadi "this can't be true, I can't be pregnant." Alwala ta dauro tayi sallah taje dining shan ruwa nanne don moha ya dawo gda, tana gama sha ta hango wata roasted chicken cikin fridge din part daya ta ballo takai baki tana cikin tonawa kawai amai ya zo mata daki ta nufa dagudu don moha yabi bayanta data gama tafito don moha na tsaye a bakin kofar bangidan "ungo" gyalenta yake mika mata "sa asibiti zamuje ko kinaso ko baki so, since last 2weeks kke abu daya am tired of seeing u like this", gefensa tabi ba tare da ta cemasa komi ba ta zauna kan gado. Don moha yac "well? Barakisa mu tafi bane?" Kai ta gyada masa hannunta ya finciko yana janta har sukayi parlour tana fadin "let go off me you're hurting me" dakyar ta iya kwace hannun nata ta zauna a kasa "wlh na gaya maka baranje asibitin nan ba". Don moha yace "haka kka ce ko?" Wayarsa ya ciro yakira ummu jalila kan if shes free tazo ynxu pls ta amsa da toh. Heedayah tuni ta fashe da kuka "ynxu kiranta kayi? Kasan sarai ynxu zata zo tafara min masifa, dama nasan kai mugu ne" suna cikin mgnan se ga ummu jalila ta shigo "ya meya faru muhammad? Heedayah me kkeyi a kasa? Me haka duk kin zube?" Don moha yace "gata nan ummu jalila tun last two weeks take fama da amai duk abinda taci seta harar aje asibiti tace bara'a je ba..
HEEDAYAH!

102
written by miemieKallo d'aya ummu jalila ta mata ta gano ciki ne da ita. Tace da don moha "ynxu muhammad matarka nada ciki baka sani ba? Kema heedayah bakisan ciki ne da ke ba?" Tuni heedayah ta karbe mgnan "ciki? Ummu jalila nifa ba ciki bane dani", ummu halila tace "rufa min baki dama ke likita ce da zakisan ko kinada ciki, amman period naki fa kinyi dis month?" Heedayah tace common ummu jalila agaban muhammad kke min mgnar period? Ummu jalila tace yoh ba mijin ki bane? Ai ba kunya a tsakaninku, answer me!" "eh mana abinda jiya ma ya tsaya, nifa na gaya wa muhammad lfyta qlou kawai abu naci ya bata min ciki, shegen fitinan sa ne yasa yaki yarda". Ummu jalila tace "kalleni heedayah!" Kallonta heedayah keyi tace "kai ban yarda ba muhammad jeka siyo min pregnancy test strip dinnan". Heedayah tace "haba ummu jalila ciki abin farin ciki ne ai inda inada ciki ai kinsan bawanda ze kaini murna da farin ciki, Allah ba ciki bane dani". Ummu jalila tace "hakane kinyi gaskia, seki sha magani ai dan aman ya tsaya". Nan heedayah ta tashy ta nufa dakinta wani ajiyan zuciya tayi bayan da ta rufe kofar, "ai wallah baran bari kusan inada ciki ba, cab! Ynxu wannan ummu jalilan nan ta fara dura min jiqaqe takuma hanani zuwa office. A parlour ummu jalila tace "muhammad nifa ban yarda da matarkan nan ba gashy nan duk idanunta sun nuna tanada ciki", don moha yace "anya ummu jalila? ai barata mana karya haka ba", ummu jalila tayi murmushi "is like na fika sanin halin matarka, anyways kasa mata ido am sure ciki ne da ita kawai tana boye mana ne". Don moha de har ynxu be yarda da zancen ummu jalila ba.
Ko fita zuwa parlour heedayah batayi ba ranan kar incase tafita amai ya xo mata, tunanin ya xatayi da cikin take amman sam ta kasa figuring out komi. Don moha kuwa da tunanin abinda ummu jalila ta gaya masa daxu yake tayi, dashy yayi bacci. Washegary! hedayah ta shirya zuwa office, egg tayi frying tana cin kadan amai yazo mata bayan tagama ta wanke bakinta daga karshe black tea ahine bata harar ba. Dakin don moha ta shiga sidak sidak tashiga ta bude wardrobe nasa ta ciro car key'n har ta kai bakin kofa don moha ya tashy "oya oya return the key", heedayah tace "haba don moha me zan zauna inyi a gda, kasan fa ba a wasa da aikin office". Don moha yace "ai office dinma sunsan bakida lfy", tace "ba na warke ba bye ni na tafi" bata jira me zece ba ta fice.
Saidai ko a office din shes weak aiki ma da kyar takeyi co workers nata ne suke ta teasing dinta "maman unborn ai da kinbar zuwa office din kibari in kin dan samu karfin jiki seki dawo," heedayah tace "wai waye maman unborn? Bafa kuda damuwa". Nan ta tashy kasancewar azahar yayi ta nufa inda suka saba yin alwala da sallah. Amai ta riga kwararowa a toilet din da kyar ta iya tayi alwala tana fitowa jiri ya kwashe ta tafadi a bakin kofar. Co worker'nta ne tashigo da sauri ta nufa kanta ta kwantar da ita kan gado "heedayah ya haka? Cikin nan na baki wahala, bakida lfya sekace dole sekin zo aiki, ina wayarki in kira mijinki yazo ya daukeki". Da kyar heedayah ke maganar tace "pls a'a karki kira sa wlh bare barni in sake fitowa ba, yunwa nakeji pls a ina zan samu black tea yi hkr". Jidda tace "toh wait for me here," daman tana zuwa da flask nata nan ta had'a ma heedayah tea ta kai mata dakyar ta iya shan rabi shidinma ta harar, bakaman daxu ba. Jidda tace "gaskia heedayah karkizo aiki gobe a banza zaki wahalar da kanki kin ganki kuwa? Kkace kar a kira mijinki?" Heedayah tace "eh i'll be fine barin dan kwanta", badan jidda naso ba ta barta.
Lokacin tashinsu nayi dakyar heedayah tashiga mota takasa kunna motar ma bale tayi driving, daga karshe jidda ce takaita gda sannan ta tsari napep. A bakin kofa ta danna door bell kafin don moha yazo ya bude mata ta zube a kasa. "Heedayah!" Nan ya kinkimeta ya ajiye ta kan 3 seater "ya haka?" yana taba jikinta yaji zafi kamar wuta a zuci yace "what if abinda ummu jalila ta fadi gaskia ne, what if heedayah is really pregnant?" Nan yabar mgnan zuci yace "baby sanda na gaya miki kar kije office yau bakida lfya amman sam kika ce sekinje am telling you ba inda zakije gbe nd wani erin ciwon ciki ne haka? Kinji tempreture'n jikin ki kuwa? Anya ba malaria bane? Asibiti zamuje gbe no argument okay?" Bata ce masa komi ba yatashy yaje had'o mata black tea. Wani wutan tsanan don moha ne yake ruruwa a zuciyar heedayah simply bcuz wai shi ne sanadin duk rashin lfyr da take fama dashy ynxu, da be raba ta da budurcinta ba da ynxu tana flexing abinta. Hannun ta tasa kan cikinta duda wahalan da cikin ke bata setaji tana son abinta, she wants to be a mother. "My baby either a boy or a girl you are, I love you but I don't love your daddy," tana ganin don moha ta daga hannunta daga cikin nata black tea din ya mika mata da wasu maguna, tea din ta amsa ta tashy zatayi d'aki gudun kar tasha a gabansa amai yazo mata, don moha yace ina kuma xaki tace d'aki am not comfortable here. Ta mike kawai seta zube Allah yaso don moha na kusa da ita take ya tare ta tea'n besamu ya zube ba daki ya kaita tace "u can go now, I will manage", don moha yace "so kke na fita ki zubar da maganin de", tace "kafini son kaina ne? Nace zan sha leave my room now".
Don moha yace "in kinga na fita daga d'akin nan sekin had'e maganin" heedayah tace "lalle kuwa bacci a d'akin nan ya kama ka dan baran sha maganin nan ba", haka suka ta yinta da don moha taki sha daga karshe yace "wlh in baki sha ba kinsan yadda ake ma yara durai? Shi zan miki nd am damn serious malaria ne ke damunki ga body tempreture'n ki ya hau, magann anti malaria ne kuma dole sekin sha kiga yadda kka rame, so kke se su mummy sunzo suga duk kin rame suce am not being a good husband to you?" Heedayah na jin don moha yace anti malaria ta kuma jin barata iya shan maganin ba cuz anti malaria's are very harmful to a pregnant mother.

HEEDAYAH!

103
written by miemie"Well bara kisha bane?" Kai ta gyada masa, tasowa yayi dgsk ze d'ura mata kuka ta fashe masa dashy "don moha baran iya shan mganin ba pls dont force me too", yace "mesa bara kisha ba? Kin gommaci kita vomiting life naki out? Yau fa sekinsha maganin nan", volume na kukanta ta kara tana hada sa da Allah. Ran don moha in yayi dubu be baci ba "shknan since u prefer to stay sick i'll let you", yana kaiwa nan ya fice tare da banging mata kofar sanda taji tsoro. Har ynxu kukan take da kyar ta iya tasha tea'n nd alhmdulillah bata harar ba. Bacci tayi me kyau se kusan maghrib ta tashy ta dafa indomie tana zaune a d'akinta tana ci tajiyo amai, dagudu ta ruga bathroom tana cikin yi don moha yashigo bathroom din yatayata wanko bakinta da kyar take takawa dan wani jirin dake dibanta akan gado ta baje.
Moha yace "baby mesa kke da taurin kaine? Mesa bara kisha magani ki warke ba, kullum cikin amai kga bakida ma karfin zama, there must be a reason dayasa bakisan shan maganin tell me, are u really pregnant?" Heedayah tace "wani erin mgn kakeyi ina zan samu ciki nifa na gaya maka am not pregnant". Don moha yace "then mesa barakisha maganin ba?" Shiru tamasa bata ce komi ba. Yace a zuci inma cikin ne dake kke boye min I'll found ouf myself, goodnight peck ya bata take tasa hannu ta goge, murmushi yamata yafice dakinsa. Cikinta ta rike "baby why are u giving ur mum a hardtime? Is it bcux I dont love ur father? Pls am sorry if u continue like this baranzo in iya ba", isha ta idar da kyar ta kwanta.
Washegary ta tashy da kyar ta shirya office bayan aman datayi sekace aikin dole, d'akin don moha ta shiga har ta dau key bejita ba sanda tazo rufe kofar yajiyota tashy yayi da sauri ya nufa kanta key'n ya kwace, "ahaka zakije office din yau? Kalleki ko karfin kirki bakida, ure not going anywhere!" Heedayah tace "seka hanani ai, thank god ba motarka bane kadai means of transportation", bakin kofa ta nufa da sauri don moha yasha gabanta key ya juya a bakin kofar, sannan ya zaro "lets see ta ina zaki fita yau" back door dinma rufewa yayi sannan ya nufa dakinsa. Ashar heedayah ta riga durawa.
Around 10:45AM don moha yatashy bayan yayi wanka ya nufa dakin heedayah ya sameta kwance bargon da ta dukunkune kanta dashy ya yaye iya face nata dakyar take bud'e idanta hannu yasa ya tab'a tempreture'n jikinta yaji kamar wuta. Custard yaje ya had'o mata da kamar barata karba ba amman dan yunwan da takeji ta amsa, kwata kwata spoons biyar tayi shima ta harar take. Tana jingine a jikin gado don moha yace "heedayah look at me, ure pregnant isn't it?" Yauma answer'n jiya takuma basa ba yadda beyi da ita ba kan ta gaya masa gaskia amman tak'i.
Acikin sati heedayah ta zube takoma kamar k'ashi da rai ba abinda yake zama a cikinta komi taci seta harar, office kam ba labarinsa. Around 4:15PM don moha na zaune a parlour ya tara kayan k'olama a gabansa erinsu tuwon madara, gullin tsiya, tsamin gaye... Ba abinda babu yana jiran fitowar heedayah. Karap! ta bude kofar dakinta da tafiyan ta kamar wanda koi ya fashe ma a ciki, fridge ta nufa tasha ruwa tundaga dining space ta hango abubuwanda suke gaban don moha kawai taji kodayin ta ya shiga har zataje ta dauka sekuma wata mind tace mata "dont u get it, don moha is playing games with you. Yanason yasan ko kinada ciki ne, nd the moment kka je kka dauka shknan ze sani", mind nata tabi da kyar ta iya had'e kwad'ayinta ta nufa d'akinta don moha na binta da kallo. Yace kinmin wayo knan dont worry I have a bttr plan in store for you.
Kash! Sede duk plan da don moha yake setting heedayah is always one step ahead of him. Rana d'aya bayan don moha ya dawo daga masjid har ya kai bakin kofan dakinsa se wani abu yace yaje ya duba heedayah dab yakaiga bud'e kofar seya jita tana kan waya tana fadin "ai baran tab'a gaya masa ina d'auke da cikinsa ba, I don't love him ni rayyan nakeso..." Haka ya kasa kunne yana sauraronta kap duk abinda ta fada yajita, take idanun sa suka kad'a sukayi ja, zuciyarsa tana me masa rad'adi. Tana gama wayan ta bud'e kofar, gabanta ne ya mumanan fad'i ganin yadda don moha ke kallonta dagani yajiyo duk abinda ta fadi hannunta yajawo ya zaunar da ita kan kujera a parlour. Ba abinda heedayah keyi se raba ido, don moha yace "so its true ure carrying my baby? Nd kka min karya that ure not pregnant?" Zatayi mgn yace "shush! Am tired of listening to ur lies, ko Allah ma sheda ne heedayah tunda kkaxo gdan nan ban taba hurting naki ba abinda kkeso shi nake miki, abinda nakasa ganewa har yau shine mesa kkayi hating dina haka? What have I done to you da kka gommaci ki kuntata min heedayah, ace you are pregnant but kkayi deciding to keep it to urself toh yau Allah ya gano dani gaskia, barin ce zan kai karanki gun mummy ko ummu jalila ba as if u do good kayi wa kanka anytime kke needing abu just let me know nd no matter me kka min know that i'll always love you" yana kaiwa nan ya fice zuwa dakinsa. Heedayah da tuni zuciyarta ta karye tayi karfin halin fad'in "toh se meh dan kasani it still wont change a fact btw us bana sonka muhammad rayyan nakeso".
Tun daga ranan word be sake had'a heedayah da don moha ba kwata kwata yafita daga harkanta, itama haka ba wanda yake cema dan uwansa ko uffan haka suke kwana su tashy. In sukayi bak'i kuma se suna pretendn as if they are on good terms, ummu jalila kuwa koda ta tambayi don moha about pregnancy'n heedayah ce mata yake shima be sani ba. Yana zaune a parlour aka danna doorbell yana bud'ewa yaga shams ba karamin mamaki tabasa ba "yanzu don moha heedayah ka aura? Bayan ina raye, mesa xaka min haka don moha kasan fa inasonka wlh wannan aure bata dauru ba dole ka saki heedayah ka aureni, ina raye barin bari wata ta mace ta mallake ka ba", don moha yace shams "what are u doing in my house? In ma wani ne ya turoki dan ki rabani da heedayah to baki isa ba". Shams tace "haba don moha after saying kanaso na zaka aureni sekazo ka auri heedayah? kace min after 2 mnths da bikinku zaka kawo ni gdanka amman har yau shiru, kana ganin ka kyauta knan?" ras mgnan ya fad'a kunnen heedayah data zo dining shan ruwa "what is she saying?" Lekawa tayi taga shams "Innalillahi so for all dis while don moha is cheating akaina, yakuma rasa da wa xeyi seda shams", gun ta nufa ta tsinke shams da mari don moha na ganinta bece mata komi ba. "Its really true bakida shame shams, ure a disgrace to all women, to in baki sani ba kisani yau don moha ba class naki bane, he's never gonna be urs tun kafin raina ya baci in miki abinda bakiso ki tattara kazaman kafafunki kbr min gda b4 raina yabaci inyi kasa kasa dake anan", ta dawo da kallonta kan don moha "get rid of this trash" tana kaiwa nan ta koma dakinta. Kuka ta fashe da ni miemie nace toh kukan meh? Bayan ke kkace baki sonsa, lalle kam heedayah akoi kishi.
Me gadi don moha ya kira dan shi bare iya taba taba shams ba,waje aka jata tace "ko ma me de na cimma burina am sure heedayah barata yarda taxauna dakai a gdannan ba, since I can't have you no one can have u either!" Da sauri ya nufa dakin heedayah dake kuka tana ganinsa ta share hawayenta yace "heedayah dont tell me kinyi believing abinda shams ta fada dazu, shes just making up stories ai kema kinsan I'll never do that to you so take kawai ta rabamu nd ure allowing her to do that by agreeing to what she said". Heedayah tace "shut up! U liar, Don moha Allah ya isa tsakani na dakai daman all men are cruel bakuda imani after getting me pregnant ynxu kaje kana flirting awaje ka kuma rasa dawa xakayi seda shams?" Hannu tasa ta goge hawayen dakeson fito mata "anyways damuwanka kaga dama ka aurota kai kasani iyaka in abinku ya isheni in tattara kayakina in bar muku gdan ne". Don moha zeyi mgn heedayah tace "i've heard enough leave my room, now!"

HEEDAYAH!

104
written by miemieDon moha yace "no heedayah believe me wlh am telling u the truth" tace "in baraka barmin dakin ba ni zan bar maka", yace "no u don't have to". Yana kaiwa nan ya fice be tsaya ko ina ba se gdan ummu jalila ya zazzage mata komi ciki harda lbr'n cikin heedayah. Murmushi ummu jalila tayi cike da mamaki don moha yace "murmushi fa kkeyi ummu jalila?" Tace "yes am happy for you, this is only meaning heedayah na sonka tunda har tayi kuka akan abinda shams ta fada, kasan me nakeso dakai?" Kai ya kad'a mata ta rage muryarta ko me ta gaya masa oho! Don moha yace "ummu jalila I cant hurt heedayah like that", ummu jalila tace "stay there kowa yyi aure yana mulmulewa kai kullum cikn damuwa matarka bata sonka do as I say kaga am telln u barakayi regretting wannan shawarar ba". Don moha yace "toh shknan" ya mika mata wayar tazuba wata number aciki ahaka ya koma gda. Sam yakasa yin abinda ummu jalila tace yayi, gashy kwata kwata heedayah ynxu bata kallonsa da daraja koda sun had'u harara take watsa masa.
One month later cikin heeayah nada wata biyu da weeks akai, ko asibiti ta je ta duba lafyr abinda ke cikinta tak'i. Morning sickness da zazzabin da ta saba yi kuwa da d'an sauki, dan ynxu tana d'an iya cin abinci sede ba kowani eri ba. Su mummy da nanny sun mata paying visit, sam bata gaya musu tanada ciki ba, amman su kam tuni suka gane dan wani hasken da ta k'ara.
Kasancewar yau saturday heedayah na gda bata je office ba, tafito daga dakinta seta labe a jikin curtain dake parlour'n kasancewar taga don moha na excercise, lekan sa, omo zokuga muscles tsayuwa tayi tana kallonsa kawai setaji sansa na shiganta, gogan namu kuwa ashe tun tsayuwanta awajen ya ganta kasancewar akoi wata glass cup a gabansa wanda yayi reflecting shadow'n heedayah murmushi yayi sannan yace "you think am hot don't you?" Heedayah taja tsuka "wani hot? Nifa ba kallonka nake ba", don moha yace "ba sekin min karya ba ga shadow'nki a nan" yana nuna mata glass cup din, bata iya tace masa komi ba, dakinta ta ruga da gudu dan wani kunyan daya rufeta. "Mstw shknan ynzu ze dauka inasonsa, what is wrong with me? Mesa nake feeling kamar inason sa?" Ni miemie nace ba kina d'auke da cikinsa ba ai dole kifara jin kinasonsa tunda kina son abin cikin kin.
Da daren ranan bayan ya dawo daga sallan isha yana zaune a parlour daidai 8:55PM ya dau wayarsa yakira number'n da ummu jalila ta basa ranan (number'n sister'nta nafeesa). Daman kullum 9:00PM heedayah ke fitowa tasha ruwa kafin ta kwanta. Tana fitowa daga d'akinta tajiyo don moha na waya kunne ta kasa setaji duk kalamun soyayya yake fadi, tuni zuciyarta ta karye dagudu ta nufa parlour'n da wuri ya yi hanging call din heedayah da tuni kuka yafi karfinta tace "wlh Allah ya isa tsakani na dakai mugu kawai banda shams kanada wata budurwa, kuma dan iskanci a gda na kake min waya da shegyar buduwarka wlh baka isa ba sena gayawa mummy". Ta kare maganan da kuka, Don moha dake murmushi yace "ya haka maman baby? kishi kke akan abinda baki so? Kefa kkace bakisona so is it wrong, nasamu wanda take sona se barin kulata ba? like d way kkeson rayyan nima haka nakeson safrah". Yana kaiwa nan delibrately yabar wayarsa a bud'e ya fice xuwa dakinsa heedayah na ganin yashiga dakin ta karasa tadau wayar messeges tashiga taga duk love mssgs suke exchanging da safrah, nan don moha dake lab'e ya na dariya ya fito ya amshi wayar "maman baby me kkemin da waya? Banason shishigi fa" yakama hanyan dakinsa gabansa tasha "wlh baran yarda ba, dama ku maza haka kuke d moment kuka samu abinda kuke nema a jikin mace se ku fara kula na waje toh wlh baraka min wannan iskancin in barka ba" don moha yace 'maman baby kin tab'a ganin inda mata ta hana mijinta k'ara aure? Kuma fa ke kkace bakisona, its simple tell me u love me se inbar kula safrah". Heedayah tace "ni zaka raina ma hnkl wlh baran fad'a ba" mayafinta ta yafa da daren ta fita zuwa gdan ummu jalila tana mata kuka. Da kyar ummu jalila tasamu tayi calming nata "ya haka heedayah da daren nan, ina muhammad?" Heedayah dake kuka tace "muhammad ne", "ummu jalila waya da budurwa yakemin a gda har mssgs da suke exchanging na gani, dan Allah ki masa mgn taya inada cikinsa ze auro min wata". Sister'n ummu jalila nafeesat dake lab'e tana jinta se dariya takeyi, itama ummu jalilan dakyar ta iya had'e dariyan ta tace "toh kema heedayah ai da naki, tun farko ke kka nuna masa baki sonsa dole ya fara neman mata a waje mana, ko kina sonsa?" Heedayah ta turo baki "ni bana sonsa" ummu jalila tace "den why getting jealous? inhar baki sonsa ai seki barsa ya nemi wacce takesonsa" "wlh baran barsa ba nidin ba rabani yayi da rayyan ba ynxu kuma seyace ze min kishiya wlh baran yarda ba". Ummu jalila tace "fine seki gyara ways naki tuj kafin tashigo miki gda ki fara nuna masa kina sonsa believe me bare kawo miki kishiya ba". Heedayah tace "ynxu bara ki masa mgn ba knan?$ Ummu jalila tace "ai banida right na hana sa yin aure ko mata uku yace ze kawo miki he has the right to", heedayah dake kuka tace "ai dama nasani muhammad kke so kke daure ma baya bani ba, inda shine ya kawo miki wannan mgn tuni zakije ki fara min mgn ba damuwa" tana kaiwa nan ta fice zuwa gda, kukanta tasha har bacci yayi awon gaba da ita.
Washegary heedayah ta tashy tun safe ta dau wata trolley'nta tana shirya kayakinta ita a dole zatayi yaji...

HEEDAYAH!

105
written by miemie


Around 8:30AM tagama had'a kayakin nata, don moha na tsaye a dining yana shan ruwa heedayah ta fito da akwatinta tana ja, kasancewar bata gansa ba yace "maman baby ya haka? Ina xakije da akwati?" Heedayah tace "bansani ba ai wlh Allah ya isa tsakani na dakai, mayaudari kawai" yana kallonta yana murmushi ta fice ko damuwa beyi ba sbd duk sun had'a baki da mummy inda yake da tabbacin can heedayah zata. Napep ta tsara har gaban gdansu ya sauketa, kuka ta kirkiro ta shiga gdan tana kuka me gadi na mata mgn ko kallonsa batai ba kujera ta nema ta zauna a parlour nanny dake kitchen tafito tayi kamar bata san meke faruwa ba, "heedayah ya haka harda akwati? Hajiya! Hajiya! Zokiga abin mamaki", nan mummy ta fito ita kadai kasancewar daddy yayi tafiya bai gari.
"Heedayah ya haka meya faru?" Heedayah dake kuka tace "mummy muhammad ne wai aure ze sake, dudu watannin mu nawa ne da aure da zece ze sake aure". Mummy tayi kamar bata san da zamcen ba tace "aure kuma? Haka kawai yace ze kara aure? Ba tareda kin masa komi ba?" Kai heedayah ta gyada mummy tace "kai heedayah ban yarda ba karya kke min nasan muh'd da hankl bareyi abinda kke gaya mun ba ko in kirasa in tambayesa?" nan heedayah tafara raba ido, "in kira sanne?" "Eh kikira san". Nan mummy ta kira don moha ya irga mata tas erin xaman da sukeyi da heedayah bayan daya gama mummy tace "baga irinta ba, da kinji mgn na da duk haka be same ki ba, sau nawa nake miki wa'axi amman kkayi watsi dshy gashy ai ynxu muh'd ze kawo miki kishiya seki san yadda zakiyi". Heedayah data k'ara volume na kukanta tace "ni wallahi baran koma gdansa ba seyayi auren", mummy tace "ji mgnan banxa dan mijinki ze k'aro aure seki gudu kibar masa gdan? Maza nanny ja mata jakarta mal idi na nan yayi dropping nata".
"Wallahi mummy baran koma ba, keda kullum kina side dina yau kuma don moha kke biyewa ai dama nasani daddy na kawai ke sona daddy! Daddy! Dan Allah come md help me" nanny tace "hkr zakiyi heedayah daddy baya gari yayi tfya" tana ja mata akwati. Mummy tace "well? Baraki tafin bane? Karfa kga dan kinada ciki kice baran dake kiba, I love you heedayah sesa zan maidake d'akin mijinki it still not late in xakiyi changing ways naki am sure muh'd bare karo miki kishiya ba", haka de tata ma heedayah wa'azi amman heedayah kam yashiga ta nan ya fita ta can ne.
Haka da kuka mal idi ya kaita gda a waje ta zauna sanda zaman wajen ya isheta sannan ta shigo daidai 11:05AM knan don moha na zaune a parlour yana breakfast yana kallo. Bece mata komi ba haka itama d'akinta ta nufa ta baje kan gado se sharb'an kukanta take abin tausayi ni miemie nace whats there heedayah? Go nd tell ur husband kinasonsa nd bare kawo miki safrah ba, amman sam t'aki jina. Don moha daya lab'e a bakin kofar yana kallon yadda taketa kuka duk seyaji he can't continue with the plan, bare iya ganinta tana kuka haka ba, har ze shiga d'akin sekuma wani abu ya hanasa, d'akinsa ya nufa ya mike kan gado yana tuanin maman baby'nsa.
Kuka ta riga yi har sanda bacci ya dauketa se azahar ta tashy ta jita duk weak gawani yunwan datakeji danko breakfast batayi ba kitchen ta nufa tayi frying chips a zatonta ko xata iya ci sam ba haka abin yake ba, tundaga parlour don moha yakejin karan aman da heedayah keyi tausayinta duk ya kamasa da gudu ya nufa d'akin yana tsaye akanta har tagama aman yataya wanke bakinta ya kwantar da ita a kan gado "baby how are u feeling? Muje asibiti?" Banza tayi dashy haka yata suratansa amman sam taki amsa sa haka ya gaji ya bari, yana fita daga d'akin tace "wlh don moha u can't have it all baran bari kamin kishiya ba".
Ummu jalila ya kira takuma basa karfin guiwa dan har ynxu heedayah bata gasu ba, the moment ta gasu zata fara kula ka so dont stop with the plan, da kayar ya amsa mata da toh.
Haka seyaji heedayah na fitowa daga d'akinta yake kiran nafeesa sister'n ummu jalila wanda heedayah ta dau safrah. Zuciyarta k'ona take mata dan ba karya heedayah akoi kishi kaman daga sama ta kwace wayar don moha tace da nafeesa as safrah "toh karuwa, ko kunya bakiji kiran mijin wata toh wlh kisani today shud be the last day da zaki sake kira min miji in bahaka ba i'll make sure you'll need a face with construction shameless woman kawai," nan tayi hanging sannan ta watsa ma don moha kallo "wlh muhammad ka sake kira min wannan shegyar a gda you'll answer to me ko kunya bakaji ina d'auke da cikinka kaje kana waya dawata banza a waje kuma ba wani had'uwan da zakui yau". Nan tayi deleting number'n safrah da don moha yayi saving da boo sannan ta ajiye masa wayar ta nufa dining ta dau ruwa ta fice zuwa dakinta.
Don moha dake binta da kallo yana murmushi sosai yace "ashe my baby is so jealous about me". In akoi abinda ke burge don moha shine yaga heedayah na getting jealous akansa, its only showing him that she loves him so much.
Bayan la'asar around 5:00PM don moha ya kuma yin wanka yasa wata farar jampa ya cokala hulan nan kyau kamar a cinyesa ya feffeshe da turare sannan ya tattaro wayoyinsa yana fitowa parlour yaga heedayah na zaune kan kujera ita da kullum a daki take kallonsa take w'ane yau ta fara ganinsa dan wani kyan dayayi kasancewar be cika sa jamfa ba duk sanda yasa seya yi wani kyau na musamman. "Hello baby gani nan fitowa, yawwa love you". Heedayah da takeji kamar tayi commiting suicide (ta kashe kanta) tace a zuci "se muga yadda zaka hadu da karuwar kan ai yau!". Taku one by one yake cikin tak'ama da isa ya nufo bakin kofar sede daya gwada bud'e wa sam yak'i buduwa, ko kallonsa batai ba hasali TV'n dake gabanta ma tayi focusing akai sosai. Bece mata komi ba yazagaya ta back door nan ma story din is dsem heedayah tayi locking kuma ta zaro keys din. Parlour'n ya koma ya tsaya a gabanta tace "ya haka malam ko baka ga ina kallo bane? Shift abeg"
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).