shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 13 July 2016

HEEDAYAH 13-14-15-16 & 17

HEEDAYAH!

13
written by miemie


4 days later** su mummy duk sun gama shiri dake yau zasui tafiyan flight nasu na 7:00AM ne, alhj lawal kuwa har yaje yayi representing dady nd the meeting was a success yaci dady yamasa godiya sosai. For 2 days kafin tafiyarsa abujan kuma yake zuwa gdan alhj ismail yana sa mai maganin da malaminsa yabasa cikin ruwan sha, a ynxu haka har ya fara controlling alhj ismail amman ba sosai ba tho befara masa maganan cin arzikin alhj s.u ba, yana jiran se in sun dawo frm washington din tukuna. Heedayah kuwa taki fitowa daga dakinta se kuka take zubawa se can dasu mumy zasu tafi sannan suka haura sama har da daddy da bai da lafyan ma, mumy tayi iya suratanta heedayah taki bude kofa sanda daddy yasa baki shima da kyar sannan ta tashy ta bude tayi hugging daddy tana ta kuka me tsuma zuciya, mumy batasan sanda tafara kuka ba itama ji take kamar su tafi da heedayah amman sch nata kuma fa? Da kyar sukasa heedayah tayi shiru suka sauko kasa, tasake hugging mummy da daddy sannan suka shige mota tamusu Allah kare ta ruga ciki da gudu balcony straight ta wuce ta na kallonsu daga sama taga mumy nata zuba bayani wa nanny, nanny na gyada kai tana gama mata maganar ta shiga mota nanny tana musu waving hand har motarsu tabar gdan. Wani sabon kuka heedayah ta soma ta dawo ciki ta wuce dakinta se kuka take zubawa pillow'nta sanda yakusa jikewa da hawaye nanny tashigo ta aza ta kan cinya tana bata hakuri da kyar ta rage kukan nanny tace "ynxu ki kwanta kiyi bacci in kka tashy anjima sekiyi breakfast mukaiki shopping ko? Mummy tace ko shoprite kkeson ki siye zaki iya siya" heedayah bata ce komi ba nanny ta kwantar da ita ta rufeta da bargo sannan ta fice, ahaka har heedayah ta koma bacci se around 10:45AM ta tashy tayi brushing ta sauka qasa tayi breakfast nanny tamata wanka suna kokarin fita don moha ya danna door bell nanny ta bude masa ya gaisheta ta, ta amsa da fara'arta "ai ynxu ma zamu fita shopping da heedayah, ko zaka bimu?" Don moha yace "toh muje" "heedayah! Yi sauri ki taho mutafi ga don moha ma yazo" heedayah na saukowa ta gaishe da don moha suka shiga mota suka wuce shoprite tun heedayah na qin sakewa da don moha har tasake dashy sukata shopping kamar ba gobe komi yagani seya dauka mata ahaka har suka gama nanny ta bibbiya suka dawo gda aka sauke don moha sannan suma suka wuce gda, nanny tasa mal idi yakai kayan dakin heedayah sannan tafara shirya mata saura a wardrobe a yayinda heedaya ke zaune a parlour tana kallon cartoon network dake ba a basu assignmnts ba kasancewar zaayi open day ran monday*** can dare around 10:00PM mumy ta kira nanny tamata ya gaijyan hanya tace "alhamdulillah, ina princess dina?" Nanny ta kira heedayah ta bata wayar mummy tace "mumy's princess ya kke?" Heedayah tace "lafya se ynxu kuka isa?" Mummy tace "eh nanny ta kaiki shopping din kuwa?" Heedayah ta amsa da "eh ina daddy?" Mummy tace yagaji yana bacci amman yace in gaishe ki that he's missing you" heedayah tace "i miss you both, daxu nayi sallah nace Allah bama daddy na lafya" mumy tace "yawwa good girl in shaa Allah ur daddy is gonna be fine ynxu kije ki kwanta kinji? Its getting late, seda safe ko muny's princess, blow me a kiss" heedaya tace "muahhh goodnight mummy" ta kashe wayar.
Ahaka heedayah tayi spending weekend dinta ba mumy ba daddy don moha ne kawai ke dibe mata kewa. Ran monday kuwa bataje sch ba dake ba me zuwa mata open day. A rana se sunyi waya da daddy da mummy sama da biyar har su daddy sukayi sati a can sannan suka fara maganan dawowa dake dr ya kuma yin tests din yaga ALS disease dinne da daddy amman 1st stage ne kawai kamar yadda dr ahmad yafadi, yakuma buqaci mumy da daddy dasu kwantar da hankalinsu evrythng is gonna be alright ya daura daddy kan medication sosai da alluarai yakuma ba ma mummy numbansa in case in wani abu ya kuma samin daddy in suka dawo gda 9ja mumy tayi godiya sosai. Bayan 2 days su mummy suka dawo 9ja duk sun gaji around 12:00AM na dare suka iso mal idi, nanny harda heedayah ma sukaje daukosu frm airport heedayah tayi missing parents nata sosai haka suma ahaka har suka iso gda kamar su cinye junansu a mota mumy nata mamaki har 12:00AM amman idan heedayah biyu.
Toh masu karatu THE BATTLE IS YET TO START, TIGHTEN UR BELTS!

HEEDAYAH!

14
written by miemie

Yau da safe around 6:00AM nanny tazo tada heedayah sch but taqi, ita atapir barataje sch ba harda kukanta amman nanny taki barinta dake mumy kwata kwata batasan wasa da sch haka sukata drama a daki amman heedayah taki sanda ta kai karan heedayah gun mummy daddy yace "eh a barta ta zauna tunda na yau ne kawai" omo zokuga murna gun heedayah harda yi wa nanny gwalo sallah kawai tayi takoma bacci se to 10:00AM ta tashy nanny tamata wanka tasa wata leggings iya guiwanta nd top nata ta wuce dakinsu daddy tayi hugging nasa sannan ta gaishesa haka tayi wa mummy ma, mummy ta dauko wasu katti kattin leathers ta mika ma heedayah "ga tsarabarki" heedayah se xumudi take takasa settling gu daya tayi nan tayi can se bude bude take a yayinda mummy ta dauko magungunan daddy kuma zata kai masa dan yasha, heedayah tafiya take bata kallon gabanta dake da baya take tafiyan kafin mummy tace meh heedayah ta bugeta drugs din duk suka fadi a kasa na fashewa suka fashe wata erin ihu mummy tasaka sanda nanny ta karaso dakin itama. Heedayah duk ta kidime a take tafara kuka, kasa fadin komi mumy tayi can tafara magana "shiknan heedayah kin gama dani da daddy'nki bansan kuma a ina zan samu magungunan nan ba a nan 9ja, kwata kwata banso zaman ki agda ba, ga erin abinda nake gudu ai bakida ido ne kalli abinda kka sa nayi anan? Mtsw get out!" This is the first time mummy ta fara yi wa heedayah masifa "kekuma nanny kin tsaya kina kallona baraki tattara gun bane?" (Da anga mummy ansan acikin frustration take magana), nanny ta shiga tattara broken glasses din, heedayah kuwa duk ta kidime kuka kawai take har takai bakin kofa daddy ya kirata "zo my princess" tana kuka ta karaso kan gadon "am sorry daddy I didn't mean for it" ta fashe dawata erin kuka daddy yasoma lalashinta "I know u didn't my princess bar kuka kinji? Ya isa" heedayah tace "mummy is mad at me, kiyi hakuri mummy bada gangan na bugeki ba" ta fice dakin da gudu ta wuce dakinta, mummy duk setaji wani iri nan da nan nanny tagama tattara wurin ta fice itama dakin heedayah ta nufa taje tana bata hakuri cikin kuka heedayah ke magana "nanny ina kinsan ba dagangan na buge mummy ba ko?" Nanny ta gyada mata kai heedayah ta cigaba "then why is she mad at me?" Kuka takeyi sosai nanny na bata hkuri** can a dakin daddy kuwa daddy bece wa mumy komai ba haka itama can daddy yyi magana dake yaga mumy bata da niyar yi, yace "my dear go nd tell heedayah sorry, bada gangan ta bugeki ba bakiga yadda ta rikice ba, she's sorry for what she did" mumy tace "habibi ni kaina banji dadin abinda na mata ba, wlh frustration ne bansan a ina zan sake samun drugs dinnan ba kuma kasan seda dr yace kar muyi wasa da dosage din" daddy yace "nasani but even still be kamata kimata masifa ba go nd tell her sorry we'll find out a way a sake siyowa ba munada numbern dr inba? so karki damu jeki bata hakuri" ba gardama mumy ta mike ta wuce dakin heedayah tana bude kofan dakin taga "heedayah nata zabga kuka nanny na bata hakuri" ta karaso tama nanny body signal data basu waje nanny ta fice, ko kallon mumy heedayah batayi ba se rera kukanta takeyi a hankali, mumy ta dago fuskarta data jike da hawaye tace "mummy is sorry my princess bar kuka kinji?" Heedayah batace komi ba, mummy ta kwantar da ita a jikinta tana jijiqata "is okay stop crying kinji am sorry, kin yafe wa mummy?" Heedayah ta gyada kai mummy tace "thank you" tabata peck a goshi bayan like 5mins suka koma dakin daddy tare, daddy yaji dadi sosai

HEEDAYAH!

15
written by miemie

Mummy ta kira dr tamasa bayani ya tausaya wa daddy matuqa cuz kafin drugs dinsa su iso jikinsa ze yi tsanani cuz shi ALS disease immediate treatment yake nema sosai, hankalin mumy ya kuma tashy daga karshe de dr ya kwantar mata da hankali in shaa Allah within one week drugs din zasu iso. Acikin wannan sati daya kuwa daddy har ya fita daga kamanninsa ciwon yayi worse sosai da kyar yake magana, tafiya dasuransu duk sanda heedayah taga daddy'nta setaga kamar itace silar tata kuka haka mummy ma. Ana jibi maganin daddy ze iso, daddy yakega kamar he can't make it gani yake kamar ze mutu, alhj lawal da ismail yasa mummy ta kira dake yau wednesday heedayah na sch mumy kuma an bukace ta a asibiti as emergency so dan dolenta ta fita tabar care din daddy a gun nanny. Bayan fitanta da like 20mins su alhj lawal suka iso nanny tamusu sannu dazuwa sannan taje ta gaya wa dady kan yayi baqi yace "ta shigo dasu daki" hakan akayi suka gaishe sa da jiki da kyar ya amsa dake ba karamar wahala magana ke masa ba yafara da cewa "alhj lawal?" alhj lawal ya amsa da "eh alhaji" daddy ya dawo da kallonsa kan alhj ismail sannan yace "alhj ismail?" Shima ya amsa, daddy ya cigaba "kunga de yadda nake ynxu rai a hanun...A..l.lah" ya tsaya yayi tari sosai sannan ya cigaba "ba dan komi na kiraku ba face dan in baku amanar business dina dan gani nake kamar i cant make it" alhj lawal yayi interrupting daddy "ko kadan alhj in shaa Allah zaka samu sauki ka cigaba da kula da business naka da iyalen ka duka" daddy yace "i hope so amman ynxu inaga kamar I cant make it sesa tun kafin in mutu nakeson nabaku amanan business dina cuz ku kadai nakeda wanda zan iya trusting, ko blood brothers dina baran iya trusting nasu as yadda nayi trusting naku ba, so pls ku riqe min amana" yasa hannu a karkashin pillown sa yakasa ciro papers din sanda alhj lawal ya taya sa "yace bani biro" alhj ismail ya miqa masa, ahj lawal harda hawayen munafinci "alhj s.u me kake kokarinyi? Pls karkayi signing papers dinnan zaka yi surviving wannan jarababbiyar ciwon in shaa Allah" alhj s.u yace "dan uwa kai fa kafada mun da abaya zaka kula min da business da iyali ko bayan raina amman is like baraka iya ba ynxu" (duk wannan magana da tari alhj s.u ke yinsu.) Alhj lawal ya goge yar kwallar munfincinsa sannan yace "ko kadan dan uwa koda last breathe dina ne zanyi sacrifising dan naga na rike maka amana" alhj s.u ya sa hannu kan papers din alhj lawal yace "kasa sunan dan uwa na alhj ismail" alhj s.u be kuma cewa komi ba yayi signing akan sunan alhj ismail ya miqa wa alhj lawal ya amsa seya barke dawata dariyan mugunta a lokaci daya. A daidai lokacin heedayah ta dawo frm sch as usual seta wuce dakin daddy sannan ta wuce nata, ta kai kofar dakin daddy knan taji dariyan muguntan da alhj lawal keyi dan yadda ta rude seta kasa gane ko alhj lawal dinne ko alhj ismail amman de tasan acikin dayansu ne, ta bude kofar kuma kwata kwata takasa, idea din bude kofar ma bata zo mata ba can se me dariyan ya fara magana "alhamdulillah finally ranan ya iso, rananda nakeson na mallaki dukiyar ka alhj s.u. I have waited for years, trusting dina dakayi is the biggest mistake dazakayi a rayuwarka, ba kula da family'nka da zanyi, business naka kuwa zan kula dashy sede ba dan in amfanar da family'nka ba a'a dan nawa family'n ne" bakin alhj s.u rawa yake yana magana cikin kuka "a.a.alhj la.w .al me kake fadi? Ashe dama ba sona kake tsakani da Allah ba? Aduk zama na dakai tsakani da Allah na rike ka bansan mena taba maka ba da zaka min wannan abu a rayuwa. Naji ka dauki arziki na kab nabar maka amman dan Allah ka kula min da iyali, 'yata heedayah pls alhj lawal yaja wata tsuka. Daddy ya dawo da kallonsa kan alhj ismail yace "harda kai alhj..." seya hau tari ya kasa karisawa kuka kawai ya hauyi sharkaf sharkaf da hannunsa rike a zuciyarsa. Irin dariyan daxu alhj lawal ya kuma yi sannan ya dau pillow ya danne wa alhj s.u sanda yaga bayya motsi. Yace wa dan uwan nasa "mu tafi" suna fitowa sukaci karo da heedayah a bakin kofa ta hada kai da guiwa se kuka take rapkawa kamar zata cire ranta atake jikin alhj ismail ya dau rawa dake shi ke rike da files din nd daga gani heedayah ta jiyo abnda suka kulla a cikin dakin baki na rawa yace...

HEEDAYAH!

16
written by miemie

"Heedayah yaushe kka dawo frm sch?" Heedayah ta dago jajayen idanunta tace "ynxu" alhj ismail yace "toh ya kke kuka ko anty ne tamiki duka?" Heedayah ta share hawayenta tace "a'a na fadi ne a sch damuke wasa" alhj lawal yace "sannu toh wuce daki kije ki huta" ta dau jakarta kamar dagaske tana ganin sun fice ta dawo da sauri ta bude kofar dakin daddy ko kallon direction na daddy batai ba hankalinta na kan cctv (spying camera) dake dakin ne kawai ta haura kan wardrobe ta ballo tana sauka suka hada ido hudu da alhj ismail yace "ke heedayah! Me wannan? Kawo in gani?" Ta zura masa ido ya sa hannu ya wabce cameran yace " so u think u are smart ko? Me kka ji dazaki ciro cctv dinnan? Wani abu kkeson ji?" Heedayah ta girgiza mai kai ya cigaba "to wallah kika kuskura kika gaya ma wani ko mumy'nki kan abinda kkaji munyi ni da baban mustapha" ya daka mata tsawa sanda ta shiga bari "sena pille kanki, kinji ko bakiji ba?" Heedayah baki na rawa tace "naji naji" ya fice, kan daddy'nta ta nufa tana jijjiqa shi "daddy! Daddy wake up pls, ka ma baban muhammad da baban mustapha duka ka kaisu gun police auntinmu tace can ake kai criminals bcuz dey are all criminals daddy wake up muje police station kaji, daddy!" Ina daddy shiru wata erin mahaukaciyar ihu ta sakar "daddy!" Nanny dake toilet sanda ta fito a gurguje "heedayah meke faruwa? Me kke kuka? Bakiga daddy na bacci bane? Kibarsa kinji. Oh har su alhj lawal din suntafi ne" duk wannan tambayoyi heedayah bata amsa mata ko daya ba daga karshe tace "nanny daddy baya numfashi" nanny tace "ke heedayah shegen manyance ne da ke, yaushe kkasan ko mutum na numfashi ko baiyi, common zo muje daki ki canza kaya kuma kukan ya isa" heedayah ta daka mata ihu "am serious nanny zo kiji" nanny ta karaso jiki na rawa tasa hannunta kusa da hancin daddy taji fa ba alamun numfashi salati kawai tahau yi ta jawo telephone ta kira mummy, maganartan ma ba fita takeyi ba "mu.m..my ki taho gda alhj ba lafya baya numfashy" "what?" Abnda mummy ta fada knan nanny ta kashe wayar. "Heedayah gaya mun meya samu daddy? Me kka masa ko haka kka samesa?" Heedayah ta bude baki zatayi magana seta tuna abinda alhj ismail ya gaya mata, ta ja bakinta kum! Tayi tsit "nima bansani ba haka na gansa since dawo na frm sch, nanny do something banason daddy na ya mutu pls" tafashe dawata erin matsanancin kuka bayan 20mins mummy ta iso ba abun ince firewa tayi ba, a gigice ta shigo gdan se dakin daddy tayi kansa tana kuka tana kiran sunansa amman ina daddy bai ko motsi, nan da nan nanny ta kirawo mal idi yashigo ya daga daddy akasashi cikin mota se emergency. Mummy, heedayah, nanny se kuka suketa rapkawa mal idi ma idanunsa duk sun kada.
An hour later dr din yafito mummy tayi kansa tare da jero masa tambayoyi, "dr how's my husband doing? Can I see him now? Dan Allah ya yake? Talk to me pls" dr yace "calm down, ko kece matarsa?" Mummy tace "sure, yes, ofcourse, definately ni ce matarsa" (bata ma san sanda ta jero wannan answers dinba) dr yace "muje office dina" heedayah ta kama sabon kuka ta kankamo mummy itama setabi su da kyar nanny ta jata jikinta sannan mummy suka fice da dr sukayi office nasa yace mata "have a seat pls" mummy tazauna dr yafara kamar haka "nakega ba se nagaya miki ba u already know mijinki is affected by ALS disease ko?" Mummy tace "yes for sure am aware, disease din na stage 1 ne" dr yace "a da knan dan ynxu da mukayi test mungano yakai stage 3" mummy ta dafa kirji "what???" Hawaye kawai ta fara zubda, dr yace "ko kinsan meya samesa ya sume?" Mummy tamasa bayanin abinda tasani, dr yace "ikon Allah there must be some explanations then...ko kinsan mijinki nada hawan jini?" Mummy tace "eh amman kuma da sauki dan ya jima bai complaining ba" dr yace "due to shock da maigidanki ya samu wanda kkace kema bakisan dalilin hakan ba yasa hawan jininsa ya hau sosai wanda yasa sa paralysing ynxu haka am sorry" suuuu mummy ta sulale kasa sumammiya

HEEDAYAH!

17
written by miemie

Dr yakira nurses aka dagata itama aka kaita wata dakin, heedayah na ganin mummy'nta a sume ta sakar dawata irin ihu sanda aka fitar da ita daga asibitin kuka takeyi sosai kamar ba yarinya ba, immediate attention aka bama mummy within 20mins ta farfado ba abin da take furtawa face "habibi na don't go nd leave me" ahaka har tayi gaining back conciousness, kuka takeyi sosai heedayah da nanny ne suka shigo, heedayah ta karasa gun mummy'nta tayi huggung nata tightly tana kuka "mummy ina daddy? Muje mu daukosa mukoma gda mubar wannan asibitin eventually we will all fall sick dan Allah mutafi" tafashe dawata erin kuka me tsuma zuciya mummy ta taso da ita daga jikinta tace "look at me heedayah" da hannunta biyu rike a fuskarta "zamu tafi gda kinji dnt worry bari daddy yadan samu sauki kadan se mutafi stop crying kinji? Bansan inga princess dina na kuka, ure tears are way expensive, kinsan menakeso dake ynxu?" Heedayah ta girgiza kai da alaman a'a mummy tace "kuje gda da nanny kici abinci kiyi sallah, pray for daddy, do ur assignmnts seki kwanta ki huta kinji? Kina tashy nida daddy zamu dawo gda heedayah tace "inason inga daddy, mummy pls ko kadan inason inga daddy na" mummy tace "don't worry ynxu daddy na bacci anjima kadan ze tashy" heedayah tace "promise me mummy" baki na rawa mummy tace "i promise mumy's princess" tabata peck a goshi tace wa nanny "ku tafi" nanny bata ce komi ba takama hannun heedayah suka fice mal idi yayi dropping nasu sannan mumy ta kirasa yakuma dwowa asibitin. Bayan tashin mummy da like 15mins dr yashigo ya dubata yaga shes perfectly fine yace "ki huta madam, Allah bada lafya" mummy tace "ameen dr pls tell me meke damun mijina? How is he? Inason ganin mijina pls he need me by his side" dr yace "calm down ynxu ki huta" mummy ta ta rokon dr da yagayamata meke damun mijinta daga karshe ya karisa gaya mata bebar komi ba, salatin mummy kawai ke tashy a cikin dakin wai ace yau an wayi gary daddy is paralysed, bayida wani amfani kuma again, dashy da babu duk daya ne subhanallah ya Allah kaba ma mijina lafiya. Baki na rawa tace "dr pls kabarni inga mijina, pls" dr yace "muje" da kyar ta mike tabi bayansa suka shiga dakin daddy dr yabasu waje, jiki na kyarma takarasa gun daddy ta dauko hannunsa dake hade da drip ta rike bibbiyu da nata a hankali hawayenta ke sauqa kan hannun daddy se suratai take zubawa tana kuka tagama tayi addu'a ta kwantar da kanta gefen daddy ahaka har bacci me nauyi ya dauketa***
Da maghrib ta farka tayi sallah tasa mal idi kwaso mata essential things da zatayi needing dan kwana a asibiti yazama dole cuz har ynxu daddy beyi gaining conciousness ba. Allah ya so time da mal idi yaje kwaso kayan heedayah na bacci da har nanny zata ta da ita sallah sekuma tace bari ta idar sannan ta tayarda ita yadda Allah yaso su knan, har aka gama diban kayan heedayah batasani ba. Mal idi na tafiya nanny ta kira mumy ta gaisheta da jiki take tambayarta ko ta dafo mata abinci ne? Mummy tace "a'a kibary kar heedayah tayi noticing wani abu zan sa idi ya siyi min" nanny tace "toh shiknan tunda haka kkace, ya jikin daddy'n heedayah?" Mummy tace toh da sauki amman kam har ynxu beyi gaining conciousness ba nanny, i dont know what to do" nanny tata bata hakuri amman wannan abu da abin dubawa aciki, mummy tace "kibary kawai sena dawo se anjima" ta katse wayar. Nanny ta manta da zancen ta da heedayah yin sallah ma gabadai. Se around 10:00pm heedayah ta tashi tayi brushing tayi alwala without anyone telling her to, tayi sallolinta tayi ma daddy addu'a sosai sannan ta zauna tana nazarin abinda tajiyo dazu kwata kwata ta kasa gane waye ke maganar ko alhj lawal ne ko alhj ismail amman dey jikinta yafi bata alhj ismail ahaka tabar tunanin ta sauko kasa tasami nanny a parlour ta karasa gunta tace "nanny ina mummy da daddy?" Kafin ta jira me nanny zatace ta dau hanyar dakin daddy tana kwala masu kira shida mummy
Share:

3 comments:

 1. nice book continue pls

  ReplyDelete
 2. muhammad abba gana20 July 2016 at 07:26

  @lil-saif,
  okkk

  ReplyDelete
 3. Abubakar Ibrahim3 August 2016 at 08:59

  Kai mugunta baiyi ba a rayuwa

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).