shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 13 July 2016

HEEDAYAH 41------45

HEEDAYAH!

41
written by miemie

Nan ya fada duniyar tunani shin ina heedayahn zata je? Kode, kode alhj ismail ne yayi kidnapping nata dan sokanci nan ya yi scrolling kan contact na alhj ismail ya soma dialing, daga wayar da alhj ismail zeyi yazo daidai da shigowar don moha main parlour jin daddy'nsa ya daga waya yasa ya tsaya be qariso ba, alhj ismail yace ''hello dan uwa?" Alhj lawal yace "ya harkoki?" Alhj ismail ya amsa da "alhamdulillah..." jin gaisuwam ba na qarewa bane don moha ya juya da niyar fita ko anjima ya dawo yakai dab bakin kofa knan seya jiyo daddy'nsa na fadin "kai gaskia rabuwa na da insata a ido nike ga tun last open day danayi wasu muhammad a makaranta..." jin haka yasa don moha juyowa ya labe tawani corner yakasa kunne yanajin mgnan da daddy'nsa keyi. Alhj ismail "yace waat? Anyi kidnapping nata? Ikon Allah," on the other side alhj lawal yace "eh nima matata ce ke ban lbr shine nace barin ji daga bakinka inade u have nothng to do with bacewan yarinyan?" Alhj ismail yace "a'a wlh ni bani bane ba ni nayi kidnapping nata ba" don moha najin haka ya zaro idanunsa waje tare da fada ma kansa "what does this suppose to mean? Me hadin daddy da heedayah da har xa'a ce shi yyi kidnapping nata gaskia somethng smells fishy I have to find out" alhj ismail yace "toh Allah kaimu goben" ya katse wayar ya leqa yaga ba kowa sannan ya shige daki a yayinda don moha kuma yakoma site nasa da kaninsa.
Heedayah ce zaune a dakin ita kadai se kuka takeyi daga ido tayi taga 15mins to 9:00PM nan ta miqe tayi sallan ishan ta, tana idarwa ta tofa addu'o'inta ta miqe ta nufa gun dressing mirror inda ta ga wayarta daxu ta duba taga wayam! Ba komi side drawers na gadon tafara dubawa ko zata samu dan wani makamin da ze taimaka mata ta iya balla wurin lock na kofar dan ta karanci windows din erin masu karafuna ta wajennan ne haka ta ta neme nemen ta ba komi a ciki daga books se books wani haushi ta sake ji if only not don moha ya dauke spoon na daxu da tayi amfani dashy ta balla screws dake jikin kofar tasamu ta gudu, bata san sanda ta fada kan gado bacci yayi awon gaba da ita ba. Mummy kuwa kwana zaune tayi.
Wasgehari! Da misalin karfe 8:30PM don moha ya tashy yayi wanka ya shirya tsaf kaninsa safyan yasha mamaki cuz don moha betaba tashy da safe haka ba kullum seya kai erin 10-11:00AM dinnnan, daya tambayi don moha ko ina zasa ma be amsa sa ba kawai ce masa yayi "in daddy ya tambayeni kace masa project ne yataso" (abunku da architecture) safyan yace "okay" don moha ya fice, a daidai restaurant na jiya ya tsaya yasiyo breakfast me rai da lfya daga can naga yawuce wata boutique ya siyo wasu dogayen kaya guda biyu dawata top da highwaist skirt guda biyu sannan yakama hanyan gdan daya ajiye heedayah ya na isa bayan yayi locking ko ina ya zarce dakin heedayah ya sameta kwance se bacci takeyi ya fita da plate na jiya ya kawo sabo ya ajiye sannan ya matso kusa da ita sanda ya gama qare mata kallo sannan ya fara shafa fuskarta a birkice ta farka datayi niyan sake ihu ganin don moha yasa ta yi shiru yace "morning sleeping beauty ga breakfast naki tashy kiyi wanka here are some dresses ki zaba aciki seki sa I'll be waiting for you outside" kafin ya jira me zatace ya fice leathern ta jawo ta zazzage kayakin dake ciki to her suprise taga harda panties da bra (ni miemie nace shegge don moha) wata tsuka taja dan haushi badan tana so bata ta tashy tanufa toilet tayi brushing sannan tayi wanka dama already ta riga tayi sallan asuba ta fito a gaban dressing mirror taga wata 'yar vaseline ta shafa sannan ta jawo daya daga cikin bra's din acikin guda biyar taga guda ukun daidanta ne biyun ne suka mata ruwa haka panties dinma a zuciya tace "dan iska kawai" daya daga cikin dogayen rigunan tasa ta nemi gu ta zauna tafara cin abincinta tana cikin ci don moha ya shigo dakin daya kafa idansa kan heedayah sanda tafara feeling somehow ta lalimo hijabinta tasa tare da jan tsaki murmushi don moha yayi a zuci yace "is like the panties nd bra are ur actual size" kujera ya jawo ya zauna kusa da ita sanda ta gama cin abincin sannan yace "so me hadinki da daddy?" Heedayah tace "I dont know" tare da watsa masa harara yayi murmushi sannan yace "jiya I heard him on the phone wani na tambayansa ko shi yayi kidnapping naki" hankalin heedayah in yayi dubu be tashi ba ita komi ya faru amman batasan don moha yayi finding out truth din ynxu cuz the moment hakan ta faru her plans will all be ruined da kyar ta taro confidence tace "sekaje ka tambayi daddy'n naka mesa ake tambayarsa ko shi yayi kidnapping dina but I assure you baraka taba jin komi daga wajena ba" don moha yace "then fine seki shirya karasa rayuwarki acikin gdan nan dama ban gaji da kallonki ba" heedayah tayi murmushi sannan tace "I care less don moha yace "fine!"**** alhj ismail na hango yana barin gdansa da alama gdan alhj lawal zasa shams na ganin ya fita takama hanyan xuwa watadaki inda take ajiye kayakinta daidai nan maman su don moha ta kirata tayi kamar bata jita ba se sauri take ta je tadau wayar ta gayama don moha ga baban nasa yafita cuz haka sukayi dashy jiya kan tana ganin daddy ze fita takirasa ta sanar dashy, kiranta mama keyi sosai ba yadda ta iya haka tajeta ta sameta mama tace "yau aiki zakiyi anan sosai inason mu fita da duka kayakin dake dakinnan tas mu share dakin tsaf!" shams kamar tasa hannu a ka tayi ihu ita tsoronta kar don moha yace yadena kula ta cuz yasata abu batai ba, tunanin wata excuse zata kirkiro takeyi*** alhj lawal da alhj ismail suna zaune a garden alhj lawal yace...
HEEDAYAH!

42
written by miemie

"Batun yarinyannan heedayah mahaifiyarta ta sake kira na da safen nan kace ba kai ka dauketa ba?" Alhj ismail yace "toh in dauketa in kaita ina?" Alhj lawal yace "toh fa, we have to find out where is she" alhj ismail yace "ka manta da maganannan kawai ko ka manta yarinyan nan tasan secret namu ai batan ta shiyafi mana alheri" alhj lawal yace "ko kadan ai this is the main reason dayakamata musan a ina take kartaje ta tona mana asiri" alhj ismail yace "toh where on earth zamu fara nemanta?" alhj lawal yayi 'yar murmushi sannan yace "leave that to me you can go now" sukayi sallama alhj ismail ya tashy ya fice gdansa isarsa yayi daidai da dawowan don moha daga gdan daya aje heedayah, atare suka shigo ciki don moha yace a zuci "wato shams ta maidani dan iska knan ince tamin abu tayi banza dani zan ko ci mata mutunci" site nasu ya nufa ya watsa ruwa can bayan azahar bayan ya shirya fita ya shiga side nasu mummy yasamu shams na cin abinci wani harara ya watsa mata sanda abincin datake ci ya maqale a wuyarta takasa hadiyewa atake tafara basa hkr ya daga mata hannu da alaman stop tayi tsit yace "wato in saki abu ki kiyi koh? Kinyi daidai" ya tashy ya fice shams nata kiransa ko kulata beyi ba lunch ya je ya siyowa heedayah sannan ya kaimata.
Mummy har tazube cikin kwana daya, ba aikinta sekuka can ta miqe ta dau picture'n heedayah wanda akayi enlargement dashy ta nemi gu ta zauna "my princess where are you? Pls ki dawo gdah I need you, karki tafi kibarni pls show urself to me" tafashe cikin wata erin matsanancin kuka. Alhj lawal ne ya kirata yake gaya mata ta kwantar da hankalinta yakai mgn har police station ynxu haka du nemanta akeyi, mummy tamasa godiya sosai sannan ta katse wayar. Da misalin karfe 4:30PM don moha yashigo gda ya nufa site nasu mama inda ya sami daddy nawaya ya tsaya yagama jin komi sanda daddy ya kammala wayar sannan don moha yace "daddy wa akayi kidnapping?" Daddy yace "ahh ba kowa maganar bata shafe ka ba so me ya kawo ka?" Don moha yace "really daddy? Ba wanda akayi kidnapping?" Daddy ya daka masa tsawa "ni kake cema really? Muhammad ba abin nace maka dan iska ba wlh amman bakada kunya ko kadan ina matsayin babanka kana gayamun mgn iya san ranka oya get out of my sight!" Don moha ya bude baki zeyi mgn daddy yace "now!" Don moha ya juya sanda yakai daidai bakin kofa yakira sunan heedayah yadda daddy zeji sannan ya fice, yabar daddy da baki wide open da kyar alhj ismail ya iya ya zauna kan kujera "taya muhammad yasan heedayah akayi kidnapping? Innalillahi Allah kasa besan abinda muka aikata shekaru dasuka wuce ba" hannunsa na rawa yakira alhj lawal ya sanarda shi abinda ake ciki alhj lawal yace "this means muhammad ne yayi kidnapping nata kokuma yasan inda take." Alhj ismail yace "qarya ne d'ana bare iya kidnapping 'yar mutane ba halan de yaji mu muna waya ne jiya inbahaka ba du rashin hankalin muhammad bare iya kidnapping mutum ba sbd haka kar kayi wa d'ana lakani," alhj lalwal yace "haba dan uwa calm down mana meyayi xafi? 'Dan ka ba dana bane? Ai ynxu tun da har munada hint abinyi me gadin gdanka zamu tambaya koyana ganinta around" alhj ismail yace "anya kuwa dan uwa? Me zai kawota gdana?" Alhj lawal yace ai nima bansani ba amman de kasan yarinyannan is aware mu muka illata mata mahaifinta ko?" Alhj ismail yace "a'a zata manta warhaka man, alhj lawal yace ko kadan yaro bai mantuwa ynxu de ina zuwa mu tambayi me gadinka muji" alhj ismail yace "to ina jiranka" ya katse wayar. Nan da nan alhj lawal ya iso gdan alhj ismail suka je gun baba me gadi bayan sun gaisa alhj lawal yace "nikam mal ahmad baka taba ganin wata budurwa a nan gdan ba?" Mal ahmad yace "kai gaskia a'a...saidai akoi wata qawar shams me aikin gdannan tana zuwa gaisheta yawanci," alhj lawal yace "ya take? Yar fara ce?" Mal ahmad yace "tabbas fara ce 'yar kyakkyawa haka duda tana yawan toshe fuskarta so baran iya tantance kamanninta ba," alhj lawal yace "toh mungode" yaja alhj ismail waje yace "ai na gaya maka, muhammad zaisan inda take kaga har gdanka take zuwa" alhj ismail bece komi ba har ynxu alhj lawal yace dan uwa lfy?" Alhj ismail yace "abun ne ya dauremin kai mesa bata zuwa gdanka se gda na? Bayan tare mukeyin komi" alhj lawal yayi kamar be jisa ba yace "kaga ynxu tunda munada idea a ina take, mubammad yakamata mufara spying, zan nemo wasu suna bin whereabouts nasa kaga inhar shi ya boyeta a wani gda we'll definately find out, amman kafin nan yakamta muyi wa me aikin naka magana" alhj ismail yace "toh kana ganin hakan ba laifi? mubar zancen me aikin kawai, amman xanci kaniyan muhammad har yayi kaurin da ze sace 'yar mutane?" Alhj lawal yayi murmushi yace "a'a kar ka ce masa ko uffan kabarsa I have a better plan," alhj ismail yace "toh shknan" alhj lawal yace "yawwa baran wuce gda Allah kaimu gben kawai anytime muhammad ze fita kamin waya nd kasamu me aikinka kamata mgn meke kawo heedayah gdan nan ne zamu gane ko ita heedayan ta manta abinda mukama alhj s.u kwanaki ko kuma bata manta ba" alhj ismail yace toh shknan xan mata mgn Allah kaimu gben" alhj lawal ya zarce gdansa a yayind alhj ismail ya shige gda ya kira shams tana dan goge gas a kitchen ya kirata ta amsa ta fito ta nemi gu ta durqushe ta gaishesa da kanta a qasa ya amsa a takaice "shams ko?" Tace "eh alhaji" alhj ismail yace ina qawarki heedayah? Har tsakiyan kanta sanda tajiyo wannan tambaya atake jikinta yahau bari dan bata san mezata cemasa ba, alhj ismail yace baki magana ne? Baki na rawa tace inayi ban san inda take ba nima, alhj ismail yace bansan qarya kalleni ki gayamun gskia nasan sarai kinsan anyi kidnapping nata so tell me ina aka kaita? Baki na rawa tace "wal...wal...wallahi ni bansani ba," alhj ismail yace "bakisan meba? Wanda yayi kidnapping nata?" Shams ta gyada kai cikin tsoro alhj ismail yace "amman kinsan anyi kidnapping nata aiko?" Nan ma ta kuma gyada kai...

HEEDAYAH!

43
written by miemie

Alhj ismail yace "qarya kke" baki na rawa shams tace "wallahi alhj ba qarya nike ba nima..." ringing din wayarta ne ya katse ta dubawanda tayi taga don moha ke kira nan tashiga sabon barin tsoro alhj ismail yace "ba wayarki ke ringing ba? Pick it up!" Shams bata ce komi ba takashe wayar ma takasa ahaka har call din ta tsinke don moha du haushi ya cika sa wato kasa shams xata watsa masa a ido for the last time ya sake gwada number din alhj ismail ya taso ya kwace wayar shams ganin don moha calling ya waro ido tare da sake baki, "so its true don moha has something to do with the disappearance of heedayah nd dole tare suke aiki da shams" rejecting call din yayi don moha yasha mamaki sosai tunanin yadda zeci uban shams kawai yake. Alhj ismail ya dawo da kallonsa kan shams da idanunta duk sun cike da hawaye sannan yace "me hadinki da muhammad? Tare kuke aiki ko? Ina kuka kai heedayah?" Shams bata ce komi ba, alhj ismail ya daka mata tsawa "talk to me!" Tana hawaye tana mgn "wlh wlh ni bansani ba..." Tas! Taji a fuskarta ta riqe gun hawaye na bin kuncinta alhj ismail yace "zaki gayamun gaskia ne ko kuma sena kira police a tafi dake acan nikega zaki gayamusu..." "a'a alhj dan Allah kayi hakuri karka kira min police" alhj ismail yace "then gaya mun ina kuka kai heedayah?" Shams tace "wlh ni bansani ba nima ji nayi anyi kidnapping nata.." alhj ismail yace "still not ready" ya dau wayarsa kamar wanda xe kira police shams tace "zan fada zan fada" alhj ismail yayi banza da ita ya cigaba da abinda yakeyi shams tace "ka tambayi don moha yasan inda take" alhj ismail yace "karya kke kema kinsan inda take" shams tace "wallah tallahi bansani ba abunda nasani nake gaya maka dan Allah karka kira min police," alhj ismail yace "mesa kukayi kidnapping heedayah? Kika kuskura kka min qarya kuma in kira miki police," shams tarasa me zatace dan ita barata iya tonawa don moha asiri ba gara ta tona wa heedayah can tace "heedayah ne take neman abu a gdannan shine..." alhj ismail yace "what? Neman abu? Wani abu knan?" Nan yayi deleting number'n don moha daga wayarta sannan yace "tattara ina inaki kibar gdannan karki sake dawowa kika kuskura kika dawo ko naganki da muhammad koda a bakin gate na gdan nan ne me hanani dauko miki police se Allah get out! Idiot kawai" ya mika mata wayarta ta fice da gudu bata tsaya ko inaba se bakin kofar gdansu tagama kukanta sannan ta shige***alhj ismail kuwa har ynxu mamaki yake "yaushe muhammad yayi kaurin da xe iya kidnapping 'yar mutane, ynxu ina ya kaita nd meyake nema a gunta? Innalillahi" nan da nan ya kira alhj lawal ya tabbatar masa da zancen alhj lawal yace "alhamdulillah ynxu tunda munsan wayayi kidnapping nata muhammad kawai zamusa ana binsa duk inda zasa kaga daga nan zamu gano inda take semu san abinyi kuma," alhj ismail yace "musan abinyi kuma? Ba sako ta zamui ba?" Alhj lawal yace "kai matsala ta dakai qarancin tunani 'danka muhammad nada reason nasa na kidnapping heedayah," alhj ismail yace "nifa har ynxu kaina a daure yake yarinyan cemin tayi wai "heedayah na zuwa gdana tana neman abu, wani abu knan?" Alhj lawal yace "abu fa kace wani abu knan zata zo nema? ko files na alhj s.u'n take nema? haha lallai kuwa barata taba samu ba" alhj ismail de yayi shiru dan tabbas yasan me heedayah take nema ba komi bane illa cctv but beh gaya wa alhj lawal ba hasali shi alhj kawal dinma besan dawani zancen cctv ba cux koda lokacin da alhj ismail ya amsa abun gun heedayah tun tana qarama be taba gaya wa alhj lawal ba nd ko a yau dinma be gaya masa ba, alhj lawal yace "kayi shiru fa?" Alhj ismail ya dawo daga duniyar tunanin dayake sannan yace "ahh ba komi ynxun ya zamui da heedayahn?" Alhj lawal yayi yar murnushi sannan yace "leave that to me" ya katse wayar

HEEDAYAH!

44
written by miemie

Nan da nan ya kira mutanensa wanda yasa suka taba robbing gdan alhj s.u bayan sun gaisa ya gayamusu aikin dayakeson suyi tare da gayamusu ze masu sendn picture'n wanda yakeson subin, guy din yace "ba matsala oga sir! Wannan ai qaramar aikine" alhj lawal yayi making it clear to them da kar su kuskura su taba lafyar don moha koda kuwa wani abun yazo ya faru, ya amsa "da karka damu oga sir yadda kace kakeso haka za'ayi" alhj lawal yace "good gben seku zo unguwan namu anytime ya fita seku bisa to his destination," ya ce "toh oga sir" alhj lawal ya katse wayar na da na ya masu sendn picture in don moha***
Exactly 7:30PM, bayan don moha yagama shirinsa ya dau motarsa ya fita ba tareda kowa yayi noticing nasa ba restaurant ya tsaya ya siyo ma heedayah abinci sannan ya nufa gdan as usual seyayi locking ko ina sannan yake shiga dakin heedayah ya sameta tana kwance kamar me bacci yana matsowa kusa da ita ta zabura don moha yace "evening my lady," ko kallonsa heedayah batai ba ya je ya dau mata plate a kitchen ya bude mata abincin tareda fadin "eat my baby" nan ma heedayah bata ce komi ba haka yata rokarta can tace "don moha untill when zaka kaini gda pls? Am tired of staying here all by my self" don moha yace "ure not alone my baby, in kinaso I can move here muna kwana tare," heedayah taja tsaki "mtsw niba abinda nake nufi ba knan, ka kaini gda pls," don moha yace "not untill kin gayamun me kke nema a gdanmu" heedayah tayi shiru zuciyarta na bugawa "taya don moha ze san ina neman abu a gdansu? Ai bawanda yasan wannan mgn daga ni se shams omg! This means that shams tayi betraying dina, Allah ya isa shams thank goodness daman banyi trusting naki ba," don moha ya katse mata tunani tareda fadin "yes? Are u ready to tell me?" Heedayah tace "shams data gayamaka ina neman abu a gdanku seta gaya maka abinda nake neman," don moha yayi murmushi 'so u've finally accepted keda shams aiki kukeyi tare," heedayah tace "ni banyi admitting komi ba cuz ina kan bakata har ynxu baraka taba jin komi daga bakina ba, ita shams din ai tasan menake nema a gdan naku mesa bata gaya maka ba?" Don moha yace "ure lying bata sani ba cuz data sani am sure zata gaya mun" heedayah tayi murmushi "then I guess tayi decieving naka kaima just as expected" can kasa kasa tace "shams aikinki na kyau" don moha yaji metace yace "what? Me kka ce?" Heedayah tace "nothing" tare da yin murmushi, don moha ya kulu sosai wato shams har ynxu tana aiki da heedayah? Lalle ma ta maidani dan iska zanko yi maganinki no one messes with don moha nd get away with it yatashy fuskar nan a tamke ya fice. Heedayah tayi murmushi "finally my plan has worked ynxu nasaka believing cewa shams tayi decieving naka kan kuna aiki da ita nd a bayan eyes naka nima tana aiki dani," ta na murmushi ta jawo abincinta ta soma ci sanda ta koshi ta idar da isha ta miqe kan gado tana tunani ya za'ayi tayi ta gudu ahaka har bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari! Da safe around 8:30AM don moha ya shirya tsaf daidai yazo shiga motarsa daddy ya kwala masa kira sanda ya duba agogo sannan ya jesa ya samu daddy zaune kan sofa ya zauna a qasa tare da gaishe da alhj ismail, daddy ya amsa da fuskar nan tasa ba yabo ba fallasa yace "ina zaka?" Don moha yace "fili xanje induba akoi wani mutumin dakeso in zana masa gda so zanje inga topography'n filin" daddy yace "ayya toh yayi kyau yawwa daman number wani abokina nake ta trying tun daxu yaqi shiga dan ban wayarka in gwada ko ze shiga" don moha beyi gardama ba ya miqa wa daddy wayarsa tare da ficewa daga parlourn scrolling kan contact list din don moha yayi har sanda yakai kan shams yayi deleting number din sannan ya wuce gallery ya danna folder'n camera pictures na heedayah ne suka bayyana wanda yawancinsu tana bacci aka dau kasu baki ya tabe yana salati sanda yagama viewing ya tabbatar da hakan sannan ya kira don moha "gashi nikega daga wayar abokin nawa ne gashy kaima yaki shiga ta naka don moha" yace "ayya" tare da amsar wayarsa ya fice nan mutanen alhj lawal suka fara binsa hanyar restaurant ya nufa bayan yaa siyo abincin yakama hanya sharada se feeling yake kamar he's been followed kamar ana binsa a baya yadaga ido ya kalli mirror bede yi noticing komi ba amman jikinsa na gaya masa ana following nasa dan haka yayi taking u turn yafasa xuwa ganin heedayahn, mutanen alhj lawal da suke binsa abun ya mugun qulad dasu harda buga sterring motar inda Allah yasa don moha be gane shi suke bi ba u turn da basu shiga bane had it been suma sun bisa sukayi u turn din da tabbas don moha zegane shi suke bi ahaka de yata bin lungu lungu har ya bace musu yana isa bakin gate na gdan daya ajiye heedayah ya duba ya duba yaga ba me kallonsa sannan ya bude gate yashige da sauri yasake rufo gate din ya shige yasami heedayah tayi wanka tana shafa mai ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta domin har ynxu batai noticing nasa ba, ta dago santaleliyar kafarta tana shafa masa mai knan tare da kwaye zanin cinyanta ya bayyana shar! Don moha besan sanda yasoma tari ba tareda jawo kofar yayi ya nufa parlour nanne heedayah ta gansa ta rufo cinyartan da wuri ta leqa taga yana palour taja tsuka sannan ta koma tagama shirinta tasa riga bayan 'yan mintuna don moha yadawo mata da breakfast din ya ajiye kan dressing mirror ba tareda yace mata komi ba haka itama heedayah, ta kai gun abincin ta bude tafara ci a hankali a yayinda don moha yake kallonta kamar TV heedayah tace "so you've finally realised shams was betraying you?" Don moha yace "what are u talking about?" Heedayah takuma yin wata murmushi sannan tace "stop behaving as if baka sani ba nevertheless, so ita shams din ta gaya maka me nake nema a gdan naku? No cuz tare muke aiki da ita," Don moha yace "ban sani ba," dariya tayi sosai sannan tace "stop fooling urself nd let me out of here cuz duk yadda kayi baraka taba sanin menake nema a gdanku ba shams is my girl tun ran farkon da kuka soma aiki tare da ita ta gayamun komi, see u are on the losing side" don moha yace "for now ba amman I assure zanyi whatever it takes har sanda zan san gaskiyar wannan al'amari" heedayah tace "ok we'll see to it then" ahaka har tagama cin abincinta bayan don moha yafita da plates din yarufo kofar da kwado ta waje sannan ya yi tafiyarsa

HEEDAYAH!

45
written by miemie

Hayaniyan mama da daddy ne ke tashy a parlour tana tambayarsa "mesa ze kora mata me aiki bayan ba wani laifi tayi ba, alhj ismail de yaqi fitowa fili ya gaya mata dalilin korar shams can dayaga abin nata is getting way much cikin tsawa yake mgn yace "so kke kisan dalilin dana kori 'yar aikinki? Kidnapping heedayah tayi yarinyar is evil" mama tace "whaat? Shams din? U must be mistaking..." daddy ya daka mata wata tsawa "enough banason sake jin any word frm you" ya fice daga parlourn, mama ta rasa na fadi*** da azahar don moha ya shirya as usual ya zarce restaurant kowani minti yana kallon mirror ko ana binsa ma yau, mutanen alhj lawal kua sunyi wayo yau ba direct suke binsa ba akoi mota daya a tsakiyarsu hakan be bama don moha daman ganinsu ba bayan ya siya wa heedayah abinci yakamaa hanyar sharada still yana duban mirror bayan daya shiga gdan daya daga cikin mutanen alhj lawal ya kira sa tare dagaya masa sunga don moha ya tsaya a restaurant bayan ya siya abinci ya zarce sharada phase 2 daidai gaban wata gda ya tsaya ya shiga...alhj lawal yace "sure? Wani colour ne gdan?" Guy din yace "brown nd milk da black gate," alhj lawal yace "guest house na alhj ismail knan aikinku yayi kyau seku jira bayan ya fito ku shiga ku tabbatar mana ko ita heedayah'n ce acikin gdan," guy din ya amsa da "toh" sannan ya katse wayar sanda don moha yayi good 30mins sannan ya fito ya rufe gate din tare da datse kwado yayi tafiyar sa bayan kamar 10mins da tafiya don moha mutanen suka fito daga motarsu su biyu suka gwada bude kofar amman ina don moha ya datse da kwado motar dayan ya koma ya dau wata abu dashy ya bude kwadon suka shiga windows din gdan suka fara bi suna kallo daga ciki can windown dayan ya taba dan uwan nasa heedayah suka hango ta hada kai da guiwa kan gado kamar me zaman makoki bayan da suka gama qare mata kallo sannan suka fice suka sake datse kwadon straight gdan alhj lawal suka nufa inda suka tarar da alhj lawal da alhj ismail zaune a garden suka karisa dayan yayi wa alhj lawal eye signal da alaman suna son masa mgn in private, alhj lawal yyi murmushi sannan yace "dont worry muyi mgnan anan" suka nemi gu suka zauna sannan dayan ya labarta masu komi alhj ismail mamaki har ynxu yake da hali irin na dansa, alhj lawal yace "aikinku yayi kyau ynxu yakamata tunda munsan inda take muyi making move namu tun wuri ynxu, dan uwa abinda nikeso dakai ka hana muhammad fita yau da gda, kukuma so nike ku dau heedayah ku kaita inda no one will ever found her, ku kaita jan dajin Allah inda namomin daji zasu cinyeta kokuma ku KASHE min ita," alhj ismail yayi saurin katse sa..."kashe ta fa kace dan uwa? taya zamu kashe heedayah tamkar 'ya fa take a garemu gaskia karmui haka ade kaita can inda bawanda ze sake jin labarinta amman de kar mu kashe ta ko daji ban yarda a kaita ba," alhj lawal yace "toh shiknan tunda haka kace kunji ai? Kar ku kasheta, ku kai ta can inda bawanda ze sake ganinta, I hope kun gane what I mean?" Dayan yace "yes oga sir mukaita can ta kudu kudu mu jefar da ita a cikin qauyen qauye, alhj lawal yace good ynxu alhj ismail kaje gda ka hana muhammad fita yau alhj ismail ya mike toh se munyi mgn" ya fice, alhj lawal ya dawo da kallonsa kan mutanen nasa tare da cemusu "KILL HER" ya fashe cikin wata maqirar dariya
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).