shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 12 July 2016

WAYE SANADI?? 27_28 &29

waye-sanadi.jpg [12:10pm, 7/11/2016] Md: WAYE SANADI? 27 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz Yana zaune kan bencin sadi na karasa fuskata a hade dai dai lokacin motar daddy ta shigo a,a safiyya ya kuka zauna anan ungo ki bude sit room a dole na karba na bude shiga nayi na samu kujera nayi kwanciyata ganin shiru ban fito ba, ya sa saifu ya shigo, nana kefa yake jira na juyo ina masa irin lalataccen kallo,na zata shima shigowa zayyi bayan ya kai masa ya dawo ya zauna "nana ya jiki? Naji sauki meye kake kirana zuwa nayi na duba ki to kayi kokari na mike zan fita saifu wannan zuwan yazo na karshe a gareka naga kana kokarin shiga min rayuwa ka sauka lafiya. Dan Allah safiyya karki tafi ina son gaya miki wata magana 'saifu na tsane ka sako daya ta hada mu to amma kaci darajar taimakon da kamin jiya ina sauraronka "safiyya kalmar da kika gayan a yanzu ta kara raunana zuciyata amma duk dahaka zan gaya miki ciwon da ke damuna cikin zuciyata,safiyya ina sonki sonki ya dade cikin zuciyata please ki taimakan ki.....' Kan ya karasa na daka masa tsawa baka da tunani saifu me ka dauki kanka dan na baka dama kake so ka wuce goda da iri, to nutsu kaji bana sonka ba kuma zan taba sonka ba na juya zan fita na juyo maganarsa naji bazan daina sonki ba, kuma zaki gane ni din masoyinkine zakiyi nadama sai lokacin da damararki ta kare, ban jima da shiga gida ba sadi ya shigo dauke da manyan ledodi biyu gashi inji bakinki yana kokarin ajiyewa a gabana na daka masa tsawa me yasa ka karbo mayar masa ba,a so, kiyi hakuri ya tafi banza kwadayayye sai kasan yadda zakayi dasu kwashe daga gabana kaine maye kaje kayi taci, sadi yi hakuri ajiye kayan ka tafi bayan fitarsa na juyo ina kallon umma me zaki yi da kayan? Nana kiji tsoron Allah yanzu sadi bai haifeki ba,kike daka masa tsawa. Kan nayi magana kaka ta shigo umma ta mike da sauri ta tarota na juyo ina kallonta na girgiza kai" haka kika kara tsufa dan Allah ki mutu mana" yi min shiru mara kunya bazan mutun ba in raina yana hannunki ki kasheni ina dariya nace bazan zauna a gidan ba kinji abinda ke daya ga kayan dubiya na bar miki tana dariya tace surukin nawa ne ya kawo. in kina sonsa na bar miki bara na tafi islamiya nayi waje. sati banje makaranta ba ina kwance daga ni sai shimi naji shigowar abba kai tsaye cikin dakina nayi saurin mikewa karsowa yayi yana murmushi zama yayi gefen gado my lovely sister kin kara kyau ya kawo hannu zai taban fuska ban san dana doke hannun ba. Abbagana hausa novels @ facebook. [12:10pm, 7/11/2016] Md: WAYE SANADI? 28 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz Meye haka kamar ba musulmi ba zaka shigo dakina har kayi kokarin tabamin jiki an gaya maka ni yar iska ce irinka ba....kan na karasa zabgan mari baki da mutunci ni zaki daka har ki kirani da dan iska za kici ubanki sai zaman gidan nan ya gagareki dan kina da kyau shi yasa nake lallabaki tunda na dafe wajen da ya maren na tsaya kamar an kafe ni ya juya ya fita karar mota ce ta dawo dani daga tunani nayi saurin fitowa har ya shiga daki bako sallama na dan na kaina ina kuka a gigicd ya juyo lafiya safiyya? Wani abun akayi miki? Cikin kuka nace dan kane ya mareni kuma Allah bazan yarda ba khalifa ya kwalawa kira ya shigo da sauri a fusace yace kai ka mare ta? Mari kuma daddy? Me ta min da zan mareta sai dai ko abba naga ya fito daga barinsu shi ya mare ki? Na daga kai safiyya meya hada ku? Dakina ya shiga ya kai hannu zai taban fuska ni kuma na doke hannun shi ne ya maren khalifa maza kira min shi tare suka sako kai kai abba me tayi maka ka mareta baiwarka ce? Daddy rashin kunya tayi min kai bakaji kunya ka kai hannu zaka taba jikinta ba? Ido ya zaro daddy sharri..... Mutumin banza yi min shiru ka juya ta rama marin da kayi mata ka kuma bata hakuri dady wannan yarinyar zan bawa hakuri har kuma ta maren daddy kar ka min haka in da ka shiga ka mareta har dakinta haka zata rama kan yayi magana na daga hann na zabga masa mari a fusace ya mike yayo kaina yaji muryar daddy in ka kuskura ka taba ta ranka zaiyi mummunan baci, kiyi tafiyarki safiyya ina shigowa naci karo da umma ina ki kaje? Umma naje dakin mijinki ko bakya so ina zuwa? Ina fadar haka na shige daki a fusace ya shigo dakin momy daman haka daddy ya zama kan wannan agolar maryam tayi karaf yaya abba ka dan ka gani sa,ar daddy kaci ba bai doke ba ni kama har dukana yayi a kanta mommy ta juyo tana kallonsa abba ni kaina sai da yarinyar ta maren sau biyu baice komai ba wata irin zabura yayi momy ta mareki? Kamar ka gani, wallahi momy sai nayi wa yarinyar nan mahaukacin duka sai dai daddy ya kashe ni.yaya abba har mota daddy ya sayi mata mu da umma sai dai direba ya kaimu. Abbagana hausa novels @ facebook. [12:10pm, 7/11/2016] Md: WAYE SANADI? 29 MUH'D*ABBA*GANA 09039016969 www.abbagana.pun.bz Ba zan sai muku motar ba in kudinkune na gani kai kuma da kake kawo zaka dake ta to bara kaji na gaya maka wallahi duk ranar da kayi gigin dukanta to kan na dawo ka bar gidan nan kaje ka nemi wani uban, Nafi kwana biyu ban hadu da abba ba dukkan suma ban hadu dasu ba yau ina zaune a falon umma khalifa yayi sallama ya shigo sannu da hutawa kaima sannu ina umma? Tunda ya fara magana ban dago na kalleshi ba sai yanzu tana kicin jin muna magana yasa umma ta leko khalifa ne? Bayan sun gaisa ta juya zubo masa abinci su sadiya ne sukayi sallama nayi saurin mikewa momy kamar a mafarki ummi fito ga sadiya fitowa tayi tana murmushi khalifa ya mike nana na dawo anjima okey khalifa na gode. Budurwar aljani meye labari? Na juyo ina harararta ban san rashin mutunci,saurayi ma n mutum baya gabana wai dan Allah yana ina? Oho masa momy tace ki dai bi a hankali mun jima muna hira sai karfe hudu suka tafi na daga rakasu na hangi abba a garden yana ganin dawowata ya taso kina agola har kika samu damar marin uwata, to wallahi ki shiga taitayinki duk ranar da tsautsayi ya kaiki kika kara karanbanin marin uwata sai kin raina kanki sai kace gidan ubanki ina murmushi na juyo mukayi ido biyj ita agolar da kake magana akanta tafi uwarka matsayi bare kai ina yi maka tuni kan maganar ubanka duk randa hannunka ya taba fatar jikina kasan wani uban gara ka zama ne lallabani dan kusan mi yanci wajen uban naka, ina fadad haka na juya ciki. Ina dakin umma ta shigo da murnarta nana Alhaji ya biya min makka babu wata murna dana nuna nana ki shirya kije ki gayawa baba da malam su zo suyi mass godiya umma meye abun zuwa godiya? Kema in na isa dake kije ki masa godiya tana fada ta fita sai washe gari na shirya da yamma tana falo na fito umma zanje gidan kaka tun jiya sai yanzu ta saki fuska to ki gaisheta kuma ki shiga kiyi masa godiya banyi musu ba na shiga yana cikin daki safiyya unguwa zaki? Fuskata a hade nace zanje na gayawa su kaka biyawa umma makka, ka ban kudi nasha mai dubu goma ya ban a bakin layin mu naga khalifa ina zuwa? Zanje gidan kakarmu ne bude motar yayi muje nayi rakiya. Abbagana hausa novels @ facebook.
Share:

6 comments:

 1. Zaenerb al-amin23 July 2016 at 04:25

  Slm inajin dadin littafinnan aci gaba

  ReplyDelete
 2. Yayi dadi aci gaba.

  ReplyDelete
 3. ABUBAKAR IBRAHIM3 August 2016 at 09:58

  Amma rashin kunyan ta tayi yawa

  ReplyDelete
 4. Havadai xatayi nadama

  ReplyDelete
 5. rashin kunyanta yayi yawa.

  ReplyDelete
 6. Gaskiya litafi yayi dadi

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).