HEEDAYAH!
77
written by miemie
Ya saita daidai kan heedayah yayi shooting sede fortunately bullet nasa ya qare, Andrew yace "what are u waiting for se police sun iso ne?" Joseph yace "damn it! bullet na ya qare," Andrew yaja tsaki sannan shima ya seta daide kan heedayah da ta manta ma so ake a kasheta duk hankalinta yabi kan rayyan yadda jini yake bulbula daga gun da aka harbesa kamar lalaceccen famfo," saidai shima nasa bullet din yaqare, a daidai lokacin suka jiyo qarar motocin police a 360 suka ja motar su suka bace a gun, ba abinda heedayah takeyi se ihu da kuka ga hannunta da jikinta duk ya baci da jinin rayyan, "rayyan pls don't die, am here u have to be strong pls for me," da kyar ya mata murmushi "don't worry I'll...awch...i'll be fine" yana magananne idanunsa suna kafewa a hankali har suka gama kafuwa, "nooo rayyan nooo you can't die pls open your eyes dan Allah rayyan pls dont go nd leave me," wata female police aka ce ta ciro heedayah daga motar datayi rugu rugu bara a zata mutum xe fito a raye cikin motar ba kowace inch ajikin motar bullet ta shige, da kyar ta iya ta ciro heedayah dan yadda ta kankame jikin rayyan tana ihu tana kuka tana cewa police din "ki sake ni pls, rayyan needs me, let go off me." Nan da nan ambulance yataho aka dau unconcious rayyan akasa acikin ambulance din heedayah tana gefensa ta riqo hannunsa tana ta rusa kuka, motarsu kuwa police da investigators ne suketa daukan picture din ana uploading a news, nanny na a parlour tana dusting TV mistakenly hannunta ya danna power button har zata kashe setaga breaking news dan haka ta tsaya tana kallo can taga S63'n daddy tace "Allah sarki wannan sak motan alhj" can setaji me casting news din tana fadin "saurayi da budurwa aka samu acikin motar wanda a ynxu haka suna Ameenu Kano kasancewar gunshot da saurayin ya samu a hannu, cikin ikon Allah budurwan tafito daga cikin motar ba tare da ciwo ba..."Hajiya! Hajiya! Kizo da sauri" mummy dake daki ta fito a gigice "ya lfy?" "Hajya da wace mota su heedayah suka fita?" Mummy tace "am not so sure amman inaga kamar da s63'n habibi ne," nanny tahau salati, "lfya?" mummy ke tambayarta, "Hajiya su heedayah, heedayah da rayyan..." sekuma ta fashe da kuka mummy da ta shiga cikin duhu tace "meya samesu nanny? Tell me" Nan aka sake fara nanata news din again salati mummy keyi itama, da gudu ta karisa daki "habibi su heedayah anyi attacking nasu" tafada jikinshi tana kuka "what? Ina suke ynxu?" "Ameenu kano" ta fada a takaice nan da nan suka duru a mota se aminu kano*** ynxu akayi da rayyan O.R(operation room) heedayah sekuka take ta rusawa tana ihu ita sam seta shiga. Zama tayi a bakin kofar a qasa tana rusa kukanta, daddy, mummy da nanny tagani kamar daga sama da gudu tayi hugging mummy tana kuka "mummy rayyan kar ya mutu pls, daddy do something to save him pls" hugging nata duk sukayi suna kwantar mata da hankali. Idanta na kafe kan red bulb na O.R din duk addu'an dayazo bakinta yi takeyi ita de Allah sa rayyan nata yayi surviving operation din. An hour later; red bulb na O.R din mutu kofar ya budu da sauri heedayah ta qarisa "doctor how is he? Did he made it?" Dr'n yace "kune family'nsa?" Daddy yace "eh how is he?" "Alhamdulillah" dr'n ya fadi "the operation was a succes mun samu mun cire bullet din he will be fine in shaa Allah," heedayah tace "alhamdulillah" tana ma mummy murmushi "dr can we see him?" Dr yace "eh amman one at a time" yana kaiwa nan ya fice mummy tace da heedayah "kishiga kigansa heedayah" tana me mata murmushi nan heedayah tashige ciki ta nufa kan gadonsa hannunsa ta riqo atake idanunta suka cike da hawaye "u made it rayyan! Am so relieved" tana shafa gashin kansa a hankali ya soma bude idansa har ya gama budewa hawayenta ne ya diga bisa kumatunsa murmushi tamasa sannan tasa hannu ta goge hawayen nata "u made it rayyan! Am so sorry this is all my fault," a hankali yake magana "no heedayah this is not ur fault haka Allah ya kaddara, am happy tunda ba ke suka samu sukayi shooting ba, atleast na iya nayi protecting naki my princess" heedayah da idanunta suka ciko tam da hawaye tace am so sorry rayyan haka Allah ya kaddara amman somethng smells fishy, nasani ko ba a gaya mun ba alhj lawal da alhj ismail are behind this mess, nd nayi promising naka se sunyi regretting hurting king dina," zeyi mgn ta aza hannunta bisa lips nasa "try not to talk ka huta kaji su mummy suna waje dey are all happy you are alive!" Murmushi yamata nan ta miqe kan zata fita hannunta ya riqo "don't go my princess" dan haka ta ja kujera tazauna a gefensa tare da riqe hannunsa ahaka ha yayi bacci sannan ta fito "mummy daddy, rayyan is fine alhj lawal da alhj ismail must pay for this," mummy tace "me kke nufi heedayah?" Nan heedaya ta kwashe labarin komi tabasu, daddy yace "they have cross the line this time, they have to pay police station zamu wuce muyi filing criminal case akansu," heedayah tace "no daddy calm down nd leave this to me in shaa Allah nida hannuna zan kamasu in kaisu jail where they belong"
HEEDAYAH!
78
written by miemie
Wayar alhj lawal ce tayi qara ya daga "hello dan uwa," alhj ismail yace "kaga news kuwa?" Alhj lawal yace "a'a wani abu ne?" Alhj ismail yace "ai mutanenda kasa aikin sun kuma failing namu, gashi nan a news basu ma iya sun kasheta ba wani suka harba ba ita ba," alhj lawal yace "whatt? How could they? Gosh wannan mutane anyi sokaye wlh mstw" nan ya kashe wayar yana nazarin abunyi***
2 days su rayyan sukayi a asibiti sannan aka sallamosu hannun nasa da dan sauki amman an daure masa, bayan sun dawo gda aka sa nanny gyara ma rayyan daki se tura baki take dan haka kawai jininta be hadu da rayyan ba dalilinta kuwa shine batta son ya auri heedayah tafison heedayah da don moha tana cikin gyara kan gadon dakin rayyan ya shigo "sannu anty" yace mata, nanny ta sako baki, bawanda ya taba ce mata anty se nanny, sosa keya ta soma "ba sekace min anty ba, nanny ma yayi," murmushi rayyan ya mata ya dago pillow ya aza kan gadon "a'a ai ba nanny ta bace ke, mesa zance miki nanny? Nide anty zanna ce miki," ze kuma daga dayan pillown nanny tace "a'a kabary hannunka na ciwo kar ka fama" ta amsa ta ajiye, "thank you" yace mata, tace "what for?" Yace "for preparing my room," nanny tace "ba komi" tana goge TV'n dake dakin rayyan yace "anty I love heedayah so much this bullet was suppose to penetrate into her body amman dan yadda nakeson ta delibrately nasa hannu na yasameni a shoulder na," nanny tace "dagaske rayyan?" Kai ya gyada mata "kai! Allah sarki rayyan gaskia kai jarumi ne nd you deserve to be heedayah's husband dan tun ynxu ka nuna cewa zaka iya kareta koda it'll take you ur life ne, Allah saka ma da alheri," "ameen" yace yana mata murmushi ta cigaba; "baran boye maka ba rayyan at first kwata kwata banson ka sbd agani na zaka kwace ma don moha heedayah sbd tun tana 'yar qarama yakesonta amman within dan time da mukayi spendn dakai ynxu naga there is something special about you no wonder kayi stealing heart na heedayah da wuri haka, kasan meh?" Rayyan dake murmushi yace "a'a anty," nanny tace "ai tun dawowan heedayah daga Edo ta canza completely kullum cikin kiran sunanka take" dariya sosai rayyan yakeyi nanny tace "amman fa kar ka gaya mata i told you so," yace "in shaa Allah anty, amman kinyi wata mgn a nan wacce ta daure min kai," nanny tace "what is it?" Rayyan yace "naji kince kinason heedayah ta auri don moha," nanny tace "eh a da kafin nasan who u truely are ba," yacigaba; "ko bakisan meya mata bane?" Cikin rashin fahimta nanny tace "kamar ya? meya mata?" Rayyan yace "shknan it seems bata gaya miki ba," nanny tace "what is it pls tell me," rayyan yace "when the right time comes zaki sani," haka nanny tata insisting har sanda rayyan ya fda mata abinda yasani, "rayyan are u sure of what u just said to me? No wonder heedayah ta canza attitude nata game da don moha amman gaskia ban yarda don moha ne yasa a kasheta ba zan iya yarda shi yayi kidnpping nata for the while da take zama a kano amman kam don moha bare iya kashe heedayah ba koyasa a kashe ta ba"*** heedayah na kwance a dakinta nanny tashigo bayan ta zauna akan gadon tace "heedayah shin me ya hadaki da don moha? I know there must be somethng da kke boyemun," "nanny na gaya miki ba komi kawai bana son shi ne, rayyan nikeso" "qarya ne dole akoi nafa sanki heedayah tun haihuwarki, gayamun pls heedayah ta," heedayah tace "tunda kinyi insisting kan sekinji fine"... nan ta irga mata komi exactly haka rayyan ma ya gaya mata daxu. Nanny tace "mummy fa tasani?" Heedayah ta kada mata kai da alaman "a'a," nanny ta cigaba "heedayah come to think of it don moha na sonki ba yadda za'ayi ace ya tura mutane su kasheki,"... heedayah ta katse ta "nanny knan da yyi kidnapping dina nan a kano kuma fa?" Nanny tace "yes anan dinma sbd yana son yasan me kke nema a gdansu ned ai keda bakinki kin fada kan har kaya yna siya miki be taba barin ki da yunwa ba so tell me taya ze sa a kasheki?" Heedayah tayi shiru daga bisani tace "toh na yarda bashi yasa a kasheni ba amman kuma da nasan da hannunsa aciki waya sani ko da daddy'nsa yake aiki," maybe daddy'nsa yayi manipulating nasa so kinga is all thesame to me nothng will change." Nanny tace "ni bawai mace sekin auri don moha bane a'a rayyan is a very cool nd gentleman amman atleast kidena blaming don moha for the crime beyi committing ba," heedayah tace only "time will tell inhar he has somethng to do with what happened to me kokuma he is innocent as how u say it.
Alhj lawal na xaune a dakinsa can ya tashy ya dauko wata brief case ya tattara duka files na alhj s.u gu daya acikin brirfcase din yasa lock sannan ya rufe ya daga katifar dakinsa ya ajiye a gun. Yanata expecting call frm Andrew da Joseph amman shiru, mgn yasoma yi wlh inhar heedayah baki mutu ba toh kisani baraki taba iya kamani ba dan nafi karfin a kamani kisani "I'll always be one step ahead of you" ya kare maganar tare da yin wata shu'umar dariya. Wayarsa ce ta hau ruri number'n Joseph yagani ba tare da bata lokaci ba ya daga...
Toh masu karatu meh wannan mugun mutumin yake shirin yi?? Shin yaya daukan revenge dinnan yake kasancewa? Heedayah na iya ta kama alhj lawal? If yes how?
HEEDAYAH!
79
written by miemie
"Aikin dana saku yin kenan? Mace nace ku kashe ko na miji?" Joseph yace "bahaka bane boss they were together acikin car din bullet din was meant for ita yarinyan se saurayin yasa kafadarsa ya samesa but karka damu duk inda take se mun kasheta kuma ba wanda ze kamamu, this I promise you," alhj lawal yace "yawwa karfa kuyi aka ma ku, ku kashemin yarinyan nan," Joseph yace "kar ka damu boss" nan yayi yanging call din.
Heedayah na zaune a dakinta tana tunanin yadda incident na ranan ya faru, daga bisani tace "for sure ranan da muka fita daga gda naga wata mota ta mirror amman ai bare yu motar mutanen bane," wata zuciyartace mata "why not?" Tace "in har motarsu ne I have to find out" wayarta ta dauko takira prosecutir's office "hello its prosecutor Heedayah S.u due to attacking dina da akayi days back inason inyi investigation dan gano waye mastermind din, so I need one bullet proove car da 3 police amman inason kar susa kayan aiki su taho da kayan gda, I need them in the nxt 1 hour"..."recorded miss Heedayah they will arrive soon" abinda comp ya fadi knan. An hour later suka kariso heedayah na bakin kofar parlour tana jiransu, drinks tayi serving nasu, kasancewar dukan su maza ne heedayah ta wurga ma dayan key'n motarta "gashy i want u guys to ride in this nikuma zan shiga bullet proove din am sure wanda aka turosu su kasheni still suna nan somwer suna jiran infito su bini su kasheni so bayan na fita kuma seku biyo ni amman ba bumper to bumper zakuyi follwing dina ba when ever wannan mutane suka fara shooting dina u guys shud try ur very best kui shooting tayar motarsu inda they cant escape anymore kunga daga nan se muyi arresting nasu," police din yace "great idea amman baki ganin is a little bit risky?" Heedayah tace "don't worry." Yadda ta fada haka sukayi bayan tafito daga gda ta leqa dama da hagu bata ga motarsu ba dan haka ta sa kai ta cigaba da tafiya can wajen junction na barin unguwarsu su Joseph sukayi parking, Andrew yace "Joseph gata can fa lalle yarinyan nan batta da tsoro yau ko wanda ze kare tanma bata fito dashy ba lol, goodbye baby" nan sukayi pulling trigger suka saukar da windows nasu suka fara shooting motar sede to their suprise sukaga bullet bai iya penetrating ta cikin motar "damn it!" Joseph ya fadi "wato tayi wayo yau da bullet proove tafito" kafin su hankara suka fara jin wee-wee karar motan police reverse andrew yayi kasancewar shine me driving din amman ina kafin su hankara sukaji tyre'n bayan su duka biyu sun sace due to gunshot da aka musu steering motar ya buga "damn it!" Joseph yace "what do we do now? Mufita mu gudu kawai" nan suka fiffito suka soma gudu mgn acikin headphone dayan police din yake "stop right there one more step nd I'll shoot u to death" atake joseph ya tsaya andrew daya ki tsaywa karan harbin bindiga yaji a sama atake shima ya tsaya nan police da heedayah suka kariso akayi arresting nasu aka sa musu handcuffs a hannu tabaya aka tura kansu cikin wata mota se police station inda aka daura hannyensu da wata chain a bayan kujera haka kafafunsu ma yadda barasu taba iya guduwa ba dan an datse chains din da kwado, heedayah na tambayarsu "waya turoku ku kasheni?" Shuru suka mata, "am talking to you ko baraku answer bane?" Andrew yace "what are u talking about miss? Ba wanda ya turo mu kawai mu mukayi deciding mu kasheki," heedayah tace "lie, liar kawai" tayi ido ma wanda suke tsaye a gefenta wasu kattin police guda 2 shocking aka samusu nakusan minti biyu sannan tace "ya isa," se faman "awchh" joseph da andrew sukeyi, heedayah tace "what? Are u ready to tell me now? Andrew yace ba wanda yace mu kasheki kawai mu mukayi deciding dan ke prosecutor ce," heedayah data fusata bata san sanda ta daga hannu zata kai masa punch ba, mazan gefentan ne suka rikota tace "ure both lying was it alhj lawal or alhj ismail that ordered you, huh? Answer me nawa ya biyaku yace kar ku fada? Tell me am ready to double his payment, tell me!" Dayan police din yace "kibarsu zuwa gbe in suka sha azaba da kansu zasu fada" da kyar aka tura heedayah waje sukuma aka fara basu azaba iri iri nakusan 1 hour, da Joseph yaga haza yace "zamu fada zamu fada," nan aka shigo da heedayah tace "yes? Waya saku?" Joseph yace "zan gya miki ne only if zakiyi doubling kudin da boss ya bamu," heedayah tace "zanyi, nawane?" Joseph yace "2million yace ze bamu," dan karya. Heedayah tace "then nikuma zan baku 4 million Just tell me," joseph yace "zan gaya miki gbe nagaji ynxu," "noo sekun fada min ynxu," police dake gefentan yce "prosecutor tunda sunce zasu gaya miki gbe se mu jira ai"... Badan tanaso ba ta fice tare da gaya ma police din kar abar kowa yayi visiting nasu, "okay ma!" Ya ce sannan ta fice zuwa gda, mummy dasu rayyan ta tarar a parlour duk sunyi tagumu, mummy ce ta taso tayi kanta "heedayah my princess ina kkaje? We were all worried sick about you kinsan fa sarai nemanki ake a kasheki taya zaki fita ke kadai?" Heedayah tace "mun samu mun kama wanda suka harbe rayyan, ynxu haka suna holding cell a police station," daddy yace "alhamdulillah so?" Heedayah tace "sunki gayamun waya turosu wai sam se nayi doubling kudin da boss nasu yabasu, I can feel it alhj lawal ne ko alhj ismail suka turosu nd sunbasu 2million kan kar su gaya, ynxu I need 4 million, the moment namasu presenting kudin zasu fada nd kunga suna fada shknan zamu iya kama alhj lawal" daddy yace karki damu ina Tundra dincan da ba a hawarta? Zamu siyar da ita a hada musu kudin i'll do whatever it takes to see alhj lawal nd ismail behind bars
HEEDAYAH!
80
written by miemie
"Thank you daddy" ta fada, daddy yashfa kanta "am the one who should be thankful da Allah yabani 'ya me protecting parents nata kamar ki, Allah mki albarka," "ameen" kowa agun ya fadi sannan mummy da daddy suka fice izuwa dakinsu take daddy ya kira PA'nsa yazo ya dauki tundra din yakai gun siyarwa at first me saya da siyar da motan yace bare siya ba nd koda ze siya ba kudi a take ba sbd ba kudi a gari ynxu, PA'n ya gaya mishi ko 4million ne ya bada ynxu sauran sedaga baya sbd ana bukatar kudin ne as emergency, hakan kuwa akayi saidai yace se zuwa gbe ze samu kudin yamasu sendn in shaa Allahm
Rayyan yace "my princess taya zaki fita without informing any of us? Kinsan yadda hankakin mu ya tashy kuwa?" Heedayah tace "am sorry my king I just had to, su suka sake pushing dina kalli fa har yau hannunka yaki warkewa," nanny data zura musu ido tace "soyayya manya su king da princess aikam heedayah abinda kkayi daidai ne sbd mutanen nan sun saita bullet din daidai kanki lokacin da rayyan ya saki ajikinshi, ganin ze taba ki ne yasa hannunsa dagan gan seya samesa," heedayah tace "what? Really nanny? Rayyan mesa kasa hannunka?".. Rayyan yace "toh me kkeso inyi? To sit aside inga bullet ya shige ki? Kema kinsan I can't do that," heedayah tace "awwn thank you so much for saving my life, I owe you my life rayyan"***
Joseph ne yace da police din "can I make a phone call?" Police din yace "with who?" Yace "with my wife ofcourse," nan aka sin ce shi number'n alhj lawl ya dura ringing daya biyu alhj lawal ya daga "hello wake mgn?" Kasa kasa joseph ke mgn yace "joseph ne," alhj lawal yace "ya har kun gama aikin ne?" Joseph yace "no boss we were caught ynxu haka muna police station," "whaattt?" Alhj lawal yayi exclaiming, "how could you? Taya zaku bari su kama ku? Mstw ynxu ya me ake ciki?" Joseph ya irga masa komi, alhj lawal yace "u can't do this to me bahaka mukayi da kai ba," joseph yace "ni ynxu ba turanci nikeson ji ba kudi kawai zaka kara dan in har ta kawo 4mil dinnan gbe gaya mata zanyi kuma a kama ka kasani," alhj lawal yace "toh toh naji nawa kukeso?" Joseph yayi murmushi "ai yadda tayi doubling kudinka haka zakayi doubling nata," alhj lawal yace "what? Bakada hankali ne? 8million abin kuma hauka ne? A Ina zan sami 8mil sbd Allah," joseph yace "toh shiknan tun da haka kace tana kawowa gbe se mu gaya mata," alhj lawal yace "a'a bara ayi haka zan nemo 8mil din," joseph yace "nd taya zan yarda zaka bamu 8mil din?" Alhj lawal yace "zan turo wata ta kawo maku kudin gbe in kuka gani ai baraku fada bako?" Joseph yace "se boss! Muna jira" alhj lawal yayi hanging. "Lalle ma joseph kake ko meh bakada hankali 8mil dan ubanka wlh baran bada 8mil ba kuma asiri na bare tonu ba nan yayi dialing wata number a wayarsa, ya kare wayar tare da fadin "toh seka aiko tan," yana kaiwa nan yyi hanging.
Washegary daddy nata jiran alert amman shiru, ya kira mutumin yace da daddy "yi hkr alhj nan da 'yan awoyi zan turo." Daidai 10:10AM wata budurwa christian tasha ado sosai ta shigo police station din tama police din bayani kan ita kawar matar Joseph ce, matar ce ta aikota ta kawo masa abinci dan haka aka barta ta shiga bayan sun gaisa da joseph da Andrew, joseph yace "wace ke?" tace qawar matarka ce, ita ce tace na kawo maku abinci, wai she's sorry bata samu ta kawo da kanta ba sbd yaranka sun fara exams tana dan musu revision nd that she loves you"...joseph yace "ayya bakomai kice mata i love her too nd the kids kice mata very soon kudin zai shigo hannunsu," budurwan ta amsa da "toh gshi abinci ne daman wai you shud eat well," tana kaiwa nan ta fice. Joseph da yunwa yaci uwarsa yace da andrew "oya oya muci," nan suka loada abincin tun kafin su gama suka fara rike maqoqaro kafin ace meh suka fara aman kumpa kafin a nemo mota akaisu asibiti poison din yaci jikinsu duk suka fadi a muce nan akace aje a nemo matar da ta shigo ynxu dan ita tayi poisoning nasu amman ina kamar aljan haka ta bace. A gdan alhj lawal na hangota harda cin tuntube dan mamakin daya kamani, ko de alhj lawal ne ya turata tayi poisoning joseph da andrew? ina cikin wannan mgn alhj lawal yace "kinyi kamar yadda mukayi planning?" Kai ta gyada masa nan ya miqa mata wata envelope na kudi "becareful kar a kamaki," tace "I know how I do my job" sannan ta fice. Murmushi ta gefe alhj lawal yayi "se muga wa ze gaya miki gaskiyan ynxu heedayah" yana kiwa nan yashige dakinsa.
Su heedayah kuwa se 1:30PM suka samu 4mil din da sauri tayi driving ta isa police station din sede da ta duba cell da aka ajiyesu bata ga kowa aciki ba dan haka ta tambayi daya daga cikin police dake tsaye a gun "Ina mutanen da suke cikin nan?" Ya amsa ta "earlier daxu dey were poisoned ynxu haka sun mutu danginsu har sun tafi da gawakin nasu"..."whaaatt????" Heedayah tace
HEEDAYAH 76----80
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
mungode
ReplyDelete