shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 13 July 2016

HEEDAYAH 31-----35

HEEDAYAH!

21
written by miemie

Da kyar ta iya tayi getting rid of tunanin a mind nata, taje tasamu su daddy a parlour tayi joinimg masu suna kallo amman fa hankalinta ba akan kallon yake ba, around 10:00pm duk sukayi seda safe kowa ya wuce dakinsa. Yau ma kamar kullum nanny ta shirya heedayah sch, atare suka isa da su don moha tana ganinsa ta fara tafiya da sauri dan kar ya mata magana, gudu yayi sannan ya iso ta ya riko hannunta ta wabce tace "muhammad leave me alone" don moha yaji mamaki sosai, "heedayah pls mena miki kke avoiding dina, atleast ki gaya mun menayi nd stop avoiding me dan Allah" heedayah ta watso masa harara "wallahi don moha in baka barni ba i'll report u to the principal's office" takama hanyan tafiya kafafunsa kasa rikesa sukayi ya sulale kasa dakyar yasamu ya tattara kansa yayi class, haka ya wuni a sch ranan so dull ba walwala a tattare dashy. Bayan da aka tashy heedayah taje tasamu aunty'nsu "ma'am what will I study in order to become somebody in the future who can arrest criminals?" Aunty'nsu tace "heedayah why are u asking?" Heedayah tace "i just want to be one" aunty tace "but u said u want to be a doctor, why have u changed ur mind?" Heedayah tace "just cuz..." Sekuma tayi shiru anty tayi murmushi "well to become someone who can arrest criminals u have to go through a law sch..." haka de ta ta ma heedayah bayani daga karshe tace "then u can now decide weather to charge a person or not after becoming A PROSECUTOR" heedayah tamata godiya sannan ta fice tabar aunty cike da mamaki dan a gaskiya heedayah na burgeta sosai kominta daban yake is like she's unique. Bayan anzo daukan heedayah sukata hira acikin mota ita da mal idi har suka isa gda, tayi dakin daddy tayi hugging nasa taga ba mummy a dakin tace "daddy yau na tambayi auntinmu me mutum ze karanta ya iya kama criminals tace min zan je law sch se inzama PROSECUTOR kaga inna zama se in kama daddy'n don moha mukaisa prison ko daddy?" Daddy yamata murmushi ta dau jakarta ta fice sukaci karo da mummy, mummy tayi hugging nata sannan ta wuce dakinta ta canza kaya ta sauko taci abinci. Haka de rayuwa ta ciagaba da kasancewa daddy da family'nsa, mummy batta wasa da maganin daddy jiki de har ynxu gashi nan ba improvement. Don moha kuwa kusan sau uku yana zuwa gdansu heedayah amman taki kulasa har ya gaji yabari hakan kuwa ba karamin affecting dinsa yayi ba, heedayah ma kwata kwata bata jin dadin abinda take masa amman ya ta iya? She can't forgive him for his dad's mistake, daddy'nshi ne yaso kashe daddy'nta, nanny tayi tayi da heedayah ta dena blaming don moha for his father's fault duda they are not so sure daddy'n don moha ne cause din rashin lafyan daddy amman heedayah taki jinta.
Bayan sati daya, yau ya kasance thursday heedayah na sch a yayinda mummy ke office tabar care din daddy gun nanny. Alhj lawal da alhj ismail na hango a gdan shi alhj lawal din, alhj ismail yace "yallaboi gashy mun samu wanda zasu siye gdan" alhj lawal yace "ahh to aikinka yayi kyau, ynxu kasan me nakeso da kai?" Alhj ismail ya girgiza masa kai da alaman a'a, alhj lawal yace "zakaje da wanda zasu sayi gdan, gdan alhj s.u ka nuna musu cikin am sure wajen dama ka nuna musu ko? " alhj lawal yace "eh amman yallaboi ai zan tauna mana asiri inna je gdan nasu dan zasu ganni gaskia baranje ba, muba ma wanda ze siyan file din gdan kawai yaje dashy ya nuna musu" alhj lawal yaja tsuka "kaifa baka da wayo Allah, taya zamu basa file din gdan? Ba seya gudu dashy ba, dolenka zakaje da shy kuma..." Alhj ismail ya katse sa "nifa baranje ba alhj" alhj lawal yayi murmushi daman already ya amso maganinsa gun bokansa ya sa acikin ruwan yace "toh shknan ni zanje, ga ruwa kasha ana zafi" ya zuzzuba musu a kofi kowa yakai baki alhj ismail yafara sha alhj lawal kuwa ya makale nasa a lebe kawai, alhj ismail nagama kurbewa bayan like 15mins alhj lawal yace "soo ya yanzun zaka je?" Alhj ismail yace "eh sosai alhj zamuje gdan alhj s.u mu saida gdansa" suka zarce da dariyan mugunta dukansu***
Around 3:00pm su mummy suna zaune a garden dukansu me gadi yazo yacemata tayi baqi tace ya kariso dasu, alhj ismail dawasu maza biyu naga, wanda a kalla dayan zeyi 48yrs dayan kuma 55yrs haka, mummy tamusu sannu dazuwa, heedayah na ganin dady'n don moha tashiga tsoro shiko duk sanda suka hada ido seya mata murmushi, daddy kuwa jikinsa yafara rawa sosai dakyar mummy tayi calming nasa down, da wayo mummy ta kora heedayah ciki amman dan wayo irin na heedayah taqi shiga ciki ta labe daga wani lungu tana jinsu. Alhj ismail yace "ya jikin dan uwan nawa?" Mummy tace "da sauki" da har zata tambayesa ya jikinsa sekuma ta fasa. Ya ja numfashy sannan yace "hajia hafsat" ta amsa da "naam" yace "kinga wadan nan mutane?" Mummy tace "eh mun gaisa ai wani abu ne?" Alhj ismail yace "gdan nan zasu siye ko ince sun riga sun siye sun zo duba ne" mummy ta zaro ido "ehh? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Alhj ismail wata erin banzan magana kake ne? Ta ya zaka siyar mana da gda? Dama du zaman da mukayi dakai ba tsakani da Allah bane? Toh wlh kayi qarya, nd kasani baraka taba siyar mana da gda ba sbd files na gdan ga ba a gunka suke ba suna gun mijina, mutumin banza amman Allah wadar din erin ku wlh kaji kunya mstww, ku tashy kubar min gda or else in kira police suzo su tafi daku wllh kaji na rantse" alhj ismail yayi murmushi sannan yace "me yayi zafi hajiya hafsa? Zamu tafi but tukuna" yasa hannu cikin aljihu ya ciro wata paper ya miqa wa mummy tasa hannu ta karba da full confidence dinta, abinda tagani cikin takardan ne yamun razana ta ba shakka wannan signature din daddy ne akan sunan alhj ismail da shaidar ya mallaka ma alhj ismail gdan nan nasa da yake ciki, da kyar mummy tayi gathering evidence tace "toh se meh? Wannan paper is not real" alhj ismail yace "dont decieve urself maman heedayah ke yar boko ce wanga paper is real tun wuri ku fara tattara kayakinku dan mutanennan suna bani kudi na i have no other option than in fita daku na karfi daga gdan nan" yasa hannu ya wabje paper'n yace da mutanen nasa "mutafi"

HEEDAYAH!

22
written by miemie

Suka kama hanya suka fice heedayah ta bisu da kallo, kafafun mummy kasa daukarta sukayi jin kanta kawai tayi a qasa, ba abinda takeyi se hawaye haka daddy ma heedayah ta kariso gun da gudu tayi kan mummy tana gogemata hawaye "bar kuka mummy na" mummy tace "heedayah take ur daddy inside" heedayah batayi musu ba ta tashi taja daddy'nta suka shiga ciki tace "daddy na bar kuka, kar ka kula daddy'n don moha dinnan ya cinye gdan in ana cinyewa ba kana da gdaje dayawa ba semu koma sharada ai ko GRA, bar kuka kaji daddy na?" Tasa hannu ta goge masa hawaye zuciyar daddy radadi take masa sosai kasa rikewa yayi jikinsa ta hau rawa sosai can anjima yabar motsi heedayah ta kwala ihu atake mummy da nanny suka iso parloun "heedayah meya faru??" Kasa fadin komi heedayah tayi se kukan datakeyi tana nuna daddy da yatsa mummy sukayi kansa ta tabbatar da daddy baiya numfashy tana kuka ta dau wayarta ta kira family dr dinsu yace gashy nan zuwa nan da nan ya iso yabama daddy immediate treatment yace "ma'am akoi dan abubuwan dayakamata kuna avoiding inbahaka ba rashin lafyan alhj will only get worse," mummy tace "ina jinka dr," dr yace "ma'am na farko, kudena yawan masa maganganun dazasu ringa tsinka masa zuciya, na biyu kudena yawan sasa kuka, hasali ma duk abinda kukasan baida dadin ji kudena fada masa" mummy tace "toh dr nagode in shaa Allah it won't happen again," dr yamusu fatan alheri sannan ya fice. Can guessroom dake sama mummy ta haura ta shige bangida ta rufe kofar ta ringa kuka kamar ba gobe batasan kuma ina zata sa kanta ba gashy abbanta bayya nan, if only yana raye da shi kadai ze iya cire ta acikin tsaka me wuyan da take ciki ynxu, kwata kawata ta manta daddy nada gdaje bayan wanda suke ciki, haka tata kuka a bangdan can heedayah taji shiru ta shiga neman mummy har Allah ya kawo ta dakin taji karan kuka a bangida ta karasa tana kokarin budewa amman yaqi buduwa, "mummy open the door, pls kibar kukan pls" itama ta fashe da kuka uwa nayi 'yan nayi miemie na gefe tana miqa musu tissue, tausayin heedayah ne yakama mummy sosai dan a 'yar shekarunta bekamata ace tana facing problems da tension haka ba, ta budo kofar heedayah tayi hugging nata tightly munmy tace "is okay my princess kukan ya isa haka kinji? Everythng is gonna be fine jekiyi sallah ki kwanta kinji?" Heedayah ta dago jajayen idanunta tace "mummy wai daddy'n don moha ya ce mufita mubar gdan nan?" Mummy ta share yar kwallarta "waya gaya miki?" Heedayah tace "ni naji da kunne na" mummy tace "heedayah listen to me, kinga banson wannan abu yayi affecting naki, karki kula daddy'n muhammad zamu bar masa gdan ai akoi Allah ko?" Heedayah ta gyada kai mummy ta cigaba "good semuta addu'a Allah kawo mana karshen wannan abu, zan nemo mana new home semu koma ciki ko?" Heedayah tace "ai ba sekin siya mana new home ba mummy, daddy yacemun yana da wani gda a sharada da GRA" se ynxu hankalin mummy yadawo jikinta ta tuna tace "heedayah Allah miki albarka ynxu zo muje daki muyi alwala muyi sallah seki huta ko?" Suka fice bayan sun idda sallah sunyi addu'a sosai mummy tasa heedayah baccin dole amman ina heedayah taki a tare suka koma daki suka sami daddy kwance akan gado da hawaye na gangara akan fuskarsa suka karasa kansa mummy tasa hannu ta goge masa hawayen tace "habibi kukan ya isa kaga dr yace kadena kuka u'll worsen ur situation ya isa pls" ta tashy ta fara duban wardrobe ta inda daddy ke ajiye files nasa taga gun wayam! Ba komi hankalinta ya kuma tashy daddy yafara motsa jiki, heedayah tace "mummy daddy nason yafadi wani abu," mummy takaraso tace "habibi wani abu ne?" Girgiza kai kawai daddy keyi da alaman a'a mummy tace "a'a meh?" Se faman jijiqa kai daddy keyi yana kokarin daga hannunsa amman yakasa sede in aka sa hankali za'a gano gun da yake aje files nasa yake kokarin nunawa, mummy tace "ba files din?" Ya gyada mata kai, tace "toh na ina? Ina ka kai?"Jijiqa kai kawai yake tayi can mummy tace "ko duka files nakan ne babu kaba alhj ismail?" Daddy ya gyada kai a hankali yafara zubda hawaye, wani tokari mummy tajiyo a zuciyarta shiknan nata ya kare kuma, takuma tambayansa ya kuma gyada mata kai heedayah tafara maganan zuciya "in ta haka envelope dana gani a hannun daddy'n don moha shine wanda mumy ke nema knan" mummy tasa hannu ta gogewa daddy hawayensa sannan tace "if only... Habibi if only zaka iya gayamun mesa kaba ma wannan mugun mutumin daka dauka abokinka ne dukiyar ka kab ba tare da kayi shawara dani ba, bansan ina zan kaimu ba ynxu, abbana bayida rai, aikina bawani salary babba bane da har zan iya biya mana kudin haya, innalillahi, sede dan abinda na samu acikin gado na, Ya Allah ka kawo min qarshen wannan masifa" ta soma maganan zuciya "Alhj lawal is my only hope ynxu, dole in kirasa in masa bayani ko ze iya taimaka mun" nan tabar maganan zuci tace "heedayah miqo min wayar daddy da tawa" heedayah ta miqo mata ta lailmo number'n alh lawal a wayar daddy sannan ta dura acikin wayarta tayi dialing ringing sau uku yayi alhj lawal ya daga "assalamu alaikum"...
To masu karatu ko wani munafincin kuma alhj lawal ze kulla se Allah kubiyoni dan ji...

HEEDAYAH!

23
written by miemie

Mummy ta tashy tabar dakin, heedayah zata bita daddy ya mata nuni da kai da alaman karta bita ta zauna, haka ta zauna amman hankalinta nakan mummy. Mummy ta amsa sallamar alhj lawal "wa alaikumussalam, ina wuni?" Ya amsa a takaice tamasa bayanin ko wace ita, yace "Allah sarki hjy hafsa, ya jikin me gdan?" Ta amsa da "da sauki, alhj lawal taimako zakamin dan Allah" ta fara kuka, alhj lawal yace "anything for you hjya, ina jinki" mummy ta labarta masa labarin bata bar komi ba alhj lawal yace "incompetence! Karya ne wlh, taya ze sayar muku da gda? Wato dan alhj s.u ya yarda dashy ya bashi amanan arzikinsa shine ze saqa masa da butulci ko? Toh wlh yayi karya kar ki damu hjy hafsa kude ku dage da addu'a nima zan saku aciki in shaa Allah bare siyar muku da gda ba, i'll try to talk to him, ynxu ma zan je gdansa..." Mummy tana kabary ko gbe kaje, alhj lawal da munafirci yana a'a hjy kibary inje ynzu(lol) "ki gaishe da alhj" mummy tace "nagode sosai alhj lawal zeji nima agaishe mun da umman mustapha" ya amsa da "toh" sannan yayi hanging. Nan mummy ta share hawayenta ta koma daki, alhj lawal ya sakar dawata dariyan mugunta yadda ya saba sannan yace "hajiya hafsa knan! Tun ba ayi nisa ba karfin ki ya kare hahahah Allah sarki"*** heedayah tace mummy ina kkaje? Mummy tace "babu alhj lawal na kira da ya taimaka mana..." daddy yafara jijiqa mata kai kamar yadda ya saba mummy tace "...habibi ni bansan me kake nufi ba kuma, alhj lawal dinne bakason mu nemi taimako gunsa?" Daddy ya gyada kai mummy ta cigaba "to gun wa kakeson munemi taimakon? kana gani de ni banda kowa shikadai ne hope namu, ai shi yanada kirki bakaman wancan la'ancaccen dan uwan naka yake ba"**** can dare alhj lawal yayi calling back mummy yake gaya mata ai ba yadda ya iya cuz is already too late, daddy ya riga ya ma alhj ismail signing papers din ko kotu sukaje bara'a sauraresu ba, mummy tamasa godia sannan ta katse wayar jikinta duk ya gama mutuwa ji take kamar tasa hannu a ka tayi ihu amman ta miqa wa Allah al'amarin dan for sure tasan yanada reason din musu hakan. PA'n daddy takira tace masa da ya nemo almajirai suje su wanke mata gdan da abbanta ya bata dake danjuma goje gobe ya amsa da "toh".
Abubuwa sunyi wa mummy yawa kwata kwata tafita daga kamanninta, heedayah kuwa tadena concentrating a makaranta kullum hankalinta nakan daddy'nta da daddy'n don moha ahaka aka sa date da zasu fara exams na third term in one week time, hakan kuwa yayi daidai da time da su mummy suka fara packing dake alhj lawal yakuma tura alhj ismail daya tuna ma mummy suyi subar gdan cuz wanda zasu dauki gda sun riga sun bada kudi. Yau ya kasance wednesday, bayan heedayah ta dawo frm sch suna zaune a dakin mummy suna packing kayakinsu, mummy tayi jugum heedayah ta taba ta "mummy kibar damuwa kinji? Ba muna addu'a ba? Allah ze amsa mana addu'an mu yarama mana abinda daddy'n don moha ya mana ai" mummy ta kirkiro murmushin dole tace "in shaa Allah my little princess kin gaji war haka ko? Bari nida nanny mu gama packing sauran kayan jeki huta kiyi karatu kinji? Kinga kuna exams nd promtional exams ne you have to read" heedayah taqi tace da ita za'a gama haka mummy ta barta se bayan maghrib suka dan huta sannan suka cigaba, sun sha rabin aikin kak gaskia cuz a yanxu hka sauran musu dakin heedayah, dakin daddy da parlour ne sun riga sun gama da kitchen, stores, dakin nanny, guestroom, dinning space.
As usual yau da safe nanny ta shirya heedayah sch. Around 10:15AM bayan mummy tafita aiki wasu armed robbers(manyan barayi) suka paso gdansu heedayah suka ma me gadi dukan tsiya harda buga masa gindin bindiga a ka, nanny tana kitchen tana dan chopping albasa itama aka nausheta a ciki take ta fadi a gun, dakin daddy suka soma shiga suka samesa zaune yana kallon news basu taba sa ba illa drawers da wardrobe da suka shiga budewa suna ciro kudade, can dayan ya lalimo drawern key din motocin gdan, sukayi searching so hard amman sun kasa gano ina mumy ke aje gwala gwalanta dake bata ajewa a gda can banki take kaiwa inda Allah yasota knan, bayan haka suka babballo plasma TV's dake gdan kap da sauran abubuwan showglass sannan suka fice, daya daga cikinsu yaja sumemmiyar jikin me gadi cikin dakinsa. sun kai kusan su shida suka dibi motoci guda shida cike da kayakin da suka sato, kwata kwata mota daya suka rage wa mummy dan iskanci wata baqar honda accord V8 suka fice daga gdan suka bar gate fangalan a bude. Daddy tun yana hawaye jikinsa na rawa yabar motsi shima

HEEDAYAH!

24
written by miemie

Bayan like 30mins da tafiyan barayin, nanny tadan lumshe ido da taimakon table dake tsakiyan kitchen din ta riqe ta miqe da hannunta riqe da cikinta tana ma kitchen din wani erin kallo nan ta tuna meya faru sunan alhj kawai takira da karfi ta ruga a guje dakin daddy tagansa bayya motsi salati ta hauyi jiki na qyarma ta kira mummy a waya tana kuka "mummy ki zo gda, kizo gda, gda ba lafya barayi sun shigo sun mana fashi, alhj baya motsi" ta fashe da kuka... Mummy tace "what!?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kasa daukanta kafafunta sukayi ta sulale qasa salati kawai take ta nanatawa har na tsawon mituna uku sannan da kyar ta tashy tabar office dinta a guje key kawai ta dauka ta fice, Allah ne kawai ya kawota gda lafya dan wata erin wawiyar driving da takeyi a bude wangalau tasamu gate na gdanta daidai bakin kofar parlour tayi packing ta fito ko rufe kofar batayi ba hasali ma a kunne ta barta ta shigo ciki da saurin gaske abinda tafara cin karo dashy shine ba TV'nta, tana kai ido kan showglass taga du an kwashe abinda ke ciki hannu kawai tasa kan bakinta ta karasa dakin daddy tasamu nanny a gefe ta rike ciki tana kuka, daddy kuwa na kan wheelchair nasa a sume wayarta ta gwada lalima taji ba alamarta nan ta tuna tabar wayar a office ta kira sunan nanny, nanny tadago jajayen idanunta "mummy har kin iso ki kira likita...wayyo cikina" mummy tace bani wayarki ta karisa ta amsa Allah yaso ma ta haddace numban family dr din, nan da nan ta kirasa ya iso ya duba daddy da nanny yabasu immediate care ba abinda mummy ke shararawa se kuka, shide dr yamata jaje yakuma bata hkr sannan ya fice. Haka har lokacin daukan heedayah yayi mummy bata sani ba se kuka take shararawa can bayan 30mins da tashinsu heedayah ta tuna gashy barata iya fitaba dan haka ta kira driver da wayan nanny kan yaje ya dauko heedayah frm sch batare da ta gaya masa dalili ba, driver kuwa a hanyan dauko heedayah wasu barayi suka tsare sa ni miemie nace wannan barayi sunyi kalan wanda suka kai fashy gdan alhj s.u daxu, suka ma mal idi tsinannen duka sannan suka kwace motarsa suka kara mai, da kyar mal idi yasamu ya lalimo wayarsa upon all dukan da suka masa ahaka yayi karfin hali yakira numban mummy har yagama ringing bata daga ba yakuma mata wata missed call din sannan ya kirata da numban nanny nanne ta daga, ahankali yake maganar "haj..i..ya yan ta'ada kije ki dauko heedayah" mummy tace "whaat!???" Kana ina? Da kyar ya iya cemata "hotoro" tace "toh keep calm, ga ni nan zuwa" nanny tana tambayar ta meke faruwa amman bata ko amsa taba tafita a gigice se hotoro can ta hango mal idi a kasa ta karasa yasamu ya tashy da kyar mummy take tambyarshi ze iya kaiwa har a dauko heedayah? Ya amsa da "eh" amman de da anga condition nasa an san bare iya ba dan jikinsa duk yoyon jini yakeyi sbd gardaman da yyi wa barayin suka shasa sosai, reverse kawai mummy tayi sukayi asibiti akayi emergency dashy tace wa dr din zataje dauko 'yarta a makaranta ta fice, heedayah har tagaji da jiran mummy tafara kuka, tana cikin raira kukanta a hankali mummy tace "am so sorry my little princess yi hakuri am late kinji?" Ta dagota ta riko mata jakarta suka kama tafiya, maimakon su wuce gda se heedayah taga mummy nabin wata hanyar daban dan haka ta tambayeta "mummy ina zamuje?" Mummy tace "asibiti heedayah, barayi sun tsare idi a hanya sun masa duka sun kwace motarki" heedayah tazaro dara daran idanunta tace "mummy! Prado dina?" Mummy tace "eh heedayah, ke akan ki tambayi jikin idi ma motarkice ta dame ki?" Heedayah ta maraice sannan tace "toh ya jikin mal idi?" Mummy tace "bari mu karisa asibitin muji" nan da nan suka isa aka tabbatar mata da cewa mal idi beji internal injuries ba kawai external ne nd anyi treating nasu, nanne mummy ta sauke a jiyar zuciya tabiya kudin treatment nasa da kudin magani sannan suka dawo gda, tun isarsu bakin gate heedayah da mal idi suka sake baki mal idi yace "hajiya meke faruwa?? Gate a bude kuma ba motoci a gdan" mummy bata ce masa komi ba dan haka yaja bakinsa yayi tsit, heedayah kuwa har yoyon miyau bakinta yafara ahaka mummy ta nemi gu tayi parking suka fiffito, mummy tashige ciki dan takaici heedayah kuwa da mal idi se kallon gdan kowan nensu keyi ko zasu ga motocin amman ina! Heedayah ta nemi gu ta zauna can inda ake parking motoci shikuma mal idi ya shiga ciki, hawaye a hankali heedayah ke zubarwa kaman daga sama taga hannu daga dakin me gadi wata ihu ta sakar duk su mummy suka fito suna tambayarta mene? Dakin me gadi kawai take nuna musu da 'yatsarta mal idi ya karasa yaga mal musa me gadi kansa du yana zuban jini salati ya sakar, su mummy sukayi kansa da heedayah mummy na salati mal idi nayi**** Alhj lawal da alhj ismail suna zaune a gdan shi alhj ismail se dariyan mugunta sukeyi ana cikin haka wayar alhj lawal tayi qara ya duba..
HEEDAYAH!

25
written by miemie

Sannan ya daga "hello?" Meshi yace "oga sir! Gashy nan mun gama komi motocin suna inda kace muyi parking nasu, anyi kamar yadda kace honda accord V8 kawai muga ragar musu" alhj lawal yace "aikin ku yayi kyau bari ynxunnan zakaji alert" meshi ya amsa da "toh oga sir godiya muke" yayi hanging. Yace ga alhj ismail "the did is done! Komi is in place ynxu acikin motoci guda shidan nan zamu siyar da duka amman zan baka guda daya" alhj ismail yace "kaifa? Baka so ne? Baraka dau dayan ba kaima" alhj lawal yace nafison ka ne dan uwa na, zan baka TOYOTA PRADO (masu karatu ko zaku iya tuna toyota prado'n da alhj lawal ke son bama alhj ismail itace motar heedayah?) Alhj ismail yace "toh nagode dan uwa", kallonsa kawai alhj lawal keyi yana murmushi yafara maganan zuciya "Allah sarki dan uwa na, motan nan ba abinda zata kara maka illa tsana dan na tabbata duk sanda hjy hafsa da 'yarta heedayah suka ganka da motan, se sunji kamar su kasheka"****
Dr yace "toh alhamdulillah nasamu nayi stopping bleeding din nd Allah yaso ba internal bleeding ga magungunan nan se yana sha in shaa Allah shknan, Allah sawaqa" mummy tace "toh dr mungode" ta dawo da kallonta kan mal musa tace "Allah sawwaka sannu" yace "ameen" da kyar. Sannan suka fice masa daga daki sukayi site nasu ita da heedayah. Ciwon cikin nannay yadanyi sauki kadan so takoma kitchen tana girki a yayinda mummy ke zaune a parlour tayi tagumi da hawaye nabin kan kumatunta heedayah na share mata, shigowar matar alhj lawal sukajiyo atake suka jiyo tace "hjy hafsa! Dan Allah kar ki gayamun dagaske ne, barayi sun shigo sun muku aika aika?" Daga idanta da tayi taga ba TV' a parlourn taga kuma an tattara kayaki cikin kwalaye dayawa kamar ana packing nanfa ta sake kidimewa. Ta kira sunan mummy, mummy ta amsa, tace "wai hjy hafsa meke faruwa? Yana ganki haka?" Mummy tace "barayi ne suka shigo mana da safen nan suka tattara motocin gdannan kap daya suka rage sannan suka sassace duk wani abu me kyau da kkasani agidannan, bayan nan suka ma musa da idi duka" "innalilliahi wa inna ilaihi raji'un" abinda umman mustapha keta fadi knan "shine kuma kke zaune a nan baraki kira police suzo ba?" mummy tayi dariyan takaici sannan tace "suzo suyi me? Zasu iya maido min da motoci nane? Ba abibda zasu iya illa investigation na qarya" umman mustpha ta matuqan tausayawa mumy sosai ta taso tayi hugging nata tana bata hkr ta kuma ce mata ta kwantar da hankalinta zatayi wa mijinta mgn in shaa Allah zai taimaketa, mummy tace ba seta fda ba masa bama tabary kawai umman mustapha tayi insisting sannan ta tambayi mummy "wannan kayaki kuma danaga anata shiryasu cikin kwalaye fa? Lafya?" Mummy tace "packing mukeyi..." kafin ta karasa umman mustapha ta katse ta "Pa...meh? Packing kuje ina? Mesa zaku tashy?" Mummy bataso gaya mata gaskiyar zancen ba tace mata kawai zata canza gda ne tunda barayi sun gano nan din, ba yadda umman mustapha batayi da mummy data hakura su cigaba da zaman su ba amma taqi seda azahar sannan tama mummy sallama ta fice. Isarta gda ta zarce dakin mijinta alhj lawal ta irga masa komi takuma buqacesa daya taimaka wa mummy, alhj lawal kamar dagaske yace wa umman mustapha karta damu he'll try his possible best harda wai dagani wannan barayi turosu akayi, ki gaya ma kawar taki karta damu za'a kai kara police station ayi invedtigation sosai har se an gano waye master mind dake behind all these mess, umma tamasa godiya sosai nan da nan ta kira mummy ta irga mata yadda sukayi da me gidan ta, mummy tadanji sanyi a ranta sannan ta mata godiya ta ajiye wayar ta cigaba da packing kayakinta dake heedayah na karatu, nanny kuwa cikinta na ciwo. Kiran maman don moha umma tayi ta labarta mata abinda ya faru itama ta tausaya wa mummy matuqa atake ta shirya tazo tamata jaje itama ta roki mummy da tayi hkr ta cigaba da zama kar ta tashy amman mummy taki nd itama bata gaya mata mesa zata bar gdan ba dan tasan muddin tagaya mata auren maman don moha da alhj ismail ze iya samun matasala dan cewa zatayi barata zauna da maci amana kamarsa ba wanda ita mummy barata so hakan ya faru ba, ahaka maman don moha ta taya mummy sukata packing kayakin se bayan la'asar ta koma gda taje tasamu mijinta ta gaya masa meke faruwa be wani nuna mata damuwarsa ba kawai de yace mata "Allah kiyaye aukuwan na gaba" itade mama batasan mesa alhj ismail ke behaving haka ba sekace alhj s.u ba amininsa bane (batasan duk ba a hankalinsa yakeyin abinda yakeyi ba, asiri alhj lawal ya masa)
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).