HEEDAYAH!
91
written by miemie
Mummy tafara da cewa "heedayah what has gotten into you kka dau wuka kina kokarin kashe kanki?" Heedayah bata ce mata komi ba hawaye kawai take ta zubarwa endlessly, haka mummy tata suratan ta amman inaa heedayah is not at all willing to answer her dan haka kawai ta bata waje, yini ranan heedayah tayi tana kuka taki ma kowa mgn a gdan illa aesha, wayarta ta bukata aesha ta miqa mata number'n rayyan tasoma dilaing.***
Rayyan darling ma duk story din same ne, tun isarsu dasu mummy gda yake kuka kamar dan yaro, zuciyarsa radadi take masa sosai, amman shi abinda yasa a ransa shine wannan abu dayayi kamar jihad ne ko agurin Allah za'a masa sakayya dan inhar don moha yacigaba da abinda yakeyi eventually mutuwa zeyi, this is like saying nayi saving life na don moha... yana cikin wannan mgn wayarsa ta soma ringing yana dubawa yaga my princess wani sabon kukan ne yaso kubuce masa haka yana gani har call din ta tsinke, sake bugowa ta kuma yi, tayi kusan 6 missed calls duk ba wanda rayyan ya daga aganinsa bekamata ba tana matar wane yayi making call da ita nd yasan for sure she loves him zata gaya masa daga karshe kashe wayar ma kawai yayi heedayah se kuka aesha tasata a jiki tana bta hakr, "aesha he's not picking my calls kashe wayar ma yayi gabadai, he dont wanna talk to me, dama rayyan baya so na nasani ni nake sonsa" "shhh" aesha tace mata "dont talk like that ai abinda rayyan ya miki me sonki sosai ne kawai ze iya miki, kiyi hkr, fuskarki zata kumbura fa kuma kinsan akoi dinner yau" abincin da aka kawo mata ma sam taki ci.
A side na don moha shima yana kwance a dakinsa takaicin duniya sun masa yawa fatan Allah ya dauki ransa kawai yake duda yasan yin hakan haramun ne amman ya ya iya? Yana cikin mgn wayarsa ta soma ringing wani frnd nasa ke kira har ta tsinke yaki dagawa, se a karo na biyu ya daga yasa a handsfree "ango ango" abinda frnd nasan yace masa knan dan takaici don moha bema amsa saba yayi hanging call sannan yace "nowadays mutane basuda matsala kawai su kira mutum suna cemasa ango mstww" wani call din ne yasake shigowa frm a diff number yana dagawa wani frnd nasa daban dana daxu yace "ango ango congratulations" nan ma don moha bece komi ba yayi hanging call din, "kode daddy ya daura min aure da wancan aneesan san ne? To wlh ni ban dauru ba dan baran taba auren any oda woman apart frm heedayah ba tunda anriga an daura mata aure ni mutuwa zanyi a gauro"... Daddy ne yayi knocking a kofar dakinsan da kamar bare bude ba jin daddy ne yasa ya bude, bece masa ko uffan ba da tafiyar daya komayi kamar wanda koi ya fashe ma aciki ya hauro kan gadon, daddy de kallonsa kawai yake daga bisani yace "oya seka dhirya kayakin ka zaman ka a gdan nan ya kare zaka tare zuwa gdanka kaima." Cikin rashin fahimta don moha yace "gda na kuma? Aww ynxu kaima korana zakayi?" Daddy yace "muhammad knan ko bakasan a ynxu haka kai ango bane?" Don moha da be dau mgnan serious ba yace daddy dan Allah excuse me banida time na jokes haka abubuwan da suke damu na kadai sun isheni, ynxu su abdul suke min wannan talk din in har aure ka daura min da aneesa to fa father u shud know ni ban dauru ba dan baran xauna da ita ba" Daddy ya dafa shoulder insa "son knan kataba jin inda ake wasa ko karya da zancen aure? Angon heedayah ne kai a ynxu haka dan kuwa dakai aka daura auren daxu bada rayyan ba akan sadaki N200k." Don moha ya xabura "are u serious father?" Daddy yace "am damn serious son," hamdala don moha yayi tare dayin sujjada "daddy kace an daura min aure da heedayah?" Se washe hakwara yake he can't keep calm heedayah is his wife (ko 'yan team Don Moha?) Daddy yace "sosai ma son" yana masa murna shima, alokaci daya kuma se murnan fuskarsa ta gushe daddy yace "ya haka kuma?" Don moha yace "rayyan fa daddy? Ina yake ynxu? how is he? Am sure duk inda yake he's not alright, people da mind erin na rayyan are hard to find ynxu daddy, rayyan yayi proving kansa as a brave guy ba kowa bane ze iya yin abinda rayyan yayi, ni ba abinda zance sede in masa godiya da fatan alheri, Allah saka masa da alheri sosai sosai," daddy ya amsa da "ameen." Don moha yace "father kanada number'nsa to in kirasa in masa godiya in person?" Daddy yace "sure na amsa gun alhj s.u daxu nima dan masa godia" nan daddy ya basa ya dura digits din a wayarsa ya gwada dialing saidai ynxu switched of dan haka yamasa message kamar haka;
"Assalamau alaikum brother rayyan indeed you are a brother sent to me from heaven, abinda kamin nasan ko blood brother na bare iya min ba I owe you my life nagode sosai Allah saka maka da alheri yasa wannan decisioin dakayi making na bar min heedayah ya kasance best decision that you will ever make in your entire life, am so grateful brother. From ur brother muhammad." Yayi sendning...
Around 8:00PM makeup artist na heedayah ta iso kasancewar 9:00PM za a fara dinner'n. Heedayah tace da ita ina zuwa tafice zuwa dakinta thank god ba kowa a dakin, key tasa tahau kan gado ta kwanta, minti 10-15 heedayah shiru dan haka makeup artist ta tambayi mummy ko lfy, mummy tace "ina zuwa baranyi fetching nata," dakin heedah direct ta wuce ta gwada budewa taga arufe knocking tayi heedayah na jinta amman sam taki budewa, mummy tace "heedayah wai meke damunki ne? Kinsan fa lokaci tafiya yake, kifito kinji?" Shiru heedayah ta mata dan haka mummy ta kira daddy a waya ta irga masa halin da ake ciki daddy yace "a mika ma heedayah wayan," tanaji mummy na fadin "ga daddy wai zemiki mgn ki bude kofar," pillow ma ta dauka ta kare kunnenta gabadai yadda mgnan mummy bare na damunta ba, tace "yau sede kuyi sabuwar amarya danni baranje dinner dinnan ba dukda rayyan yace inje amman baranje ba am sorry" wani haushi mummy da daddy suke bata right now, taya barasu gaya mata wannan muhimmiyar mgn ba suka barta tayi looking like a fool a gaban mutane, for what they did suma se ta musu abin kunya shine na kin zuwa dinner'
HEEDAYAH!
92
written by miemie
"Yanzu heedayah baraki bude kofan nan ba?" Ba suratan duniyan nan da mummy batai ba amman ko a bakin zanin heedayah, daga karshe ma bacci ne me nauyi ya dauketa tashasa sosai. Karfe 9:00PM mutane suka fara hallara hall da za'ayi dinner, kunya ta cika mummy batasan yadda zata fara sanar da mutanen anyi cancelling dinner'n ba har 10:00PM amarya da ango basu zo ba dan tuni nanny ta kira don moha ta fada masa halin da ake ciki dan haka shima be bata lokacinsa yaje ba. Daddy ne yayi making announcement din, wasu mayun kam sanda sukaci abinci sannan sukayi gda. Dama ya kamata tun kafin dinner'n akai amarya gdan dangin miji amman dake dangin rayyan ba a nan kano suke ba saisa aka bar heedayah a gda koda kuwa da aka daura auren da don moha ma fact din still be canza ba. Around 10:40PM daddy ya kira don moha daya zo da kansa ya dau matarsa nd bame escorting nasu.
11:00PM daidai ya masa a gdansu heedayah main parlour yashiga yana zaune a kasa daddy yamasa nasiha sosai sosai me ratsa jiki yakuma ce dashy duk sanda yama heedayah ba daidai ba baretaba yafe masa ba, don moha yadau alkwarin never to hurt heedayah, mummy aka tura taje tafito da heedayah daga dakin taje tagama suratan duniyarta heedayah taki fitowa tun ji datayi gdanta za'a kaita ynxu ta fashe dawata erin matsanancin kuka ita sam barata je ba, spare key'n dakin ta aka nema sama da kasa a gdan babu sanda aka balla gun lock din kofar aka tsinceta kwance a kasa se kuka takeyi daddy ne ya dago ta "haba my princess sekace wani aljani aka daura miki aure dashy? Oya ya isa yi shiru, anytime muhammad yamiki ba daidai ba ki kirani ki gaya mun ni zansan me zanyi dashy kukan ya isa ko?" Da kokuwa aka samu aka sauko da ita kasa ko lura da don moha ma batayi ba se borin ta take tayi, ba yadda mummy batai da ita ta mata mgn ba amman sam taki ita adole tayi zuciya dasu. Ta kama zanin mummy ma taqi duk haushinta takeji rigar aesha takama ita sam barata bar gdan ba da kyar din kyar aka sata cikin mota se kuka takeyi, daddy yace da don moha "kaga de it is not easy for her so kabita a hankali, Allah baku zaman lfya" ya miqa masa key'n gdan don moha ya amsa da "ameen nagode daddy" sannan ya fice.
Yasami heedayah a gabar motan tana kallon window tana kuka qarisawa yayi ya shiga motar yakunna me gadi ya bude masu gate suka fice, sun danyi tafiya sannan ya tsaya ya yahuza suya ya siyo musu kaji, heedayah bata ce masa ko uffan ba haka shima har isarsu gda yayi parking motar sannan yace "heedayah yi hkr kifito" banza dashy tayi tanata kuka abinta har ya shiga ciki ya ajiye kajin kan dining yakuma lekowa heedayah bata fito daga motar ba, baba megadinsu yasa yama heedayah mgn. Wani dattijo ne shima kap yayi suratan duniyarsa amman sam kamar ba da ita ake ba, motar don moha ya shiga shima ya rufo kofar "since ure not coming in lets stay here together," sunyi kusan awa acikin motar ita da kanta zaman ya isheta sannan ta bude motar tafito bayanta don moha yabi straight dakinta ta nufa ta zube kan gado se jan numfashy take dan kukan data tayi. Kajin don moha yasa mata a plate yahado dawata soft drink ya nufa dakintan ya ajiye mata kan bedside drawer, "here eat pls nasan u must be hungry" nan ma bata ce masa komi ba yata suratan sa amman sam taki amsawa dakanshi yagaji yace da ita "goodnight" yakai daidai bakin kofa heedayah tace "ka rabani da rayyan, the one I love are you happy now? Today is suppose to be the most happiest day of my life, don moha kamin ruining day na, all I want you to know is that you are not a husband to me," don moha zeyi mgn tace "shhh come nd take ur gabbage out of my room" tana nuni da plate din. Bece mata komi ba yafice izuwa dakinsa ruwa ya watsa sannan ya kwanta ya zura wa ceiling ido yana tunanin how heedayah zatayi accepting nasa as her husband har bacci yayi awon gaba dashy. Heedayah kuwa da kayan jikinta ta kwanta.
Washegary da asuba ya tashy yayi sallah sannan ya nufa dakin heedayah ya sameta tana bacci kanta ya nufa ya tsaya yana zura mata ido "heedayah why can't u understand that I love you, I can still feel it kema kinaso na is just that ure all confused ynxu but no matter what kisani i'll nva rest untill kinyi acceptn dina as ur husband nd no matter how hard u try to push me away frm u zan nayin iya kokari na to protect you nd be close to u, this is how much I love you." Se ynxu yaga hannunta me bandage ma, hannun ya riqo yayi kissing sannan yayi tapping nata a baya "kitashy kiyi sallah" ko motsawa batai ba sau biyu ya mata hakan sannan ya fice, yana fita ta bude ido ashe ba bacci takeyi ba. Tace "Then u will waste ure entire life waiting for the day zanyi accepting naka as my husband cuz I'll never accept you not ur kind, a da ban tsaneka ba don moha but what you did now only made me hate u the more," nan ta tashy taje takama ruwa tayi alwala da ruwa ya taba yankanta yamata ciwo sosai, tana idar wa takoma bacci around 7:30AM ta tashy tayi wanka ta nufa kitchen ta hada breakfast nata for all this while don moha na bacci ko kararta beji ba, tana gama ci tashirya key'n motarsa dake parlour ta daga ta fice zuwa office. Kowa a office yayi mamakin ganinta amaryan data karbi leave na 2 months meze kawota gun aiki kuma? Kode ba ayi auren bane? *Eh" tace musu "auren was canceled" ayya kowa ke fadi "ya akayi haka?" "Long story" tace dasu, "so ina case da muke kai dinnan, can we proceed?" " Yes" suka ce mata.
Don moha kuwa se 10:45AM ya tashy bayan yayi wanka ya leqa dakin heedayah yaga ba alamanta yaduba ko ina acikin gdan ba sign nata, yana fitowa waje yaga ba motarsa me gadi ya tambaya kan "ina heedayah?" Baba yace "tace min office zata," don moha yace "toh shknan ba damuwa" ya komo ciki ya zauna kan kujera, "taya zata fita office, amarya ta taba zuwa office ne?" Sam yakasa amsa wannan tambayarsan, tea da snack yayi having for breakfast tun 2:00PM yake expecting xuwan heedayah amman shiru bai so kai karan ga gun mummy ko daddy ba dan baya son haddasa trouble.
92 cont....
Nanny yakira ya irga mata halin da ake ciki, nanny da mamaki yacika ta tace "amman heedayah meke damunta da take abu kamar wanda batada hankali kayi hkr ko babana it'll take time b4 tayi learning truth din but kasani heedayah loves you so much tanayin hakanne kawai dan tayi getting on ur nerves," don moha yace "ba komai nanny just karki gaya ma su mummy banason suyi scolding nata," nanny tace "but why don moha? Ai wannan rashin hankali takeyi kuma tasan gaskia sarai da gangan takeyi mesa bara'a fada wa daddy yamata mgn ba?" Don moha yace "noo nanny just let her be nasan wat shes going through is not easy ynxu mu fadawa daddy ya kirata ya mata masifa ba abinda ze haddasa mana se bala'i very soon zata dawo gda just promise me baraki fadawa kowa ba kema na gaya miki ne cuz you've aways been on my side"
Nanny da tausayin don moha yakamata gabadai tace "Allah sarki muhammad in shaa Allahu hakurinka will not go unrewarded, Allah maka albarka," "ameen" yce sannan yyi hnging call din. Heedayah shiru shiru se 6:00PM ta dawo gda don moha na zaune a parlour ta shigo ta wurga masa key' motarsa tare da fadin "man motarka danayi exhausting i'll pay u back 2moro" tana mgn nanne tana karisawa gun fridge taciro ruwa ta zauna akan dinning chair tana sha, don moha yce mata "ni bance ki biya ni man mota ba, motan is all urs but ina kkaji? U made me sick worried about you Tun safe se ynxu kka dawo" Heedayah bata amsa saba sanda ta kwankwade ruwan tas sannan tace " oh sorry mr. Tun ba aje ko inaba kafara zargi na? Well its upto you kaga dama ka dau yawon gantali na tafi be dame niba nd also bakada right da zaka tambayeni ina naje kamar yadda na fada maka jiya to me ure not my husbnd ina kan bakata har ynxu so stop behaving as one, nd for the fact dat u were u worried sick about me, dama nace maka ka jirani ne? Ban fada ba so there is no need for u to say u were worried about me" tana kaiwa nan ta shige dakinta. Shide don moha bece komi ba uzuri ya mata sbd yasan there is every right heedayah tayi acting haka shide addu'arsa Allah gano da ita gaskia. Wayarta data ciro daga cikin jakarta ne taga 10 missed calls from angelic mum wurga wayar tayi akan gado tafada toilet tayi alwala tayi sallah, tana idarwa call din nanny yashigo dagawa tayi bayan gaisuwan da sukayi nanny tace "ai na dau ko wayarki ta shiga wani lungu ne, mummy ta miki missed calls baki dauka ba ko baki gani bane?"
Heedayah tace "eh nagani," nanny tace "so baraki kirata ba?" "Yes" tace "baran kirata ba ina harda ita acikin masu boyemin gaskia." Nanny tace "amman Allah shryeki heedayah ni bama wannan ba u cant forever be mad at ur mum keda kanki zaki sauko ki kirata, batun abinda kkayi yau na kiraki in miki mgn taya zaki fita tun safe har uku baki dawo gda ba kuma ba tare da kin tambayi izinin mijinki ba?" heedayah tace "wait, wait miji? Dama inada miji ne?
HEEDAYAH!
93
written by miemie
Nanny dake salati tace "lalle heedayah ynxu irin tarbiyyan da nida mummy muka baki knan? Tambayana ma kke kinada miji, dakyau wlh tun wuri ki ajiye shashancin nan da kka dau ma kanki kiyi ma mijin ki ladabi da biyayya dan kuwa aljannarki na tafukan kafafunsa," heedayah dake sauraron nanny kamar radio tace "wannan kuma shi ya dama yaga dama ya take dan to me his not my husband," nanny tace "toh wlh heedayah sa'arki daya dan don moha yace kar in sanardasu daddy in bahaka ba da kinshiga taitayinki dan nasan daddy bareji wannan shashancin da kkeyi ya barki ba haka mummy ma." Heedayah tace "nikam nanny inada aikin yi se anjima" nan ta katse wayar.
"Wato don moha tun ba'a je ko inaba yafara kai qara lalle kuwa ze gaji yabari tunda shi ya kwaso ruwan dafa kansa da kansa." Kitchen ta nufa ta aza indomie dan yunwan da takeji tana saukewa don moha na dawowa frm masjid bata ce masa komi ba haka shima daki ya nufa ya rage kayan jikinsa yataho dining table din ya dau saucer yana zuba corn flakes dan yasan ko be bude flasks dinba ba food aciki kallonsa heedayah takeyi har yagama hadawa sannan tace "ace mutum na namiji amman se uban kai kara" murmushi yayi ba tareda yacemata komi ba har ta gama cin abincinta tayi daki.
Tunanin rayyan ta soma bata san sanda tafara kuka ba "ashe dis was what baba aleesha meant time data cemin akan soyayya tsakani na da rayyan rubucacciya ce saidai..." sekuma tayi shiru "ashe saidai wannan don moha zezo ya shiga tsakaninmu," hawayenta tasa hannu ta goge "baba u should have told me da tun lokacin se inyi avoiding rayyan"... Isha prayer nayi ta idar ta kwanta, don moha kuwa yunwa ce tasa sa a gaba sanda ya fita ya sayi abinci yaci sannan ya kwanta. Washegary ta shirya da safe kamar jiya kan zata office saidai bataga key'n motar sanba yau, bata damu ba a fadinta zata tsari koda napep ta je tana zuwa bakin gate taga katon padlock dake mata sallama, baba me gadi takira kan yazo ya bude mata yace "hjy ai bani nasa kwadon ba alhj ne yasa key'n ma na gunsa," heedayah tace "lalle kam" ciki takoma tafara knocking a kofar dakin don moha tana "kafito ka bude min gate din office zan tafi" yana jinta yaki koda motsawa haka tata suratan ta yana jinta wasu talks natan ma dariya suke basa batada choice haka dan dolenta takoma daki ta zauna can zamar ya isheta tadau wayarta tana kallon pictures nata da rayyan dinta. Se kusan to 10 don moha yafito daga daki bayan wankan da yayi be ganta a parlour ba amman yana kyautata zaton tana daki. Kitchen ya shiga yayi frying egg yaci da bread nd tea yana cikin having breakfast nasa heedayah ta leko parlour'n tace dashy "se ynxu kaga daman fitowa? Kasan karyanka kace zakayi imprison dina a gdan nan kuma ni anjima zaka kaini gda in dauko mota ta dan baran iya juran wulakancinka ba," murmushi don moha yakeyi yana kallon news yadda kukasan bada shi take maganar ba. Gabansa tasha "wai me ka maidani ne muhammad? Ina maka mgn kana harkan gabanka," kallonta don moha yasoma yi sekace ze cinyeta ita kanta sanda kallon yabata tsoro tace "nd stop looking at me like that." Yace "naji seki shirya anjima muje" yana kaiwa nan yakai plate din kitchen yaga tun cup dayasha tea dashy jiya da safe ma heedayah bata wanke ba har tafara tara musu kud'a a gda shiko don moha in akoi abinda ya tsana itace kazanta dakinta ya nufa yaganta da mac book nata kome takeyi aciki oho yace "baby bakiga dishes dinnan har kud'a sun soma bin kai ba, tunda ba shara zakiyi ba u shud atleast wash the dishes" banza tayi dashy nakusan 2mins sannan tace "kaima ai naga kana da hannu if u can't bear seeing houseflies a gdanka u have to options ko ka sallameni ka kawo wacce zata na maka wanke wa ke kokuma ka wanke da kanka, had it been rayyan ne kai da ko baka tambayeni ba zan wanke dishes din da kaina, so excuse me pls." Bayan kallonta da ya qare yafice zuwa kitchen din shi yayi wanke wanken da kansa, karar kwanuka heedayah tajiyo a kitchen sidak sidak ta leqa tagansa yana wanke wanken a zuci tace "daidanka knan." Karar doorbell tajiyo da sauri taje ta bude wata kyakkyawar mata ce wanda zasuyi shekaru kusan daya da mummy da wata basket a hannunta, sannu da zuwa heedayah ta mata "bismillah ki shigo anty" bayan ta zauna heedayah ta gaisheta "ina kwana anty?" Matar ta amsa da fara'arta "sannu amarya, se gaku a unguwarmu, gda na shine nxt to naku ta dama tafiya nayi nima se jiya da dare na dawo me aiki na take gaya mun munyi baki a unguwar, sesa kika jini shiru," heedayah datake wasa da zoben hannunta tace "ayya ba komai anty." Matar tace "sunana ummu jalilah, amaryar tamu fa?" Heedayah dake murmushi kamar 'yarziki tace "heedayah suna na"...ummu jalila tace "masha Allah ga breakfast ne dama na kawo muku zan wuce office kar nayi latti" tana miqa ma heedayah basket din. Amsa heedayah tayi tana godiya "ayya mungode toh, zan gayawa ango yana bacci ne yanzu." Ummu jalilah tace "bakomi" nan ta tashy har heedayah ta bud'e mata kofa sega don moha yafito daga kitchen da kitchen towel a hannunsa yana goge ruwan hannunsa, kan ummu jalilah ya daure ba ynxu heedayah tace mata ango na bacci ba. Gaisheta don moha yayi ta amsa da fara'arta "ai har zan tafi dan amarya tacemun kana bacci" tana mgnan tana kallon heedayah dake sosa keya tana raba ido. Don moha yayi murmushi yace "eh bata san na tashy bane," ummu jalilah tace "ayyah to sannunku dazuwa."
Heedayah tace "baby gashy fa ummu jalila ta kawo mana breakfast," don moha yace "ayyah mungode anty." Ummu jalilah tace "ba komai barin wuce" suka mata Allah kare sede har ynxu kanta a daure there must be somethng going on btw amarya da angon nan.
HEEDAYAH!
94
written by miemie
Kallo ta watsa masa sannan tace "sannu da aiki u must be hungry ga abinci nan sekaci" ta ajiye kan centre table dake parlourn ta nufa dakinta. Daidai 4:15PM heedayah tagama shiri tafito parlour bata ga don moha ba dan haka tayi dakinsa ta samesa yna kwance akan gado "ya haka? Ba zaka kaini gda ba? Ko ka manta ne?" Don moha yace "kin shirya ne?" Ba tare da ya kalleta ba, "lalle ma wlh kai babban dan rainin wayo ne in baraka kaini ba bani key'n motar is not as if I need ur company daman." "Kijirani barin shirya" ya cemata, sanda taja tsuka sannan ta fice nan da nan yasa wata sky blue jampa wanda ya mugun masa kyau ya cokala hulan nan kamar a cinye shi dan kyau heedayah dake zaune a parlour turaren don moha ne ya buga mata hanci bata san sanda ta juya ba kallo tamasa head to toe sannan ta fice yana biye da ita ya rufo kofar gdan, ya bude motar tashiga ta zauna suka fice. Bawanda yace ma dan uwansa ko uffan acikin motar ahaka har suka isa gda. Doorbell don moha ya danna nanny ta bude tare da musu sannu da zuwa tana hararan heedayah, zama yayi bisa sofa heedayah kuwa ta haura sama zuwa dakinta ta dauko makullin motarta tana saukowa takai bakin kofa, don moha yace "ina kuma zuwa?" Da kamar barata amsa saba sekuma tace "gda," don moha yace "baby bara ki jira mu gaisa dasu mummy ba seki tafi?" Heedayah tace "wai sau nawa nace maka stop calling me ur baby, inba kaddara bama..." tana cikin masifa mummy da nanny suka sa kai a parlourn dan haka tayi shiru, mummy tace "heedayah lafya? Ma muhammad kke ma masifa ko me nake gani?" Nan tasamu waje ta zauna, don moha ya sauka har kasa ya gaishe da mummy, ko amsawar kirki batai ba tace "muhammad meke faruwa haka?" Yana murmushi yace "ba komai mummy heedayah ce ta damu seta zo ganinki shine na kawota."
Nanny tace "wallahi hjy karkiji muhammad kwata kwata bayason a ga laifin heedayah ko jiya ban gaya miki bane kawai," mummy tace "gaya min bema?" Nanny na kallon heedayah tace "office tafita tun safe se uku ta dawo gda ba tare da ta tambayi izinin muhammad ba haka ta tayar masa da hankali." "Whaat!?" Mummy tayi exclaiming "heedayah baki da hankali ne? Kuma ana miki mgn kina tsaye?" nan ta nemi waje ta zauna kusa da don moha mummy tafara balbale ta "irin taribiyyan dana baki knan? Dan kin samu muhammad me hkr sesa kke raina masa hnkali ko? Toh dama daxu mukayi mgn da nanny kan za'a samo miki me aiki amman tunda haka abin naki yake nafasa u'll b d one to tidy up nd take care of ur house urself. Haba mana duk erin soyayyar dana nuna miki da abinda zaki saqa min knan princess?" Don moha ne keta bada hkr itakam bata ce komi ba haka har daddy yazo ya samesu ana kan mgn daya tun daxu shima yayi fada sosai. Suka kuma bama mubammad hkr sannan suka rakosu waje, Heedayah tayi gun motarta mummy tace "ina kuma zakije da motar?" Heedayah tace "gda mana"...mummy tace "dan kisamu kina yawon banza ba, ba inda zakije da motar bani key din." Heedayah ta shakwabe fuska "dan Allah mana mummy" tana kallon daddy ko ze dan sa baki, daddy yace "my dear tayi gaskia nasani sarai aka baki motar nan yawo zakina zuwa da ita, ba inda zakije da motar kawo key din duk sanda kkayi hankali niko na miki alkawari koda motoci uku kkeso zan baki," badan tana so ba ta basu key din tashiga motar se basarwa take.
Se kuka heedayah take ma don moha acikin mota tana ja masa Allah ya isa, don moha yace "haba baby kukan ya isa mana, face naki zeyi swelling fa?" Harara ta watsa masa "wlh ka kuma cemin baby ban yafe ba wayoo rayyan dina" haka har suka isa gda bata bar kukan shashancin ba. Tunda incident din yafaru ko mgn tadena ma don moha, shiko baya son forcing nata yin abinda battaso abinda yake hadasu da heedayah kawai tada ita sallan asuba.
Yau kimanin sati 1 da bikinsu heedayah da don moha knan tunda tazo gdan bata taba daukan tsintsiya da sunan shara ba to talk more of mopping da dusting dakinta kawai take tsaftacewa, ita kanta bata ma san dakuna nawa bane a gdan dan ko damuwa ta zagaya gdan ma bata taba yi ba. Abinci kuwa koda ta dafa daidai bakinta ne nd ba wankewanke don moha ne ke mata wanke wanke. Yau da yamma don moha na kitchen yana washing dishes heedayah ta shigo daukan cup ashe dan ruwan omo ya diga a kasan tana takawa se tsantsi ya kwashe ta, ta fadi a kasa wata ihu ta tsala don moha besan sanda ya jefar da glass plate dake hannunsa ya fashe ba ya taho kanta da sauri "baby zaki iya tashy? Sorry bansan ruwan ya zube acan ba," masifa ta fara masa "dama taya zakasani bayan ba tsakani da Allah kake wanke wanken ba just admit it kanaso ka kasheni ni ne, wlh don moha Allah ya isa daba dan kai ba da warhaka muna enjoying honeymoon namu da rayyan ka kama kayi meddling into our lives"...duk wannan mgn datakeyi acikin kunnen ummu jalilah data shigo musu gaisuwa yau batare da sun sani ba, baki wangalau ta sake "wannan wace erin amarya ce wato wankewanke take sa angontan? Gaskia yakamta amata gyara ai wannan bayi bane.' Door bell ta danna heedayah ta mike da kyar taje ta bude mata "sannu dazuwa ummu jalila" tana kirkiro murmushin dole saidai yau babu fara'ar ranan a fuskar ummu jalila shigowa tayi ta zauna kan kujera, "ina angon yake?" Heedayah ta rasa me zatace kar ta kuma yin karya kamar na ranan. ummu jalila tace "yana kitchen yana miki wanke wanke ko? Haba heedayah da girman ki da hankalinki kke abu kamar 'yar qauye wacce bata waye ba, kira min shi." Heedayah da tuni jikinta yayi sanyi tashiga kitchen din "kazo ummu jalila na kiranka"** kafin su fito ummu jalila taga wani erin kurar da parlourn yayi da alama tunda tazo gdan ma bata taba shara ba tabe baki tayi tace "lalle kam akoi babban gyara anan." Tare suka iso parlourn da heedayah suka zauna kan kujera daya kafin ya gaishe da ummu jalila ta riga sa fadin "wai meke faruwa ne a gdan nan? Tun ranan dana fara zuwa nasan somethng smells fishy in ba wai kunnuwa na sun min karya ba wanke wanke naji heedayah na fadin ka mata, eh ko a'a?" Tuni don moha yace "a'a fa ummu jalila ba haka bane tadanji ciwo ne a hannunta saisa nake tayata wanke wanken," ummu jalila tace "ya sunanka?" "Muhammad" yafadi a takaice.
Tace "qarya kakeyi muhammad, ina inda kkaji ciwo heedayah mugani," nan heedayah ta soma kame kame, "ynxu ke heedayah abinda kkeyi kin kyauta knan? Am very sure iyayenki basu san abinda kkeyi ba, kalli parlourn nan kin taba sharesa tunda kkazo?" Shiru heedayah tayi, "magana nake miki, kin taba sharesa?" Heedayah ta kada kai da alaman a'a ummu jalila tace "subhanallah, heedayah! Kina matsayin amarya amman ace baki taba share gdanki ba? To talk more of mopping. Dan kinsamu miji me hkr ko?"
HEEDAYAH!
95
written by miemie
"Mgn nake miki," heedayah data sa da kanta kasa tace "a'a"... "Toh mesa kke yin abinda ke kanki kinsan ba daidai bane? Kalli gdan nan ko sharesa baki taba yi ba, mijinki kkesa yana miki wanke wanke, kina ganin ahaka ne zaki shiga aljanna?" heedayah da tuni kuka yafi karfinta tace "a'a kiyi hkr xan gyara." Don moha yace "ummu jalila yi hkr ya isa haka kinga kuka takeyi, zata gyara in shaa Allah" Ummu jalila tace "bawani zaki bama hkr ba, kiga yadda mijinki baya son aga laifinki duda shi kansa yasan abubuwan da kkeyi ba daidai bane yet yana defending naki, wa mijinki zaki bama hkr." Heedayah ta dawo da kallonta kan don moha tace "kayi hkr," murmushi ya mata "ba komai baby ni bakimin komi ba," ummu jalila tace "kinga na miji knan ynxu abinda nikeso dake kije ki kare wanke wanken da kanki." Ba musu ba gardama ta mike ta nufa kitchen ta tattara broken plates din don moha ya tashy zebi bayanta ummu jalila ta dakatar dashi "zoka zauna mui wata mgn," haka ya zauna tace "naji heedayah na fadin daban dan kai ba da ynxu haka tana honeymoon da rayyan, what does she mean?" Muhammad yayi shiru dan harga Allah beyi niyan fada ma ummu jalila a thing ba amman haka tata insisting har se sanda yabata lbr mystery'n dake behind life nasa da heedayah. Bayan daya gama bata lbr tace "a gaskia kai ka cancanta ka auri heedayah dan tun tana 'yar qaramar ta kake sonta, pure nd true love kake mata nd tabbas heedayah ma na sonka kaima kawai tana pretendn to love rayyan ne sbd shakuwan da sukayi with time zata learning truth din kaji baba na? Ka cigaba da hkr nikuma na maka alkwarai zansa heedayah a gaba in gyara ta." Godiya don moha ya mata sosai, tace "toh maza kaje daki ka huta" badan yanaso ba ya nufa dakinsa itakuma tasamu heedayah a kitchen suka karisa wanke wanken tare sukayi shara da mopping ko ina a gdan akayi dusting TV dasu showglass, se yau heedayah tasan 4 bedrooms ne a gdanta!
Ko ina se yalki yakeyi suka kuma kunna turaren wuta tuni ko ina a gdan ya mamaye da kamshi. Ummu jalila tace "ynxu nxt abinyi seki aza muku abinci, ki tambayesa favorite dish nasa seki girka masa ni zan tafi gda akoi inda zani." Heedayah tace "toh ngd Allah kare," ummu jalila tace "pls heedayah ki kula da mijinki, muhammad nasonki sosai kiga yadda baya son a ga laifinki, kiga yadda ya dage seya aureki, ki taimaka kiyi loving nasa back kimanta da wani rayyan a rayuwarki, kinada miji kin san ko haramun ne kina yaba mijin wata a gaban mijinki?"... Wa'azi da nasiha sosai umnu jalila ta mata sannan ta fice. Heedayah taji duk jikinta ya mutu ga wani kasalan datakeji ryt now rabuwanta datayi irin wanga aiki barama ta iya tunawa. Kitchen direct ta wuce ta aza spaghetti wanda yasha hadi da kayan marmari sosai ko ina a gdan kamshin girkin yakeyi tana gamawa ta juye a flask ta hada kan dining takai wa baba me gadi abinci for the very first time. Dakin don moha ta nufa ta tsincesa yana bacci karisowa tayi kusa da gadonsa tana kallonsa ta na fadin "why can't I see the good in you? Duk sanda na ganka don moha ji nake i hate you sbd kaine sanadin rabuwa na da rayyan, i've loved rayyan so much in just a blink of an eye ka rabani dashy, do u think it'll be easy for me to accept you as my husband? Noo its not baran iya accepting naka as mijina ba gomma muta zama a hakan kawai sbd har ynxu inason rayyan" har zata tada shi kan yaje yaci abinci sewata zuciyar tace mata ta bary haka ta koma dakinta.
Tana fita don moha ya bude ido, "with time eventually heedayah you will learn to know that I love you nd zakiyi accepting dina as your husband, i'll be waiting for that day"*** Bayan yayi wanka ya fito ya nufa dining yaci abinci, ba abinda yakeyi a zuciyarsa se sama heedayah albaraka dan gaskia she is a wonderful cook. Yana gama ci yanufa dakinta ya sameta zaune kan gado se kuka take zubawa a rikice ya kariso gabanta yana tambayarta ko lfya? "Leave my room" ta fada, "is all bcuz of you don moha ynxu kasa ummu jalila ta dauka am a bad person, parents dina ma duk sun kasa understanding what am going through kai kadai suke tausayawa..." "Its not like that heedayah inda zaki iya yayyafa ma zuciyarki ruwan sanyi kiyi learning truth din da duk haka be faru ba."
"Naji! whatever leave my room a banza yau bayana naciwo sbd kai," "sorry" yace mata "ko kina needing massage" Tace "massage? Ai baran barka ka tabani ba, as how I told u before you are not a husband to me taya zan barka ka tabani? Karka ga dan yau nayi shara nayi girki kadau it'll continue this way nayi ne kawai sbd ummu jalila amman kasani ina kan bakata!" Don moha be kuma ce mata komi ba ya fice cuz anytime heedayah takira sunan rayyan duk seyaji wani eri not that yana kishin rayyan ne but he can't help the feeling. Cikin wata jakarta ta dauko zoben rayyan tana wasa dashy a hannunta hawaye na gangarowa kan chicks nata "why do u hve to leave me my king? Mesa zaka cusani cikin bakin cikin rayuwa? Here I am inada miji amman nakasa basa kaina bcuz all I do is to think of you, duk sanda na gwada faranta ma don moha rai se tunanin ka ya fado min a rai, rayyan I love you duda abinda kamin I still love you" hannu tasa ta goge hawayenta ta dauko wayarta tayi dialing number'n rayyan har ta tsinke ba'a daga ba, haka tata kira daga karshe ma koda ta gwada is switched off. Haka ta wuni ranan tana kuka.
2 weeks later.
Bari mu leqa bangaren RAYYAN muga;
A unguwar maitama hills dake ABUJA cikin wata bungalow na hango rayyan yana kwance a wata daki bisa kan gado kallo daya na masa nasan he's going thru a hard time, sallamar sistern sa aaliya na jiyo, amsawa yayi sannan ta shigo "brother lunch is ready," ko amsata beyi ba sanda ta kuma nanata abinda ta fadi sannan yace "okay ina zuwa." Bayan 5 mins yafito yasamu family'nsa zaune kan dining suna jiran fitowarsa, bayan ya zauna mami tace "haba rayyan sekace mutuwa aka maka? Kalli yadda ka zube kayi baki? Tun zuwan mu abuja ko office baka sake leqawa ba, na gaya maka abinda kayi wa muhammad will not go unrewarded Allah has a better plan for you, kacire son heedayah a zuciyarka kaji son? Ya isa haka pls," ya amsa da "in shaa Allah mami i'll try my best" daddy yace "Allah maka albarka rayyan, am so proud of you, we are all here bcuz of you, ka curo mu daga kauyen da muka saba zama ka kawo mu abuja gashy kasa aaliya a sch, all thanks to alhj S.U. Allah yaci gaba da maka budi yakuma baka mace ta gari wacce zata kula mana da kai," mami da aaliya suka ce "ameen" rayyan yace "ba komai daddy is the least I could do." Befi spoons biyar yayi ba yaji ya koshi.
Washegary! Ya shirya tsaf cikin suit ya ja motarsa ya wuce office duk staffs nasa sunji dadin ganinsa danko sunyi missn nasa babu kmar PA'nsa ma ANEESA SA. Dan since frm the very first time tayi setting eyes nata kan rayyan tayi feeling love at first sight masa simply bcuz of his personality, son rayyan takeyi sosai saidai har yau bata san taya zata sanar dashy ba dan kuwa ko kallonta rayyan bayayi not as if yana mata wulakanci amman ko kadan baya bata time koda dan hira ne suyi kasancewar kullum yana cikin tunani, ko yazo office ba abinda yakeyi signing papers ma da kyar yakeyi. Aneesa ta kasance black beauty, ga hips dinnan masha Allah! Ga iya wanka da turenci kuma, takai mace aduk inda ake neman mace!
HEEDAYAH 91----95
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
Mungode
ReplyDelete