shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 13 July 2016

HEEDAYAH 26----30

HEEDAYAH!

26
written by miemie

2 days later, su mummy sun gama packing kap, an wanke musu sabon gdansu, taje tayi hayan masu mota irin trailers dinnan suka iso, har sun fara sa kaya cikin mota. Heedayah tana sch dake exams sukeyi but ranan friday zasu gama. Bayan manya manyan trailers sun gama kwashe kayakin tas suka fara tafiya, mal idi na cikin mota yana leading nasu to new home. Da mutane kadan mummy tayi sallama bataso shiga gdan alhj ismail ba so kawai tayi wa matarsa waya ta gaya mata, bayan sun gama waya mummy taja daddy cikin mota da taimakon nanny sannan ta rufo gdan ta bama mal musa keys din gdan daya kai wa mal ismail, hakan kuwa akayi, bayan ya kai masa ya dawo su mummy suka fice suma, basu dau lokaci dayawa ba suka iso sabon gdansu dake unguwar danjuma goje. Gdan de ba yabo ba fallasa yana da kyau ba laifi 3 bedroom flat ne da parlour, dinning seda kitchen store. Nan da nan aka shiga sauqe kaya su mummy suna shiryawa a inda ya kamata kafin a dauko heedayah sun kusan shan rabin aikin, lokaci nayi mal idi yaje ya dauko heedayah, tana ganin a canza hanyan gda ta tambayesa dalilin hakan, be boye mata ba yagaya mata shiru ne ya biyo baya haka har suka isa sabon gdan nasu tafito daga mota ta tsaya kallon gdan ba garden inda aka ajiye mata swings da slides nata, ba inda ake aje musu numerous motocinsu ba BQ inda ta dan saba labewa sometimes...mal idi yace "mushiga daga ciki ko heedayah?" Batace komi ba tabi bayansa suka shiga adaidai lokacin mummy ke fitowa daga wata daki tamata oyoyo heedayah ta kariso gun mummy, mummy tace "ya exams?" Heedayah ta amsa da "fine" mummy tace "good Allah bada sa'a, zo muje kiga dakinki ko?" heedayah bata ce komi ba, mummy ta riko fuskarta tace "stop worrying dear everythng is going to be alright in shaa Allah, anjima kadan za'a zo a hada miki swings dinki ko?" Heedayah ta gyada mata kai suka wuce dakinta yadda yake a can babban gdansu haka yake ma a nan ba abunda ya canza, arrangements din komi irin na canne hakan kuwa ba qaramin dadi yayi wa heedayah ba sede dakin can yafi wannan girma ta dago idanunta tace "thank you mummy, ina daddy?" Mummy tace "yana daki, ki canza kaya sekije ki samesa" tabata peck a goshi heedayah ta ce "toh" mummy ta fice heedayah tacire uniform nata tasaka wata yar kantinta sannan ta fito parlour taga dakuna biyu, daya na facing dakinta daya kuma na can ta duba na kusa da dakintan bata ga kowa ba sannan ta wuce dayan tana budewa taga daddy takarasa da gudu tayi hugging nasa se faman murmushi yake mata tace "daddy do you like our new home?" Daddy yamata murmushi sannan ya gayada kai tace "nima inaso amman nafison wancan, wannan gdan bekai wancan girma ba daddy" daddy ya gyada mata kai tacigaba "don't worry xanyi karatu sosai sena zama prosecutor se inyi arresting daddy'n don moha mu karbo gdanmu ko?" Murmushi sosai daddy keyi ya gyada mata kai, yafara kokarin daga hannunsa dan yashafa kanta amman ya kasa tamasa murmushi ta dago hannunsa ta rike tana wasa dashy tana basa labarin abinda ya faru sch.

HEEDAYAH!

27
written by miemie

Alhj ismail kuwa ana kaimasa key'n gdan alhj s.u ya daga kafa ya wuce gdan alhj ismail ya kaimasa, alhj lawal yayi praising nasa sannan yabasa key'n motar heedayah wato prado shiko ya amsa se faman godiya yakeyi can seyayi shiru alhj lawal ya tambayesa "ko lfy?" Yace "dan uwa ynxu in kai motan nan gda kanaganin ba matsala?" Alhj lawal cikin rashin fahimta yace "wace erin matsala kuma?" Alhj ismail yace "iyali na man, in ta ganni da motar ai zata san motar gdan alhj s.u ne dan kowa ya sansu da mota" alhj lawal yayi wata jaririyar dariya sannan yace "ya kake magana haka? Da sukadai ne masu prado a kano gaba dai? In zaka dau motarka katafi toh in bahaka ba zan saida ita" alhj ismail yace "toh shknan" Alhj lawal yace "toh ko kaifa? Kaga ko an tambaya sekace ka siya wa yaranka ne ana kaisu makaranta...(masu karatu ku dubi wani hada gu a wurin alhj lawal wato yana so ne bayan an fara kai yaran alhj ismail wato muhammad da safyan makaranta da motar heedayah, mummy taga motar ta tabbata shi alhj ismail dinne ya turo musu barayi dan dama can a baya alhj lawal ya gayamata kan barayin nan turo su akayi. Anan ke nan se maganan shi alhj lawal din ya tabbata, mummy tasake trusting dinsa nd bara ta taba suspecting nasa ba) Ni zanyi tafiya ma gbe nakeji, zani abuja inje in duba company na alhj s.u dake can, alhj ismail yamasa fatan alheri sannan ya shiga motar da alhj lawal yabasa ya dawo gda yayi parking dinta a inda yake parking motocinsa. Can da yamma matarsa ta dawo frm office taje parking motarta taga sabuwar prado a gda, ta gyara parking na motar ta sannan ta shige ciki ta wuce dakin alhj ismail yamata sannu da zuwa sannan take tambayarsa "sabuwar motar dake wajen fa? Wani ne yakawo ajia?' Ya amsa da "na siyo wasu muhammad ne, ana kaisu makaranta" mama tace "wow yaayi kyau sosai Allah kara budi" alhj ismail yace "ameen".
Washegari! Nanny ta shirya heedayah sch mal idi yyi dropping nata acikin honda V8 kasancewar ita kadai ta rage ynxu se mercedes benz E350 4matic na mummy. Bayan ya sauketa sega motar su don moha wato prado'n heedayah tasha gabansu suka fiffito shida qaninsa, heedayah da mal idi suka tsaya kura wa motar ido heedayah tace "tabbas wannan mota tace" mal idi kuwa na fadin "tabbas wannan motar heedayah ce" ze mata magana knan tafara tafiya a hankali don moha ya karaso yakira sunanta ta amsa abin yabasa mamaki dan rabuwarsa data masa mgn ya jima, sannan yace "how are you?" Ta amsa da "fine" tadanyi shiru sannan tace "nice ride erin nawa wanda barayi suka sace mana ranan" don moha yace "ayya in shaa Allah, Allah zai maido dawani karki damu" heedayah bata kuma cewa komi ba har ya kaita class sannan ya juya can yana tafiya seyana tuna abinda heedayah ta fadi mar, wait firstly, "heedayah has not been talking to me, so mesa tamin mgn yau?" Wata zuciyar tace masa "just cuz tana son kushirya ne" wata zuciyar kuma tace "a'a fa zauna kayi tunani bayan da kuka gaisa metace maka?" Don moha yace "cemin fa tayi nice ride ita ansace mata motarta erin wannan" zuciyar takuma cemasa "toh ai tana nufin wannan dinne kenan nata da aka sace" atake wata zuciyar tace "ko kadan ita de kawai tana fada maka ne kasani ka tausaya mata" haka de yata sake sake a zuciya yakasa figuring out komi. Ahaka har aka tashy, mal idi yazo daukan heedayah bece mata komi game da abinda suka gani ba da safe itama haka suna isa gda ta dau jakarta tayi ciki tafara kwala wa mummy kira, mummy na tare da daddy a dakinsa ta amsa heedayah ta karaso tace "mummy, mummy naga mota na da barayi suka sace a wajen driver nasu don moha an kaisu sch dashy yau" mummy tace "whaat??? Heedayah look at me, are you sure?" Heedayah ta gyada mata kai, mummy tace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un alhj ismail! Abinda zaka saka mana dashy knan? Bayan ka siyar mana da gda still be isheka ba sanda ka turo yan fashy suka mana aika aika? To wlh kasani Allah ya fika, mugu, azzalimi, maci amana kawai" ta fashe da kuka heedayah tace "stop crying mummy ki kai karansa gun police auntin mu tace mana in aka mana sata mukai kara gun police because police is our friend ze dawo mana da abunmu" duk wannan mgn da sukeyi daddy na jinsu zuciyarsa wata irin radadi take masa ba abinda yake yi a zuciyarsa se faman jan Allah ya isa wa alhj lawal da alhj ismail. Mummy tace "let him be, in yanaga yana da wayo ai Allah yafisa mude mu dage da addu'a jeki canxa kaya kici abinci, Allah miki albarka my princess" heedayah tace "ameen" tama mummy peck a kumatu sannan ta je gun daddy taga idanunsa duk sunyi ja sun kada tace "dnt cry daddy ta matso kusa da kunnensa tace masa "ba nace zan zama prosecutor watarana ba? Zan karbo mana gdan mu da motan mu, I promise" shima ta basa peck a kumatu sannan taja trolley jakarta ta fice zuwa dakinta
HEEDAYAH!

28
written by miemie

2 days later, baban alhj s.u wato alhj umar kakan heedayah knan ya kira mummy ta daga ta gaishesa cikin girmamawa kamar yadda ta saba, yake cemata kwana biyu shiru, lafya daiko? Mummy bata boye wa sirkinta komi ba ta bayyana masa everything alhj umar yasha mamakin rashin hankalin da dansa wato alhj s.u daddy'n heedayah yyi na signing wa bare files na companies da properties nasa yaba ma mummy hkr yace itama da nata laifin mesa bata kirasa ta gayamasa halin da ake ciki ba yana raye, ta nuna shi ba kowanta bane knan, Mummy tabasa hkr yatambayi lafiyar heedayah, mummy "tace tana lafya" alhj umar yace to ta kwantar da hankalinta ze turo mata maqudan kudi ta kula da heedayah da kanta, ta kuma gaishe da daddy da jiki, yaso shigo musu amman shima baida lfya sosai haka hjy hadiza ma (maman alhj s.u knan), mummy tamasa godiya sosai sannan ya katse wayar.
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa su mummy acikin small home nasu, kakan heedayah yaturo wa mummy kudade sosai wanda taqi nuna min nima wai dan gulma ta tayi yawa. Dashy ta bude 'yar business nata cikin ikon Allah sana'arta ta sayar dasu provisions, kayan sawa, accesories, bedsheets, kayan kitchen yake ta bunqasa, dubai take zuwa ta siyo su wani sa'in harda heedayah ma take zuwa in suna hutu, daddy kuwa alhmdllh rashin lfyrsa na sauki sosai mummy sun kuma komawa washington DC dr daya taba duba daddy da abaya shi ya kuma dubasa yakuma tabbatar wa mummy cewa ALS disease na daddy ya kusa sauqowa to stage 2 ya rubuta mata sabin magunguna ahaka suka dawo 9ja. Matayen alhj lawal da alhj ismail kuwa basu fasa kaiwa mummy visit ba duda ita bata taba kaimusu ba wani sa'in umman mustapha harda shi mijinta alhj lawal suke zuwa gaishe da mummy yamusu shopping sosai kuwa, alhj ismail kuwa betaba zuwa ba dake alhj lawal ya hanasa. Don moha da heedayah kuwa abun nasu worse yake ta zama dan a sati befi tamasa mgn sau biyu ba, mummy ta nemo wa heedayah malamin islamiya har gda yake zuwa yana karantar da ita nd tana picking sosai. Shekaru da dama sunja, akowace rana kuwa heedayah tashi take da sabor tsanan alhj ismail...

*!9 YEARS LATER!*
Wata kyakkyawar budurwa na hango acikin jifatu store dake jihar KANO. Se diban kaya takeyi kamar hauka takusan cika trolley'n da take ja, tana sanyaye ne dawata jar lace da kwalyarsa green ba qarya tasha dinki me tsada ga kayar daidanta kamar a jikinta aka dinka, riga da skirt ce fitted sosai yafito da dirin wannan budurwa sosai tadau green gyale ta yafa a kai ta nannade sa a wuya da shoe nd bag nata red, se leqe nake inga wace wannan budurwa dan ba qarya tabani class! But nakasa dake ta toshe fuskarta dawata dark sunglasses nide miemie ina biye da ita ina sana'ata ta gulma ahaka tagama diban abinda yamata tajeta gun biya tayi joining layi, bata jima da tsayuwa ba wani hadadden guy ya iso layin shima ya tsaya a bayan mu nide se kallonsa nake nakasa gane ko dan nigeria ne ko erin kyawawa 'yan sudan dinnan masu golden skin ne, layi na xuwa kan wannan budurwa ta miqa kayanta akafara totaling, bayan da aka gama aka gaya mata kudinta N65,760 ta dago side bag nata dake rataye a kafadarta ta ciro bundle din N500 guda ta ajiye a gefe sannan ta ciro ta N100 shima ta ajiye a gefe making N60,000 kenan sauran N5,760 tashiga irga su kamin ta gama wannan guy dake bayan mun ya ajiye wasu kudade masu yawa kamar wanda budurwannan ta ajiye amman sede nasa yadan fi yawa da kadan yace ma wanda ake biya kudin "count this" nan yashiga irgawa, budurwan kuwa ta sake baki wangalan tana kallonsa takasa fadin komi sanda cashier din yagama irgawa yace "sun cika alhj harda chengi ma" ya miqo masa change guy din yace "hold it kasha drinks dashy" cashier se washe baki yake yana masa godiya, nan da nan aka dura kayakin wannan budurwa cikin manya manyan ledoji guy din yakira wasu da su bita su kaimata motarta. Nan ne bakin wannan budurwa ya budu tace excuse me! Tare da ciro dark sunglasses dake fuskarta kyanta yasake bayyana.(ni miemie na bude baki harda digan miyau nike da kyar na rufe nace "wa nake gani kamar 'yar little 8 year old heedayah da na sani shekaru 9 da suka wuce?" Daga sama naji ance min ""ai heedayan ce" na tabe baki nace "gaskia Allah yayi hallita a nan Masha Allah". Heedayah tacigaba da mgna wa guy dinnan...

HEEDAYAH!

29

written by miemie

Cikin siririyar muryarta "is there a problem here?" Guy din ya sakar mata wata shu'umar murmushi sannan yace "lets find somwhere nd talk" heedayah ta dibi kudinta tasa a jaka takama hanyan fita guy din yana biye da ita, wanda suka dibi ledojin ma haka bata tsaya ko inaba se gabar wata mota qirar KIA 2016 ta danna security a jikin makullin motar ta budu sannan ta bude musu booth suka sa mata ta sallamesu da dari biyu suka mata godiya, nanne ta dawo da kallon ta kan wannan guy tace "well?" Yace "I am aasim nd you are?" Da fuskarta a daure tace "heedayah" yace "wow nice name, uhm kar nayi keeping naki waiting is like ure heading to somewhere" yasa hannu cikin aljihu ya ciro card nasa yace "ga card dina maybe u could call me semui proper introduction" da kamar heedayah barata amsa ba sekuma ta amsa bata ce masa komi ba tashiga motarta tafice, se mamaki guy din yake bata taya ze cire N65,760 ya biya wa mutumin da yafara gani yau? Lalle kam ahaka har ta iso gabar wata makekiyar mansion ni miemie nace "lalle rayuwa juyin masa, yaushe su heedayah sukayi wannan gda? Ina gdan gadon mummy?" Honk da tayi ya katse min tunani, mal musa ya bude mata ta karasa gun parking motoci tayi parking motarta.
Wow gaskia gdannan ya hadu sosai za'a iya cewa yafi gdansu na da da kyau sede wancan din yafi wannan sarari, ga motoci har guda 4 a pake da KIA, hyundai 2015, benz S63 dakuma prado shigen irin na little 8 year old heedayah sede wannan ya dan fisa kyau dake new model ne. Tace mal musa dan taimaka min mukai wannan leather bags din ciki ta diba shima ya diba suka shiga ciki suka ajiye, wata kyakkyawar mata na hango zaune akan sofa tana kallo na tabe baki "kaai gaskia wannan tamin kama da mummy'n 8year old heedayah" daga sama akacemun "ai itance" nace "wow haka tayi qiba..." heedayah ta bugeni ta karasa gun mummy'nta ta dale cinya ras! Mummy tace mata "sannu da zuwa" tace "yawwa mummy ai bakisan meya faru ba yau a mall" mummy tace "mefa?" Nan heedayah ta fara labarta mata, ni miemie nace "gaskia ba'a raba mutum da halinsa wato har yau heedayah tana nan da halin bada labari" tana gama bata labari ta curo card din aasim din ta miqa wa mummy, mummy tace "ke kuwa ai dole ya kashe kudi kaman ya kashe banza pilot ne fa!" Heedayah ta miqe tare da fadin "shi ya dama, his won problem" ta nufa gun fridge a dinning area ta dauko drink ta bude takai baki, mummy tace "ke heedayah haka rayuwarki zata kasance miki knan?" Heedayah ta turo baki kan ze taba bango "nikuma menayi ynxu?" Mummy tace "baraki kirasa ba?" Heedayah tace "in kirasa yamin me? Nace bemin ba." Mummy tace "tohhh zancen kenan kullum *ni bemun ba* shin heedayah until wen maza zasu fara miki, kisani dis is a very bad habbit kke tshy dashy ure no more a child ure now 17years old", heedayah tace "ai nasani mummy" mummy tace "den mesa kke shutting maza haka? Baki taba saurara wa na miji bafa, harta cousin naki ammar yaron sister na yace kin masa anman haka kka ki kula sa, uhm uhm fa heedayah kiyi a hankali" Heedayah ta taso frm inda take zaune tazo ta zauna kusa da mummy sannan tce "aure kkeso inyi ne?" Mummy tace "ko kadan nafison kiyi karatu amman kuma dat doesn't mean zakina ma maza abinda kkeyi, ynxu me laifin wannan aasim din kiga almosg 70k ya kashe miki gshy da profession me kyau" heedayah tace ni mummy ba aure da saurayi bane a gaba na, tun ba yau ba ina gaya miki I WANT TO BE A PROSECUTOR. Mummy tace "bakiji mena fada miki ba knan, kiyi overlooking abinda alhj ismaill ya mana, yau shekaru nawa heedayah? Ke baki mantuwa ne? Ai akoi Allah gashy cikin iko da rahamarsa ynxu rayuwar mu taka irin ta da, daddy'nki kawai muke jira yaji sauki, ai akoi Allah kuma Allah ba azzalumin kowa bane, kiyi wa Allah kibar fadin ke prosecutor zaki zama, bama haka ba, kefa mace ce heedayah ba na miji ba ko kin manta ne?, had it been na miji ne ke Allah zan barki ki karanta wannan criminal law kinsan ko shekaru nawa zakiyi kafin ki zama prosecutor din? Dan sekinyi obtaining undegraduate degree na 4years sannan kishiga law sch nakusan 5 yrs, heedayah 9 years wasa ne? kiyi tunani pls ni I cant force u kiyi abinda bakiso abinda kkeso shi zakiyi but u can always count on my blessings. Heedayah tace...

HEEDAYAH!

30
written by miemie

"Thank you mummy but kisani nayi promising daddy, I don't care about ages dinnan koda it'll take me to my last breathe ne zan zama prosecutor inyi revenging wa daddy, kuma zancen in fara kula samari niba aure zanyi ba" mummy tace "heedayah nikuwa in har nina haifeki karki zama prosecutor ki karanta simple course naki ko business admininstration kowani sociology nanda shekara biyu kiyi aure abunki, mutuncin ki knan" heedayah ta zaro daradaran idanunta "haba mummy am way better than that, nd bana so muna arguing akan abu daya kullum ya isa haka pls" mummy tace "toh heedayah in kinga kin karanta wannan criminal law toh a bayan raina dan ba yadda zaayi ace ke kadai Allah yabani sannan ina ganinki kina misleading rayuwarki, u shud either choose ko ki karanta simple course naki kokuma kiyi aure" heedayah cikin tsawa tace "am not doing either of them" ta ruga sama dakinta da gudu tasa lock ta kifu kan gado se sharara kuka take tayi abinta sanda tayi me isarta sannan ta dauko 'yar diary nata tayi rubuntunta ta ajiye ta dauko ipad nata tacigaba da research nata akan criminial law tana cikin yi wayarta tayi qara dubawanda tayi taga admission later inta tsalle ta buga ta sauqo qasa da gudu bataga kowa a parlour ba sede karan nanny da takeji a kitchen, tayi dakin daddy inda ta tarar da mummy na hada masa drugs nasa ta karasa gun daddy da kyar ya daga hannunsa amman ya kasa kaiwa kan heedayah dan haka tadaga tasa yamata murmushi tace "daddy look admission later na yafito" ta nuna masa wayar bayan yagama karantawa yamata murmushi sosai heedayah tace "daddy talk to mummy wai baran karanta criminal law ba sede tamin aure" daddy ya daure fuska mummy ta karaso da drugs na daddy, daddy ya jijiqa mata kai da alamun "a'a" mummy tafara zazzaga bayani still daddy yaqi backing nata shide yace abar heedayah tayi abinda takeso badan mummy naso ba tace "to shknan Allah sa hakan yafi alheri amman du sanda wani abu ya sameki kar keda daddy'nki kuce banyi mgn ba," heedayah ta taso tayi hugging mummy tace "thank you" mummy tace "Allah sanya alheri," nan taba daddy maganinsa heedayah ta kwaso kayakinta data siya daxu takai daki tagama shryasu sannan ta sauqo tasami nanny a kitchen ta gaya mata kan tasamu admission nanny tamata murna sosai, washegary ita da mummy sukajesu BUK suka gama processing komi, wannan knan.

Bari mu leqa family'n alhj ismail da lawal.
Alhj ismail na hango zaune a garden na gdansa shekaru sun qaru kam harda 'yan furfura yana dan karatun newspaper nasa akayi honk a bakin gate, honk akeyi sosai, alhj ismail ya tsaya ganin waye wannan me honk haka megadinsa ya tashy ya bude gate motar don moha yagani qirar audi 2016 sabuwa pil baqa, azuci alhj ismail yace dama nasan ba dan iskan da zeyi wannan danyen aikin inba kai ba. Neman gu yyi sannan yayi parking har ynxu be kashe waqar daya qure acikin motar ba sanda yakusan 3mins sannan ya tattaro wayoyinsa ya kashe waqar yafito sanda nayi tuntube dana gansa. Na sake gurza idanuna dan in tabbata abinda nake gani gaskiya ne, don moha ya girma sosai ya zama saurayi he's now 23 years old kyau kam ba'a cewa komi ga body kamar na justin bieber packs nasa daidai basui yawa ba basui kadan ba, ga muscles nan a hannun nasa gwanin sha'awa yana sanyaye ne cikin jeans da wata shirt me long sleeves amman ya nannade hannun zuwa iya elbow insa wanda hakan yasake fidda body figure nasa, gashin kannan kamar sui mgn dan yadda suke qelli tafiya ya soma yi wane wani boss daddy'nsa alhj ismail se kwala masa kira yakeyi amman ko kadan baiji dake headphone ne a kunnesa ya qure yana jin beats abinsa, me gadi ne karaso ya tabasa nanne ya jiyo, me gadi yace "naga alhj nata kolla maka kira tin daxu" don moha yace "where is he?" Me gadi yadanyi yar murmushi yace "gahi can a garden, niko don moha kadena min turencinnan kasan ba ganewa nake ba" murmuahinsa dayasaba yi yayi masa sannan yace "kaima kayi zuciya ka koya" yana karasawa gun daddy ne yana maganan....ya nemi gu ya zauna alhj ismail yace "kai ynxu muhammad rayuwar daka dauka wa kanka ya maka knan? Sekace ba dan musulmi ba, koda yaushe kana cikin jin kidi toh wlh ka maida hankalinka nan ba london bane kanajina ko?" Don moha kam kidinsa yakeji bema san me daddy'nsa ke fadi ba sanda alhj ismail ya wurga masa newspaper inda ke hannunsa sannan ya dawo hankalinsa yacire headphone din, alhj ismail yace "ka maidani dan iska knan ko? ina maka mgn kana jin waqa ka kiyayeni fa muhammad" don moha yace "ayi hkr" alhj ismail yace "tashy kabany gu," ya miqe ya fara tafiya yana shan corner ya maida headphone nasa, side nasa da kaninsa safyan ya nufa ya samesa zaune a parlour yana game ya xauna a sofa nxt to him yace "kaifa bakada aiki kullum cikin game" safyan yace "toh ya zanyi? ya naga kajuma haka kuma?" Don moha yace "old man ne ya ajiye ni wai yana mun waazi" safyan yace "lol ba dama old man an samu sana'a" suka kwashe da dariya
Share:

0 comments:

Post a comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).