shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday, 28 July 2016

HEEDAYAH 106-----110

HEEDAYAH!

106
written by miemie


Don moha yace "bani key din", tace "baran bayar ba ai na gaya maka yau baraka had'u da karuwar can ba, sede in taceiling zaka fita". Don moha yace "heedayah nace give me the key", bata ko tankasa ba ta tashy ta nufa dakinta tayi locking murmushi sosai yakeyi. Haka har na k'imanin sati suke cikin abu d'aya ranan kam heedayah harda seizing wayan don moha, kishinsa take kamar hauka ita kanta tasan ynxu kam tana son don moha sede tace da kanta bara ta tab'a gaya masa ba sede san ya kasheta!
Yau ta kasance tuesday, heedayah bataje office ba instead se kwalya takeyi tana gamawa tasa wata lace nata riga da skirt electric blue daya bala'in mata kyau bayan ta yafo gyalenta yadda matan aure sukeyi ta d'au side bag nata daidai 9:30AM knan ta nufa d'akin don moha dake zaune kan gadonsa da alama tun daxu ya tashy dan da kaya ma ajikinsa yanata danne danne a laptop, tace "ina car key naka?" ko kallonta beyi ba yace "cikin wardrobe" abin yabata mamaki don moha da kullum cewa yake shi zeyi dropping nata a dsetination nata segashy yau ko kallonta ma beyi ba bale yace ze kaita, abin ba karamin kona mata rai yayi ba. Ta dage tace "asibiti fa zanje"... Nan ma be kalleta ba yace "yayi kyau adawo lfya". Key'n ta dauka har takai bakin kofar d'akinsa tana jiran yace ze kaita amman sam be fada ba. Cewa tayi "yanzu don moha baraka ce zaka kaini ba? Kasan fa am pregnant driving dinma da kyar nake iyayi". Don moha dayasan this was coming yana murmushi yace "okay wait for me" nan yayi shutting system d'in yace "lets go". Tunda suka shiga motar ba wanda yace ma kowa ko uffan haka har suka isa asibitin don moha yayi all processes daya kamata.
Suna zaune a layi suna jiran ganin dr heedayah ta juyataga duk wajen mata masu ciki ne wasu suna ta hira gwanin sha'awa da mazajensu suna dariya, wasu kuma sun kwanta ajikin mazajensu suna bacci gonin sha'awa. Tsuka taja ta dawo da kallonta kan don moha dake ta danne danne a wayarsa dagani chatting yakeyi hannu tasa ta wabce wayan "kai ynxu a asibitin ma seka nuna halinka dubi kaga, see caring husbands kai kazo kanata chatting dawata karuwa". Don moha dake murmushi yace "toh who's fault is it? Do u even allow me to touch you? The answer is no so give me back my phone" heedayah tace "wlh in kaga na baka wayar nan se mun isa gda" ta jingunu a jikin kujerar ta rufe idanta. Murmushi sosai don moha yayi ya tsaya yana kallonta. Haka har turn nasu yayi suka shiga ganin dr inda akayi scanning cikin aka gano d'an d'aya ne kuma baby'n na cikin koshin lfya wataninnsa uku cus! 'Yan magunguna dr'n ya rubuta mata na rage amai da morning fever yakuma buk'aceta da tana kokari tana cin abinci, godia don moha ya masa sannan suka fice. A wata pharmacy suka tsaya sayan magani kasancewar babu a asibitin. Don moha yace "i'll be right back wait for me", heedayah tace "we are going together nasan dawa zaka je ka had'u a can?" Murmushi yayi sannn yace "okay then lets go maman baby",
Ahaka suka isa pharmacy'n wata goodlooking nurse ce agun nan don moha ya mika mata dr's note din nan da nan ta kwaso magunan tayi total don moha ya biya sede se kallon don moha take wanda tuni heedayah ta gano hakan. Ko kallon heedayah batai ba tace "mr handsome, what do they call you?" Don moha yace "muh'd" tace "awwn nice name am..." Heedayah ta kaste ta ke "wace erin nurse ce? Da na shigo nan ban gani a notice board naku kan seducing mijin mutane na cikin service dakuke rendering ba mstw don moha koma mota ka jirani xan amshi change din". Don moha yace "haba maman baby ki d'an rage masifa mana", ya dawo da kallonsa kan nurse din yace "am sorey pls..." hannunsa heedayah ta finciko tayi waje dashy sannan ta dawo ciki "ehem bani change din, mata nowadays bakuda shame wlh" nurse din tace "yi hkr dan Allah wlh bansan mijinki bane", heedayah tace "dama taya xaki sani bayan all u do is to stare at him mstw" ta kwace change din taje tasamu don moha a mota tace "lets go". Bece mata komi ba ya kunna motar suka fara tafiya can yace "haba maman baby banji d'adin abinda kka ma nurse incan ba"... Katse sa tayi "wlh ko ka min shiru ko nayi seizing bakinka just as how nayi seizing wayarka daxu". Don moha yace "seizing bakina? U want to kiss me knan". Heedayah tayi kamar bata jisa ba yace ko? Tace "ai in ta kama zanyi abinda yafi kissing naka ma, ni in gode wa Allah ma aikinka bana zuwa office frequently bane da Allah kad'ai yasan cin amana na da zaka nayi tunda a gaban idona ma bakaji kunyan yi ba". Murmushi sosai don moha keyi kishin heedayah ba karamin taifya masa da imani yake ba!
Ahaka har suka isa gda. Ya ballo mata magunan da ruwa ya bata tasha, yace "toh bani waya nan", tace "baran bayar ba se 2night" tana kaiwa nan ta nufa d'akibta tasa lock tasamu ta kwanta. Se 10:00PM ta kai masa wayarsa nan take wani alhj ya kirasa daga kaduna kan yana son don moha ya xana masa gda but it'll be best in shi don mohan zeje kadunan yaga topography'n land din seya san kalan gdan da ze zana masa. Don moha yace "no problem banida schedules gbe zan shigo in shaa Allah", ahaka sukayi sallama.
Heedayah tace "gbe zaka shiga ina?" Don moha yace "kd aiki ne ya taso are u coming 2 days kawai zanyi in dawo, lets go together ko maman baby?" Heedayah tace "akan me zan bika? cemaka akayi banida abinyi? Kaje kai kad'anka kadawo Allah kiyaye hanya". Tana kaiwa nan ta fice zuwa d'akinta da tunani aranta ta kwanta "what if nabarsa shi kadai ya tafi yaje yayi sabin emmata acan gashy an gaya mun wannan 'yan matan kd akoi iya wanka da seducing maza, chab! What shud I do now?"***** Washegary around 10:00AM don moha ya gama shirya kayakinsa da breakfast yafito parlour sega heedayah ma tafito da akwatinta tana ja. Abin mamaki! Wasn't she the one who said barata bisa ba? Baki ya sake yana kallonta, "maman baby ya haka? Kin canza mind naki ne? Kokuma gda zaki? Tace "binka zanyi" batare da nuna damuwa ba "Lol I know u'll miss me daman u can't go a day widout starring at my face right?" Tsuka taja "mstw karka bata min rai in fasa zuwa, meh a fuskarkan? Duk kyan ka ka kai justin bieber ko omar borkan ne? Nifa dalilin dayasa zan biki dan ban yarda da kai bane, gara na sa maka ido in bahaka ba emmatan kd'n nan shegu ne ynxu se su..." Sekuma tayi shiru don moha dake dariya yace "se su miki snatching dina ko? Lol mutafi toh, kinyi sha drugs naki?" Kai ta gyada masa "ga akwatina kai min mota" tayi taga murmushi yayi yaja both akwatinsa da nata yayi waje dasu yasa a booth ya dawo ya rufe duk windows na gdan yayi shutting lights din sannan sukayi sallama da baba me gadi suka hau hanya!

HEEDAYAH!

107
written by miemieKira'a don moha ya kunna musu a motar, heedayah kuwa resting kujerar ta tayi ta kwanta comfortably ba tare da ta ce masa komi ba. Kafin su bar garin kano don moha ya tsaya a gdan mai yayi full tank, tun daga lokacin heedayah tasoma jin amai dam warin man data shak'a. Don moha yayi da ita kan ya maida ita gda tunda batada lafya sam tak'i cewarta yana son yaje yayi flirting da 'yan matan kd ne, gara ko mutuwa zatayi ta bisa, haka sukata tafiya. Basu tafiya me nisa sesun tsaya tayi amai a haka har suka isa kaduna inda suka sauka a ASAA PYRAMID HTL.
Heedayah ta gaji sosai ko fitowa daga mota ta kasa ga jikin ta du ya tashy, kafafun nan duk sun kumbura. Don moha ne yayi assisting nata ya kwantar da ita kan gadon dakin daya kama musu sannan yaje yafito da akwatunansu. Se sannu ya ke mata, "yi kokari kiyi sallah, kinji?" Da kyar ta tashy tayi toilet nanma amai sosai ta rigayi sannan ta dauro alwala tafito taga don moha baya nan, sallah ta idar ta mike a gun jikinta zaafi kamar wuta. Yana shigowa ya nufa kanta da sauri "maman baby jikin ne haka? Ko zamuje kga doctor?" Kai ta kad'a masa "just get me some black tea". "Toh" ya fadi ya kira waya yayi ordering mata black tea nan da nan aka kawo ko karfin shan tea'n ma bata da dan haka don moha ya bata nd alhmdllh bata harar ba mganin ta tasha ya kwantar da ita. Kaya ya canza ya feffeshe da turare duk heedayah na kallonsa sanda yazo fita tace "ina kuma xakaje?" Yace "zanje in samu wanda xan zana masa gda ne, muyi mgn". Heedayah tace "wlh karya ne in har dgsk na miji zakaje gani shine harda canza kaya tun ba'aje ko ina ba kasoma nuna halin ka ko?" Dariya sosai yakeyi how heedayah can get jealous. Ya dawo kan gadon ya zauna a gefenta "wlh shi xanje gani don't worry I promise ko kallon 'yan matan waje baranyi ba so dont worry kinji? Get some rest, okay?" Peck ya bata a goshi yau kam bata goge ba har ya kai bakin kofa sannan tace "come back safely okay?" don moha yyi murmushi sannan yace "sure mmn baby" ya fice. A hnkl bacci ya dauketa se bayan la'asar don moha ya dawo ya tada ita tayi sallah yamusu ordering fried rice nd chicken sam heedayah bata iya taci ba dan tasan the moment tace xata ci hararwa zatayi kallonsa kawai take yanda yake tacin abincinsa tana jin sansa na shiganta. Sanda ya gama ci sannan ya lura da plate nata yaga ko tab'a abincin batai ba yace "maman baby ya baki tab'a food naki ba?" Tace "cuz nasan koda naci xanyi vomitting nasa out", don moha yace "baby na baki wahala ko? Sorry toh me zaki iya ci instead amiki ordering, u can't stay hungry". Heedayah tace "black tea kawai zan sha" nan yamata ordering tasamu tasha ba tare da ta harar ba.
Bayan data gama sha ta mike kan gado yace "maman baby xaki iya fita yau kuwa?" Tace "why do u ask?" Yace "I was thinking ko zamu fita kiga garin kd". Heedayah tace "ni baran iya fita ba banajin d'adi saidai in zaka fita kai kad'ai" don moha yace "sure?" Ta gyada masa kai, kayansa na daxu ya mayar ya sake feshewa da turare sannan yace "toh na tafi", tana kwance kan gado tace "wlh baraka fita ba, instead kace kaima ka hakura amman sekace ka tafi? Ni wlh baran yarda ba come back ban yarda da kai ba kabari zua gbe in na d'an samu sauki se mu fitan tare".
Murmushi sosai don moha keyi daman shima bai da intension na fitan kawai yayi ne dan ya tsokanota. Dawowa yayi ya rage kayan jikinsa ya haura gadon ya kwanta shima yace "zo in d'an miki massaging legs naki naga duk sunyi swelling nd nasan u must be exhausted yau", heedayah tana so tana kaiwa kasuwa "ni bance maka ba am fine" ko sauraronta beyi ba ya zaunar da ita ya soma massaging mata k'afa a hankali har tayi bacci ya kwantar da ita yayi hugging nata tightly har shima yayi baccin se bayan maghrib suka tashy, yayi alwala itama tayi ya jasu sallah. Da daren ma black tea ta sake sha ta kwanta bayan don moha yagama zanen da yakeyi yayi joining nata kan gadon yaga heedayah ta tura pillownta can gefen gadon matso da pillow'nsa yayi kusa da nata tuni ta fara masifa "muhammad me haka? Kwana zamui tare? A'a gaski ni ban yarda ba na d'au fa kaima zaka kama d'akin ka ne". Don moha yace "haka kkace?" Kai ta gyada yace "toh shknan" wayarsa ya d'au yayi pretendn kamar yana waya "hello baby? I'll call u back yau kam sekin gaji da hira dani"... Yana maganan yana barin d'akin ya rufo mata kofar. Tashy tayi tafara safa da marwa a d'akin "omg! what do I do now? Ashe dama ce masa nayi ya kwanta kan wannan seater d'in ynxu zeje yata waya da wancen shgyan wlh baran yarda ba", mayafinta ta yafa ta fice zuwa gun secretary'n wajen "uhm pls wani yazo nan ynxu yayi booking room?" Secretatary'n tace "maza biyu ne sukayi booking room ynxu ko xaki iya describing nasa?" Heedayah tace "he's tall haka, fair"... a zuci tace "should I say he is handsome?" Nan tabar maganan zucin tace "zaki gansa d'an kyakkyawa haka". Secretary'n tace "ohh muhammad ko? Room 16 yayi booking. Kai gaskia ya had'u, haka kawai naji ina sonsa nd dagani baida aure koda yana dashy ma it wont change my intentions why asking, kinsan sa ne?" Heedayah tace "toh karuwa miji na ne, wlh ashe gaskia ne ku 'yan kd haka kuke kinji kunya wlh banza kawai nd kisani miji na yafi karfin secretary kamar ki, harda wani koda yanada aure it wont change ur intensions, to wlh in ba wai so kke ki k'are rayuwarki da konannen fuska ba tun wuri kifita daga harkan mijina kokuma na miki kaca kaca da acid a wannan mumunar fuskarkin muga ya zakice kinason mijin wata nan gaba". Ta k'are mgn tare da watsa mata harara.
Nan ta nufa room 16 knocking takeyi kamar zata b'alla kofar yanaji shikuwa yasan sarai itace wayarsa ya d'au kamar yana waya yaje ya na bud'e mata kofar yana "okay babe i'll call u back ina zuwa"...hannu tasa ta wabje wayan ta kashe ko lura taga ba wayan gaske bane ma batai ba dan kishi, hannu tasa tafra buginsa "wlh muhammad bakada shame, ynxu dan nace kabar d'akin seka bari dgsk kaxo nan kuma kana waya dawata karuwa, ni ka barni ina renon cikinka, Allah ze saka min" sekuma ta fashe da kuka. Don moha dake dariya sosai yace "ikon Allah! Maman baby! Yi hkr to bar kukan", kokarin hugging nata yake ta fara kai masa duka ko ta ina tana kuka da kyar yayi hugging nata tightly inda bara ma ta iya buginsa ba se kuka takeyi yace "am sorry toh barin yi wayan ba kiyi seizing se gbe kibani zo in rakaki d'akinki" heedayah dake kuka har ynxu tace "ni kazo muje mu kwanta tare tsoro nakeji", dariya sosai yakeyi yace "toh muje", tare suka kwanta pillownsa na kusa da nata itakuma ta juya masa baya taki basa bedsheet din dan mugunta ga wani sanyin da akeyi. Dukunkune kanta tayi dashy, don moha kam se dariya yakeyi dan ba karya heedayah akoi kayan dariya kokarin yaye bedsheet din dake jikintan yake tana sake damdamesa a jikinta "wai me haka muhammad? Bacci fa xamuyi ba wani abu ba", don moha yace "toh a bani hakki na", har zatace "bara'a bayar dinba" seta tuna wa'azin da ummu jalila ta mata kan duk macen da mijinta ya nema had'a kwanciya da ita ta hanasa badan wani kwararren reason ba mala'ikun rahama suna tsine mata. Kuka ta fara yi ta jiyo tana kallonsa "don moha dan Allah karka min haka ka tausaya min banida lfya wlh ynxu in har na yarda maka gbe ko tashy kan gadon nan baran iya ba pls kace ka hakura banason tsinuwan mala'iku, kaji?" don moha dake kallonta yana murmushi yayi shiru bece komi ba ta kara volume na kukan nata "pls mana muhammad pls kace ka hakura"

HEEDAYAH!

108
written by miemieYace 'xan hakura under one condition", heedayah tace "ai nasan da karuwarka ne ta tambayeka da tuni ka hkr widout a 2nd thought". Don moha yace "only if xaki cemun kinasona se in hkr", shiru tayi yace "oh baraki fad'a ba knan?" Nanma shiru, fuskarta ya leqa yaga idanunta a rufe kamar me bacci murmushi yayi yace "na hakura maman baby, anything for you sleep good". Goonight kiss ya bata shima ya kwanta ahaka har sukayi bacci...
Da asuba suka tashy sukayi sallah sannan suka koma bacci se pass 11 suka tashy wanka sukayi one by one ga yau heedayah ta tashy da karfin jiki har breakfast dinma tasamu ta d'an ci chips din. Wata fitted riga da skirt nata tasa sekace bame ciki ba ya bala'in mata kyau shima don moha shirinsa na kullum yayi jeans nd shirt ya rufo kofar har sun kaida fita bakin kofar htl din sega secretary'n jiya don moha yace "ummi, har kin iso ne?" Tace "yes sir morning". Don moha yace "how was ur night?" Heedayah dake hararan ummi taja tsuka "mstw" sannan taja hannun don moha suka bar gun, shide kallonta yake yi cike da mamaki how jealous she can get.
GAMJI PARK suka je 'yan mata da samri ne masu class a gun ga weather'n wajen so sweet kujera ya nema musu suka xauna ya saya musu snacks da drinks yakawo ya bud'e mata drink nata heedayah nata kalle kalle dan wajen ya burgeta. Sipping drink din take a hankali can idanta yakai kan wata beb da tabar duk abinda takeyi tana kallon don moha tuni zuciyar heedayah ta fara mata k'ona "tashy mu tafi muhammad" ta fad'i a takaice. Yace "but why? Har kin gaji da nan dinne?" Tace "kalli wancan banzan tun daxu kai take kallo ni wlh gbe da ka gama aikinka da baka gama ba tafiya xamuyi mstw", tashi mana hannunsa ta rike dagan gan tabi ta gaban wancen beb dake kallon don moha ta watsa mata harara sannan suka wuce haka sukata yawo ranan , su le' villane, halims, royal tropicana, ba inda basu je ba daga karshe pixie dixie suka je inda wata ta taso tundaga gun xamanta tazo wajen su don moha ta tsaya daidai gabansa ba tare da ta kalli heedayah ba tace "hello handsome, suna na Saaly baby tun daga can kamin kyau shine nace barin xo mu gaisa, ko zamu iya exchanging contact? Believe me you're hot". Murmushinsa me kara masa kyau yayi yana kallon heedayah sannan ya dawo da kallonsa kan Saaly dake kallonsa itama yace "sure here's my card, am muhammad" Yana mganne yana kokarin ciro card nasa daga pocket nasa, Kafin ya hankara heedayah dake tafasa dan kishi ta mike ta tsinke saaly da mari tas! Kukeji duk mutanen gun suka juya suna kallonsu kafin Saaly ta hankara heedayah ta k'ara mata wata marin "in iyayenki basu koya mki tarbiyya ba ni zan koya miki shameless woman kawai karuwar banza karuwar wofi!" Se ynxu bakin Saaly ya bud'u tace "what? Did u just slapped me?" Heedayah tace "an marekin ki sake min wata mgnan da bata gameni ba kiga ko baran k'ara miki wata marin ba", don moha kam is totally speechless ba abinda yakeyi se kallon heedayah.
Saaly ta d'aga hannu itama xata mari heedayah nanne don moha ya mike tare da rike hannuntan "don't u dare slap my wife!" Nan fa mutane suka shiga tsakaninsu dan duka don moha keda niyan yi ma Saaly. Take heedayah taja jakarta ta nufa gun motansu cikin fushi, zuciyarta tana me mata k'ona wasu zafaffun hawaye suka fara zubo mata, da sauri don moha yabi bayanta yasameta gun motar nufowa gabanta yayi "heedayah pls stop crying its not good for health yi hkr kinji?" " Open the door" ta fadi ba tareda ta kalle sa ba, nan ya bud'e mata tashiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima "baby pls say something, ni wlh bansan gurl din banza haka bane, i was just joking bliv me I have no intension of giving her my card, am so sorry pls don't be mad" haka yata suratansa bata ko tanka masa ba se zubda hawaye take tayi. Suna isa htl din ta fito tabar masa kofar a bud'e ta nufa dakinsu kwanciya tayi kan gadon tana sharara kuka hannun sa taji akan kafadarta mikewa tayi shima ya mike mari ta tsinka masa me rai da lfya "how could u muhammad? Me ka maidani, just bcuz kaga ina getting jealous anytime akanka shine kake taking d'ina for granted? Is that it? Answer me me!" Don moha yace "no baby pls let me explain bahaka bane kiyi hkr pls", heedayah tace "what explanations? Don't u get it muhammad? Am doing all this bcuz I LOVE YOU! I LOVE YOU MUHAMMAD..." sekuma tayi shiru ta fashe dawata erin matsanancin kuka. Don moha daya kasa fad'in komi yayi hugging nata tun tana kokorin kwace kanta daga jikinsa takasa se kuka take rusawa kanta yayi kissing "I LOVE YOU SO MUCH MORE my baby pls forgive me, I've never once had a girlfriend duk faking nakeyi I just want to know ko kinaso na, am so sorry for playing with ur feelings stop crying kinji?" Kukan takeyi har ynxu a hankali ya saketa tasa hannu ta goge hawayenta tare da juya masa baya, don moha ya kira sunanta tace "excuse me pls I want to be alone" bekuma fad'in komi ba ya fice mata a d'akin.
Wani sabon kukan ta fashe da wanda ita kanta batasan dalilin yin kukan ba haka ta tayi har sanda bacci barawo ya saceta, koda da don moha ya shigo yaga har tayi bacci blanket yaja ya rufeta dashy yayi kissing nata a kumatu sannan yace "Am so sorry for hurting ur feelings heedayah, it is the only way da nasan zan iya bi dan in gano ko kinaso na pls dont be mad"
Bayan maghrib ta tashy tayi sallah tana kwance kan gado don moha yshigo da'akin baya ta juya masa yace "baby me xakici for dinner? Pls dont punish urself for my mistakes, kinga in baki ci abinci zeyi affecting baby'nmu" Bata ce masa komi ba tea yamata ordering nanma tayi kamar bata gani ba haka yata bata hkr a daren ranan amman sam bata tanka sa ba.
Daidai 10:20PM don moha ya gama abinda zeyi ya haura gado ya sameta yaga ta jima da bacci, shafata yasoma yi a hnkl tana jinsa bata hanasa ba, ba ta kuma basa go ahead ba, ba abinda takeyi se zubda hawaye ahaka har don moha ya rabata da kayan jikinta suka wula duniyar ma'aurata. Ba karamin jin d'adin hadin kan da heedayah ta basa yayi ba se albarka yaketa suburbud'a mata. Hugging nata yayi tightly ahaka sukayi bacci. Da asuba ya tasheta ya d'aga ta yakaita toilet bayan ya had'a mata ruwan zafi ba gardama ba zagi tagama wankan ta tafito ya jasu sallah. Bayan sun idar ya matso kusa da ita ya kwantar da ita a jikinsa "my baby am so sorry kinji? Am sorry for hurting ur feelings pls stop being..." Be kare maganar ba heedayah tayi shutting nasa tare da basa wata hot kiss, sun kusan 3mins suna abu d'aya sannan ta sako sa ta riko fuskarsa "u don't have to be sorry MR ROMANTIC it is all my fault da tun farko da ban nuna maka cewa bana sonka ba u wouldn't have done all that, so am sorry for making u believe that I don't love you. I do love you muhammad since when I was a little girl nake sonka har ila yau ina sonka nd I'll love you forever, your love runs in my veins". Nan ta tashy ta d'au wata zobe cikin jakarta "here, tin randa aka daura mana aure rayyan yace in baka wannan nak'i bcux I was mad nd confused lokacin, so I want u to have it now" hannunsa ta d'ago ta sa masa tare da hugging nasa I love you muhammad" hugging nata shima yayi "there is no amount of words in this world dat can show u how much I love you" ta sakosa tana masa murmushi "nd also akoi honeymoon da rayyan yace muje dakai that was since da aka mana aure still shima nak'i but now inason bayan mun koma gda lfya kamana all processes din muje dubai muyi honeymoon namu acan, it still not late aiko?" Kai ya gyada mata dan he's totally speechless se gani yake kamar a mafarki abin ke faruwa!

HEEDAYAH!

109
written by miemieGado suka haura yana rungume da ita har sukayi bacci. Se 9:00AM suka tashy sukayi wanka one by one sukayi having breakfast, yau ma batayi amai ba, maganinta ya ballo mata ta sha, sannan yashiga tattara masu kayakinsu, heedayah tayi tayi dashy daya bari suyi tare amman sam yak'i. Yana gama had'a musu ya jawo akwatunan suka rufo kofar, sannan suka fito duk sanda suka had'a ido murmushi sukeyi wa juna romantically!!! A wajen biyan bills suka tsaya don moha yace "barin yi paying bills din ko maman baby na?" Heedayah tace "okay ina jiranka", don moha yace "bara ki biyoni ba? Kar ummi tace...' Be kare maganar ba heedayah ta aza hannunta kan lips nasa tana murmsuhi sannan tace "I trust you my mr romantic nasan u won't cheat on me", peck yabata a kumatu sannan ya fice nan da nan ya biya ya riko hannunta suka shiga mota agaban gdan mutumin da ze zana ma gda ya yi parking ya shiga ya basa zanen sannan yafito suka kama hanya yaukam ba amai se hirarsu na masoya sukeyi acikin motar har suka iso garin kano, a wata eatery suka tsaya sukaci abinci nanma sanda aka kusan yin drama, waitress na wajen ta soma wa don moha wata erin kallo, nan fa uwar kishi ta tsayar mata, se hkr don moha ke bata sbd yadda mutane suka juyo suna kallonsu amman heedayah tak'i jinsa sanda ta wanke waitress din tatas! Sannan taja hannun don moha a fusace suka fice. Acikin motar don moha yace "my baby my baby, I love the way u get jealous", kallo ta watsa masa sannan tace "wlh in muka tafi Dubai dinnan nik'af zan na sa maka sekace maita kowa ta ganka se tace ka mata", don moha dake murmushi yace "kamar yadda kema na miki ba", duka takai masa a hannu a hankl suka soma dariya duka**
Akwatinansu ya ciro musu daga motar bayan sun iso gda, megadi ya musu sannu dazuwa. Ya bud'e kofar gdan heedayah ta baje kan kujera dan wani gajiyan datakeji ruwa ya dauko mata ya kwantar da ita a jikinsa ya bud'e mata tana tasha tana kallonsa. Bata gama shanyewa ba se suka ga ummu jalila kamar daga sama a parlour'n nan kunya ya rufe heedayah dan yadda tawani baje a jikin don moha kokarin jan kanta take daga jikinsa shi kuwa sewani kara matseta yake ummu jalila tace "toh maras kunya kun gannin ma baraku gyara ba?" Don moha yace "what? Is it a crime dan mata ta ta kwanta a jikina?" Ummu jalila tayi murmushi sannan tace "shigo da abincin nafeesa tunda sunki gyarawa" nan tashigo dashy heedayah tace "so nafeesa ke kka had'a baki da don moha kuka ta playing games dani ko?" Nafeesat tace "eh mana baga ynxu kun shirya ba!" Heedayah ta dawo da kallonta kan don moha ta basa peck a kumatu sannan tace "barinje in watsa ruwa" "okay baby" ya fad'i nan ta mike tashiga d'aki tabar su ummu jalila da baki wangalan!
Sede har ynxu murmushin fuskartan takasa gushewa bayan tafito ta cancare kwalya tasa wata arnen kayakin da bata tab'a sasu ba, dududu tsayin kayan a iya cinyarta ya tsaya gashi ya bala'in matseta yakuma mata kyau. In bawai an fad'a bane bara'a dau heedayah nada ciki ba kasancewar doguwa ce se cikin yabi tsayinta. Ko data fito kuwa su ummu jalila basu nan cire kunya tayi ta tako har gaban don moha daya sake baki yana kallonta rungumesa tayi yace "woow! Ure looking..." Be kare maganar ba tayi kissing nasa haka tun daga ranan heedayah(baby) da don moha(mr romantic) suka soma shiri.
A koda yaushe cikin romancing juna suke kullum suna makale da juna, office ma bata san zuwa ynxu dan bata san ta rabu da mr romantic nata, kullum setace batada lfya.
Koda sukaje gda mummy da daddy sunji dad'in ganinsu kan su a had'e ynxu, key'n motarta daddy yabata tace ita sam barata karb'a ba dan duk inda zataje mr romantic nata ze kaita! Within sati don moha yayi getting musu ticket nasu to DUBAI. Ana gobe zasu tafi suka je sukayi wasu mummy da ummu jalila sallama, sannan tabi ta office ta karb'a leave. Haka da daren rannan bayan shirya kayakinsu da suka gama suka kwanta, as usual don moha ya fara mata abinda ya saba yaukam yanayi heedayah na mayar masa da martani tuni na bugo legediz benz d'ina nabar musu d'akin a 360.
Washegary! Suka tashy yau kam wankan ma a tare sukayi, akasha tab'e tab'e a tooilet sannan suka fito suka shirya atare suka had'a breakfast bayan sun karya heedayah tasha drugs nata. Don moha ya fiffito musu da luggages nasu yasa a booth sukayi sallama da baba me gadi sannan suka wuce airport around 10:00AM jirginsu ya iso, kaninsa safyan ne ya tafi masa da motar sa gda.
Nan da nan sukayi boarding sukayo addu'an tafiya kowa yayi fastening seatbelts nasa sede heedayah akwai tsoro since datake karama anytime jirgi ze tashy mummy take hugging yau da ba mummy don moha ta yi hugging gamgam ta rufe idanunta a hankl jirgin ke tashy har yagama tashy nanne ta sakosa yasa musu wata movie a Ipad nasa sukayi sharing earpiece suna kallon tare daga can heedayah ta kwantar da kanta bisa shoulders nasa har tayi bacci kansa shima ya aza akan nata yayi baccin koda waitresses na jirgin sunzo wucewa se sun tsaya kallon wannan lovely couple din!
Tafiya me nisa sukayi sannan suka iso DUBAI INT'L AIRPORT daga can don moha ya tsare musu taxi inda ya saukesu a daidai gaban "LE ROYAL MÈRIDIEN BEACH RESORT AND SPA" inda ya musu booking d'aki masu aikin wajen suka shiga musu luggages d'aki ya biya su sannan ya rufo kofar already heedayah ta baje kan gado, gadon take masa nuni da hannu tana bubbugawa da nufin yazo shima tsalle yayi ya jawota jikinsa nan suka hau kissing juna ni miemie nace "oh! Wannan mutane take it easy kafin ku cire bakin junan ku"

HEEDAYAH!

110
written by miemieIsha prayer suka idar, wata hadaddiyar jacuzzi ce a toilet d'in me running ruwa da kansa signal da gira don moha ya mata nan suka dauro towel suka shiga cikin jacuzzin atare suna hira suna sipping drink nasu da ke gefe don moha na tab'e tab'e. Sunfi awa cikin jacuzzin sannan suka fito night gown nata tasa wanda dashy da babu du d'aya ne sannan suka kwanta cikin so da kaunar juna!
Washegary kuwa duk suka makara sallan subh se da safe suka idar wayar don moha dake kiran sallah ma beyi ba ranan, suna idar wa suka koma bacci se after 11 suka tashy ya musu ordering breakfast bayan sun karya sukayi wanka suka fita ganin gari wajajen shak'atawa da dama suka je irinsu Sharjah Museum of Islamic Civilisation, Dubai meseum, Sharjah arts meseum, ba abinda heedayah keyi se tuna time da suke zuwa da mummy in tazo siyan kaya. Sede kamar a Nigeria haka 'yan matan larabawan nan suke ta kallon don moha, heedayah kuwa ji take kamar ta siyo nik'af tasa wa mr romantic nata dan abar kallonsa. Hannunsa ta rik'o yadda da angansu za'a san matarsa ce.
Sega republic park nd zoo sukaje yasaya musu wani cotton candy d'ika d'ika sannan suka fara trying out diffrent swings da suke wajen suna ta kashe selfie, heedayah na ma ummu jalila sendn. In tak'aita maku labarin they had morethan fun ranan se bayan la'asar suka dawo gda all tired! Dan haka suka mike kan gado sukayi bacci se bayan maghrib suka tashy, sukayi sallah yamusu ordering abinci suka ci don moha ya riko hannun baby'nsa sannan yace "my baby zamuje asibiti gbe ko?" Heedayah tace "asibiti kuma mr romantic? An tab'a zuwa asibiti a honeymoon ne, I thought fa in munzo nan no more zancen zuwa asibiti, ka fa sani banason abu da asibitin nan wari yake min". Don moha yace "come on baby nan fa ba 9ja bane, a 9ja ne kawai asibiti yake waari believe me nan asibitinsu kamshi yake nd you'll like it, yi hkr ko maman baby, ba abinda zasu miki kawai scanning xa'ayi muga how our baby is doing shknan", heedayah tace "mr romantic kaima kasan wannan fararen mutanen da shegen bin diddigin abu ko mutum is fine se sun kwakulo masa rashin lfya trust me ba amfanin zuwa hsptal dinnan tunda ynxu bana morning sickness, ba amai..." ta dago hannunsa ta aza kan cikinta "tsaya kaji... Kaji baby'n ma yace daddy am fine" dariya sosai don moha keyi "evn still baby yakamta muje" ba yadda beyi da heedayah ba sam tak'i harda guntun kwallarta, ba yanda ya iya da maman baby'nsa haka ya barta isha nayi suka idar suka kwanta yauma gogan namu be barta ba haka suka ta sha'aninsu abinsu.
Kash! Sede yau not like yadda heedayah ta saba tashy da karfin jiki, yau kwata kwata ta tashy ba lfya ko dan ciye ciyen data tayi jiya dasu swings data trying jiya ne ya juya mata ciki ya ta da mata jiki oho! Suna cikin bacci tana rungume ajikin don moha around 7:00AM kawai tajiyo amai da gudu ta fad'a toilet shima da sauri yabi bayanta se sannu yake mata amai ta rigayi sosai kap! sanda ta harar da abinda ke cikinta tana gamawa yayi flushing ya wanke mata baki sannan ya d'aga ta cak ya dawo da ita kan gadon. "My baby ya haka? Jikin ne?" Murmushin dole ta kirkiro "no nakega d'an ciye ciyen danayi jiya ne don't worry I'm..." Bata kare maganar ba tafara ganin stars akanta kawai ta fado jikin don moha idanunta se kafewa suke tuni don moha ya shiga tsoro, "baby let me get a taxi yanzu muje asibiti kinji? Stay still" wuyan kayansa ta kama "pls no don't just get me some black tea shknan", don moha yace "what do u mean don't? Kiyi hkr muje asibitin su duba ki" kuka ta fara masa haka ba yadda ya iya yamata ordering black tea shi da kansa ke bata rabi tasha tace masa ta koshi yaki jinta se d'ura mata yake amai kawai ta kwararo masa a jiki both jikinsa da nata ya b'aci cak ya d'agata ya kaita toilet yazo yayi taking care of wajen sannan sukayi wanka tare nan ma takasa fitowa daga bathroom din cuz any moment ta tsaya se jiri ya kwashe ta.
Kwantar da ita kan gado yayi kaman daga sama suka soma jin wani irin bala'in sanyi duba window'n da zeyi yaga its snowing wato anayin snow gashy kwata kwata basu dauko kayan sanyi daga gda ba dan basu zata snow ze iske su ba. Windows din ya rufe duka amman se kaman bud'e su yayi dan su can sanyin su ba kaman namu bane room heater'n ya kunna musu ya dauko mata wata kayarta me nauyi ya tayata sawa amman se shevering (b'ari) heedayah keyi dan sanyin da takeji hannunta yasoma murza mata ko zata dan yi feeling warm amman ina hugging nata kawai yayi tightly daga k'arshe ya rufesu da bargo ahaka har tasamu tayi bacci.
Se 11:25AM suka tashy ya tayata tayi brushing shima yayi sannan yamusu ordering breakfast kwata kwata ta kasa ci black tea kawai tasha shidinma ta harar ga wani uban sanyin da akeyi. Siyasa ya mata da wayo yace tashirya suje su siyo kayan sanyi badan tanaso ba ta dau mayafinta tayi rolling yadda arabs keyi suka tsari taxi a shopping mall suka tsaya, shi kadai ya shiga dan heedayah barata iya juran tafiya ba. Inda yasayo musu wasu manya manyan electric jackets nata purlple nd white nasa red nd black, sannan kuma da handgloves da head warmers acikin taxi'n ya sa nasa sannan ya sama ta itama nanne taji sanyin ya d'an ragu godia ta masa sannan ta kwanta a jikinsa. Driver'n yace "sir where are we heading to?" Don moha yace hospital. Heedayah tace "what? hspital yin meh? Ni baran..." Bata kare maganan ba ya had'a bakinsa da nata shiru tayi bata kuma cewa komi ba sanda ya sakota sannan yace "not a word pls baby," badan tana so ba tayi shiru haka suka isa asibitin don moha ya sallemi taxi driver'n sannan suka shigo unlike a nan 9ja su ganin dr acan is easy processes kad'an don moha yabi suka shiga ganin dr nan ya tambayi heedayah meke damunta ta kalli don moha sannan tace "ai wlh baran ce masa komi ba tunda kai kayi insisting se munzo seka gaya masa meke damu na". Don moha yyi gyran murya sannan ya zazzage wa doctor'n komi nan akayi scanning cikin aka ga baby'n na cikin koshin lfya, dr ya basu pregnancy clues da dama ya kuma rubuta mata wasu drugs da basuda karfi wanda barasu yi affecting baby'nta ba sannan ya bukaci amata allura. Nan fa heedayah ta soma tada bori a asibitin ita wlh bara a mata alluran ba. Dr yace "wow ur wife must be afraid of injection huh?" Don moha yace "yes dr don't mind her i'll calm her down thank you" ya amshi note din ahaka suka rabu.
Wajen chemist dake asibitin suka nufa wata kyakkaywar balarabiya ce nurse din yadda taga heedayah na kuka tun kafin a mata alluran ta mugun bata dariya tace 'oh! mother to be, don't cry like that u'll hurt ur baby its just an injection nd believe me i'll take it easy on you". Ko kallonta heedayah tayi ne ma, se kukanta takesha musamman ma data ga nurse din na matso alluran daga syringe din ta dawo da kallonta kan don moha "mr romantic pls do somethng karka bari tayi injecting dina pls" se kuka takeyi. Don moha yace "close ur eyes" sam tak'i yace "trust me nd close it nd don't open dem seni na ce ki bud'e" badan tana so ba ta rufe a hankl ya mikar da ita ya daga kayanta yadan saukar da bakin leggings data sa ta ciki, nan ta dandamesa tana "wayyo Allah mummy na dan Allah karki bari su min allur..." Bata kare magann ba ya hada musu baki yayi ma nurse din ido a hankl tasa alluran nan heedayah ta sake gamgame idanta tare da matso don moha a jikinta daga nan bata sake jin komi ba har se sanda don moha ya sako bakinta sannan yace "see? Kinga har an gama baki ma sani ba".
Heedayah ta juya tana kallon nurse din dake mata murmushi tace "did u inject me?" Kai nurse d'in ta giada mata sannan ta dawo da kallonta kan don moha tana wasa da mayafinta jawota jikinsa yayi nan nirse din tabasu drugs din tace "sauran allurai guda biyu kuma", (karku manta da turenci suke wannan mgn) heedayah tace "what? Wlh baran sake dawowa nan ba" murmushi don moha yayi ma nurse d'in sannan ya mika mata card nasa "call me pls" suka fice, acikin taxi d'in tayi lamo a jikinsa hat tasoma bacci har suka iso htl din bata sani ba, daukota yyi kamar baby yakaita har d'aki sannan ya kwantar da ita har ya juya ze tashy seta riko kolan rigar sanyin sa da idanunta a rufe take mgnar "stay with me mr romantic don't leave me pls" murmushi yyi yabata light kiss a baki sannan a hnkl ya janye hannunta daga kamun data masa ya jawo pillow ya kwanta a gefenta se kallonta yakeyi yadda take baccinta a hnkl hannunsa ya aza kan cikinta ahaka har shima yyi baccin...
Share:

0 comments:

Post a comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).