shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 22 July 2016

HEEDAYAH 86-----90

HEEDAYAH!

86
written by miemie

"can u feel it?" Kokarin kwatan hannunta take amman takasa "heedayah I love you nd I know u know that nd I can also feel it that you love me too, nasan kawai kina pretendn to love rayyan ne so dat kiyi hurting dina but deeply inside your heart baki sonsa ni kkeso nd koda kina sonsa ma is bcuz u are being fooled by ur feelings mesa barakiyi following heart naki ba we've been together tun childhood and ke kanki kinsan how much i've been protecting you abinda zaki saka min dashy knan? bayan kinsan tunba yau ba nayi promising kaina kan i'll never marry any other woman apart frm you," cikin tsawa yace "answer me heedayah!"
Heedayah da idanunta suka cike da hawaye tuni tayi karfin hali tace "let go off me don moha" da kyar ta iya ta qwata hannunta ta goge hawayenta sannan tace "I dont know what you are talking about all I know is da zanzo nan ban fada ma boifrnd dina kan wani namiji ze kama min hannu ba, forgievness naka nazo nema in har u are not willibg to forgive me shknan i'll go" tana kaiwa nan ta fice daidai takai bakin kofa don moha yace "I've forgiven you heedayah, ba abinda zaki taba tambaya a waje na in hana ki" zuciyarta takuma karyewa da kyar ta iya fadin "thanks" dan kukan dakeson fin karfinta da gudu ta fice izuwa motarta kuka takeyi kamar ba gobe sanda ta gama shan kukarta sannan ta kunna motar tayi tafiyarta, maganganun don moha ne kawai suke ta mata wasa a hankali bayan ta isa gda ta hango rayyan na zaune a garden yadda ta barosa gunsa ta nufa yace "har kin dawo ne? Yayi forgiving nakin?" Kai ta gyada masa tare da kirkiro murmushin dole amman kallo daya ya mata ya ga idanunta sun danyi ja, "why? Kinyi kuka ne princess?" Murmushi take masa tana kada kai da alaman a'a "banyi kuka ba mesa zanyi kuka bayan 've got you!" ta fadi a takaice, rayyan ya riko fuskarta "don't lie to me princess kinyi kuka ga face naki is all swollen keda da don moha ne?" Bata san sanda wata sabuwar kukan ta kubuce mata ba, tana kukan tana mgn "my king pls forgive me am so sorry," rayyan dayasan this was coming yace "why? What for?" Dan dama da biyu ya turata gun don moha sbd yagano ko still tana da feelings masa, nd inhar tayi kuka to ya tabbata tana son sa knan in batayi ba kuma toh... Heedayah tace "its don moha, dan Allah kaje kayi confronting dinsa yadena cewa ya na sona," lalashinta rayyan yyi har sanda tayi shiru sannan yace "my princess I want to ask u somethng nd I demand nothng but the truth tell me do you still have feeling for don moha?" Heedayah da bata taba tsammanin wannan question daga bakin rayyan ba tace "haba rayyan how could you, dama nasani tunba yau ba bakasona nice kawai nake dying maka, ko kishi na bakayi kana tambaya na ko inason don moha," rayyan yace "ba haka bane heedayah in har kinason sa I can give up on you bcuz ur happiness is all that matters to me weather u like it or not he is ur first love you can't deny it, nd as the saying goes first lpve never dies," heedayah da ranta yagama baci tace "okay fine nasan don moha was my first love nd najima da kashe love nasa a zuciyata u are the one I love rayyan so pls in har kanaso na like I do don't ever talk about don moha in my presence again!" tana kaiwa nan ta mike hannunta rayyan ya riko yana mata murmushi "am sorry princess yi hkr mu zauna" "o'o" tace rayyan yace "plss mana princess or do you want me to go down on my knees?" Kai ta gyada masa amman dawasa take shikuma ya dauka serious sega rayyan yana kneeling agaban heedayah "omg!" ta fadi "how could you? Wasa fa nake, get up pls" rayyan yace "this is how much I love you am ready to sacrife koda last breathe dina ne in har it'll make you happy," hannu tasa ta dago sa tare da hugging nasa "I love you so much more my king"**
Washegary da safe around 10:30AM acikin high court dake garin kano, samari da 'yanmata, iyaye da dattijai, umma, mummy, daddy, alhj ismail, don moha, rayyan, heedayah nanny dade sauran mutane duk suna zaune akan kujera judge na shigowa koya ya mike sanda ya zauna sannan kowa ya zauna bayan 'yan mintuna aka fito da alhj lawal da handcuffs a hannunsa aka tsaida shy awani gu, bayan gaisuwa lawayer'n su heedayah yayi presenting duk evidence dayake dashy, bayan evidence din aka kira eye witnesses bayan rantsuwan da sukayi suka gabatar da shedansu, judge ya dawo da kallonsa kan alhj lawal "bawan Allah shin kayi denying wadannan accusations din?" Kai alhj lawal ya kada masa da alaman a'a, judge yace "kanada lawyer'n da ze iya denying maka wannan accusations din?" nan ma yakuma kada kai, judge yace "toh masha Allah according to the 1999 constition any person found gulity of the above stated crimes here, he/she will spent 30yrs imprisonmnet" yana kaiwa nan ya buga table din sau biyu "court is dismissed" nan aka fita da alhj lawal ba abinda umma keyi se kuka bata san ta ina zata fara gaya ma mustapha wannan labari ba su mummy suna bata hkr bayan sun iso gda daddy yayi hugging heedayah "thank you so much heedayah, Allah miki albarka, yabaki yaran da zasui standing miki kamar yadda kka standing min nima," kowa ya amsa da "ameen," cikin motar ta koma ta ciro briefcase din wanda tayi amfani dawata karfe ta bude kwadon, "gashy daddy na cika maka promise dana dauka kan sena kwato maka files naka gun alhj lawal nd sena kaisa jail, now this belongs to you" amsa yayi ya duba yaga duk files na gdaje, filaye da conpanies dinsa ne murmushi sosai yake yi "nagode sosai 'yata heedayah," mummy ta nufo gunsu itama tayi hugging heedayah tana me sa mata albarka rayyan da nanny kuwa suna kallonsu suna murmushi suma.
Alhamdulillah! Atlast! The awaited day has come, heedayah ta yi fulfilling promise data dauka ma daddy'nta kan setayi arresting alhj lawal, atlast! They will live peacefully ynxu...
HEEDAYAH!

87
written by miemie

Tana shiga dakinta ta dau dayar wayarta ta kunna aesha roomie tafara kira bayan sun gaisa aesha tace "ai bakida mutunci roomie, ace tun tafiyarku kka kashe wayarki kullum sena trying amman bai shiga," heedayah tace "ba haka bane frndy tun dawowa na nafara aikin daukan revenge dina," aesha tace "so? Kin samu kin dau revenge din?" Heedayah tace "in shaa Allah ynxu haka alhj lawal na jail an basa 30yrs imprisonment," aesha harda daka tsalle "wow na miki murna sosai sosai yasu mummy da rayyan ko?" Heedayah tace "eh kowa lfya ya kuke a can?" Aesha ta amsa da "fine too nikam yaushe zaku sa mana date ne muzo musha biki tunda kin dau revenge naki," heedayah tayi dariya sannan tace "ai karki damu very soon" haka sukata hira aesha nabama heedayah hiran samarukanta***
Kwanaki da dama sunja yau kimanin 3 months knan heedayah da rayyan soyayya sukeyi like never before, akoda yaushe suna tare, yayi completing business class nasa, da daddy yayi niyan basa secretary a company'n mummy amman sbd files na sauran conpanies dinsa daya samu ynxu yaba ma rayyan daya daga ciki wanda yake abuja, nd alhamdulillah rayyan na running business din me kyau, sau uku yake zuwa a kowane sati nd duk sanda zeje heedayah tace se ta bisa amman its not possible sbd ba aure aka musu ba balle a barsu su tafi tare, dan haka daddy yace zeyi ma daddy'n rayyan ayi ayi asa date na bikin, he'll be the one to take care of everythng. Da na setting eyes na kan rayyan sanda naci tuntube dan wani ajeboter daya zamo ynzu kwata kwata aka gansa bara'a dau girman kauye yayi ba dressing kam heedayah ta koya masa ba aikinsu kullum cikin daukan selfie tare. Don moha kuwa na nan abin tausayi yayi aure yaki kuma shi kansa yasan inba miracle ba, heedayah barata auresa ba, ba yadda daddy beyi dashy kan ya cire love na heedayah frm heart nasa ba amman ina bare iya ba cuz bashi ke controlling heart nasa ba, he was affected by her love ever since childhood haka yake kullum cikin tunani har ya dan zube kadan, abin tausayi ;(*** Yau ranar ta kasance saturday heedayah bata da office yau rayyan kuma na gda dan haka suka shirya fita date da yamma around 4:40PM, rayyan ya fito daga dakinsa yana sake dawata "Giuseppe Zanotti" designer takalmi dawata jean pencil trouser na CK, haka shirt na jikinsa ma, sannan ya daura wata blazer sak kalon takalmin nasa akai, dawata transparent (reading) sunglasses a fuskarsa, gashin nan tasha mai da combing, wasu manya manyan azurfa ne guda biyu a hannun damarsa daya kuma a na hagu dawata bouzet designer agogo, daga idan da zeyi yaga princess nasa tana decending daga kan stairs din da takunta dai-dai kamar yadda ta saba tasha wata english gown red da karinat black ta ciki tayi rolling da black gyale da shoe nd bag nata suma black tana gama saukowa rayyan yace "wow! looking stunning as always," "you too" tace masa sannan suka shiga wata honda accord V8 dagani motar rayyan kenan shi ke jansu har suka isa izuwa wata eatery inda sukaci abinci daga can suka wuce zoo, se kusan maghrib suka dawo gda suna shiga cikin gda suka ga ko ina duhu kamar daga sama sukaji "HAPPY BIRTHDAY PRINCESS," heedayah was overwhelmed with joy ta juyo ta kalli rayyan, "you did all this?" Kai ya gyada mata "happy birthday my princess" wata dimemiyar shopping bag ya miqa mata tana budewa taga the bag of her dream wato "prada" tun ba yau ba takeson jakar gefensa kuwa wata karamar package ne tana budewa taga wata white gold dankunne da necklace bata san sanda ta daga hannu zatayi hugging nasa ba gyaran murya yayi yana mata ido kan su mummy suna wajen, sosa keya tayi "my king these are way expensive, ko baka siya min ba nasan you love me," rayyan yace "me na ce miki? Duk sanda na fara earning kudin kaina zan saya miki abu dashy, so dont question why, okay?" Kai ta gyada masa "thank you so very much, I love you" ta nufa gunsu mummy, "mummy daddy kalli abinda rayyan ya siya min" mummy tace "wow gashi harda prada'n da kkeso" shima rayyan din ya kariso inda suke godiya mummy da daddy suka masa, yace "pls ku daina in kuna min godiya nikuma inyi muku meh?" Nan mummy da daddy ciki harda nanny suka bama heedayah birthday present nata itama tayi murna sosai tamusu godiya bayan su daddy sun dawo daga maghrib prayer suka ci abinci sanda suka gama sannan rayyan ya nufo gun heedayah yayi kneeling agabanta yaciro wata pack a aljuhunsa ya bude mata tare da fadin "will you do me the honour of becoming my wife?" heedayah da kuka yafi karfinta da kyar ta iya ce "yes I will with all my heart" yazo sa mata zoben yaga already akoi wanda suka taba exchanging dan haka yasa mata akan sa yazama 2 rings a yatsa daya, nanma dan murna heedayah ta manta zata kuma hugging nasa ya mata ido sannan ya dawo wajen zamansa ya zauna daddy yace "oh zamani! My dear mu ina mukayi wannan engagement a bikinmu?" Mummy dake dariya tace "aifa habibi nan gaba kuma canzawaa abin zeyi, bature da iyayi kawai toh ynxu me amfanin engagemnent din?" Heedayah dake ta admiring diamond engagemnt ring nata tace "kaji mummy da wani zance, engagement dinnan is showing zan auri rayyan no matter what!" Mummy tace "tohhh ynxu princess ko kunyan daddy ma baikiji knan?" Da gudu ta haura stairs izuwa dakinta ta bararraje akan gado murmushin fuskarta kam sam yaqi gushewa...

HEEDAYAH!

88
written by miemie

Se can dare around 11:00PM da ta tabbata su mummy sun kwanta tafito sidak sidak zuwa dakin rayyan knocking tayi a hankali har ya fara bacci shima sanda tayi kusan sau uku sannan ya taso ya bude mata hugging nasa tayi tace "this is for my birthday present," sannan ta sako sa takuma hugging nasa again "nd this for the engagement ring" 'my pleasure" yace, "me kkeyi har ynxu bakiyi bacci ba?" Tace "how can I sleep? I can't keep calm you'll soon be mine," rayyan yayi murmushi sosai 'am already urs ai my princess, go nd get some sleep okay?" Peck yamata a goshi sanda ta haura sama sannan ya rufo dakinsa ya kwanta da tunaninta yayi bacci. Washegary da safe PA'n daddy yaje yamasu heedayah booking flight kan zasu Edo state ayi mgnar bikin, a wunin ranan aiki suka tayi can da yamma mummy ta tura rayyan kan suje suyi siyayya masu mummy, jifatu suka nufa inda suka kwaso kayaki sosai.
Washegary around 10:00AM jirginsu ya tashy tafiyan awa daya da 'yan mintuna sukayi suka iso garin Edo daga can suka tsari taxi zuwa UHUNMWONDE. Su mummy sunyi murnan ganinsu sosai aaliya kam kamar zata haukace ba qarya kam tai missng rayyan, bayan abincin da suka gama ci suka fara tattaunawa akan zancen date na bikin daga karshe a ka yanke date din 11th may wanda yazo daidai da birthday din rayyan wch is in 3months time kenan, kwana daya sukayi washegary suka juya. Aaliya nata murna abikin brother zataje kano.
Days move by so quickly, yau kimanin 2 months 2 weeks knan kwata kwata saura 2 weeks bikin heedayah da rayyan, gdansu na nan a unguwar new GRA komi aciki an gama shiryawa shirin arrival na amarya da ango kawai akeyi, gdan ya hadu to the extreme tsayuwa dan describing gdan ma bata lokaci ne believe me innace muku gdan ya hadu! Heedayah kuwa tun 1 month to bikin tafara shan gyaran jiki, skin nata na nan kamar baby's butt so soft ga wani farin data kara. Katin aure aketa rabawa ko ta ina, PA'n daddy ne yakaima alhj ismail card na auren, suna zaune a parlour shida don moha aka danna doorbell nan don moha ya miqe ya bude bayan gaisuwan da PA yayi masa sannan ya tambaya "alhj na gda?" Don moha yace "eh wani abu ne?" PA ya miqa masa card din "daman card din auren heedayah 'yar alhj s.u ne" yana kaiwa nan ya fice, kasa motsi don moha yayi cak ya tsaya agun hawaye ne masu xafi suke gangarowa daga idanunsa daddy yazo ya riko sa ya ajiyesa kan kujera, "muhammad hkr zakayi Allah nada reason nasa na hanaka auren heedayah mude addu'an da zamui Allah sa hakan shi yafi alheri," don moha bece masa komi ba ya tattara kansa ya koma site nasu kuka yakeyi kamar dan yaro zuciyarsa tana masa kona sosai sosai abin tausayi, tun daga ranan abinci ma don moha ya dena ci su daddy sun rasa ya zasui dashy, shi in har bare auri heedayah ba to ya gommaci ya mutu , this is simply bcuz he loves heedayah so dearly***
1 week two days later ana washegary za'a fara events na bikin, su aesha ne, su mummy dasu aaliya da sauran dangin daddy da suke maiduguri duk suka hallaro kano. Rayyan ya fita izuwa jifatu dan siyo ma heedayah wata slipper datake bukata bayan yasiyo yana fitowa suka hadu da don moha bema ganesa ba dan wata erin ramar da don moha yayi kallo daya rayyan ya masa yagano yana cikin matsala babba ma kuwa, karisowa kusa dashy don moha yayi ya mika masa hannu suka gaisa sannan yayi congratulating rayyan, rayyan ya masa godiya, don moha yace "can we talk pls?" Rayyan yace "sure" wata eatery dake kusa da jifatu suka karasa bayan sun zauna rayyan yace "kadan yi sauri i need to get this to heedayah" yana nuna masa ledan. Don moha yace "okay" ciro wayarsa yayi yakai kan hoton little 8 years old heedayah ya mika ma rayyan at first bema gane wace bace se can yace "isn't this heedayah?" Don moha yace "thats her, my first nd last love, the queen of my heart, the person that her love will never be erased frm my heart, ever since da aka haifi heedayah tun ina 7 years old na fara sonta nd nayi promising kaina in ba ita ba i'll nva marry any oda woman. Tho heedayah na sanka i can still feel it tanaso na am sorry inhar abinda na fada ynxu ya bata maka rai"...rayyan dake sauraron don moha kamar radio yayi swiping picture din still hotonta da don moha ne da sch uniform ma ajikinsu tayi dariya sosai ta aza hannunta biyu bisa wuyansa tana tsaye a bayansa. Don moha yace "I know what am about asking you beyi making sense ba at all but inda kaine a situation dina u'll do thesame too, I can't stand by inga heedayah ta auri wani ba ni ba nd nasan bani da power'n da zan iya sata tasoni ko ta aureni kai kadai zaka iya saving life dina sbd in har heedayah bata aureni ba then my life is useless rayyan pls help me, asking of this makes me feel selfish but i have no other choice dan Allah ka taimaka min nasani heedayah na sona kawai she cant admit it to me ne bcuz she's pretending to love you, nanny'nta da bakinta ta gaya min heedayah ta taba promising nata kan she'll marry me what brought about all these misunderstandings was bcuz ta dauka ni naso na kashe ta. Rayyan I know ure a good person baraka iya shiga tsakanin masoya guda biyu ba amman inhar baraka iya granting dina this one favour ba, I can't force you sbd rabuwa da masoyi ba abin wasa bane, it'll be okay by me ni zan hakura tunda dama yazama min dole," wayarsa dake kan table ya dauka "thank you for your time, Allah baku zaman lfy" yana kaiwa nan ya fice zuwa motarsa kansa yasa akan sterring se kuka yakeyi kamar dan yaro rayyan na ganinsa acikin eatery ta window duk seyaji wani iri kuma, "dan tunba yau ba nasan heedayah na son don moha, kamar yadda don moha yace he's affected by her love itama hakan ne she's affected by his love too, but I can't sacrifice heedayah for him, koda bata sona kamar d way she loves him, ni ina sonta I love heedayah so very much I can't bear to lose her," wata zuciyan tace masa "kwata kwata yaushe kuka hadu da heedayah amma kana fadin u can't bear losing her what of wanda ya fara sonta tun da aka haifeta fa?" Rayyan yace "kai noo saidai don moha ya hakura I love my princess soo much I cant give her to u don moha am sorry" yana kaiwa nan shima ya fice. Yana isa gda ya haura dakin heedayah daidai lokacin aka gama zana mata lallenta wanda ya bala'in yin kyau, mummy data ga shigan rayyan dakin tace "rayyan bawai an hana ganin amarya ba?" Ko jinta beyi ba ya sa lock a kofar dakin daga shi se heedayah se me lalle, heedayah tace "my king kasamu slipper din?" Murmushi ya mata "sure my princess" ya nufo kanta ya ajiye mata ledan wani erin kallo yake mata kamar wanda yafara ganinta yau, hannunta me lalle tasa masa akan hanci kai ya kada a gigice tsabagen tunani yatafi da hankalins, hannu yasa yagoge amman ina gun har yayi baqi heedayah tace "tunanin meh kake haka my king" "I can't bear losing you" ya fadi a hnkl, heedayah tace "eh? what?" Kafin yyi mgn tace

HEEDAYAH!

89
written by miemie

"Awwwn ure looking more cute da black lalle akan nose naka," tana murmushi, murmushin shima yamata tace "I love you my king i've been asking you ina zamuje muyi honeymoon namu kace min its a suprise so as ur wife to be I demand an answer ynxu tell me pls pls pls," rayyan kuwa in akoi abinda yakeso befi yaga heedayah tana abu kamar baby ba yace "okay okay a Dubai nakeso muje," heedayah ta bude hannu zatayi hugging nasa yace "wait wait! Lallen hannunki fa," tace "argh! but I still need the hug" murmushi yamata yabata light hug sannan yaciro wata sarka a aljihunsa heedayah tace "wow a necklace!" Rayyan yace "nd its for you," heedayah tace "really? Kullum de kana cikin bani gifts," rayyan yace "yes bcuz I love you but this one is different frm the rest," cikin rashin fahimta heedayah tace "what difference?" Bayan ya sa mata sarkan yace "this is to let u know that I'll miss you," heedayah tace "miss me kuma?" Ya bude baki zeyi mgn mummy tazo tana bubbuga kofar "wlh rayyan zamu gamu dakai, ynzu ace ba a son a sake ganin amrya se ranan biki amman kai kashiga, ohh! Nan da yan kwanaki za'a daura muku aure se ku cinye kanku," dariya sosai rayyan da heedayah sukeyi bayan ya bata peck a goshi yace "i'll see you tomorrow," heedayah tace "take care" sannan ya budo kofar mummy ta maresa a hannu "oya to ur room!" A daren ranan kwana rayyan yayi yana nazarin abinda don moha ya gaya masa in har beyi koki gameda abinda don moha ya gaya masa ba yazama selfish knan***
Washegary da dare around 9:00PM aka fara pre wedding dinner heedayah kam ansha kyau kamar ba gobe haka rayyan dinta ma kasancewar kayanta white ne seda kwalya black shikuma yasa bakar shadda, biki ne na kece raini su aesha se shan selfie akeyi da amarya da ango, don moha kuwa na dakinsa takaicin dunia sun masa yawa. Se 12:20AM aka rufe taro ba abinda rayyan yake se kallon heedayah. The nxt day akayi kamu shima yayi sosai farar ashoke heedayah tasa ya bala'in mata kyau, the nxt day akayi walima da dare kuma akayi mother's eve shima ya hade sosai, ansha budiri kam kamar ba gobe biki ne na 'yan manya, daddy ya kashe kudi sosai a bikin one nd only daughter'nsa haka mummy ma. A yammacin ranan kasancewar ango bai attendn walimah rayyan ya fita ko ina yaje oho se can dare ya dawo ya shirya sukaje mother's eve kallon dayake ma heedayah yaukam yafi na kullum har sanda ta far tsarguwa. Bayan an watse taro har sun dawo gda can cikin dare around 3:15AM rayyan yama heedayah waya akan tasan duk yadda zatayi tafito yana son mta mgn, satar idan mummy tayi tafito ta samesa a dakinsa, tare da fadin "lfya my ango?" Murmushi yamata kawai ya kamota yayi hugging nata sam yaki saketa heedayah kuwa ta rasa why yake acting strange haka bayan daya sako ta ne tace "my ango ya haka? Tun ranan naga yanayinka ya canza ko ure not happy to be my ango ne?" Hannunsa ya aza bisa lips nata "shh dont talk like that I can't tell you how happy i am right now" hannayenta duka biyu ya dago yayi kissing nasu one after the other "my princess promise me one thing," heedayah tace "anything!" Rayyan yace "no matter what the outcome might be tomorrow know that I love you okay?" Cikin rashin fahimta heedayah tace "wani outcome kuma my king, what are u talking about?" Rayyan yace "nide just promise me," heedayah tace "anythng for you I promise!" Tana masa murmushi, haka rayyan yata mata wasu erin suratan da baganesu takeyi ba sun kusan awa daya a dakinsa sannan tace "i have to go kar mummy tafara nema na" goodnight peck ya mata a goshi har ta kai bakin kofa yace wait ya karisa gunta yayi hugging nata tare da cemata "I love you very much heedayah," "I love you too" tace masa sannan ya bude mata kofar yana kallonta har sanda ta shige daki yadawo cikin dakinsa a hankali ya soma zubda hawaye...
Washegary ranan da za'a daura aure knan around karfe 9:45AM su daddy duk sun kama hanyan zuwa masallaci saide heedayah ta waiga ta waiga bataga rayyan dinta ba, mummy dake geferta ta tambaya, "mummy ina rayyan?" Mummy tace "ai tun daxu ya wuce shikam da frnds nasa" heedayah tace "ohh okay toh." A wata babbar masallacin juma'a aka daura auren MUHAMMAD ISMAIL DA HEEDAYAH S.U AKAN SADAKI N200,000. Bayan tofa fatiha da aka gama aka dawo gda irin masu buga kalangun gargajiyan nan duk mummy ta hanasu shiga ciki dan kar da dogon bakinsu su kira sunan angonta as muhammad instead of rayyan. Heedayah na zaune a daki ita dasu aesha da sauran cousins nata se tsokanarta suke adole amarya daga bisani ta mike zuwa kan dressing mirror tana ganin fuskarta kawai se idanta yakai kan wata paper wanda aka ninke sa kamar wasiqa hannu ta miqa ta daga wata zobe ce tafado daga ciki kallon zoben sosai tayi "tabbas wannan zoben dana bama king dina ne ko ya manta ne jiya yabari anan?" Tana cikin wannan mgn taga RAYYAN a rubuce ajikin paper'n da hanzari ta bude tafara karantawa kamar haka;
My dearest princess, I hope as how you are happy right now with a smile on ur face, that smile will still remain even after reading this letter. Inason ki maida hankalinki sosai ki saurari abinda nakeson fada miki nd kisani nayi hakan ne bcuz I love you so very much, aynxu haka ke matar aure ce amman saidai ba mata ta ba, matar muhammad ce ke dashi aka daura aurenki daxu nikuma in Allah ya yarda ina Edo state ynxu." Noo noo" heedayah take fadi take idanunta suka cike da hawaye tafara zubda hawaye kamar lalacaccen famfo... "Ever since frm the day nayi setting eyes dina akanki, love at first sight was the thing nayi experiencing, I want you to be urself heedayah kisani I've loved you nd I'll forever love you, you'll forever be the princess of my heart. I've learnt that don moha na sonki although nima ina sonki but nasan not as how don moha does tun kina 'yar qaramarki don moha yakeson ki, tun baki san meh love ba, bekamata in just a blink of an eye inyi taking naki away frm him ba, don moha na sonki sosai sosai I can feel it he will make a wonderful husband and a great father to your kids, attached to this letter akoi ring din da kka taba bani inason kiba ma don moha ring din pls am asking of this favour frm you, in kka min hka kin gama min komi my princess, nd dinner'n da za'ayi yau da dare I want u to participate, dont think that nayi hakan ne bcuz I don't love you noo nayi hakan ne bcuz dis is how much I love you, you'll be happy with me but ure life will be even more happier with don moha, after bikinku inason kuje kuyi honeymoon naku da don moha a Dubai, my princess in kka min haka kin gama min komi, Allah bada zaman lfya yakuma bada zuriah dayyiba. From your brother rayyan."
Su aesha da suke harkokin gabansu kawai sukaji karar fadin heedayah a kasa da gudu sukayi kanta wasu suna a nemo ruwa wasu suna a kira mummy...

HEEDAYAH!

90
written by miemie

Aesha dake ta tapping din heedayah tana kiran sunanta amman sam heedayah sunan rayyan! rayyan! kawai take ta ambato, nan wanda suka kira mummy suka shigo dakin a tare mummy ta amshe heedayah gun aesha, "heedayah my princess take it easy pls nasan exactly how ure feeling now but hkr zakiyi kinji?" Da kyar suka daga heedayah suka kwantar da ita kan gado kamar me aljanu ta miqe tasa gudu mummy na binta tana "ku kama ta! me gadi ka rufe gate! karku bari tafita!" Heedayah takai daidai bakin gate me gadi ya datse kwado jijjiga kofar takeyi kamar zata ballasa tana ihu tana kiran sunan rayyan, mutane se raba ido sukeyi ya amarya haka? Mummy ce ta karasa to dafa kafadar heedayah, hannun mummy ta cire daga kan kafadar ta tare da fadin "dont touch me mummy," mummy da bata taba jin wannan mgn daga bakin heedayah ba tace "my princess kishigo ciki bakiga kowa yana kallonki ba? I'll explain everythng to you" da kyar da gardama ta iya taja heedayah izuwa dakinta tasa lock sannan ta dawo ta zauna kusa da heedayah da har ynxu hawaye shar shar suke zuba a fuskarta mummy tafara;
"yau da safe na ajiye miki letter'n da rayyan ya bani jiya. Jiya lokacin da mukeyin mother's eve rayyan yaje yayi booking emergency flight bayan ya dawo ya sameni a daki yake gaya mun yadda sukayi da muhammad, nd sbd yadda yakeson ki ya hakura dake gara muhammad ya aureki tunda tun kina 'yar qarama muhammad yake sonki he's sure muhammad ze kula dake maybe fiye da shi yadda rayyan dinma ze kula dake wanda both you nd I know that is true, ban taba gaya miki bane heedayah but tun kina karama nagane muhammad nasonki dalilin dayasa ban hana rayyan yin abinda yayi niya ba knan, daddy naje nasamu na irga masa komi a inda yakira alhj ismail ya sanardashy, halin da muhammad yakeciki as how alhj ismail ya fada mana shi yasake bamu karfin guiwan hadaku aure dashy dan ko abinci yabar ci, a ynxu haka muhammad shima besan an daura muku aure ba, sbd da haka ki rungumi qaddara heedayah am very sure muhammad ze kula dake ya rike amana." Shiru ne yabiyo bayan mgn mummy dan kwata kwata heedayah batada niyan yin mgn, se hawaye take har ynxu ba brake, mummy tana jijiqata "my princess pls say somethng pls kinji? Kinsan akoi dinner yau rayyan ya bukaceni da in rokeki ki yarda kije wannan dinner, in barakije danni ba kodan rayyan kije kinji?" Still nan ma bata ce komi ba, dan haka mummy kawai ta fice kan zata dawo anjima in heedayah tadan sauka. Tana fita heedayah ta soma rusa sabuwar kuka, kuka takeyi sosai kamar wadda takeson fidda ranta ita ynxu bama rabuwanta da rayyan ba, taya mummy zata boye mata wannan muhimmiyar al'amarin harda mata karya yau da safe da ta tambayeta ina rayyan, how can she? Tace "my life is useless ynxu tunda rayyan is not my groom what do I have to live for? For don moha? Probably Nothing," kofar ta tashy zata rufe daidai nan aesha takeson sa kai ta shiga dakin da sauri heedayah ta rufe kofar tare da sa masa lock. Aysha tafara buga kofar "heedayah me kke sonyi? Ki bude kofar kinji? Yi hkr dan Allah..." tana ta suratai amman sam heedayah is not willing to open the door dagudu taje ta nemi mummy ta fada mata suka taho tare se buga kofar sukeyi heedayah dake cikin dakin side drawers take budewa one by one da sauri tana neman wuka, can cikin wata drawer tasamu wata karamar wuqan cutting fruits daidai kan radial artery dake hannunta tasa tafara yankawa, take jini yafara bulbula...lips nata ta cize dan wani erin zafin dayake mata.
Batayi nisa da fara yanke kanta ba aka tunkudo kofar daga waje ihu mumny ta tsala "HEEDAYAH! da hankalinki?" Da gudu ta karisa ta kwace wukan dan haushi bata san sanda ta tsinke heedayah da mari ba tas! Kukeji, "kashe kanki kkesonyi dan kawai baki auri rayyan ba?" this is the first time ta taba marin heedayah, tuni jiri ya kwashe ta tace, "ba kawai bane mummy baraki taba ganewa" tana mgnan tana sumbulewa qasa har tafadi a sume. Kuka mummy keyi wayarta tasa nanny ta miko mata ta kira family dr sannan ta kira dady ta gaya masa tare daddy da dr suka iso daddy shima duk ya kidime, dan har ynxu hannun heedayah be bar bulbulan jini ba nan da nan dr yasamu yayi stopping bleading din yayi treating yankan sannan ya mata alluran kashe zafi tare da rubuta mata wasu antibiotics.
Mummy kam se kuka, daddy na lalashinta seda heedayah tayi baccin 2 good hours sannan taf farka motsa kafafunta ta soma daidai nan idanun mummy suka kai gun ta, ta taso daga kan kujerar da take kai ta nufo gun heedayah, take ta kau da kanta zuwa other direction din.
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).