HEEDAYAH!
8
written by miemie
*yau kamar kullum nanny ta shirya heedayah sch mumy tayi dropping nata, tun daga ranan basu kuma samin misunderstanding da baby ba sometimes ma tare da don moha suke zuwa class na heedayah suyi spendn break tare, acikin kankanin lokaci baby ta shaku da heedayah har class nasu sumtimes heedayah ma na zuwa in su basu samu zuwa mata ba, hakan ba karamin dadi yakeyi wa don moha ba.
A gda kuwa alhj s.u na zaune a garden shi kadai dake mumy ta tafi asibiti alhj lawal ya shigo ya tashy yayi welcoming nasa suka koma garden yasa aka kawo masa snacks da drinks suka gaggaisa se tattaunawa suke akan rayuwa. Alhj lawal yace "dan uwa naji wai ka bude gun saida mota dakuma wata company a abuja, toh a gaskia ina mai tayaka farinciki Allah yakaro arziki me albarka" alhj s.u yaji dadi sosai ya amsa da "ameen" sekuma alhj lawal yayi shiru hakan yasa alhj s.u tambayarsa ko lafya yace "ahh ba komai kawai mutuwa na tuna, alhj s.u in a yau zan fadi in mutu ka kula min da iyali da sana'a sbda kai kadai nayi trusting a duniyannan nd no one else not even my blood brothers" alhj s.u yace "haba! Dan uwa kabar zancen mutuwa in shaa Allah ma baraka mutu ynxu ba" alhj lawal yayi murmushi sannan yace "ai ba wanda yasan ran mutuwan sa balle na wani, tsab zan iya fadi in mutu a yau nide abu daya nike bukata a gun ka, kawai ka rike min amanar company na da iyali na, kamin haka toh ka gama min komi. Ni na manta nema da na taho da files na company na inyi signing maka in case..." Kafin ya karasa alhj s.u yayi interrupting nasa by saying "alhj lawal dan Allah kabar maganannan, bara fa ka mutu ba inshaa Allah muna nan har auran yaran mu" alhj lawal yace "toh shknan dan uwa naga kamar bakason rike min amana ne, nide a iyaka zama na dakai na so ka tsakani da Allah koda ayau ace kafadi ka mutu wlh zan kula maka da du abinda katafi kabary, why is it hard for you to say zaka min haka nima" alhj s.u ya taso ya dafa sa sannan yace "ko kadan dan uwa kamar yadda kace zaman tsakani da Allah kakeyi dani nd ure willing to take care of my family nd all koda bayan rai na to wlh nima haka ne, zan rike maka amanan duk abinda kabary kawai de kabar fadin zaka mutu dinnan kana sani feeling uncomfortable, u have my words" yagama maganan da murmushi alhj lawal yace "naji dadin maganan nan naka dan uwa allah bar mu tare" alhj s.u yace "ameen" haka de suka ta hiran rayuwar mu na yau da kullum se dawowan heedayah alhj lawal ya ce ze tafi alhj s.u ya rakasa. Yana isa gda ya wuce dakinsa wata dariyan mugunta ya saki, "Hahahahahah alhj s.u knan my plans have just begun arzikin ka seya dawo hannu na mark my words" ya dage gira daya***
Heedayah na zaune akan study table nata tana assignmnt nata nanny ta shigo da telephone tace "gashy don moha nason miki mgn" ba tare da bata lokaci ba heedayah ta amsa tasa akunne "hello" don moha yace "my baby ya kke?" Ta amsa da "lfya" a takaice dake nanny na tsaye a kanta don moha yace "what are you doing now?" Tace "assignmnt bah, I got to go" "don moha yace wait pls" ina heedayah ta riga tayi cutting off call din a hankali yace "I love you my heedayah" sannan ya ajiye wayar. Nanny ta tsaya kallonta, heedayah tace "any prob?" Nanny tace "walakanci ko?" Heedayah ta yakune fuska sannan tace "nikam nanny dan Allah kibarni inyi assignment dina, am giving him all i can, remember am just 8 yeara old, bansan me love ba, i dont know how it feels amman baki appreciating dina, am angry at you" nanny ta karaso inda take ta kwantar da heedayah a jikinta tana shafa gashin kanta "nanny is sorry my heedayah, ure right ure still young nikuma ina saki yin abinda be dace kiyi ba starting today zan ma don moha magna yadena takura miki u need some space" heedayah ta dago kanta tace "ko kadan nanny tho bansan me love ba but i want to be with don moha" nanny tace "i love you my heedayah yi ki gaka assignmnt naki kiyi sallah in miki wanka ki kwanta ko?" Heedayah ta gyada kai sannan tce "amman ni zanyi da kaina kinga fa a class namu yawanci su sukeyi ma kansu wanka" nanny tace "kar mu ma fara kinsan mumy tace sekin kai 9 zaki fara wanka da kanki" cikin shakwaba heedayah tace "ni o'o ni zanyi da kaina" nanny tace "shknan tunda kince haka ina wayata in kira don moha in gaya masa har ynxu ana miki wanka" ta kama hanyan fita da saurin gaske heedayah ta sha gabanta "o'o kar ki fada masa Allah zemin dariya nayarda ke zakimin wankan" nanny tayi murmushi sannan tace "yawwa jeki gama homework naki toh" ta fice heedayah takoma kan study table nata ta cigaba da assignment nata tanagamawa tayi sallah nanny tamata wanka ta sauka dining taje taci abinci ta wuce dakinsu mumy ta dale gado sukata hira da mumy da daddy har bacci yayi awon gaba da ita
HEEDAYAH!
9
written by miemie
Yau ma kamar kullum nanny ta shirya heedayah sch. Around 9:00AM daddy ya tashy ba lafiya da kyar yayi wanka yayi breakfast daga yace ze dauki abu se hannunsa ya kasa haka in yace zeyi magna ma da kyar, daga yace zeyi tafya se ya fadi, du nanny ta kidime ta rasa me ke mata dadi, mumy ta kira a waya ta gaya mata halin da ake ciki a gigice tabar du abinda takeyi ta karaso gdah tana ganin dady idanunta suka cike da hawaye ta karasa kansa "habibi me ya sameka? U wer perfectly fine just yestarday, tell me dan Allah whats wrong? Nanny kin basa wani abu ne?" Da kyar daddy ke magana yace "bar kuka dan Allah am gonna be fi..n..e" ya gwada share mata hawaye amman ina ya kasa hannunsa is as good as useless mumy se kuka da kyar ta kira family doctor ya taho within 30mins dan hold ups, yayi duk wani possible tests dayakamata yayi amman ina yakasa figuring out meke damun daddy, nan fa hankalin mumy ya kuma tashy ba abinda takeyi se kuka nanny na lalashinta da kyar tayi shiru tacewa dr yusuf "dr me kake nufi da bakasan me yake damun mijina ba? Kana nufin baka iya aikinka bane ko me?" Dr yusuf yace "not at all ma'am nayi duk abinda yakamata inyi theres only one possible answer" mumy tace "tell me mene?" Dr yusuf ya mata body signal da alama ta biyi shi waje baison dady yaji, sun kama hanyan fita knan daddy yace "my de..a..r" sekuma ya shiga tari mumy tayi kansa "try not to talk pls, sorry ina zuwa ynxunnan" ta mike daddy ya kamo hannunta da kyar ya iya fadin "ya gaya miki maganan anan" idan mumy cike da hawaye tace "dr yuauf say it to both of us" ba tare da ta kalli direction nasa ba, hakan ya sa dr yusuf ya karaso cikin dakin yace "alhj am not so sure amman inaga kamar ALS DISEASE ke kokarin kama ka, wannan abu yafi karfi na you have to see someone better than me dan ni karatu na bekai can ba" salatin mummy kawai akeji a dakin "me kuma ALS disease? tell me dr yusuf" dr yusuf yace "am not so sure ma'am sesa nace kuje kuga consultant yamuku all possible tests daya kamata" mummy ta goge hawayen fuskarta sannan tace "yes for sure zamuje amman before then ka gaya mun me wannan ALS DISEASE?" Dr yusuf ya ja numfashi sannan yace "shi wannan ALS DISEASE ko AMYOTROPHIC LATERAL SCLEROSIS progressive disease ne dake affecting nerve cells, progressively yake affecting nerve cells na brain dana spinal chord in har baayi immediate treatment ba haka zeta cinye nerve cells har ya kaiga rashin mgana, ko cin abinci ko dauka da ajiye abu kokuma numfashi and other voluntary movements. Also, yana sa fadi sumtimes kamar in mutum yana tafiya kawai seya fadi shi kadansa. Shi wannan cuta maybe inherited wani sa'in kuma Allah na jarabtan bawa ne dashy base gado ba, ba a cika samun sa ta nan sosai ba anfi samunsa ta can gun turawa kuma... " sekuma yayi shiru yakasa magana idanun mummy cike da hawaye saura suna ambaliya a fuskarta tace "kuma meh? dr karkaji komi cuta ai ba mutuwa bace tell us pls" dr yusuf ya cigaba "in har ya tabbata ajikin mutum, bai wuce 20yrs ze mutu that is if beci jikinsa ba knan, some die in 3-5years time inkuma yaci jiki sosai dole a nema ma mutumin ventilatory support dan taya sa numfashi. Abun dana sani game da ALS disease knan" Allah ba alhj lafya mumy tace "ameen dr nagode, so kanaga akoi consultant da ze iya mana wannan tests din ya tabbatar mana da komi a asibitinku?" Dr yusuf ya gyada kai da alamun eh mumy tace toh masha Allah na gode ta tashi ta dauko jakarta ta ciro card nata ta mika masa "pls ka ce ya kirani" dr yusuf ya amsa ya fice mumy ta bi bayansa toilet na dayan dakin ta nufa ta rufe kanta tasha kuka kamar ba gobe tunanin rayuwa ba habibinta kawai takeyi ga yadda heedayah keson daddyn'ta da kyar ta wanke face nata ta fito ta koma dakin daddy ta samesa har yayi bacci dake dr yusuf ya masa allura ta kwanta a gefensa tana tunani har bacci yayi awon gaba da ita***lokacin tashinsu heedayah nayi driver yaje ya dauko ta, suna isa gda ta wuce dakinta ta canza kaya ta sauko taci abinci sannan take tambayar nanny "daddy yana gda ko ya tafi?" Nanny tace "daddy'n ki na nan heedayah saide baida lafya" heedayah ta mike tsaye "daddy baida lfya? Nanny tell me ure joking" kafin taji amsar nanny ta ruga a guje ta nufa dakin daddy tagansa kwance dashy da mumy ta karasa kansu tana jijiga shi "daddy nasan bacci kawai kakeyi amman lafyarka kalau ko? Wasa nanny takemin nasani" mummy ce ta jiyo ta ta tashy, "my princess yaushe kka dawo? Daddy na bacci barshi kinji" heedayah ta fashe dawata erin matsanancin kuka "mumy tell me daddy is not sick antyn mu ta gaya mana sickness often leads to death" banason daddy na ya mutu...
HEEDAYAH!
10
written by miemie
Ta rungumeshi tana kuka, mummy bata san sanda ta fara kukan ba itama tayi hugging nasu all tace "daddy'nki bare mutu ba kinji heedayah ciwon kai ne kawai ke damunsa yasha magani yana bacci anjima kadan ze tashy so worry not, okay?" Heedayah ta gyada mata kai mumy tace "yawwa my princess..." wayar mumy ce tayi kara tana dubawa taga new number jikinta yabata dr dinda dr yusuf keson hadasu ne nd bata san picking call din a gaban heedayah seta wayince tace "jeki kwanta ki huta kinji?" Heedayah batayi gardama ba ta tashy ta fice ta jawo kofa amman seta ki tafiya ta labe tana sauraran mumy ta daga wayan "hello" meshi yace "dr ahmad speaking" suka gaisa da mumy yake gayamata test din kawai ze iya yi ya tabbatar musu ko daddy nada ALS disease ko baida amman bare iya treating nasa ba dole suje abroad abasa immediate care, mumy ta share kwallan dake kokarin fito mata sannan tace "dr pls is the disease a deadly one? Ba a iya surviving nasa?" Dr yace "it depends amman gaskia its rare" mumy tace "toh thank you yaushe zamuzo?" Dr ya gayamata suzo gbe kamar war haka tayi godiya sannan ta katse wayar. Heedayah ta ruga upstairs da gudu tana isa dakinta ta fada kan gado kuka takeyi sosai har nanny tashigo bata sani ba, nanny tayi kanta "mumy's princess why are you crying?" Heedayah ta dago jajayen idanunta tace "daddy bai da lfya nanny, naji mumy na waya da wani dr tana tambayansa ko ciwon is deadly, pls ki fada mun gaskia whats going on? Daddy na ze mutu ne? Pls nanny" ta kuma fashewa dawani erin kuka nanny ta jawota jiki tana jijikata "shh daddy'nki bare mutu ba in shaa Allah heedayah just kisa sa cikin addu'a kinji?" Heedayah ta gyada mata kai nanny tace "yawwa yanxu kwanta kiyi bacci" tayi mata kiss a goshi ta jawo bargo ta rufeta dashy sannan ta fice. Tana sauka suka ci karo da mummy, nanny tace "ya jikin daddyn heedayah?" Mumy tace "yana bacci, ina heedayah? Tana dakinta ne?" Nanny tace "eh ynxu na kwantar da ita se kuka takeyi wai daddynta ze mutu that ta jiki a waya kina fada" mummy ta ma rasa na cewa hawaye ne kawai suka fara bin fuskarta "nanny tell me pls me zanyi? Wannan wace irin rashin lfya ne nanny? Just yestarday he was fine yaukuma ya tashy da rashin lfya" ta goge hawayenta "innalillahi!" Nanny ta rungumota tana bata hkuri "addu'a kawai zamu sa sa in shaa Allah ze sami sauki".***
Kafin ace meh rashin lafyan alhj s.u ya zagaya ko ina, alhj lawal na ji ya gode wa Allah now is the right time to make my move ya dau wayarsa ya kira alhj ismail suka gaisa yake gaya masa "ai shi ynxu ma zasa gdan yaje ya duba dan uwansa" alhj lawal yace "nima zanje amman se anjima, dama in tuna maka ne game da zancen dana maka ranan now is the right time to make our move" alhj ismail ya daka masa tsawa "dakata! Ina nan akan bakata,Allah shryeka amman nikam de baran taba cin amanan dan uwana ba" ya katse wayar yana mamakin wannan dan uwan nasa, alhj lawal ya buga hannunsa kan table "i'll do what ever it takes in karkato da 'yar kwakwalluwarka ka amince da wannan shawarata" nan ya dauko wayarsa ya kira wani mutum da gani erin malaman nan ne wanda ake kira da boka "hello malam, magani nikeso ka bani" karar wata erin mahaukaciyar dariya na jiyo sannan yace "lawal! Wani erin magani?" Alhj lawal yamasa bayanin komi at last malamin yace "toh ai wannan aiki ce me sauki, kana sa masa maganin nan acikin ruwa sau 3 yasha shknan kai zakana commanding nasa" alhj lawal yace "toh toh nagode" malamin yace "ba godiya ba tukun! Kudi na zaka bani N100,000" alhj lawal yace "ba matsala so zan shigo anjima" ya katse wayar, murmushin mugunta yake sakar wa shi kadai acikin dakin***
Around 4:10PM daddy ya tashy mumy tayi assisting nasa yayi sallan azahar da la'asar duka sannan yaci abinci, heedayah yafara tambaya, mumy tace "tana bacci" karan door bell suka jiyo nanny taje ta bude alhj ismail da family'nsa ne mumy tayi welcoming nasu, duk suka gaishe da daddy da jiki, don moha yake tambayar mumy "ina heedayah?" mumy tace "tana bacci" haka har suka tafi heedayah bata tashy ba. Can to 6 ta tashy tayi brushing tayi sallan azahar da la'asar itan da bata san yin sallah amman yau harda biyan bashi tayi wa dady'nta addu'a sosai sannan ta sauka kasa taci abinci ta wuce dakinsu daddy dagudu ta karasa gunsa tayi hugging nasa yashafa kanta "my princess" tadago kanta tace "daddy lafyarka kalau ko?" Daddy yamata murmushi "i am fine my baby" itama tamasa murmushin ai yau auntinmu tace "ingaishe mata ku, next week open day, zakuzo min both of you ko daddy?" Daddy yace "sure my princess, nida mummy zamuje miki" haka sukata hira mumy taga heedayah is not ready to keep quiet da wayo ta korata dakinta, karan door bell suka jiyo heedayah ta karasa ta bude alhj lawal ne shima da family'nsa ta koma daki takira mumy, mumy ta musu sannu dazuwa ta shiga dasu daki dake daddy ya kwanta suka gaishe sa da jiki aka dan taba hira alhj lawal yace zasu tafi amman gobe in shaa Allah ze dawo mumy tayi godiya ta yi musu rakiya. Tana dawowa ta shirya bacci can around 12:00AM na dare mumy ta farka tafito parlour se zuba kuka takeyi hannu kawai taji a bayanta a rikice ta juya taga heedayah "mumy mesa kke kuka?" Mummy ta sharre hawayenta "ba kuka nakeyi ba my princess abu ne yashiga min ido" heedayah tayi hugging mummy***Alhj lawal na tsaye a parlourn gdansa se safa da marwa yakeyi tunanin ya zeyi yayi gaining trust na alhj s.u yake can wata dabara tazo masa ya tafe hannu tare da fadin "Allah kaimu gobe" ni miemie nace ko me wannan mugun mutumin ke shirin yi gobe oho
HEEDAYAH!
11
written by miemie
Yau da safe nanny ta shirya heedayah sch da kyar dan har kuka take ita barata sch ba yau zata zauna da daddy'nta a gda sanda daddy yasa baki sannan ta yarda aka kaita. Tare suka isa dasu don moha da sauri yakarasa ya sameta ta gaishe shi yake tambayar ta ya jikin daddy takasa cewa komi class nasu heedayah suka wuce sanda akayi ringing bell na 8:00AM sannan ya wuce class nasa. Around 9:30AM su mummy suka shirya zuwa asibiti inda suka hadu da dr ahmad suka gaisa sannan yafara aikin tests din da yakamata yayi within an hour ya gama ya mika wa mumy, hannunta na kyarma ta amsa ta bude taga positive atake idanunta suka cike da hawaye amman tayi kokarin hadiye kukanta dan tasan du tashin hankalin data ke ciki bekai wanda daddy ke ciki ba, daddy yace "positive ko?" Mumy ta gyada masa kai ta riko hannunsa tare da fada masa "we are in this together" dr ahmad yayi gyaran murya yace "in shaa Allah karku damu ciwon beci jikinsa ba, yana 1st stage ne so there is possibility he can survive it, zan muku recomending seatle grace hospital dake washington, Allah bada lafya" mumy tace "ameen mun gode se anjima" da kyar daddy ya mike suka fice driver ya dawo dasu gda, dady na zaune a parlour mumy na gefensa tana waya da PA'n dady kan yazo ya karbi passports nasu yamusu booking flight ya amsa da "yes ma'am lafya?" Mumy tace "in kazo zaka sani" ta katse wayar. Door bell aka danna nanny ta je ta bude alhj lawal ne ya karaso suka gaggaisa yake gaya wa daddy kan jiya wani abokinsa na san siyan mota TUNDRA so ya kaisa gun motor sale na daddy nd yabasa acct number'n daddy ma sauran su jira alert kawai, mumy tayi godiya sosai haka daddy ma, bayan like 15mins alert yashigo wayan daddy, mummy na dubawa taga har abokin nasa ya turo kudin 9 million. Daddy yace "a gaskia samin frnd kamar ka a zamani irin tamu ta ynxu da wahala u've proven urself that zaka iya kula min da business koda bayan raina nd for that nagode" alhj lawal na washe baki yace "ahh bakomai"can azuciya kuwa cewa yake "keep on trusting me zan dau asaran dayafi 9mil dan arzikin ka yazamo nawa, bawani abokina da ya siya motarka ni na siya" mummy ce tayi breaking mai tunani "bari nanny ta kawo maka abinci mana" yace "a'a am full" daddy yace "inda zaka iya min wannan abu dan uwa" alhj lawal yace "mefa alhj? Zan ma komai musamman a condition da kake ciki ma ynxu" daddy yce "akoi wani meeting da zaayi ne daman a abuja, colours industry zasu saida 3% na shares nasu..." Ya tsaya yin tari sannan ya cigaba "naso zuwa amman a gaskia hakan ba me yuwa bane dan nan da 4-5 days zani washington a dubani a can" alhj lawal yace "ayya Allah bada lafya alhj ,in shaa Allah i'll try my best zan maka komi mude Allah baka lafya" alhj s.u yace "toh nagode Allah biyaka, meeting din will be held in 3 days time so prepare pls" alhj lawal yace ba matsala alhj anything for you, am very grateful daka bani wannan dama and in shaa Allah bazan baka kunya ba" alhj s.u yace "ba komi nine da godiya" hira kadan suka taba alhj lawal yace zaya tafi mumy ta rakasa sannan ta dawo ciki. "Gaskia wannan abokinka nada kirki sosai habibi Allah kawo dalili ka masa wata alherin kaima" dady yace "ameen" karan door bell again suka jiyo nanny ta bude PA'n daddy ne ya gaishesu cikin girmamawa yakuma tambayi ya jikin daddy? mumy ta amsa da "da sauki" takuma masa bayanin komi aciki harda dalilin su na zuwa washington din, shide addu'a kawai yatayi Allah bama daddy lfya.
Fitan alhj lawal ya zarce gdan alhj ismail ya wuce garden ya tura me gadi daya ma alhj magana, kafin alhj ismail ya fito alhj lawal ya barbada maganin da malaminsa ya basa acikin wata jug daya ga ruwa a ciki, bayan 7mins alhj ismail ya karaso da fuskarsa a daure ya zauna alhj lawal ya gaishe sa ya amsa tare da cewa "alhj lawal in har kasan maganan banzan da kake min for the past days kazo yi dan Allah kayi hakuri katafi, dan baraka taba samun hadin kai a guna ba" alhj lawal yayi murmushi sannan yace "ko kadan dan uwa Allah ya ganar dani nima, in shaa Allah baruwa da arzikin alhj s.u ynxu ma daga gdansa nike, nanemi gafararsa kuma ya yafe min har yace ma zanyi representing nasa a wani meeting da za'ayi a abuja nanda kwana uku" alhj ismail yace "dakata karka raija min wayo mana" alhj lawal yace "wallahi ba karya ba ai baran rantse akan karya ba in kuma baka yarda ba gashi kirasa kaji, i know it'll be difficult for u to believe me but either ka yarda ko ba ka yarda ba nagano gaskia nima ynxu arziki nufin Allah ne kamar yadda kafadi min a baya, daman sharrin shedan ne ba komi ba" ya zuba musu ruwan dake cikin jug din acikin glass cups dake gabansa ya mika wa alhj ismail sannan yace "toast!" Alhj ismail kallonsa kawai yake amman be yarda dashy ba suka dan buga glass na ruwan sannan suka danyi sipping kadan, alhj lawal kam be sha ba dake yasan meyasa a ciki. Alhj ismail yace "in har abinda kafada min gaskia ne to nagode wa Allah da ya amsa addu'ata yasa ka gano gaskia, Allah yabamu sa'an cin nasara akan shedan" alhj lawal yace ameen, a zuciyarshi kuwa dariyan mugunta kawai yakeyi***
Heedayah na dawowa from sch ta wuce dakin dady yamata sannu dazuwa tabasa peck a goshi sannan ta tambayesa "daddy ya jiki?" Ya amsa da "da sauki my princess, ure prayers keep me moving, nogode ko?"tayi masa murmushi sannan tayi hugging mumy ta wuce dakinta, tana fita mumy ta fashe da kuka, dady yace "mekuma na kuka my dear? Kukanki na sake kashe min guiwa kince we are in this together but is like ure giving up already" mumy tace "ko kadan habibi wallah heedayah kawai ke ban tausayi zamui tafiya in 4-5 days time and open day nasu monday kasan bareyi muje ba, nd heedayah will never understand koda she'll ma, bansan taya zan fara fada mata ba" takuma fashewa da wata erin kuka daddy yace come here tatashy ta karaso gunsa yayi hugging nata tareda cewa "everything will be fine in shaa Allah"
HEEDAYAH!
12
written by miemie
Yau ma kamar kullum nanny ta shirya heedayah sch, tare suka iso da baby suka wuce class nasu heedayah take tambayar heedayah ya jikin dady'nta? Heedayah ta amsa "da sauki" amman kwata kwata kamar ba heedayah me surutun da baby tasani ba, she's so quiet nd calm ynxu don moha na isowa shima yawuce class nasu heedayan suka gaisa se 8:00AM suka bar class nasu heedayah. Auntinsu ma tayi noticing, heedayah bata concentrating sosai a class a koda yaushe cikin tunani take bata masan me ake koya musu ba, hakan kuwa ba karamin ta mata da hankali yake ba, during break ta kira heedayah tata gaya mata kalamu masu dadi masu kwantar da hankali kan kar ta damu her dad is gonna be fine, heedayah tadanji dadi, ahaka har aka tashy heedayah bata wani yi surutun kirki ba, mal idi yazo ya dauketa a mota ma se surutu yake mata ita kuwa amsarta daga "eh" se "a'a" ahaka har suka isa gda ta wuce dakin dady kamar jiya tabasa peck a goshi tayi hugging mumy sannan ta wuce dakinta ta canza kaya ta sauka kasa taci abinci takuma haurawa sama dakinta dan yin home work nata, tana cikin yi mumy tayi knockin sannan ta shigo ta zauna kan kujera tace "my princess zomuyi wata mgn" heedayah ta taso ta zauna kan cinyar mummy, mummy tace "kinsan daddy baida lafya ko?" Heedayah ta gyada mata kai, mumy ta cigaba "nida daddy zamui tafiya saturday ko sunday zamu kai daddy asibiti dr ya dubashi" heedayah tace "that means baraku zo min open day na on monday ba knan mummy?" tagama maganar idanta cike da hawaye mummy tace "don't cry sweetie, in muka dawo zamu miki nd kinga babansu muhammad ma ai ze iya miki ko heedayah ta?" Ta sa hannu ta goge mata yar hawayenta, heedayah tace "ni banason babansu muhammad yamin, na hakura baran je sch ba ranan, in kun dawo zakumin ba? Promise?" Baki na rawa mumy tace "promise" heedayah tadanyi murmushi tace "ina zakuje nd yaushe zaku dawo mumy?" Mumy tace "kinsan washington DC dake united states?" Heedayah ta girgiza kai da alaman a'a mumy tayi murmushi tace "but am sure auntinku ta gaya muku inda white house yake ko?" Heedayah tace "laaaa se ynxu na tuna white house gdan mr president is situated in washington DC in america" mumy tace "excellent my princess to can zamuje da daddy dr yaduba shi, me kkeson in siyo miki?" Heedayah tace "ni toys nakeso dayawa da manya manyan teddy bears wanda suka yini a girma" mumy tayi dariya sannan tace "in shaa Allah zan siyo wa princess dina. One thing, my heedayah baraki koma islamiya ba? Kinga fa rabuwan ki da islamiya tun primary 2, yi hakuri kifara zuwa kinga se kiyi wa daddy addu'a ya warke da wuri ya je miki open day ko?" A lokaci daya mood na heedayah ya canza dan in akoi abinda ta tsana ynxu befi islamiya ba dalilin kuwa shine kan dukan dawani malami yataba mata wai dan ta taho da babyn wasa aji tun daga ranan heedayah tace barata sake zuwa islamiya ba duda dady yaci mutuncin malamin dan har police station sanda sukaje but still heedayah tace ita barata sake zuwa islamiya ba, shi kuwa daddy yace abarta tadan huta kunji dalilin rashin zuwa islamiyar heedayah knan. Heedayah tace "ni mumy baranje islamiyan nan ba malaman islamiya are wicked suna dukan mutum kinga auntinmu na sch bata dukan mu, ni baran je ba zanyi wa daddy addu'a a gda" mummy tace "heedayah kin taba ganin wanda bai zuwa islamiya? Naji bakison zuwa islamiya zan nemo miki malami yana zuwa yana miki a gda aikinga that way bare miki duka bako?" Heedayah ta gyada kai mummy tace "sekiyi concentrating kinji mumy's princess? Now finish ur assignmnt" tamata peck a goshi sannan ta fice**
HEEDAYAH 8-9-10-11 & 12
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.