shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 15 July 2016

HEEDAYAH 51----55

HEEDAYAH!

51
written by miemie

Sun sha tafiya me nisan gaske, heedayah kuwa tayi bacci ta tashy duk bata san inda take ba, shide me dan hankalin duk sanda ya juya ya ganta seyaji wani iri she's too beautiful to die conciousness nasa bare iya barinsa ya kashe ta ba there has to be a way yayi stopping dan uwan sa daga kasheta, amman besan ta ina ze fara masa maganar ba. Bayan 8hours suka iso garin Edo state still basu tsaya ba suka kama hanyar wata qauye me suna UHUNMWONDE, nanma sanda sukayi tafiyar 2hours sannan suka isa still wannan mutane basu tsaya ba, tafiya suke tayi acikin wannan qauye can gabar wata daji suka tsiya heedayah nata kalle kalle kamar wacce ta zare, mugun ya ciro bindigan nan nasa ya dura bullets biyu a ciki sannan yace da dan uwan nasa "lets get this job finished" ya sa hannu ze bude motar, dan uwan nasa yace "wait pls dan haka ya tsaya yace dan Allah kar mu kasheta, raba ta da mukayi da iyayenta da masoyanta ma kadai ya isheta takaici kalle ta fa," suka juya suna kallon heedayah wanda itama ta tsaya kallonsu kamar cartoon harda musu murmushi, me dan hankalin yace "isn't she cute? Dan Allah kar mu kasheta na yarda mu jefar da ita a nan mu tafi lets spare her pls kar mu kasheta," mugun ya rasa me zaice shima de har ga Allah jikinsa yayi sanyi daga bisani yace "toh shknan ayi kamar yadda ka fadi amman fa kasan oga sir baida kirki ynxu yazo yagane ba kashetan mukai ba ai kasan there would be a big problem nd ni banson abu ya hadani da oga sir gaskia," me hankalin yace "how will he even findout in ba wai kai zaka masa gulman ba, bare taba sani ba in har muka ja bakin mu mukayi shiru, this shud be our little secret" nanne mugun ya ajiye bindigar tare da fadin "okay then," suka fiffito daga motar mugun ya ciro heedayah suka kama tafiya cikin dajin, duk qarar tsuntsaye ko ta ina can sewani abu kamar tsuntsu amman da fuskar kaza da kafafun doki suyi kamar zasu cafke mutum sekuma su sake bacewa, wani sa'in kuma kamar qarar dariyan mutum haka akeji dajin de abin tsoro ne matuqa suma kansu Allah Allah suke su ajiye ta su fice daidai tsakiyar dajin mugun yayi wulli da ita tafadi a qasa kan wata glass wanda ya shige cikin cinyarta kara ta sakar sosai wanda dajin ya dauka se echoing din karar ihunyan akeji ko ta ina abin tsoro a 360 suka bar gun suka shige motarsu, a garin Edo suka yi parking suka nemi wata htl inda suka sauka, mugun ya kira alhj lawal bugu daya biyu ya daga guy din yace "oga sir gashy fa mun gama aikin mun kaita can wata daji a wata qauye inda muka kasheta am sure by now namomin dajin ma sun cinyeta" alhj lawal ya barke cikin wata erin muguwar dariya "well done ku jira kudinku 1mil both of you, dan wannan ba qaramin aiki kuka min ba, one more thing this shud be btw us banason ku gaya wa kowa," guy din yace "you can always trust us oga, so se gbe zamu kama hanya zamu dan huta yau," alhj lawal yace "inade kudin dake gunku ze isheku ku?" Guy din dason kudi wai "a'a" alhj alwal yace "toh karku damu ynxu xakaji alert sannu da kokari ko" sannan ya katse wayar nan da nan ya tura masu 100k sukayi wanka bayan sun je sunyi withdrawing kudin suka shiga zagaya gari****
Hawaye heedayah keyi sosai ga jini se balbala yakeyi daga jikinta, glass din ya yanke ta sosai, can erin tsuntsaye masu fuskar kaza da kafafun doki ya taho kan heedayah da sauri ya bugeta aka da kafafunsa atake ta fadi, a garin fadi ta buga kanta kan wata trunk na bishiya atake ta qeyanta ya fara zubda jini tun tana gani dishe dishe idanun nata suka soma kafewa ahaka har suka kafe. Allah ne kawai ya kare heedayah, duk wani abin da yaso ya tabata seya canza hanya haka namomin daji da dama suka ta zuwa amman dasun fara matsowa kusa da ita se Allah yaqi basu nasara. Bayan 2 hours na hango wata tsohuwa tana tafiya cikin dajin duk corner inda tabi se namomin dajin su soma gudu kamar tsoronta suke gata nan de tsohuwa futuk! Duk doro ga fuskar nan tata abin tsoro dake fara ce sosai tana sanyaye da wani erin kaya kamar lifaya ta zagaye jikinta dashy har kanta ma kadan kadan daga gashinta da sukayi fari ake dan gani, tafiya takeyi cikin natsuwa tana dan tsintar fruits kamar su apple, orange, banana dawasu herbs tana sawa cikin wheel barrow datake turawa haka can ta hango wani abu kamar mutum kwance a qasa abin ya bata mamaki sosai dan its not usual dajin nan is known as THE EVIL FOREST mutane basu yawaita shiga ba ko hunters ma basu shigansa saboda it is believed that ghost of the dead lives in it itama wannan tsohuwa dake ta yawo aciki tana hakan ne sbd tanada super natural powers wanda suke saving nata frm any harm, tana kaiwa kan heedayah ta tsunguna taga duk jikin wannan budurwa da jini a zatonta ma ta mutu ne kunnenta ta matso dashy kusa da heart na heedayah kome taji oho se ta dago ta taba gefen wuyarta cikin wata yare wanda ban taba ji ba amman ga dukkan alamu igbo language ce tace "tana raye" nan tayi casting wani spell akan heedayah dagani tsafi takeyi bayan tagama senaga heedayah taja wata erin doguwar numfashi da kyar ta iya ta daga heedayah ta sata cikin wheel barrow din tahau turata daidai gabar wata hut ta tsaya ta bude kofar sannan ta shiga ta kwantar da heedayah kan wata katifa daga wani lungu taje ta dauko wasu ganye dawani abu kamar ruwa ta hada cikin wata kwarya sannan ta fice ta aza kan wuta bayan some mintues ta duba sannan ta sauke tasa cikin wata sabuar kwarya ta nufa dakin dashy inda jini yake zuba daga cinyar heedayah ta yaga kayan tasa hannu taciro glass din da karfi sanda heedayah ta sakar dawata irin ihu nan tsohuwar ta sake casting wani spell kan heedayah sekuma tayi shiru tashafa mata maganin da ta dafo agun atake gun ya warke shar! Kamar ba'a taba jin ko yanka a gun ba haka ma tamata treating na kanta daga karshe tasa mata kadan daga cikin mgnin a baki amman heedayah taqi hadewa sanda ta mata casting spell sannan ta hadiye atake ta soma zufa bayan 20mins tadan motsa jiki tareda lumshe ido

HEEDAYAH!

52
written by miemie

A hankali ta soma bude idanta har ta budesu tas tafara bin dakin da kallo, saidai har ynxu takasa gane ina take ta dan miqe ta zauna nanne idanta suka kai kan wannan tsohuwa ihu ta sakar tsohuwar tace mata "shhhh karki damu baran cutar da ke ba" cikin harshe erin na daxu, heedayah da bata gabe me matar ke fadi ba tacigaba da ihu, daga bisani kuma se tayi shiru ta tsaya zura wa tsohuwar ido sosai can kuma seta fashe da dariya, abin yaba ma wannan tsohuwar mamaki sosai kode mahaukaciya ce yarinyan? Se kalle kalle heedayah keyi har ynxu nan tsohuwar ta matso kusa da heedayah ta dafa kanta tayi casting spell kan heedayah atake heedayah ta sume tsohuwar ta gyara mata kwanciyanta sannan taje ta aza musu girki se can dare around 10:40PM heedayah ta farfado da hannunta riqe akanta tana kokarin tuna abubuwanda suka faru a baya dagani se ynxu ta dawo hankalinta daga bisani tace "dan Allah karku kasheni ku min rai dan Allah" a daidai wannan lokaci tsohuwar tashigo heedayah na ganinta ta tsala ihu bata taba ganin farar mata kamar wannan ba inba dai a film ba gata tsohuwa sekace aljana "baiwar Allah dan Allah kar ki kasheni nasan duk don moha ne ya turo ku dan Allah kiji qaina karki kasheni pls zan gaya muku menake nema a gdansu," nan ne tsohuwar ta gano heedayah bahaushiya ce ta kariso gabar heedayah da in banda bari ba abinda takeyi tsohuwar tace "'yar budurwa kar ki damu ba abinda zan miki kinji? Bar kuka" nanne heedayah tadan samu peace of mind ta sa hannu ta share hawayenta, heedayah tace "ina nike pls? Ina wanda suka daukoni cewar zasu kasheni ina suke? Kuma ina ne nan?" Tana bin dakin da kallo tsohuwar tace nima bansan sunan wannan qauye da muke ciki ba amman de bamu da nisa daga EVIL FOREST inda na tsinto ki....nan ta lbarta ma heedayah duk abinda tasani, cikin kuka heedayah ta daga hannayenta biyu sama tare da gode ma Allah da ya kareta daga sharrin don moha da mutanensa sannan ta dawo da kallonta kan tsohuwar da itama kallonta take tace "dan Allah wace ke?" Tsohuwar tace sunana "aleesha," heedayah tace "musulma ce ke?" Tsohuwar tace "eh kusan haka," heedayah zata sake mata wata tambaya aleesha tace "kefa ya sunanki?" Heedayah tace "heedayah suna na" aleesha tace "sannu heedayah karki taqura wa kanki ynxu ga abinci acan" nan ta tashy ta dibo ma heedayah ta amsa amman takasa ci, aleesha tayi murmushi sannan tce "ci 'yata ba abinda nasa miki aciki you are safe now no one will hurt you," dakyar ta iya takai cokali baki ba gishiri ba maggi salam da kyar ta iya tadan ci kadan dan kora yunwa tana gamawa ta tambayi aleesha ko karfe nawa, aleesha tayi wani magic sannan tace "11:20PM 'yata," cikin tsoro heedayah tace "you use magic? Are u a soccerer?" Aleesha ta gyada mata kai "I was born with it," heedayah takasa fadin komi duk tsoro ya cika ta daga bisani tace "inason inyi alwala" aleesha takuma yin magic sega qwarya cike da ruwa tace "hungo yi," heedayah tace "a'a inajin tsoro," aleesha tace "ba abinda ze miki karki damu" da kyar ta gwada sa er yatsan ta aciki taga ba abinda ruwan yamata sannan ta saki jiki tayi alwala tayi sallah ta nemi gu ta kwanta bata kuma cewa aleesha komi ba haka itama aleeshan. Washegari da safe around 8:30AM heedayah ta tashy da rogowar ruwan datayi alwala dashy jiya tayi yau sannan ta zauna tana kallon aleesha, bayan 'yan mintuna aleesha ta tashy itama, heedayah tayi kamar tana bacci, aleesha tayi murmushi sannan ta fice daga dakin bayan some minutes ta dawo da abinci a hannunta ta ajiye a gaban heedayah, heedayah ta gaishe ta aleesha ta amsa sannan tace "muci abinci ko?" ...bayan sun gama ci aleesha tace "heedayah bani labarinki dan ga dukkan alamu ke ba 'yar nan bace," heedayah tace "eh aleesha ni 'yar maiduguri ce amman a kano nike da zama," aleesha tace "zaki iya kirana da baba" tare da ma heedayah murmushi, heedayah tace "toh baba" itama ta mata murmushin, tacigaba da bama aleesha labarin kanta bata bar koda tsinke ba, aleesha ta mugun tausayawa heedayah sannan tace "Allah sarki 'yata kin sha wahala sosai a rayuwarki gaskia, never trust anyone a wannan zamani amman abinda bangane ba har ynxu heedayah shine mesa don moha yakeson kasheki? Kamar yadda kka ban labari ai yana sonki then mesa ze so ki mutu?" Heedayah tayi shiru sannan tace "wannan kuma se Allah, nima kiban labarin kanki," aleesha taja numfshy sannan ta fara kamar haka...

HEEDAYAH!

53
written by miemie

"Kamar yadda na gaya miki sunana aleesha, shekaruna 78 a duniya, ni igbo ce gaba da baya na garin Imo, dangi na du christians ne iyayena ma muslinta sukayi, ni kadai suka haifa tun ina 'yar qarama suka rasu due to car accident da sukayi daga lokacin na soma zama gdan wata aunt dina wanda tasa ni nayi ridda nakoma christian, ta tsane ni sosai bawanda ta tsana a fadin duniyar nan kaman ni wani sa'in aljana ma take kirana badan komi ba wai dan fari na yayi yawa haka na girma cikin wahala alokacin da na kai 20yrs ne na fara discovering super natural powers da nike dashy, ba karamin tsorata nayi ba na gwada gaya ma wannan aunt dina ta koreni daga gdan ta acewarta ni witch ce haka uwata ma, i was lonely ba wanda na sani har Allah ya hada ni da miji na wanda yasoni tsakani da Allah christian ne shima, soyayya me qarfi ce ta shiga tsakaninmu wanda har ya kai ga aure ahaka aka mana aure duda iyayensa where against the marriage, ahaka har Allah ya albarkacemu da yarinya ta mace wanda yasa mata sunan mamanshi chidinma, shekarun chidinma 15 a duniya ita da mahaifinta sukayi car accident alokacin dayaje daukota daga sch bayan sunyi hutu, atake chidinma ta tamutu"...ta tsaya ta share hawayenta sannan ta cigaba, "mijina kuwa sanda yayi jinyan wata biyu sannan shima Allah ya dau abinsa, tundaga lokacin in law na tasani a gaba sam wai ni na kashe mata danta haka suka sani nasha ruwan da aka masa wanka, nakuma kwana da gawan sa dan a zatonsu ni na kashe musu da bayan an birne sa ne ta korani daga gdanta haka na ta tafiya batare da nasan inda nike zuwa ba har Allah ya kawoni wannan destination danike yau, da ba dan powers da nike dashy ba dana jima da mutuwa nima, toh fa kinji lbri na knan"...heedayah taja numfashy sannan tace "Allah sarki baba u've been through so much hardships, " aleesha ta mata murmushi sannan tace "yes my fairy god daughter," cikin rashin fahimta heedayah tace "ur fairy god daughter kuma?" Aleesha ta gyada mata kai "nasha mafarki cewa akoi wata budurwan da zata zo ta maye min gurbin 'yata chidinma nd wannan budurwa ba kowa bace illa ke," heedayah tamata murmushi sannan tace "naji kince kinyi ridda, to har ynxu a christian kke?" Aleesha tace "no nakuma zama musulma, musulma ce ni amman saidai bansan komi kan muslunci ba cuz tun ina yar qarama iyayena suka rasu" heedayah tace "toh masha Allah baba zan koya miki duk abinda ya kamata, I need a favor frm you pls, yakamata insan inda nake, I need to get back home inyi fulfilling destiny na nazamo prosecutor," aleesha tace "then we have a very long way to go, dan kinga na farko ban san ina ne nan ba as u can see nikadai ce ke rayuwa a nan amman gaba da evil forest akoi wata qauye acan kinga in har zamu sami mutanen gun zasu iya gaya mana sunan qauyen"...heedayah ta katse ta "what of money? I need money inyi kudin mota dashy," aleesha tace "its been long rabuwa na da kudi nakega tun randa nabar garin mu Imo ban sake sa kudi a idanu na ba" heedayah tace "ba kinada magic ba? Ki fito mana da kudi mana" aleesha tayi murmushi sannan tace "magic dina baida karfi ynxu 'yata daga healing mutum se protection nake iyayi nd nothing more," heedayah bata ji dadin hakan ba tace "toh ynxu ya knan?" Aleesha tace "abu daya nake tunani in xamu iya yin wata 'yar sana'a wanda a kowani asabar in aka bude kasuwa a wani waje dake qasa da nan se mu kai mu siyar ahaka zamu na tara miki har se in ya cika kudin mota" heedayah taji dadin wannan shawara sosai ahaka sukata sorting out abubuwa da dama daga karshe suka yanke hukuncin kai diffrent types of fruits kasuwan tunda aleesha na iya shiga cikin evil forest.
GARIN KANO; motar don moha na hango a unguwar su heedayah, anjima kadan yafito yayi tambaya yakuma komawa motan ya tuqa haka ya tayi har sanda Allah yakowasa gabar gdan su heedayah bayan kwanaki biyar da ya jera yana neman gdansu. Parking yayi a waje yayi knocking me gadi ya bude masa amman kwata kwata mal musa be gane don moha ba shide don moha be ce masa komi ba illa tambayar sa dayayi ko nan ne gdansu heedayah? Mal musa yace "eh nan ne saidai heedayahn batta nan yau kimanin sayi uku knan da batanta ba'a san inda take ba don moha yayi kamar besani ba ya tausayawa mal musa sannan yace "maman ta fa tna nan?" Mal musa ya gyada masa kai "kashiga daga ciki," don moha ya karisa a gaban entrance door din ya tsaya ya danna door bell bayan some seconds nanny ta taho ta bude saidai bata gane fuskar ba dan haka ta tsaya tana kallonsa daga bisani tace "dan saurayi wa kake nema?" Don moha yace "nanny?" Nanne nanny ta gano don moha ne takira sunansa da karfi harda hugging dinsa "yaushe a gari haka? Ashe Allah ze sake hadamu, kai gaskia ka girma sosai ai ban gane ka ba shigo shigo..."

HEEDAYAH!

54
written by miemie

Ya nemi gu akan sofa ya zauna nanny tace "don moha manyan gari, meya kawo ka gdan namu?" Don moha yace "gun mummy na zo," nanny tace "a minute ina zuwa," tare suka dawo da mummy, har qasa don moha ya durqushe ya gaishe da mummy ta amsa cikin fara'arta saidai kallo daya aka mata asan tana cikin tsaka mai wuya, bayan sun gama gaisawa da mummy tace "kode gun heedayah kazo? Ai heedayah batta nan ta bata yau kusan 3 weeks da batan ta knan" sekuma ta fashe da kuka, don moha yace "yi hkr mummy abinda yakawo ni knan nima," cikin rashin fahimta mummy tace "kamar ya knan son?" Don moha yace "nasan suwa suka yi kidnapping heedayah saidai ban san inda suka kaita ba but believe me xanyi iya kokarina in samo ta, inde tana raye," mummy tace "muhammad? Kace kasan suwa suka yi kidnapping heedayah ta?" Don moha ya gyada mata kai, mummy tace "suwaye ne dan Allah, tell me, tell me pls, kaji son?" don moha yama mummy qarya "nima sunce na kuskuara na gaya ma wani zasu kasheni but I assure you zamu samo heedayah sooner or later, akoi abinda nakeson ki sanarda ni mummy, tell me all that you knkw pls karki boye min komi," cikin rashin fahimata mummy tace "mene knan?" Don moha yace "yawancin kullum b4 ayi kidnapping heedayah se taje gdanmu dasunan tana neman abu, shin me take nima?" Mummy ta dafe qirji! "gdan ku fa kace muhammad?! Me zekai heedayah gdan ku innalillahi?" Don moha yace "calm down mummy tell me metake nima pls?" mummy tace "wallah tallahi muhammad bansan me heedayah take nema a gdanku ba I have no idea ma gdanku take zuwa kullum cemin take zata gdan frnd dinta" tacigaba da kukan da takeyi don moha yace "is okay bar kuka amman bakida idea ko kadan?" Mummy ta gyada kai, don moha yace "but me tsakaninsu da daddy? Naji ranan ya ambaci sunanta a waya yana cewa bani nayi kidnapping dinta ba," salati mummy kawai takeyi "muhammad na rasa me nayi wa daddy'nka ya gommaci ya riga sa rayuwata cikin matsala a koda yaushe," don moha yace "wacce erin matsala knan mummy? Me daddy ya miki feel free nd tell me pls," mummy ta goge hawayenta tace "babu son, dont mind me" don moha yata insisting amman mummy taqi gaya masa komi dan batasan tayi turning 'da akan mahaifinsa itade ta bukacesa da ya samo mata heedayahnta kawai, don moha yace "in shaa Allah I promise u this," seya bude baki ze gaya wa mummy kan cewa tun farko shi yafara kidnapping heedayah sekuma yayi shiru dakyar ya ce "mummy I need to tell you this," mummy tace "ina jinka son," nan don moha ya kwashe labarin komi yaba ma munmy, sabon kuka mummy tafara "muhammad mesa zakai haka? Mesa?" Don moha hkr de yake ba ma mummy yana neman gafararta amman takasa cewa komi daga bisani tace "na yafe maka muhammad amman dont ever try to do that again kome bekamata kayi kidnapping heedayah ba shes still a child to me kasan wherever she is 2day kaine silan komi muhammad mesa kayi haka?" Hkr still yake bata can ya miqe ze fice mummy tace "muhammad as u said daddy'nka has somethng to do with this is true cuz shekaru dayawa da suka wuce akoi sanda daddy'n heedayah baida lfya dan haka ya mallaka ma daddy'nka arzikinsa tas filayensa ne, companies dinsa harta gdaje da sunan sbd yayi trusting daddy'nka, da daddy'nka ya tashy saqa masa kuma seya dibe komi ma kansa harta gdanmu shi ya siyar mana that was the reason y muka bar gdan namu na unguwarku" bata ma gaya ma don moha prado inda ke gdansu da na heedayah bane dan kar abin yayi yawa. Atake don moha ya soma jin jiri "how can my dad be so evil? Mesa zeyi haka, why, why?" Hawaye yasoma yi mummy na lalashinsa bayan dayagama kukansa ya durqushe har qasa yana neman forgiveness na mummy on behalf of his father ji yake kamar ya kashe daddy'nsa "this means time da heedayah ta taba fada min "nice ride, kamar nawa wanda barayi suka sace min" she means wannan ne motar tatan, omg! Heedayah am terribly sorry if only kin gaya mun meke kaiki gdanmu nd me kke nema u could have been safe with ur family now, mesa kka gommaci boye min wannan muhimmiyar mgn, why heedayah? Can wata zuciya tace bcuz she loves u nd bata son ta raba ka da daddy'nka, don moha yace you should have told me still, kka sa akan gaskiyar ki na riga baki wahala I am so sorry heedayah pls forgive me I promise i'll make it up for you one day****
EDO STATE; kwanaki da dama sun ja yau kimanin 2 weeks knan, heedayah da aleesha se shiri sukeyi dake yau saturday ce akoi kasuwa, bayan sun gama shirin heedayah ta dauko basket of fruits din ta rike a hannu tace da aleesha "mu tafi ko?" Aleesha tace "yes 'yata" suka rufo hut nasu sannan suka fice tafiya me nisa sukayi sannan suka iso kasuwar cike yake da mutane dam wanda kowa harkan gabansa yakeyi, suka nemi gu suka ajiye basket nasu can wani kyakkyawan matashy fari sosai da ka gansa kaga igbo, bare gaza shekaru 26 ba, ga gashy nan ko ta ina sajen nan ya hade da 'yar gemun da yake tarawa, sanyaye yake cikin jeans da polo shirt red wanda ya amsa skin nasa, ga dukkan alamu yazo siyan kaya ne, ta gefen su heedayah ya tsiya ya siyo wata 'yar gyale kalan na tsofi haka dagani wa mamansa ne, heedayah de kallonsa takeyi suna hada ido ta sa da kanta qasa, wannan saurayi yayi murmushi tare da matsowa kusa da basket nasu heedayah "how much does this apple cost each? N50?" Heedayah taja tsuka mstw "'inyamuri da san banza, no its N200 da fuskar nan tata a tamke tana kallon gefe a ganinta wani erin iskanci ne zece mata apple N50 ai duda anan kudu apple ba tsada amman worth nasa yafi N50 mana saidai N100, saurayin yayi murmushi wanda ya sake fidda kyansa dimples nasa suka bayyana dan sarai yanji abinda tace yace "koh emmata?" Heedayah ta zaro dara daran idanunta dan koda wasa bata zata yana jin hausa ba sede data lura da kamanninfuskar sa siririya ce ba kamar na inyamurai me fadi ba, duk setaji kunya tafara kau da kai yasa hannu a aljihu yaciro wallet nasa ya miqa ma heedayah N400 ya dibi apple biyu heedayah na "hey, hey wait your change I was only kidding" yana jinta yaqi juyawa ya cigaba da tafiyarsa. Heedayah ta kalli aleesha tace baba kiga wannan guy din? Aleesha tace "lets be thankful yana da kudin ne," bayan shi mutane 'yan kadan ne wanda basu fi 3 ba suka dan sayi lemo shknan, heedayah bata ji dadin hakan ba amman aleesha ta kwantar mata da hankali

HEEDAYAH!

55
written by miemie

Ahaka har suka isa gdah, suka aza girkin rana heedayah har ynxu mamakin wancen guy din takeyi, "how is it even possible? N400 a zamanin nan, chab! He must be rich."
3 days later aleesha ta tashy da rashin lfya, batta jin dadi sosai dan haka taba heedayah bucket da ta je ta dibo musu ruwa acan gaba da evil forest, dan tasamu tayi curing kanta, haka heedayah ta soma takawa tayi tafiya medan nisa sannan ta iso gun famfon, da mutane dayawa dan haka itama tabi layi, daidai anzo kanta bayan ta ajiye bucket nata zata fara pumping ruwan knan, hannu kawai tagani kan nata meshi yace "let me" juyawanda zatayi suka hada ido hudu da guy na ranan wanda ya siye apples nata guda biyu kan N400 yau ma jeans ne da wata yellow T shirt a jikinsa tace "you! Again" yamata murmushi, pumping ruwan ya soma yi da hannu daya abinda mutane biyu keyi kokuma in mutum daya ma seyayi da qarfi da hannu bibbiyu, kallonsa kawai heedayah keyi yadda muscles na hannunsa ke going up nd down in yana pumping ruwan, yana gamawa ta matso zata daga yace "noo a princess like u is not allowed to carry a bucket full of water, let me" heedayah tace "am not a princess," guy din yace "you are to me, so where are u heading to?" Heedayah tace "argh! 'Inyamuri banda san banza harda maita mstw," sanda ta gama maganan a fili sannan ta tuna ashe yana jin hausa hannu biyu ta aza kan lips nata "omg! he must have heard me, what do I do now?" Dariya guy din yayi sosai ba qarya wannan lady is so funny, heedayah tace "gimmie my bucket, I have to go" yace "lets go" badan tana so ba suka soma tafiya tare yana riqe da bucket din bawanda yace ma wani ko uffan daga bisani guy din yace "princess whats ur name?" Heedayah tace "I don't have a name" guy din yayi murmushi sannan yace "well i'll say your name is Zainab? Aysha? Fatima? Maryam? Hafsat?..."se jero sunaye yakeyi, daga qasa qasa heedayah tace "duk maitab ka baraka taba iya guessing suna na ba," jin haka guy din yace "koh? Baran iya guessing sunanki ba?" Heedayah tace "eh!" Yace "lol okay na yarda u've won this, can u guess my name also?" Heedayah tasoma lissafo sunayan 'inyamurai kamar haka; ozioma? Osinaci? Emeka? Chika? Sopuluchi? Azuka? Chi.. Guy din yayi interrupting din heedayah "AZUKA! Thats my igbo name, my islamic name is RAYYAN, you really are intelligent, kin iya kinyi guessing name dina ni nakasa," seya bama heedayah dariya yadda yake maganan kamar yaro tace "dont be such a girl, suna na HEEDAYAH!...Kace ur islamic name is rayyan?" Ya gyada mata kai daga can kasa tace "toh dama 'inyamuran nan akoi muslims ne?" Jin haka rayyan yace "yes princess, what a nice name heedayah! But what is the meaning?" Can qasa qasa heedayah tace "ohh ni wannan inyamuri kacika surutu" ashe gogan namu kan yaji ta yace "toh shknan nayi shiru," abin yabama heedayah mamaki kowani magna tayi a hankali seyaji wani erin kunne ne dashy? Tace "heedayah means guidance (kaariya)" rayyan yace "excellent starting today u'll be my guider(me bada kariya)" tadau a zuci take mgna tace "koba guider ba, dan rainin sense nida kai wa ze guiding wani?" Ashe kam a fili tayi maganan rayyan can't help it ynxu kam dariya yakeyi sosai, heedayah tace "wai nikam meka maidani sekace mahaukaciya daga nayi mgn ka tsaya kana min dariya, pass me my bucket i'll walk it frm here" rayyan yace "sorry princess..." heedayah ta katse sa "nifa na gaya maka am not a princess" Rayyan yace "pardon me, so tell me where are you frm sbd frm all seeing keba yar nan bace," heedayah tayi kmr bata jisa ba rayyan yace "hello?" Nan ne tace "eh ni ba 'yar nan bace am frm maiduguri state," rayyan yace "so its true dama ance 'yan maiduguri are slim and beautiful so are you," heedayah ta masa murmushi yace "yes princess ina jinki what brought u to our land, the igbo land?" Heedayah tace "am not telling you" rayyan yace "haba princess plsssss lets find somewhere nd sit" heedayah zatayi mgn yace "shhh" akan wata dutse suka zauna gaba da evil forest, ya ajiye bucket din agefensa sanan yace "ina jinki princess" heedayah taja numfashi sannan tafara basa labarinta kamar yadda taba ma aleesha...tana gamawa tace "kaji abinda ya kawoni igbo land knan"...rayyan yace "what a pitiful life you've lived, don moha da daddy'nsa have to pay for everythng," heedayah tace "in shaa Allah nd thats why nake nemar hanyan da zanyi in fita daga nan inje in qarisa karatu na inyi taking revenge," rayyan yayi sjiru heedayah tace "lfya?" Rayyan yace "its not as simple as u see kinga har yau elders namu sunqi gaya mana sunan wannan waje da muke, we are just living like this taya zaki iya barin nan harkisan where u are heading to?" Heedayah tace zanyi whatever it takes, rayyan yace "me too I'll do whatever it takes inga kinyi taking revenge naki heedayah, i'll help u whenever u needed any help," heedayah tace "thank you, kaifa? Tell me about yourself too," rayyan yace "ready?" Heedayah ta gyada masa kai tare da yin murmushi yace "mahaifina is an igbo man whereas mahaifiyata kuma fulani," heedayah kallonsa take cikin rashin fahimta, yace "I know u must be confused Ko? Taya fulani da igbo zasui aure? Kar kidamu zakiji komi" yacigaba...
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).