shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 20 April 2016

SAUYIN RAYUWA 6-7 & 8

sauyin-rayuwa.jpg

[9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page6vBABY ZAHRA Shirye shirye ake babu kama hannun yaro Dafe dafe sukeyi gabaki daya gidan yakaure da daddadan kamshin abincin inna da kaisa inna ta iya girki sosae shiyasa kaisa ma ba abarta abayaba gurin iya girki mai dadi, sun gama aekin su tsaf sannan sukayi wanka wannan duk shirye shiryen da akeyin anayine domin zuwan abban abuja da muktar, can gurin misalin karfe 6:30 na yamma motar alhj usman yafaka akofar gidan mal malami, mal ne yataso shida kansa yatari dan uwansa da dansa, acikin dan yal watattan murmushi ba yabo ba fallasa muktar ya rungumi mal malami baisan meyasa ba haka kawai yana son mutumin aransa shiyasa ma yake iyayi mai dariya, cikin gida suka shige, alwala suka farayi kasancewar magriba tarigada tayi, bayansun idar da sallahr ne suka shiga cikin gida kaisa ce ta fara jera musu abinci agaban su, saida tagama sannan tadan zauna agefen taburmar tafara mika gaisuwar ta wa abban abuja, da dariya ya amsa bayan sun gama gaisawan ne tajuya gefen ya muktar tace ya hanya ya muktar dakyar ya iya ce mata fyn fa! Inda sabo ta saba da hakan don haka itama bata damuba ta tashi tayi shigewar ta cikin gida abinta BABY ZAHRA [9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page7na BABY ZAHRA wayar sace ta haukara alamar ana nemar sa a wayar, tashiyayi ahankali yashiga cikin mota yadan kwantar da site in motar sannan ya amshi kirar, cikin sassanyar murya tace sweet anwuni lfy, kusan 3scn kafin ya iya cewa fyn nd u, "same" kawai ta iya ce mai sannan cen sai tace albishirin ka sweet yace mata goro fari ko jaa yace mata fari, tace to zakabani kyautar farar goro, yace mata sosae ma kuwa, tace to maimartaba yace yana son ganin ka, wata daddadar ajiyar zuciya yayi sannan yace atakaice dai kin kusa kidawo tawa ko, lumshe ido tayi cikin jin dadi kafin tace insha Allahu kuwa, sae yace mata to kema albishirin ki, cikin sauri da son jin abinda zaice tace mai goro, yace mata yanzu haka ina cikin jajere, wata er ihu tasaka, wanda hakan har saida yajawo hankalin kuyangunta zuwa gurunta, da sauri falmata tace ina fatan dai lafiya uwar gijiya ta, hannu kawai ta daga mata alamar lfy sannan tabar gurin, da sauri tace mai sweet shine baka shigo cikin gari ka kwana ba, cikin kasaita yace mata tare da Abba na muke da sauri tace oho, to inda Abba zai yarda ae da kunshigo ta fada in yasoma sai ayi magana gabaki daya, shiru yayi nadan wani lokaci kafin yace to zan tuntubeshi inji, dadi yadada kama nasreen, sannan suka dan sha soyayyar su da suka saba kafin daga bisani sukayi sallama akan goben zaizo

Share:

3 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).