shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday 20 November 2015

KAUNA CE SILA*** 4---5

kauna-ce-sila.jpg

[8:26AM, 11/21/2015] Bana: KAUNA CE SILA 4












MUHD-ABBA~GANA







bayan taci abinci tayi sallah na fada mata ina so don Allah naje gidan yayarta nayi kamar sati daya Zan gaishesu na kuma fada musu na gama lafiya tace to bakomai bayan kwana biyu da dawowar mu mahaifinmu ya dawo ya sauka a gidan mun yi murna sosai daganina sannnan shima yayi min nasiha mai ratsa jini.lokacin ne ma yake fadamin cewa dama y ahanani sauraran samari ce don ban kammala karatuna ba amma yanzu ina da dama kula duk wanda nake so amma ba hakan yana nufin na kawo masa kare da doki gida ba na kula sosai don nasan halin shi ya kuma cewa sakamakon ku yana fitowa zan nemar miki gurbin karatu sai ki zama cikin shiri nace to na gode har na tashi zan tafi sai yace ga wannnan naki ne na karba ina godiya ina shiga daki na bude sai naga wani kwali mai kyau karami ashe waya ce mai kyau kirar panasonic gaskiya wayar tana da kyau sannnan da layi n glo na bude ina ta murna umma tace lalle to an gode sai ayi mata caji tukunna koh nace to bakina yaki rufuwa dan murna wai nice da waya yau a wannnan ranar ne mauna zaune nida umma a tsakar gida muna hira naji sallamar wani yaro dan makotanmu yana cewa wai ana sallama da mamaa nace inji ea kuma sai yace jibirne nace wa umma kai da alamar ban ji dadin kirana ba sai umma tace tashi kije ai gaisawa zaku yi na tashi don nemo mayafin kayan jikina jibrin wani dan layinmune daya dade yana cewa yana sona tun ina makaranata na sha ji ana fada idan nazo hutu a bacin yan unguwa wai yana cewa ni zai aura ni dai sai dai nayi murmushi yau ya kai yi min kwanta idan yaga ina siyen abu a...








MUHD-ABBA~GANA






www.abbagana.pun.bz
[8:31AM, 11/21/2015] Bana: KAUNA CE SILA 5








MUHD-ABBA~GANA





Waje ko shago haka bana kawo komai idan nayi la akari da yanda yan layin mu muke zaune kamar uwa daya uba daya na fito na sameshi a kan dakalin makwaftanmu nayi masa sallama ya amsa da fara a yace min mamaa ina wuni nace lafiya daga haka ban sake cewa komai ba yayi dan jan numfashi kadan yace mamaa kamar bakiji dadin zuwana ba ko nace a'a me ka gani yace najiki shiru ne nace to mai zance yayi dariya yace dama nazone na miki murna sannnan na kara jaddada miki ra ayina akan ki gaskiya ina sonki kuma in Allah ya yarda aurenki nake so nayi a take naji gabana ya fadi ba tare da nasan daliliba amma ban bari ya gane ba nace Allah ya mana zabi mafi alhairi yace ameen nace masa kaga hadan kamar ruwan za a fara bara na shiga gida yace min to ga wannnan ya miko min leda nace ka barshi na gode yace wallahi sai kin karba na karba ina masa godiya ina shiga na tarar da umma tana t tattare kaya don har an fara iska da alamu yayyafi na shiga na ajiye na fito ina tayata da safe da muka tashi ranar juma'a ne t fito zata tafi nace mata ga abin da ya bani jiya tace me yasa kika karba? nace wallahi rantsewa yayi tace shi kenan amma gaskiya bana so ki saba da karbar abin samari dan haka hatsair ne babba nace mata to zan kiyaye da yamma nayi wanka nayi kwalliyar juma'a nayi kyau gaskiya sosai don wata atamfa na saka mai ratsin purple a jikina










MUHD-ABBA~GANA


09039016969



www.abbagana.pun.bz
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive