shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 9 September 2015

INDAI KINSAN KINA SOYAYYA TO KIKULA DA WANNAN SAQO KI KARANTASHI.

vampire2.jpg

A MATSAYINKI NA MACE BUDURWA INDAI
KINSAN KINA SOYAYYA TO KIKULA DA WANNAN
SAQO KI KARANTASHI.
(1) ki tsayar da saurayi guda daya tak na kirki
bisa la akarai da ayyukan sa da halayensa na
zahiri.
(2) kitabbata kina sonsa sosai kuma shima yana
sonki sosai.
(3). Kada ki yarda kidade da saurayi, ko kishaqu
dashi ko ki nuna masa tsananin so batare da
iyayensa sun gana da iyayenki ba.
In yaqi turosu kirabu dashi tunkafin yagama sace
zuciyarki.
(4). Kizama mebin shawarar iyayenki, da neman
shawararsu a harkar soyayya, kada kibi shawarar
Qawaye ko saurayi kobin shawarar zuciyarki.
(4). Kada kiyarda a kawo miki gulmar saurayinki
ke kuma kidauka koki kama zargin sa.
A'a sai kinyi bincike na adalci ko kingani da
idonki.
(5). Kada ki kuskura kiyiwa saurayinki qarya
kizama me fada masa gaskiya ,da yimasa bayanin
komai iya saninki.
(6). Kizama me yawaita addu'ah da bawa Allah
zabi a dukkan lamarinki..
(7). kikiyaye zargi da binciken laifinsa matuqar ya
sanar dake komai bai 6oye miki gaskiya ba.
(9). kidauka dan adam tara yake bai cika goma
ba, kinga zai iya kuskure, dan haka sai kiyi masa
afuwa.
(10). kizama me kare mutuncin kanki ,da kuma
kulada matsayinki batare da girman kaiba ko jan
aji ga masoyi...
JAN AJI A SOYAYYA BA ABIN DAYAKE HAIFARWA
SAI NADAMA.
idan saurayinki ya tsaneki ko yagudu yabarki ko
kin rasa wani abu da yake baki, kiyi haqury kada
kijuya masa baya, kisa masa shakka a ransa
yadinga tunanin anya kuwa kina son sa da
gaske ???
KEDAI KAWAI KI KARE MUTUNCINKI DA IYA
TAKUNKI
(11). Kada kiyarda ki sakarwa saurayinki fuska
yana shigo miki da kalmomin da basu daceba ko
dabi'u.
kamar yace zai samiki zobe, ko zaiga awar
waronki ko zaisa miki jaka, ko zaiga fulawarki ,ko
zai auna kaurinki dadai sauransu.
SABODA HAKA KIZAMA ME BATA RAI ADUK
SADDA KIKAGA HAKA, KODA YATAFI KIRABU
DASHI, DAMAN BA NAGARI BANE, SOYAKE YA
BATAKI.
Wakilin shaytanne.
(11). Kizama me yiwa saurayinki Al-qawarin nuna
masa soyayya bayan aurenku, sannan dayi masa
biyayya dai dai gwargwadon
iyawarki.
KISANI DAYAWAN SAMARI AKWAI
MAKIRCI.
Wani yasan ba aure zaiyi ba amma zaizo yabata
miki lokaci.
Wani soyake yakoyi zance sai kawai yazo wajenki
yayi tayi miki qarya batare dakin fargaba zai dasa
miki ciwon so, YA KORAR MIKI SAMARIN KI
NAKIRKI.
Wani kuma kawai so yake yana zuwa wajen fati
dake.
Saboda haka zaina saya miki kaya kala kala yana
fira da ke zai fake da cewa SAI YAGAMA School
KO SAI BAYAN YAGAMA KARATU ZAI TURO KUYI
AURE.
Duk fati ko fikines zai daukeki kutafi.
Wani kuma soyake kawai yana taba jikinki yaji
dadi koda bai kwanta dakeba, saboda
haka zaita binki sauda qafa yana
soyayya dake.
Wani kuma so yake ya bataki.
Irin wadannan samarin sunfi kowanne hatsari.
Idan yaganki yana sonki yana fara karantar
halayenki IDAN YAGA KE USTAZIYACE TO ZAIYI
SHIGAR USTAZAI HARDA
LITTAFIN SA A HANNU ,HAKA ZAITA KAFA MIKI
TARKO HARSAI KIN FADA.
Idan yaga 'yar BOKOCE zai fito miki a dan boko.
Idan yaga ke yar duniya ce toshima a hakan zai
fita.
Irin wadannan samarin har kayan mungani
munaso suna kaiwa budurwa, har iyayensu suna
turowa daga qarshe daya kwanta dake shikenan
yabiya buqatarsa, bazai bari kisami cikiba zaibaki
qwaya da zarar yaga baki da ciki yasan yayi free
tunda yasami abinda yake nema, zai Qirqiri laifi
yalaqa miki domin ku6ata a karbo kayan sa daga
gidanku, koma yabar miki kayan...
Irinsu akwai makirci da nuna tsagoran soyayya
ga budurwa, domin sukanyi kukan hawaye a
gaban budurwa duk da sunan so amma yawanci
domin ya raunana zuciyar kine.
Yakan maqale miki har unguwa yana rakaki koda
yaushe.
YAR UWA IN SOYAYAYYA TAI GARDAMA WAYE
YAFI SHAN WUYA DA
TOZARTA ???
SHIN ANAIWA NAMIJI CIKIN SHEGENE KO
BUDURWA AKEWA ???
IDAN ABIN KUNYA YAFITO WAYE ZAI ZAUNA A
GIDA KO MAQOTA BAI ZUWA
DAN KUNYA NAMIJI KO MACE ???
MEYASA NAMIJI ZAI IYAYIWA YAN MATA BIYAR
CIKI BATARE DA AURE BA AMMA INYAZO NEMAN
AURE SAI ABASHI ???
IDAN KUWA MACE TAYI CIKI SAU DAYA DA
KYAR TAKE AURUWA KOMA SAI TABAR
GARIN ???
MEYASA MACE INTAI CIKI AGIDAN SUMA
TSANARTA AKEYI ,AMMA NAMIJI DAYA KAWO
RAGO DA KUDIN ICE SHIKENAN ???
MATA NAWANE SABODA CIKIN SHEGE SUKABAR
GARINSU KO RAYUWARSU
TA GURBATA AMMA SHI NAMIJI KAMARMA BAIYI
KOMAI BA ???
KO KAMUWA KIKAI DA MUGUN CIWO
WAZAI KULA DAKE YABAKI KUDIN MAGANI DUK
WATA ???
KINTABA GANIN ANSA WUQA A
WUYAN NAMIJI ANCE INBAKA FADI WACCE
KAYIWA CIKIBA SAINA YANKAKA ???
AMMA WA AKEWA HAKA ???
'Yar uwa kada dadin soyayya, ko dan kudin da
saurayi zai baki kodan zai saki a gaban mota
,kodan wasu yan riguna dazaina saya miki HAKAN
TASA KIBASHI DAMA HAR YASANKI 'YAMACE
WALLAHI KIN KADE.
IN HAKAN TAFARU TO KITUBA GA
ALLAH (S.W.T) DOMIN SHI MAI GAFARANE.
FATAN "TAFARKIN TSIRA" ANAN SHINE, ALLAH
YASHIGA TSAKANIN NAGARI DA MUGU.
ALLAH YAHADA KOWACE YA MACE DA SAURAYI
NAGARI DA ZATA KAISU
GA AURE NAGARTACCE.
MUMA MAZAN ALLAH YABAMU MATA NAGARI.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive