JININ AL'ADAH
JININ AL'ADA DA HUKUNCE-HUKUNCENSA
NA
MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO
FITOWA TA 2:
JININ HAILA DA HIKIMAR YIN SA:
Kalmar (Haid) ( ﺍﻟﺤﻴﺾ ) a larabce ta na nufin
"zubowar wani abu da kwararowarsa".
Amma a shar'ance kalmar (Haid) ta na nufin
wani jini da ya ke fita daga gaban Mace, a wani
lokaci sananne, ba don wata cuta ba.
Wannan shi ne ake nufi da jinin haila a
shar'ance. Sai dai duk da cewa jini ne da ya ke
fita ba don wata cuta ba, ko rauni, ko haihuwa
ba, amma ya na da banbamci tsakanin wata
Mace zuwa wata, kowace Mace gwargwadon
yadda Allah Ya halicce ta, ko kuma yanayin
wurin da take rayuwa.
Hikimar yin sa kuwa ita ce: Jaririn da ya ke cikin
ciki, ba zai iya cin abinci, kamar yadda wanda ya
ke wajen ciki zai ci ba, don haka sai Allah Ya sa
Mace take fitar da wannan jinin, yayin da bata
da juna biyu, idan kuwa ta yi ciki sai wannan jini
ya zama shi ne abin da Jaririn zai rika
amfanuwa da shi, ta hanyar cibiyarsa, ta inda
jinin zai shiga jijiyoyinsa ya zamar masa abinci.
Wannan ita ce hikimar samar da wannan jini,
don haka sau da yawa idan mace na da ciki, jinin
haila kan dauke mata, haka ma idan ta na
shayarwa, musamman ma farkon shayarwar.
Wata kila saboda wannan jinin ana mayar da shi
a sarrafa shi wajan samun nonon da yaron zai
sha. Wallahu a'alam.
LOKACIN FARA JININ HAILA DA ADADIN
KWANAKINSA:
A saurari fitowa ta 3 in sha Allahu Ta'ala
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.