shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 21 September 2015

RAYUWAR***NIHILA-3

rayuwan-nihila.jpg

RAYUWAR NIHILA 3

Sun koma gida beejay ta Kara tunatar da ita batun alkwarin rufe sirri
tace da ita tayi shuru tace toh.. wannan kenan! Suna waya ne da
hisham yake kara tunatar da ita irin sonta da yake nihila kin sauya
mun rayuwa kin canja ni gaba daya wasu abubuwan da nake da yanzu
kusan duk na bari tace wasu irin abubuwa yace hmm bazaki gane ba
sai a hankali nidai pls keep my love I promise I will be the best u ever
had n I will make u my wife! Ummm hisham kenan...
yana can yana tsula tsiyar shi son ranshi a kasar cyprus wanda shi a
ganin shi wayewa ne ya kawo hakan Ga neman mata ga zuwa clubs
kowace rana saiya yi attending ba'a barin shi a baya shima wai bazai
bawa shedan kunya ba... nihila tace yau kam bari ta shiga
account din hisham na insta tayi bincike tana shiga taga pictures
kusan 30 ta shiga ta fara duba comments duk wani abokin shi da taga
yayi comment shima sai ta shiga account dinsa ta duba hmmm me
zata gani saiga pictures din hisham baja Baja da emmata a clubs ya
kamo wannan ya kamo wancan ta ji kaman an caka mata wani
abu a zuciyanta.. nima daganan saida naji rasssss.. batasan sanda
hawaye ya zubo mata a idonta ba tayi munching picx din duk ta ajiye..
comments din mata kam kala kala kan pics dinshi daga wnda yake
cema sweetheart sai me my wife da dai sauransu ta ajiye wayanta ta
rasa meke mata dadi tasaka waqar bhula dena(forget me) na ashiqui ta
risgi kuka son ranta saida idonta sukayi luhu luhu har bacci ya dauketa
anan sausan tazo ta sameta ta dau wayanta ta bude kawai saitaga
picx aiko ta tura taje ta nuna ma momin su waiga samarin da nihila
take so en iska marasa tarbiyya...
Ran momin su da yayi dubu saida ya baci ta sameta a daki ta mata
tas tace tunda taki jin maganan ta bazata bada wayan ba sai taga
canji a tattare da ita.. tayi kuka sosai da taje skul take gaya ma
habibaty tayi ta bata hakuri sannan tace mata itama ta hakura da
hisham din mana tace mata inaa bazata iya ba tasan hisham yana
sonta ita kuma ta dau alkawarin she will change him for good koda
bazata aure shi ba amma bazata barshi a munanan halayen da yake ba
na sabon Ubangiji habibaty tace shikenan Allah ya baki sa'a... watan
ta kusan daya ba waya har sun gama exams dinsu sannan da kyar da
rokon beejay momi ta bata wayanta hisham kuwa hankalin shi dayayi
dubu saida ya tashi da bai saba jin wayanta a kashe ba kullun suna
waya ko chatting sai yayi tunanin kodai taji labarin halayen sa shiyasa
ta guje shi tanata jimamin abun a zuciyar shi.. kawai saiga call dinta
ya shigo ya dauka yace haba sweet ina kika shiga for weeks inata
nemanki saita mishi karya tace ai wayanta ne ya fadi saida ta siya
sabo yace kaii har kinsa naji sanyi a raina plss kina sanar
dani irin haka tace to shikenan insha Allah bazata kara ba.. yace
yauwa my nihila dats y i love u more n more each day tace I love you
most.. A zuciyanta tana mamaki halin hisham kaman bashi ta gani da
emmata ba abun ma har ta kasa yarda duk da ta gani da idonta... tace
a ranta akwai ranan tonan asirinka!
Share:

3 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive