Mace tagari
TA GARI Mace tagari; Ita ce wacce zata auri
mutum ba don wani abu da yake dashi ba, na
kudi, ko mulki, ko wata burga ta duniya masu
gushewa, a'a sai don addininsa, da amanarsa
kawai, wanda zai sa suyi rayuwa a duniya cikin
jin dadi, su mutu su samu aljannar Ubangiji
Allah, saboda sun so juna don Allah, sunyi aure
akan da'ar Allah, sannan sunyii zama irin wanda
Allah yayi umarni da ayi tsakanin ma'aurata a
musulunci. Ga wasu daga cikin siffofin mace
tagari: (1)Kiyaye lokutan Ibada koda yaushe
(2)Kiyaye sirrin Miji duka (3)Juriya da Hakuri
akan alamarin aure (4)Wanka da Ado wato
tsafta da ado (5)Gyaran Jiki (6)Kwantarwa da
miji hankali a koda yaushe(7)Kiyaye Lokutan sa
dan biya masa buqatar sar (8)Dauwama kan
neman ilimin addini bisa yardan miji (9)Gudun
Zargi (10)Taimakawa Miji akan aikin allah ba
saboba (11)Danne Fushi (12)Tarbiyantar da 'ya
'ya da sauransu Mace Tagari bata aikata
kishiyoyin abinda ambatonsu ya gabata, haka
zalika bata:_ (1)Daukaka sautinta akan na
mijinta (2)Satar kayan abinci, kudi da sauransu
(3)Saka sharadi in miji yazo zai tara da ita. Ita
ce wadda a duk lokacinda miji ya kalleta zai jii
farin ciki ya lullubeshi, so da kaunarta ya kara
karuwa a cikin masarautar zuciyarsa. Ya Allah
ka hadamu da irin wadannan matan Super fast
UC Browser, save 9
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.