shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday 24 September 2015

KALLO***DAYA-3

kallo-daya.jpg

KALLO DAYA

3


washe gari hanadi ce rikeda umma dake murkususu a tsakar daki tana kuka saboda ciwon umma daya tashi gashi yaya jafar bayanan umma tayi wani irin mika nan take ta suma a gigice hanadi ta fita da gudu tsabar rudewa ma ko dan kwali babu a kanta ballantana nikab tabi layin gidansu neman taimako, karaf taji ta bangaje wani tayi taga taga xata fadi yayi saurin rikota jikinshi a gigice tace Kati hakuri bansan da mutum ba cikin sanyin muryarta mai dadin saurare dago kanta tayi sai karaf idanuwansu suka sarke ana juna a ranshi tasbihi yayima Allah wanda ya halicce wannan kyakkawar fuska ba wani bane illa ya HYDAR kafin ya dawo daga dunyar tunani ya nemta sama da kasa ya rasa nan take xuciyarshi ta kamu da wannan yarinyar da yayima KALLO DAYA tak! A fili yace kodai aljanace sbd kyaun yarinyar gashi kuma y nemeta sama da kasa ya rasa. Cikin tsaananin sanyin jiki ya juya
A bangaren hanadi Kuma gida ta koma anan ta taradda yaya jafar da umma zaune ciwon ya lafa cikin farin ciki ta rungume umma tana hawayen farin ciki umma tace auta kuka ya kare koh tayi murmushi kawai ta tashi ta dauko nikab dintah ta daura xamanta keda wuya saiga yaya hydar yayi sallama cikin husky voice dinnan nashi a take taji gabanta ya fadi ta sunkuyar dakai kallo daya yayi mata ya dauke kansa a ranshi yanajin muguwar tsanarta tareda tunanin aljanar yarinyarda yayima kallo daya .a ranshi yace munafuka suka gaisa da umma tareda tambayarta ya jiki da amsa da kulawa daganan ya ajiye mata manyan ledodi guda biyu cikeda kayan dubiya umma tayimai godia tareda sa albarka suka fita tareda ya jafar domin xuwa masallaci kasancewar magriba ta kawo kusa itama hanadi ta mike tareda mamaki a ranta na irin tsanarda ya hydar ke mata gaisuwace kadai ke hadasu koshi ba kulllum bah tabi baki tayi a fili tace kaika sani.
09039016969
Share:

2 comments:

  1. Dan allah ka taimaka min 1da2 na daga kallo daya

    ReplyDelete
  2. dan allah ka posting 3 na kallo daya

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive