shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 9 September 2015

INSIYA 15

insiya.jpg

INSIYA 15
*********NA***********


.muhd-Abba~Gana
a firgice na tashi na ganni a wani jeji ba gida gaba ba gida baya ga shi yau kwana na biyu ban ci abinci ba balle ruwa gashi yauwa nake ji yau ni insiya na shiga uku ina zan sa kaina? sai na tashi ina cikin tafiya ban san inda zanje ba kawai tunani nayi ko zan dace in samu gida in shiga ina tafiya ina tangadi kamar wacce ta bugu da barasa abin Allah har rana ta fadi ban ga gida ba sai na zauna a wata gindin bishiya dan in saurari mutuwa ina zaune sai naga ganyen bishiyar nan suna fadowa koraye sharr da su abin sha'awa da sauri na dinga dibarsu ina ci wani daci wani dan bauri bauri haka na koshi na dinga ci har san dana koshi dan a lokacin ko kashi na gani ina iya ci ballantana ganye.
toh yau ake wata ga wata kishirwa na keji sosai dan har na fara shakuwa ku a gashi ba ruwa ballan tana in sha.ina zaune ina tunani ya zanyi ai kuwa sai wata dabara ta fado min da sauri na tashi ina dube--dube na zo bishiyar na fara dukanta,Allah ya bani sa'a na huda bishiyar sai na sa bakina wajen bishiyar inda na huda ina tsotsar ruwan kadan kadan yake fitowa gashi kuma da daci.
sai dana dan koshi sannan na cire bakina naji bakina sai daci yake waya sani ma ko maganin shawara yake kona basir? koma wannene ai bazan rasa su ba to ai shikenan tunda na sha ruwa da magani.
kuma na kara gaba to idan narafi ina zanje? ga shi magariba ta kusa duk da ba kiran sallah zan jiba ballantana agogo,kai ashe ko sallan asuba ban yi ba ballan tana su azahar bari in tashi inyi taimama tunda na koshi.sai kuma mu gode masa dan Allah shine abin godiya dan ba dan Allah ya kare ni ba ai da yanzu ina tukunya anyi karfe su dani.
kai amma da sun ji dadi, nan nayi dariya kai ni ma insiya da abin dariya nake bari ma in tashi in yi sallah nan na tashi na yi taimama sannan na kama sallar sai da na idar da sallah nan na roki Allah ya kubutar dani daga cikin wannan bala"in da wahala da na fuskan ta.
nan na yi addu'o'ina na tashi na ci gaba da tafiya ga shi duhu ya fara yi can ina kan tafiya ina kasidar yabon manzon Allah (S.A.W) ta wani mawaki da ake ce masa fadar bege, dan ina son kasidarsa ta "FARKON MAFADI" .can sai nayi sa'a na hangi hasken wata wuta haba sai na kama sanbada sauri dan na sani babu makawa akwai mutane kai sai na ga saurin da nake ma kamar bayi nake ba,haba sai muka fara suburbuda gudu tare da muhd Abba lolz!.
sai dana kusa zuwa wajan su sai na tako maciji ai kuwa yasare ni chass! a kafamuhd-Abba~Ganam

www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive