shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday, 28 September 2015

Mijina yanayin kwai.

banaio.jpg

MIJINA YANAYIN KWAI.
Ko akwai darasi acikin wannan labarin ???
Wata rana wani mutum ya auri sabuwar
amaryarsa, suna cikin fira sai dadin fira ya
kamashi.
Sai yace da wannan amaryar tasa.
Nagaya miki wani sirri nawa bazaki gayawa
kowaba ?
Sai amarya tace Eh angona.
Sai yace da ita:
Nifa inayin kwai kamar yadda kaza takeyi.
Sai amarya ta gyara zama tace da gaske kake ?
Sai yace Eh amma dan Allah kada ki gayawa
kowa.
Sai tace to.
Wata rana wata qawarta tazo wajenta suna cikin
fira sai tace da ita:
Zan gaya miki wani sirri amma dan Allah kada ki
gayawa kowa.
Sai tace to.
Sai amarya tace mata mijina yanayin kwai.
Sai tace mata ke banason karya sai tace:
Wallahi shine ya gaya mini yace kada na gayawa
kowa.
Sai tace to shikenan kada kisami damuwa.
A karshe dai wannan kawa ta gayawa kawarta
har zance yaje kunnen sarkin garin.
Sai yasa aka kirawo wannan mutumin yace masa:
Wane Labari nakeji acikin gari cewa kanayin kwai
menene gaskiyar wannan maganar ???
Sai kunya takama mutuminnan yarasa abinda
zaice.
Daga can yadago kai yakalli sarki yabashi amsa
da cewa:
Ranka yadade Matata nakeso na jarraba shiyasa
na tsokaneta da haka:
Gaskiya amana tayi karanci a wannan zamani.
Allah kabamu ikon kame bakinmu.
Share:

3 comments:

  1. Dan Allah akwai yadda zamu iya downloading novels from this blog

    ReplyDelete
  2. Dan Allah a karanta mana sireena 3

    ReplyDelete
  3. muhammad abba gana1 October 2015 at 14:19

    @hajia, akwai contact me via whatsapp zan miki explaining

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive