shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 9 September 2015

INSIYA***14

insiya.jpg

**muhd-Abba~Gana


innalullahi wa'inna ilaihi raji'un me zan gani dana tashi? ganina nayi a wani daki a kwance da sauri na tashi sai naga wasu mutane a zaune daga su sai gajeren wando kansu a aske.
yau ni insiya a wane tashin hankali na dada tsintar kaina a ciki? ina yin kuka sai jin wani mutum nayi yana yin magana akalla mutumin zai kai kimanin shekara hamsin da biyu
yarinya kina cikin masifa da tashin hankali amma ina zaton Allah zai tsare ki dan kina tsintar kanki a ciki baki ce komai ba sai neman tsari daga ubangijinmu to baba dan Allah a ina nake? yace yarinya kina gidan yan yankan kai"da sauri na tashi inalillahi wainna ilaihi rajiun yau ni na shiga uku dama zama nayi su abba suka kashe ni ai dana huta bude kofa ne ya tsayar dani daga tunanin dana ke yi wani mutum ne ya shigo bakikkirin da shi kana ganinsa kasan bashi da imani amma ni abin days bani mamaki da ganinshi kags musulmi kuma gashi yayi shigarsa ta kamala irin ta musulmi amma zuciyarsa ba imani.
maganar sa ce ta tsayar dani kai ku tashi tu tafo nai sauri nafita nice a gaba dan ni gwara su yankani na huta tunda daman yankan kai nayi na gudu kunga na yanka suma sun yankani ai shi kenan jamilu an rama masa.
wata tsawace ta razanar dani ke koma ban da ke da sauri nakoma jikina sai rawa yake naje na zauna sai kuka nake .mutanen nan su uku aka fita da su lailaha illalahu"ina ji wani mutum yana kakari kamar rago yake kakari idan an yanka shi haka mutumin nan yake yi bayan mintuna biyar zuwa goma sai naji shuru gashi saura ni kadai ce a dakin sai can naji shigowar wasu mutane su biyu wallahi sai abim yadada daure mi kai domin kamar yadda wancan mutumin yake musulmi su ma haka suke musulmai sun yi shigarsu ta kamala.

tsawa ce ta tsayar dani daga tunani da nake.haba tanimu ya zaku dinga kawo min irin wadannan mutanan masu yawaita bautar Allah? to wallahi idan dai bamu yi a hankali ba harkarmu zata iya watse wa ayi maza a fita da mai baurin naman.kwarai kuwa hakan akayi,
yace to alhaji insha Allah baza'a sake ba".

muhd-Abba~Ganawww.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive