shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 15 September 2015

MENENE HUKUNCIN YIN SAMARI GUDA UKU GA BUDURWA ?

abbagana.jpg

Salam, dan Allah malam ina neman karin bayani
akan maganar danakeji a bakin mafi yawan iyaye
suna cewa yarinya budurwa sai ta samu manema
3 kafin ta zabi guda 1.
Abisa fahimta ta malam ina ganin bai dace mace
ta tsaya jira ba har wai sai tasami samari 3 da
zarar ta samu 1 wanda aka yadda da addininsa
da halayensa kamar yadda musulunci ya tanadar
sai a tsayar da magana akansa.
Amma a wannan lokaci zakaga yarinya budurwa
suna tare da saurayi kimanin shekara 1 sannan
hakan bai hanata kula wasu ba shi zaisa a ransa
ya samu matar aure sun gama fahimtar juna
amma da zarar wani yafito sai kaga iyaye suna
cewa ai dama mace addinin yabata damar
sauraren manema 3 kafin ta tsayar da guda 1 a
ciki basa duba waccan dadewar dana bayan yayi
yana nema.
Awasu lokutan ma har manya sun san da
maganan daga both side koda dai ace ba'a kawo
kudin aure ba ko sa rana amma ni ina ganin still
haka din bai dace ba.
Dan Allah malam yaya abin yakene ???
Nagode ka huta lfy.
(Daga Amina Nana)
AMSA
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
Eh babu laifi domin mace samari da yawa sunce
suna sonta.
Amma shari'a bata bayar da dama akan ta tsaya
dasu gaba dayan suba.
Ita macen zata iya sanya wani dan uwanta yayi
mata bincike akan wanda hankalinta yafi
kwanciya dashi a cikinsu.
Addini yabayar da za6i akan cewa:
Zaka iya auren Mutun mace ko namiji domin
abubuwa kamar haka:
1. Addini.
2. Kyau.
3. Nasaba.
4. Dukiya.
5. Tarbiya.
Amma daga Qarshe sai akace yafi kyau ku aura
domin addini da tarbiyar, saboda sune kan gaba.
Bai kamataba ga iyaye su amsa maganar wani
mutum a shafe samada shekara guda yana
soyayya da 'yarsu daga baya suce zasu rabasu
batareda wani dalili mai Qarfiba, Hakan
cutarwane.
Idan basu yarda dashi ba meyasa suka amshi
batunsa tun farko ?
Sannan idan akace baza'a auri kowaba sai mai
addini to sukuma sauran mutane yaya za'ayi
dasu ???
Yakamata mudinga yin aiki da lura.
Allah ka aurar ga matasanmu ga ma'aurata
nagari.
WALLAHU A'ALAM.
Share:

4 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive