MUNGAMA SALLAH ASHE LIMAN YA MANTA BASHI DA TSARKI.
MUNGAMA SALLAH ASHE LIMAN YA MANTA
BASHI DA TSARKI.
Assalam Malam mune mukayi sallah muna
idarwa sai liman yace ya manta yayi fitsari baiyi
tsarki ba.
Shin zamu maida wata sallah ne kokuwa ta
limance kadai ta6aci, tunda mu da tsarkinmu ko
har tasama tayi daidai ???
AMSA:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To dan uwa sallar liman ta6aci, kuma dole ya
sake.
Amma ku sallarku ta inganta, a zancen mafi
yawan malamai.
Saboda dalilai kamar haka:
1. An rawaito daga Umar- Allah ya yarda da shi
cewa:
Yataba yiwa mutane limancin sallar asuba, bayan
angama sallah, sai yaga maniyyin mafarki a jikin
tufansa, sai yasake sallah, amma mamun basu
sake ba.
2. Sayyidina Aliyu yana cewa:
"Idan mai janaba yayiwa mutane limanci, zan
umarce shi yayi wanka, yasake sallah, amma
bazan ce da mamun su sake sallah ba.
3. Abdullahi dan Umar - Allah ya yarda dashi -
yata6a yiwa mutane sallar asuba, sai yatuna
bashida alwala, sai yasake amma mamu basu
sake ba.
Abin daya gabata aikin sahabbai ne, aikin sahabi
hujja ne, in ba'a samu wani sahabin yasaba masa
ba.
Domin neman Qarin bayani duba: Almugni 1\419.
Allah shine mafi sani.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.