shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 21 September 2015

RAYUWAR***NIHILA-4

rayuwan-nihila.jpg

RAYUWAR NIHILA Part 4

Sun gama exams dinsu lafiya aka fara shirye shiryen candy dinsu
murna a wurinsu ba'a magana dan a kansu ne za'a fara graduation
ceremony... ranan candy sunsha kyau ita da bestyn ta habibaty sunyi
shigen white and black Ga gown dinsu royal blue da white ya karbesu
sosai aka fara gabatarwa inda aka kira Nihila Muhammad Tahir tazo ta
bada opening speech ta fito da takunta na kasaita kaman gimbiya taje
ta bada kaman wata baturiya nan aka dau tafi raf raf raf sai shewa ake
an bada prizes da dama wanda kusan rabi ita ta dauka tayi kukan farin
ciki bayan taro sun dau pictures sosai da jawad ganin karshen zaman
su yazo yanzu sun bude wani chapter a life dinsu sunyi kukan rabuwa
da jona sabida shi zai tafi university of herriot watt a dubai ne
karatunshi.. it was a day of happiness and wonderful memories a life dinsu wasu Sun karba numban juna saboda keeping in touch...
Hisham nacan nata shirye shiryen project dinshi na kammala
university yanata Allah Allah ya dawo Nigeria Dan yazo yaga sahibar
sa Allah cikin ikonsa ya gama komai ya fito da result mai kyau ba
laifi.. ya yi visa Nigeria tayi masa kira mum dinshi tasa an
dauko shi a airport yanata kalle kalle gombe ya canja mishi sosai dan
ya kusan shekara koma fi be zo gida ba.. yana isa dakin maman shi ya
wuce tayi masa oyoyoo ya gaisheta ya zauna suna labarin yaushe
rabon duniya da ayyaraye yace ina daddy tace bayanan yaje office
saiya dawo zasu hadu.. Ya ce a siyo mishi layin mtn yana sawa ya kira
nihila taji mamaki sosai da taji yana Nigeria yace mata dama surprise
yake son mata tayi mishi sannu da hanya.. daddy shi ya dawo da
maghrib yaje ya sameshi har parlour uban ya rungumi dansa sukayi
musabaha ya gaisheshi sunata labari saiga mum dinsa tazo tace ooh yanzu alhaji da yaron nan ne ka zauna sai hira kake kaman wani sa'an
ka yace haba ke kuwa altine in banyi dashi ba dawa zanyi shi kadai fa
nakeda ai dole in soshi.. WANE NE HISHAM? Dane daya tilo ga alhaji
jameel pindiga tunda sukayi auren zumunci da altine yar wajen
ummansa ce shekaran su 5 Allah be basu rabo ba ana shida ta samu
ciki ta haifa da namiji aka sa mishi hisham daganan kuma shiru ba
aihuwa ba labarinshi.. son dau son duniya Sun daura mishi primary
kawai yayi a nigeria Amma secondary da university duk a cyprus yayi..
Hisham fari ne ba kuma fari har can ba yanada kiran maza wanda suka
amsa sunan su dan daga nesa zaka hango abs din da Allah ya masa
Ga faffadan jirgi da tsayi he's just the perfect guy da mata ke so saidai
duka wannan kyan Dan maciji ne dan kuwa zuwansa Cyprus ya lalace
da neman mata da zuwa clubs sa'a daya dai baya shaye Shaye...
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive