SAURAN BIYU
Anyi wasu barayin
lemu su biyu. wata rana sunje
kasuwa sun satolemu sai sukaje
makabarta zasu raba suna cikin
rabawa sai ga wani yazo zaisha
ganye sai yaji ana cewa kai ga
naka nima ga nawa daga jin haka
ai sai gogan naka ya ruga a guje
yaje gun liman yanazuwa yasami
yace "ga mala'iku chan a
makabarta suna rabon yan wuta
da yan aljanna". nan take sailiman
yace muje in gani. To dama
lokacin da barayin zasu shiga sun
yadda lemu guda biyu da liman
sukazo sai liman yaji ana chewa
kai ga naka nima ga nawa to lemo
ya kare saura guda biyu a waje
sai sukaji basayin nan sunce a
kwai biyu a waje kai daya ni
daya . . Ai koda gogan naka liman
yaji haka sai yafita a guje yace
wallahi sune wallahi sune
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.