shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 9 September 2015

INSIYA***17

insiya.jpg

INSIYA 17
**********NA***********


muh¤d-Abba~Gana

idan mun zauna a waje to bayan wasu yan shekaru kuma sai mu tashi mukara gaba shi yasa nake fada miki dan jauro yace na same ki na fada miki,insiya wallahi bana son rabuwa dake,dole ne ya sanya insiya kwarangwatsa nina san abin da nake ji ki daina kuka kiyi hakuri duk maganar da take min bakinta baya fitar da hausa kamar mu yadda muke fadarta dan insiya mata ke gaya min ta kara da cewa insiya kiyi hakuri nace tumba kin san dole ne inyi kuka dan ina tunanin ina zan je idan na barku insiya ni ko ina son ki bani labarin ki" nan naji wani suladarin hawaye ya keto min nan ina kuka sai na kada baki nace wa tumba ai ko wallahi tumba zan baki labarina amma ki daukar min alkawarin cewa komin daren dadewa zamu nemi juna.
insha Allahu inji tumba ta daukar min alkawari zamu nemi juna nan na zauna na ba tumba labarina tun daga farko har karshe rufe bakina keh da wuya sai na ga tumba tana fitar min da hawaye tana sharewa da bakin zaninn ta.
lallai insiya kina cikin tashin hankali to yanzu yayan babar taki yana abuja kuma kin san inda yake? a'a ni ban san a inda yake ba,amma dai dole ne in tashi in nemi shi sai dai ku tayani da addu'a.
yanzu yaushe za ku tashi? nake tambayar tumba ta shaida min sai tace da ni jibi zasu tashi na shaida mata insha Allah ni zan tafi gobe koh ina zanjeh? sallama ce ta tsayar da mu wai insiya to zo inji bako na waiga na ce masa ya shaida ma bakon gani nan zuwa nan take na nufi wajan bako.

da isata na tarar da shi a tsaye da yar sandar sa nan na tsunguna ina gaisheshi sai naga yana amawa cikin rashin walwala da naga haka sai na tambayesa dan Allah bako me akayi maka naga duk babu walwala a tare da kai, tunda nake da kai ban taba ganinka a wannan yanayia ba" yace insiya ba dole ki ganni haka ba don na tambayi baffa cewa da ke za ki tashi yace a,a bada keh za"a tashi ba wai keh gida zaki tafi shi ne abin yake damuna wallahi insiya tun jiya na kasa bacci saboda tunaninkia.insiya to yanzu idan muka rabu shi ke nan ba zamu kara haduwa ba? sai kawai naga bako yana hawaye nan na ji jikina duk yayi sanyi nace haba bako yaushe za muce mun rabu kenan? in Allah ya yarda zamu kuma haduwa,by abba gana amma ni abin da nake so da kai ka daina yawan tunani dan kar ka shiga cikin wani hali to yanzu insiya yaushe zaki tafi? nace bako zan tafi gobe in Allah ya kaimu,yace to insiya ba dan na zo na tambaye ki ba da sai dai ace kin tafi? insiya anya kuwa kina sona? nace wallahi bako nima yanzu ake fada min wai tun tuni sun kasa fada min dan haka dan Allah kayi hakuri sai kuma mun kara haduwa.nan nan naji hawaye ya cika min ido to insiya in an jima zan dawo "to a dawo lafiya nan muka rabu da shi cikin rashin jin dadi
yau ni insiya zan bar cikin jejin falgore inda nake zaune sa fulani nan na fito da kayana mutane suka hadu masu kuka suna kuka masu bankwana sunayi.


muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive