shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday 23 September 2015

RAYUWAR***NIHILA-9

rayuwan-nihila.jpg

RAYUWAR NIHILA Part 9

Nan dai suka garzaya sai asibiti doctors suka shige dashi ciki sun fito
suke cewa yayi regaining memory dinshi za'a iya ganin shi inya tashi
daga bacci suna shiga dakin ya fara motsi bude idon da zaiyi ya fara
da nihila ta matso kusa da gadon akace gatanan nan dai iyayen sa
suka yi hamdala.. ranan a gidansu nihila aka taru Dan jin bakin kowa
nan ne suke gaya ma iyayen nasu ai sune wanda suke fada musu tun
da can da suke cewa bazai yiwu ba su auri juna baban nihila yace kaji
jameelu Allah mai iko ba yanda baya abunsa ashe Dan gida nema ni
ban sani baban hisham yace ai Allah ba ta yanda baya abunsa in dai
ya rubuta zai faru magana ta kare.. HISHAM ne tambayan daddyn
yanda yasan baban nihila yace mishi tare suka tashi neighbors ne tun
suna yara kuma abokai makaranta daya sukaje tafiyan shi university ya
dawo ya samu muhammad bayanan da en gidan su wai sun kaura sun
bar garin kuma ba wanda ya barwa sallahun inda suka kaura yaji ba
dadi Dan sun saba sosai tun yarinta tare suke komai farat daya ya
neme shi ya rasa sai gashi su zasu hadasu suke neman hana alkhairi
amma da ke Allah yayi gashi sun hadu da juna.. sai musan yanda
za'ayi kan maganan yarannan a turo manya ayi magana tunda dama
suna son junansu baban nihila ya basu labarin auren da tayi hisham
har yaji wani abu ya tokare shi ya zaci an Dan dana amaryar sa
nima na Dan dara aka ce masa ai ran auren Allah ya dau ran abunsa ya
ji sa'ida a ransa
Saura sati daurin auren nihila da hisham sai shirye shirye suke kowa
ransa kal amma nihila ta dau alwashin saita yi maganin gogan ladan
karyan da ya mata yazo gida Dan tambayanta abunda take bukata taci
kwalliyan ta cikin wani lace turquoise blue mai ratsin pink Ga daurin
nan an kafa shi tasa powder kawai da lip gloss ta fito da Dan gelenta
kan ta iso ma turaren ta yayi sallama ta zauna kujera kusa da shi gogan naku fa bakin sa yaki rufuwa sai kallo yake ya saki baki
tace da dai ka kulle bakin naga kuda zai fada ya kwashe da daria yace
kaii madam bakida dama aike din kin tafi mun da hankali tace ahh
kai Dan Allah dai yace wallahi kuwa wai mene ake ta Shan kunu tace
hakan nake muradi yace umm ran gimbiya shi dade ai yanda kikeso
haka za'ayi ta Dan murmusa ta juya ido nan dai suka tattauna kan
abubuwan da zasuyi da kuma abunda zata bukata ya bata kudi ya
tafi...... ranar jumm'a daurin aure nima nace zan gayyaci su halyma
qawata da erta amna er disin sidin bayan ludayi A yau ne aka daura auren NIHILA Muhammad da HISHAM jameel bil
adama sun taru a wurin kam ba'a magana anyi reception na gani na
fada da dare kuwa dinner aka tafi tasha kyau sosai ma mutane an
hallara a wurin dinner nagano su marwanatu su phary su maryamah
sai hange suke ko zasu Ga ango da amaryanace inaaa bazan
bari a gansu ba tukunna kowa yana zaune ango ya doso hall
rike da hannun amaryarsa sun balain yin kyau sun kuma dace da juna
hisham baki har kunne sai daukan su picx ake tayi har suka zauna
anyi barnan kudi an ci ansha an hantse nima dai nace rana daya na
mai gayya ne shiyasa na dan taka rawa aka gama dinner aka
watse hisham ne ya Maida amaryarsa gida suna mota yayi parking
yace mata u look so beautiful my beloved wife kanta na kasa
tana wasa da yatsunta wani sabon kunyan shi takeji ya kama
hannayenta ya rike tayi ta sake amma ta kasa nan ta fara masa
shagwaba yayi hakuri ya barta ta shige ciki yace shi ina ruwansa shida
matar sa ina ruwan wani da kyar dai ya yarda ya barta ta fita ta shige
washe gari aka kai amarya gombawa diban fari ba'a kwan damu ba an
tashi damu mudin kenan amarya tasha kukan rabuwa da
dangin ta washe gari kowa ya koma inda ya fito daga amarya sai ango
...umm muje zuwa
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive