shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 18

.: WACE CE ITA..?? 18
Na ABBA GANA
Dama an hana mai gadi ya barta ta fita, itama
an hanata zuwa gurinsa ba gunda take zuwa
daga aiki sai aiki...
Sai yau cikin ikon Allah gata waje, Ta kalli gidan
da tafito kallon sosai, gidane na gani na fada,
kusan duk unguwar ba gidan dayakaishi tsari da
girma, tayi yan kalle kallenta, ta samu guri ta
zauna anan taga yan mata nakai da komowa ko
wacce kayan jikinta abin kallone fuska duk fenti
ta kalli yanda suke tafiya kamar basason taqa
qasa, aranta tace lallai birni birnine bata taba
ganin yan birniba saiyau. Amma ita iya sanin ta
karuwai ne basa yawo da gyale, amma taga
wayannan manya dasu amma basa saka gyale
kodai karuwanne?, haka dai aranta tayi ta saqe
saqe har guraren yamma sannan ta koma cikin
gida.!
Tana shiga taga farhaan da wata mata, aranta
tace matansa uku kenan, lallai suna qoqari,
Bata takansuba dama bayi tazo, wucesu tayi ta
fita abin ta bawanda ta ko kalla balls gaisuwa,
budurwar ta kalli farhaan waye wannan?? Yace
watace,! to WACE CE ITA?? Mai aikice, amma
batada ladabi shine kota gaida mutane, look
hafsa! ba ruwanki da masu aikiin gidan mu
please, ke kullum kikaxo sai kin kawo Qatar
masu aiki haba, Bawai komai bane illah bayason
rigimar iffaat yanxu sai ta zubar mai da
mutunci, ya qara da cewa kuma ma kurmace
bata iya magana Dan ki fita hanyarta, tace Allah
sarki,
Yaja budurwarsa ya wuce daki da ita, kwanan
hafsa biyu a gidan. ranar iffat ta dawo daga
kallon mutanen unguwa da takeyi da yake tun
lokacin ta daina mai magana tadaina yini gida
hatta aikin ta dainayi, ta fado ba sallama, sai
hafsa ta kalleta a yamutse ke Dan kina kurma
baki iya ishara da hannuba Ko uyayenki basu
koya miki gaisuwa bane? Kai Allah wadaran
halinki, ran iffaat ya baci amma guduwarta data
korota tafi mata tsayawa masifa Ta kalleta
kawai ta mata tsaki ta wuce bayi abinta, Dan
abinda takeji ya matseta!! ta qare ta fito tana
waqarta ta badi ba rai soyayyah jigon
rayuwa......., nan ma hafsa ta qara magana,
wallahi sai na sa farhaan ya koreki duk masu
aikin gidannan suna gaisheni amma bandake
Mara kunya kawai, waike kurmako?? da ganin
idonki nasan ba kurma kikeba iskancini kawai
kurmace ke waqa .dama farhaaan duk masu
aikin da yake mafi yawa yan matanshi suke sa
yana korarsu, wasu kuma baqin halinsu kesa ya
koresu, iffaat har zata tankata nan ma sai ta
mata kallon banxa tayi tsaki ta wuce abinta.
hafsa kamar an tsikareta dama idan kayi masifa
akayi banza dakai yafi haushi, ta janyo iffaat ta
wanketa da mari....
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive