shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 24

WACE CE ITA..?? 24
Na ABBA~GANA
Nan ma dariya tayi ai baka sannibane, ta fara
bashi labarin ta'addancin da takeyi a qauye, ya
jinjina mata sosai kuma ta bala'en burgeshi Dan
yanason yaga mace mai kamar maza, anan ya
gane duk abinda yan matansa suke fada akanta
gaskiya ne,
Abinda yaxo mishi gona hafsa da tayi da ruwan
zafi yace Kena da gangan kika xubawa hafsa
ruwan zafi? Ta kalleshi ta kanne mai ido ai
muguwace, kuma ita tafara xubamin ruwan kana
kallo bakace komaiba, sannan akanta kamin
mari biyu ita ma tamin daya shiyasa duk cikin
matanka nafi tsanarta, kuma da gangan na zuba
mata ruwan,? Ke yanxu data qonefa??
Aaaaaaaa miya dameni badai na rama ba!! Ya
kalleta da kyau yarinyace sosai kuma lallai
batada wayo ko kadan ga shegen surutu...
To yanxu dai ki riqa aiki da kyau zan siya miki
duk abinda kikace waccan qawar taki tana tafiya
dashi qauye idan zaki tafi gida, yatashi ya wuce
dakinsa, yabarta tanata zuba, aranshi yace lallai
da yana kula yarinyar nan da ta debe mishi
kewar qanwarshi farahnax Dan ya kula akwaita
da shegen surutu ga saurin sabo saidai sabon
baya hana tama mutum rashin kirki Dan yaji
yanda take danbe da qawarta dijeee !!!
Kamar kullum bayan fitar farhaan taje S pool tayi
wanka da yake shi yake debe mata kewar kogin
garinsu, tayi wanka abinta ta qare tabi ta lanbu
taci abinda xataci ta fita doguwar rigar da
farhaan ya bata lokacinda batada lafiya ta saka
sai ta mata kyau sosai, tana zaune tana wasa
da qasa sai ga yar baqarta tazo tayi kwalliya
baqinta sai kyalli yake tayi kyau tsab tsab da ita
da takalminta masu tsokane duniya, ba abinda
yake burgeta irin yanda take wani Dan tuntu
saman kanta ( acucu maza take nufi) yana
burgeta matuqa amma batasan yanda
zatayishiba ta qare zamanta, ta koma gida da
tunanin yanda zatayi wannan abin na saman kan
yar baqarta, tayi tunanin Idan ma gashintane
zaiyi irin na Yar baqa, tinda gashinta yanada
tsawo sosai tunda tazo gidan da kitso bata
tsefeshiba.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive