shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 31

WACE CE ITA..?? 31
Na ABBA GANA
Rayuwa tana tafiya ayanda aka sameta, Tun
bayan komawar iffat qauye takejin garin baya
mata dadi amma bata gane komaiba sai take
dauka kamar sabon da tayi da mutane birnine
suma birni sunyi kewar iffaaat sundan saba da
ganinta da tsiwarta idan sun tuna sai suyita
dariya, idan ma farahnax tana magana akan
rashin kirkin da iffaat ta mata sai su nuna mata
ai itace batada gaskiya, akan me zata
daketa,kusan duk bayan iftaar idan suka zauna
sai anyi labarin iffaat tun farahnax bataso har
abin itama ya riqa bata dariya kuma yana
burgeta, duk Wanda yaji shaqiyanchin iffaat sai
ta burgeshi, umma dai ta kula farhaan yaji dadin
zama da iffaat, ranar bayan buda baki umma
take cewa inaga bayan sallah mu tura azo
mana da iffaat, naga duk kowa yaji dadin zama
da ita, tunda yanxuma kaga bazamu komaba
kai kadai zaki tafi ka kammala karatunka , koya
kuka gani, eh umma duk sun amince,
Iffaat ma zaman qauyen baya mata dadi matuqa
kuma tanajin dadin harka da qawayenta saidai
mafi yawan lokaci takanji tayi kewar umma, duk
ta zauna takanyi labarinsu, amma bata bada
labarin farhaaah,
***********************
Yauda gobe ba wuya a gurin Allah, Ramadan ya
qare anyi sallah lafiya su iffaat yan mata sai
gantali akeyi a gari, ba mijin aure, ba
mashinshini, abin yana damun iyayensu bama
dijee ba da take yar lukuta ga manyan duwawun
da suke biye da ita, gasuda tsini idan tana tafiya
sai ta Dan duqe cox suna mata nauyi nima Jabo
Dana ganta na dauka turosu takeyi, ita rukayya
dama kamar bulala take, iffaat kuwa hips ne
kawai take dashi mazaunanta basuda tudu irin
na dijee dijee a gida tsini ake cema dijeee sabida
tsinin maxaunnan ga gafafuwan nan nata kamar
doya, qirar maxa takeda Allah ne kawai yayita
mace...
Akwai wani mai tura kura yana saida ruwa duk
qauyennan shi kadai yake saida ruwan masu
dadi, yakan sakawa ruwanshi alim idan sukayi
kyau sai ya fita saidawa yazo neman auten dijee
kuma an bashi, shima kasada yayi dan duk
qauyen nan bai samu mataba sabida tsananin
muninsa sai yazo neman Dije iyayenta suna
Neman kai da ita tuni suka sallama, rukayya
kuwa wani Dan uwanta za'a hadata dashi, su
ippatu daikam ba Kowa har yanxu.
Bayan sallah da sati biyu....
Ranar iffaat da qawayenta sunje yawo sun dawo
sukaga mota mai kyau iffaat tasa aranta kamar
tasan motar amma ta manta ina tasan motar,
tana sanye da atamfarta ta sallah da yake yanxu
gayu sukeyi an daina yawo ba takalmi duk sun
iya acuchi maxa ataqaice duk qauyen ba Wanda
yakaisu gayu da iskanci, motar ta tsaya gabansu
farhaan taga ya fito daga motar, ai da gudu taje
ta rungume shi, ba tareda damuwaba tanata
dariya, su umma suka fito ai batasan dasuba
tasaki farhaan taje gun umma ataqaice dai taji
dadin ganinsu matuqa, farhaan rungumeshin da
tayi yaji qamshin sure din daya bata yace kullum
ta riqa gogawa Rexona na aloe vera ne kuma
long lasting protection ne yace lallai yarinya ta
waye harda saka turare....
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive