shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 34

WACE CE ITA..?? 34
Na ABBA GANA

************
Tun ranarda farhaaah yabar naija gidan yake
yiwa iffaat duhu da girma tin bata baiwa abin
muhimmanci, amma tana damuwa matuqa yanxu
har taji abin yana neman ya gagareta, haka
takejin zuciyanta na wani bugawa duk lokacinda
ta tunoshi, idan aka kira sunanshi sai taji kamar
zuciyanta tafito waje, ta rasa gane yanayinda
takejin ita ba wayoba bare ta gane cewa ta
kamu.
A duniya iyayen farhaan sunada kirki kuma sun
mata halacci a rayuwarta a matsayinta na yar
aiki amma sun mayar da ita kamar yarsu An
nema mata mai lesson, haka an sakata
makaranta tana zuwa, haka tana zuwa gun
malamin hadda da farahnax suna karatu tare,
gata da saurin fahimta so gun lessen da yawa
ake mata karatun,
Duk karatunnan da take lokaci daya idan ta tuna
farhaaah sai taji ta manta komai hatta takan
manta WACE CE ITA, In short rayuwa a gidan
bata mata dadi ko kadan, umma tasha
tambayarta mi yake damunta amma saita fuske
tace ba komai idan aka matsa sai tace ta tuna
babantane!!
Sau tari zuciyanta takan mata qunci taji batason
jin komai sai taje lanbu ta haye bishiya tayi kuka
son ranta, ba Wanda yake jinta a gurin, idan ta
qare ta dawo gida idan ma idonta sun nuna
takance bacci tayi,
******
An Sami Hutun makaranta anan farahnax tasa
rigima sai an tafi Canada gun Yaya farhaaah, da
yake ita iffaat karatunta a baibai yake shi yasa
takeshan wahala a gun lesson yanxu haka ko
Hutu batada sabida anason a mata jumping to
jss3 hakan yasa karatun ya danqaremata. Sun
shirya tafiya canada Abba ya kaita gidan wani
abokinsa Ajiya har su dawo daga Canada din.
Kuma yace yarsace,
gidan sunada mutunci abinda ya bani mamaki
shine nan ne gidan su Yar baqa wato zainb
khalifa sun mutuntani coz Basusan gaskiyar
Wace ce ni ba, Dan zaman da nayi gun zainb
khalifa na koyo abubuwa ba kadan ba gata very
friendly saidai tacika rawar kai da jiji dakai sai
qaryar yaruka kala kala, gashi malama iffaat
yanxuma take koyon turanci bare wani yare,
Dan sati ukun da nayi da yake zainb akwai
surutu sai na rage jin zafinda da nakeji idan na
tuna farhaaah, Allah mai iko tanason tayi tadin
farhaan da yar baqarta idan ta tuna WACE CE
ITA sai taja bakinta ta dinke,Dan ta kula kamar
Yar baqa bunsurace Kowa so takeyi.
Satin su umma uku suka dawo, sun mini tsaraba
kamar nice yarsu, ba abin da yafi bugeni kamar
kayan da farhaan yace a kawomin, da body
spray na Rexona da sure, idan naji qamshinsu
yakansa na riqa wani tunanin da ni kaina bana
gane mi nake ciki ..
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive