shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 33

.: WACE CE ITA..?? 33
Na ABBA GANA
Iffaat an dawo birni system dinda Dana yanxu ba
daya bane cox yanzu aikinta yafi Nada sauqi
yanxu dakin farahnax take gyarawa Dana
umma...
Ranar iffaat ta qare aiki tana zaune ita kadai a
Palo umma da Abba duk sun tafi aiki farahnax ta
tafi skull taji sallamar mace ta amsa tashigo, wa
zata gani yar baqarta, wacce take kwaikwayon
gayu a gurinta, batasan lokacinda ta miqe
tsayeba ta washe mata baki ta gaisheta a
mutunce kamar ba itaba, yar baqa ta amsa tana
mamakin waye wannan mai fara'a haka, duk da
har yanxu da sauran qauyancinta batayi kama
da house girl ba, ta zauna tana tambayar
farahnax, tace ai ta tafi makaranta, amma ta
kusa dawowa, suna zaune ta kawo mata ruwa
da abin tabawa iffaat sai satar kallonta take,
aranta tace ita ba wata kyakyawa bace sai iya
gayu, Allah ya nuna mata ranarda zata zama Yar
gayu irin wannan. Tana chikin tunani saiga
farhaan ya fito, tana hangoshi sai naga ta sa
hannu a jaka ta dauko turare ta qara fesewa a
hankali ta mayar da sauri, batasan na gantaba,
ta gyara zama tana wani murmushi.
Farhaaah ya Iso,
Tana wani kashe murya, yanda tamin magana
daban yanda tamai daban wato akwai banbanci
tsakanin mace da namiji ko duk chikin
gayunne,?? Yaya farhaan kayi wuyar gani, ya
dan sosa qeya abubuwan ne sai a slow zainb, ya
kike yasu hajiya? Lfya lau tana wani maqe
murya, araina nace dama sunanta zainab dama
sai ita ance duk zainb haka suke da rawan kai
da kurin banxa.. yanda take masa duk sonda
nake mata sai naji lokaci daya na tsaneta, ta
bani haushi, narasa dalilin da yasa raina ya
baci.!! Kodai dan ta cika kurine yasa haka oho,
hira suke dashi tasaki jiki tana fari da ido tana
kashe murya tana Neman gindin zama,
Ihuuun farahnax naje zainb khalifa kece gidan
mu haka?
Kai I miss much wallahi tunda kikazo
bangankiba ina kika shigane? Wallahi karatunne
kinsan sai a hankali,! hahaha hadda Ku gifted
karatu na Baku wahala, chaiii dariss God
oooooo, farahnax akwaiki da zolaya,sukasa
dariya tajata suka wuce daki...
Bayan sun wuce farhaaah ya juyo kaina yan
mata yar gidan umma, har yanxu ba'a iya gayun
bane, na harareshi na zubar Dan duk na
tsaneshi duk haushi yake bani daya biyewa
wannan zainb din, ya min kallon banganeba
Mina miki kuma? namai kallon ya rage naka ni
tashi na wuce dakina, na barshi yana mamakin
mi ya faaru yarinya kamar hawainiya lokaci daya
sai ta sauya, bayan da safee sun gaisa koma
miye ya rage nata.
****************
Farhaaah yaune zai wuce Canada karatunsa,
ana tadin rabuwa naji yana cewa yakamata
asaka yarinyar chan makaranta, umma tace
itama tayi wannan tunani Dan ranar taga yanda
take sallah ban iya komaiba hatta alwula ma
bata iyaba Kowa ya aminta da shawarar
farhaaah na Sanya iffaat boko ..
Farhaaah dai ya baqunci Canada yabar iyayensa
da kewa.
Muje zuwa muji yanda su iffaat za'a fara karatun
boko idan ta waye ya style din zai koma.!!!
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive