Idan nasami raka'a uku a sallar azahar ya zanyi wajen rama dayar ?
Tambayata anan shine:
Misali:
Sallar azahar ina zuwa sai na tarar anyi raka'a ta daya lokacin da zasuyi zaman tahiya ni kuma ina da raka'a daya, kenan lokacin da zasuyi ta ukku ni kuma lokacin nike da raka'a ta 2 lokacin raka'a ta 4 ni kuma inada 3 to anan yaya zanyi malam ???
(Daga Musa Isah Hassan).
AMSA
-----
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
Ga yadda zakayi.
Idan kasami raka'a uku wato.
Raka'ar farko daka riska, kasamu an karanta fatiha da sura a sirrance, sannan akayi zaman tahiya, kaga su a wajensu raka'a ta biyu kenan kai kuma a wajenka raka'a ta farko.
Sannan aka tashi aka kawo Raka'o'i guda biyu ko wacce sai aka karanta fatiha a sirrance babu sura.
Sai akayi zaman tahiya, kaga kanada raka'a 3 sukuma hudu.
To sai katashi kakawo raka'a daya ka karanta fatiha da sura a 6oye.
Kaga waccen ta farkon da baka samuba, ka cikata kenan.
ALLAH SHINE MAFI SANI.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.