shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 21 July 2015

Allah kuwa matan wannan zamani kuna biyayya ga mazajenku na aure ???

bana3.jpg

DOMIN KE DA MIJINKI.
««fitowa na 3»»
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Biyayya ga miji ba mai iyawa sai mace ta tagari.
Da yawa mata suna so ace sune wadanda Annabi
(S.A.W) ya sifanta dinnan da (Nagari) saidai
biyayyar itace tayi qaranci, ko za ayi saidai a
gabansa, idan ya matsa an watsar kenan.
Wallahi na taso na taras ada iyayenmu mata
magabata suna kwatantawa.
Furaat bn Sa'ib yake cewa Umar bn Abdil'Azeez
yacewa matarsa lokacin daya ganta da wani
jauhari da ubanta yabata.
"Ki za6i Daya cikin Biyu, kodai ki mayar dashi
baitul mali ko kuwa kibani damar rabuwa dake!
"Tace"A kan mene ?
Nafi sonka sama da ninkokinsa"
Sai yasa aka mayar, yayin da yarasu dan uwanta
Yazeed yahau karaga sai yace in tana so zai
dawo mata dashi, sai tace:
"Wallahi sam!
Mijina ya hanani amfani dashi a lokacin da yana
da rai sai bayan yarasu zan dawo dashi ?
"To mace kenan tagari a gidan miji na gari.
Asma'u bnt Kharijatul Furaziy take cewa 'yarta
ranar budar kanta cewa:
"Yanzu fa kinfita daga sheqar da aka qyanqyashe
ki zuwa shimfidar da baki santa ba, da abokin
rayuwar da baki san shiba, ki zamar masa qasa
sai yazamar miki sama, kizamar masa shimfida
zai zama miki turaku, ki zamar masa baiwa, zai
zama miki bawa, kar ki nace wajen neman
abubuwa domin karya gujeki, kar kiyi nisa dashi
domin karya manta dake, idan ya matso, ki
kusance shi, idan yaja jiki, kema ki dan ja da
baya, amma ki kiyaye hancinsa da kunnensa da
idonsa, karya shinshini komai a wurinki sai
qamshi, kar yaji komai sai kyakkyawan abu, kar
yaga komai sai wanda zai burge shi.
Mace tagari takan yi qoqarin tazamar wa mijinta
aljannarsa ce, batason taga gazawarta a
idanunsa, don haka takan yi farin ciki idan taga
murmushinsa, takan damu matuqa in taga
fushinsa koda bada ita yake ba.
Bata jinkiri a wajen abinci, kuma ta iya dafawa
batare da almubazzaranci ba, itace amintacciyar
abokin shawararsa, mai iya riqe masa sirri, bata
yarda wani yasani ko waye kuwa, sannan ga
taimako.
Allah sarki!
Wani mutum yatashi tafiya hajji yana tunanin
abin da zai barwa iyalinsa, sai matar tace karya
damu ga masara can a gidan wane, buhu 12 ta
saya.
Sai yayi mamakin inda ta samo kudin, tace masa,
wanda yake bayarwa ne, in akayi aikin gida kudin
yaragu sai ta 6oye saboda tunanin gaba, yau
kusan shekara 7 kenan ko fiye, da faruwar hakan,
gashi yau sunyi mana rana.
Allah kuwa matan wannan zamani kuna biyayya
ga mazajenku na aure ?
Matsayinka na namiji idan kasami mace irin
wannan wane yanayi zaka tsinci kanka ???
Sai mun hadu a darasi mai zuwa.
Insha Allah.
Share:

1 comment:

  1. hmm gara aringa tunasarwa dn mata mafiya yawa anshagaltu da dny mungode sosai da tunasar damu dakukeyi dn sanin mhimmanci maxajen mu.

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive