shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Sunday 19 July 2015

BAYANI AKAN KISHI.

pict0182-1.jpg

DOMIN KE DA MIJINKI.
««fitowa ta 1»»BY ABBA-GANA
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Kishi wani abune mai kyau idan aka saka shi a
wurin daya dace, yakan zama mummuna idan ya
zarce yadda ake buqatarsa, kamar yadda ake
sarrafa dawa akeyin kamu da ita asha, idan aka
jiqata kwanakin suka wuce sai ta zama giya, ko
ruwan kwakwa da yake zama bammi da
sauransu.
kishin maza zaizo a wajen Miji na Qwarai bayan
nagama da Matata Gari.
Mace tagari takan nisanci mummunan kishi
domin yakan rage qaunarta a zuciyar mijin batare
da ta saniba, wata matar takan yi kishi da uwar
mijinta, wata har da 'ya'yan da ta haifama bawai
'ya'yan kishiya ko ita kanta kishiyar ba.
Irin wannan kishin yakan 6ata gidane gaba daya,
ya 6ata rayuwar aure data maigidan da 'ya'yansa
har da ita kanta matar.
A dan iya shekarun da nayi, naga matar data
kashe kanta saboda kishi, wai bazata zauna da
kishiya ba.
Naji wacce tanemi ran mijin Allah ya qwace shi.
Naga wacce tanemi sabautashi maqwabta suka
kai masa dauki.
Sannan naji wace ta zubawa kishiyar da
'ya'yanta fetur zata saka wuta Allah ya qwacesu.
Naga wace ta saka aka kori mijin daga wurin
aikinsa.
Naga wace take addu'ar Allah ya talautar da
mijin don karya iya aure.
Wata tasa an kashe kishiyar.
Wata tanemi an haukatar da ita.
Wata tanemi sakin matar.
Wata ta sayar da lahirarta gaba daya don kawai
wani dadi maras tushe a duniya.
kai ni naga wace ta saka 'ya'yan kishiyarta a
gaba, bata qaunar jin alherinsu.
Wai dacewa duk wadannan suna ganin abin da
sukeyi daidai ne.
Irin wannan yasa magabatanmu Allah yasaka
musu da alkhairi maganarsu a ranar budar kai
tafi qarfi wajen hana mummunan kishi.
Shiyasa Abdullahi bn Ja'afar (R.A) yayiwa 'yarsa
nasiha a ranar kaita daki dacewa:
"Inayi miki kashedi da kishi domin mabudin saki
ne.
Kul da yawan zargi don yakan kawo qiyayya.
Kisaba da tozali"
Kishi yakan wargaza gida ne.
Shiyasa yazama dole a wajen mace tagari ta
nesance shi.
Macen data kamu da wannan cutar ta kishi zaka
riske ta kullum a cikin tsoron cewa wata zatazo
ta qwace mata shi.
Shin me wancan take dashi da ita bata dashi ???
Me wancan takeyi da ita bata iya ba, ko kuma
bazata koya ba ???
Idan budurci ne shekara Daya tayi yawa zaku
zama uwaye.
Idanma ke kin sanshi samada ita, kin gaje gidan
da 'ya'yan farko, ashe itace zatayi kishi dake.
Meyasa kike kishi da ita ?
Haqiqa kishi ba qaunar miji bane, kawai shakka
ne da tsoro na rashin mijin.
Wato galibi mata basu da sakankancewar zuciyar
mijin a kansu, don haka zasu kadaita hankalinsa
akansu koda arziqi koda tsiya.
Matan Annabawa da sahabbai sunyi kishi, amma
nason ace mijin ya amfana dasune kawai, na
neman yardar mijin ne a lahirance, kowa tana
qaunar samun lada.
Shiyasa wata ta iya kyauta da kwananta, don ba
shine matsalarta ba, aljanna take nema tareda
manzon rahama, ko kin fahimci Hausata ???
Ku biyoni a darasi na 6.
Insha Allah.
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive